check your best novels here

Monday 20 February 2017

NO DA AMINIYATA!!!52 to 56

[21/11/2016 17:13] bilyn Abdul: 21~November~2016



NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM



52

............Babu dad'ewa uncle G! yadawo d'aukeda su aunty hafsat, cikin matuk'ar fainciki sopy ta taresu, suma dai sunyi farin cikin ganinta, musamman ma Aysha.
    Sopy tacika musu gaba da kayan abinci, aunty hafsat ta ce, "o ni, k'anwata yaya zamuyi da wannan abinci haka, saikace masu cikin zani.
   Sopy tayi dariya tana fad'in duk nakune aunty, aii d'anyar fata bata fashewa.
  Sukayi dariya suna fad'in lallaikam, yau zamuci har mu kasa tashi, fareeda ta fito tana musu sannu da zuwa, suka amsa suna binta da kallo, dan basu santaba, ta zauna tana wasada Sayeed d'an gidan Libabatu.
    Uncle G! yafito, jikinsa sanye da farar shadda tas d'inkin nasa dai bodane kamar kullum, tayi masa matuk'ar k'yau,sai tashin k'amshi yakeyi, ya d'ora hula da farin gilas siriri.
   Aysha ta ce, "yaya ina zakaje, yad'an kalli bak'in agogon dake d'aure a tsin tsiyar hannunsa, ya ce, "Aysha xanje masallacine ko.
  Ta ce, "dan ALLAH zanje.
   Ya girgiza kai yana fad'in A'a bazanje dakeba, masallacin nan bakamar na gida bane.
   Sopy tafito daga kichin hannunta d'auke da tire, ganin uncle G! ya d'au kwalliya saita tsaya tana kallonsa.
   Ya kanne mata ido d'aya, tad'anyi murmushi tana nuna masa su aunty hafsat da idanu.
   Shima murmushi yayi tareda d'aga kafad'a alamu, so what, sopy ta ce, "uncle sai ina?, ya ce, "lallai kin manta yau juma'a?, ta ce, "o, masallaci fa ko??, ya jin jina mata kai yana lumshe idanu, ta ce, "to ALLAH ya tsare.
   Yad'an yima sayeed wasa yana fad'in amin sopyna, sayeed yashiga wangale baki yana mik'a masa hannu.
   Uncle G! ya d'aukeshi yana fad'in yaro masallaci zanje, yad'an yimasa wasa sannan yamaidashi wajen fareeda ya fice yana fad'in saina dawo.
   Sukace to adawo lafiya.

Yau kam sunasha hira abinsu, sopy tasha firar gurum, sun kawo masu tsaraba irinta k'yauye, tasu data gwaggo, babama ba'a barsa abayaba.
   Sai k'arfe hud'u uncle G! yadawo, sopy ta taroshi amma bakamar yanda ta sababa, saboda yau tana jin kunyar bak'i, ya zauna yana fad'in wash ALLAH!!; na.
   Su duka suka dawo da kallonsu gareshi,  Libabatu ta ce, "yaya ka gajine.
    Ya kwantar da kansa jikin kujera yana fad'in wlhy kuwa sosaima kuwa, sopy ta kawo masa ruwa, ya tashi yakarb'a yasha yana mata murmushi.
   Yagama sha ya mik'o mata kofin, ta karb'a tana fad'in abincifa uncle?, ya ce, "zanci dan wlhy ina jin yunwa.
   Sopy ta nufi kichin tana masa dariya, ta ce, "a ajiye a dinining ko akawo nan, ya mik'e yana fad'in kawo nan, sai naci muna hira, amma bari nafara watsa ruwa tukuna.
   Ta ce, to.
 Sunan zaune suna hira yafito sanye cikin k'ananun kaya, sopy takawo masa abinci, yanaci suna hira.
    Da magriba yatafi sallah, sukuma sukayi a gida.
   Saida akayi isha'i yadawo, yadawo musu da gasashshen tsire mai dad'i, sukaci suna farin ciki.
    Uncle G! ya ce, "oh, Safiyya namanta, albishirinki?, da sauri ta ce, "goro fari tas uncle.
  Ya ce, "to saiki kawomin goron sannan, sopy ta ce, "to mikake so?, yay shiru alamar tunani, can yad'ago yana mata wani irin kallo, wanda har yabata kunya, ta duk"ar da kai k'asa.
   Uncle G! ya ce, "alawar madara nakeso, ta yi d'an murmushi, dan ta fahimci inda yadosa, ta ce, "to kad'auka ka samu.
    Babu wanda ya fahimci inda zancensu yadosa, sai fareeda Dan haka ta had'e rai, tana jin haushi, azuciyarta ta ce, "jara babbu kawai,
  Ya murmusa, ya ce, "to, Asiya ta haihu d'azu, tasamu d'a namiji.
   Sopy ta k'an k'ame Aysha tana murna, ta ce, "uncle yaushe zamu?, ya ce, "to sarkin zumud'i aii k'ya bari sai gobe ko.
  Ta ce, "ALLAH yakaimu.
  Su aunty hafsat sukace amin.

Saida sukaga kowa ya kwanta sannan suka tafi d'akinsu suma, a d'aki uncle G! ya rungume sopy yana fad'in, yaufa ranar tadaban ce, ta d'ago tana kallonsa, ta ce, "miyasa yau tazama tadaban?.
    Ya murmusa, ya ce, "kedai zoki bani alawar madara, sopy ta rufe fuska tana fad'in kai uncle ALLAH karage abinda kakeyi, agaban su aunty kake fad'ar wata alawar madara.
   Ya ce, to aii basu ganeba ko?, ta ce, "aiiko sun gane, sundai yi shirune kawai.
   Ya jawota saman k'irjinsa yana fad'in, bawani ganewa dasukayi, saidai idan fareeda dan naga tanata b'ata rai.
    Sopy ta sumbaci k'irjinsa ta ce, "banida matsala da wannan.
   Uncle G! yayi dariya, ALLAH sopy ke muguwace, nakula kwanannan kin sako fareeda a gaba fa.
    Sopy ta ce, "niban sakata gababa, nagadai kawai rainin hankalinta yafara yawane.
   Nafito ina fad'in bari nad'an lek'o su fareeda suma, d'akin na tura ahankali nashiga, suduka sunyi barci, babu wani mai kwakwkwaran motsi, da sauri nafito, nadawo d'akinsu uncle G!, amma saidai kash harsun rufe d'aki, nadawo baya da haushi, dan naso naga miye alwar madarar da sopy zata bawa uncle G!, dan nima naje nabawa nawa mijin................





Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[24/11/2016 13:52] bilyn Abdul: 24~November~2016




NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM



53

..........Su aunty hafsat suna jin dad'in zama da sopy, to itamadai sopyn gareta hakane, tanajin a zuciyarta idan da haka dukkan dangin miji suke gsky da an zauna lfy a akasar hausa.
       "" dan kiyayyar dangin miji tana tasiri wajan ruguza tubalin ginin rayuwar aure, tana haddasa gaba da kiyayya nazumincin family guda biyu, yanasa 'ya'ya da tsanar dangin mahaifinsu, adalilin k'iyaya dasuke nunawa mahaifiyarsu, to ALLAH yasa mu gyara amin.""
      Uncle G! ya umarcesu da su shirya yakaisu suyi barka suduka, amma sai fareeda ta ce, "ita bazata jeba, zata zauna agida.
    Uncle G! ya ce, "yaza'a abarki agida ke kad'ai ai zaki takura, karki damu babu abinda zai faru sai alakairi, tunda suka fad'a da bakisu sun yafe miki.
   Fareeda dai tatsaya tsayin daka akan bazata jeba, haka suka hakura suka barta.
    Uncle G! yanaso yayi barci agidan, amma saboda gudin abinda zaije yadawo saiya hakura yafita.
    Su sopy suka shirya suka tafi, bayan ummy tazo tayi musu jagora.
    Da gudu sopy tashiga gidan tana kiran aunty Asiya, taje ta mamik'e katon jaririn da aunty Asiya ta haifa, wata sabuwar kaunarsa tana ratsata, jitake kamar itama tasamu k'ani ciki d'aya.
    Ummy tak'araso da su aunty hafsat cikin d'akin, aunty asiya ta ce, "ALLAH ya shiryaki sopy, shine kikayo gaba kika bar baki abaya.
    Libabatu ta ce, "ai bakomai tana murnane, anan suka wuni, akasha fira, su aunty hauwa'u ma sunzo, da zainab da Nafisa, aiko akasha hira kamar sun saba dasu aunty hafsat.
   Muna nan zune saiga gayyar 'yan professional writer  suma sun iso, sopy tayi matuk'ar farin cikin zuwansu,  tashige cikinsu anata shan hira da tambayar ina fareeda ta ce," musu tana gida suka barota.
    Sai wajen karfe biyar muka bar gidannan, bayan munci munsha daga mai k'yau, can na hango marakisiyya da madina sunata k'atuwar lauma, nayita harararsu dan karsu bamu kunya, amma ina saida sukaji sunyi nak, harda tambayar sopy wai kozasu sami wanda zasu kaima saratu ta fatima pii, dan karsu basu labari suji haushi akan su basu ciba.
    Da haushi ya isheni saina yo waje batareda najira amsar da sopy tabasuba.

     Agajiye suka shigo gida, sun tarar da fareefa a falo tana kallo, tayi musu sannu da zuwa, suka amsa suna zama, sopy ta ce, "fareeda uncle fa??.
    Saida ta yatsine baki sannan ta ce, "bai dawoba.
   Ko babu komai sopy taji matuk'ar dad'i da faruwar haka, dan dama bataso tabar fareeda da uncle G! agida d'aya su kad'ai, dukda tayi matuk'ar yarda da uncke G! d'in, amma tana tsoron sharrin shaid'an uban had'in tuggu, dakuma fareeda uwar gidansa, uwar cin amana.
    Agurguje sopy tayi wanka, tazo ta d'ora abinci, saboda kar uncle yadawo babu abinci agidan, kan kace mi gida ya kaureda kamshi mai dad'i, Libabatu taje kichin d'in tana tsokanar sopy, wai mitake dafa misu su manyan masu gida, sopy tayi dariya tana fad'in ai kune na robar, yanzu ina had'awa na k'arfenne, suka tuntsure da dariya harda tafawa kamar k'awaye, kai jama'a wannan zama yana burgeni, dangin miji kamar danginka.
     Sai gab da magriba uncle G! yashigo, agurguje yay wanka yanufi masallaci, sai bayan isha'i yashigo, sannan suma sunyi sallah, yashigo musu da kayan marmari, sukaci abinci suka k'oshi sannan aka shiga hira mai dad'i, saida sha d'aya tayi uncle G! ya ce, "bari suje su kwanta dan gobe sunada makaranta, badan angaji da hirarba kowa yaje ya kwanta.

Da safe da wuri sopy ta tashi tahad'a karin kumallo, suka shirya sukaci itada uncle G!, suka bar musu nasu, sukai musu sallama suka tafi, suma suka bisu da addu'ar dawowa lafiya.
        A maranta sopy tana tareda Nadiya, dan yau bataga zalihaba rediyo mai jini.
   Haka suka cigaba da karb'ar lectures har zuwa karfe shidda na yamma, uncle G! ya d'akkota suka dawo gida.
     Lafiyayyen abinci suka tarar su aunty hafsat sunyi, dan haka suna yin wanka sukaci abinci bayan sunyi salloli.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, kullum sopy sukan biya suga jariri kafin su tafi makaranta, takan had'a musu abincin safe ta gyara gidan kafin su tafi, sukuma suna yin na rana, saidai sopy ta lura fareeda bata aikin komai agidan sai su aunty hafsat, itadai saidai abata taci ta kwanta tayi barci, dan haka faridar tayi wani irin k'yau tak'ara farida kiba.
     Sopy bata tab'a tanbayarta miyasa bata aikiba, dan bata bukatar hakan.
    Da haka akasha sunan d'an gidan uncle kabeer, yaci sunan baban su sopy wato ibrahim, za'a rinka cemasa khalil, anrak'ashe an kwalle, ansha shagali, fareedama taje wajen sunan, saidai tanata rab'e2 saboda tsoron 'yan uwa saita saka nik'af, ba wanda ya ganeta saisu zainab, suma sai suka shareta sukayi kamar basu ganetaba.
     Mukan baruwanmu, danta shagalinmu mukeyi, uncle G! ma sun had'ama abokansu walima dai2 karfinsu, anzo antayasu murnar samu d'a.
     Sai wajen sha biyu suka koma gida, kowa yanemi makwanci ya kwanta saboda gajiya.
   Da safe da wuri sopy takoma gidan uncle kabeer ta taya kannan aunty asiya aiki suka gyara ko'ina tsaf.

Satinsu libabu biyu sukai haramar komawa gida saboda yara dasuka baro, uncle G! ya had'a musu shatar ta arzik'i suka tafi suna kewar sopy itama tana kewarsu, har kuka tayi konace sukayi, dan har auty hafsat saida ta matse hawaye, shikansa uncle G! yaji babu dad'i, dan zuwan 'yan uwansa ya k'ara masa farin ciki, saboda k'yaunar dayake musu, fareeda kanta saida tad'an matse hawaye saboda sabo, dahaka dai suka tafi suka barmu da kewa.

Yau tsawon kwanan su aysha biyu da tafiya, gida yakoma yanda yake, yau babu aiki dan haka sopy taje ganin masu jego, tabar uncle G! yana barci ad'akinsa, fareeda kuma tana falo.
    Fitar sopy babu dad'ewa zuciya tashiga zuga fareeda bisaga gurguwar shawara, har zuwa sha biyun rana bata gama aminta da shawarar zuciyartaba, saidai zuciyar tata taci gaba da karanta mata tafsir mai wuyar fassara, ta kalli agogo karfe sha biyu da kwata, tad'an murmusa tanada tabbacin ba yanzu sopy zata dawoba, tamik'e da suri tashiga wanka, tafito ta tsara kwalliya, mudai muna lab'e muna kallon ikon ALLAH, tagama tsaf tad'akko wata yololiyar rigar barci tasa ka, ta feshe jikinta da turare, d'akin uncle G! mukaga ta nufa, kunsan ALLAH nikaina 'yar rahotonku saida numfashina yaso ya d'auke, amma haka na lallab'a nabi bayanta.
     Ta shige d'akin tana ran gwad'a, ta maida k'ofa ta datse da key, tabi uncle G! dake kwance saman lafiyayyen gadonsa da kallo, dagashi sai gajeren wando yan barcinsa hankali kwance, dan yasha maganin mura.
    Fareeda ta k'awata fuskarta da murmushi tana wani sake gyara zaman rigarta, tabbas yau saita aiwatar da abunda tadad"e tana buru, koda sopy tayi nasarar hanata auren uncle G! tofa yau saitayi nasarar had'a makwanci da ita, dan babu makawa saita saka uncle G! ya bata ruwan dazai gusar mata da k'ishir warta.
     Ta taka ahankali harzuwa jikin gadon nasa, ahankali takai hannu zata tab'ashi kamar an ce yafarka, saiya tshi afirgice, cikin tsoro da fargaba yake kallon fareeda babu abunda yake ambata sai ""inna lillahi wa'inna ilairraji'un, "" wallahu galibun ala amrihi, wad'an nan sune addu'oi  in dasuke fita daga kan lab'b'ansa, fareeda kuwa tana gabansa tana wani jujjuya jiki da salo2 na yaudara, wanda shaid'aniyar zuciyarta take koyar da'ita.
    Adai2 wannan lokacinne kuma sopy tadawo, ta tab'a k'ofar taji arufe, bataso ta tadashi dan haka taje d'akinta ta d'akko wani key d'in, bata damu da rashin ganin fareedar ba, dan atunaninta tana kichin tana girki.
    Ji sukai ana bud'e k'ofa, cikin tsananin tsoro da firgici suka maida hankalinsu awajen, sopy ta bud'e k'ofar saidai tuni zuciyarta ta yi tsawa maikama da saukar aradu, ko kwaran kwatsa, binsu take kawai da idanu, dan kallo d'aya zakai musu kaga alamun rashin gsky atareda su............................

Turkashi musu karatu, komai zai faru a wannan gida yau, lallai kila yau sai an kwatanta yak'in duniya nafarko awannan gida. Nima kaina a tsorace nake bare fareeda da uncle G!!!!!!!!!. 


Kuyi hak'uri darashin type na kwana biyu. 






Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[24/11/2016 16:33] bilyn Abdul: 24~November~2016




NI DA AMINIYATA!!!




NA BILKISA IBRAHIM



54

...........Sopy tayi wani wawan tsale ta cakumi wuyan fareeda, wata muguwar shak'a tayi mata irinta mutuwa, idanun fareeda suka fiffito, tafara kakarin fitar rai, dan numfashinta sai safa da marwa yakeyi, uncle G! sai k'ok'arin b'an b'areta yakeyi amma yakasa, yarasa wane irin k'arfine da sopy.
     Ganin idan yay sakaci zata iya halaka yarin yar mutane, saiya saka k'arfi ya finciketa daga kan fareeda.
    Fareeda tafara murza wuya dan taji shak'a, sopy tak'ara kukan kura saman fareeda, kokawa ta kaure tsaka ninsu, dukda sopyce take jibgar fareeda wannan bai hana fareeda kare kantaba, uncle G! kuwa wajen k'ok'arin rabasu aka bashi naushi a baki, dole yay baya hannunsa rik'e da baki.
    Su sopy kuwa tuni sunkai falo, duk abinda kowa yasamu makawa d'an uwansa yakeyi, dan danan suka hargitse falon, babu abinda kakeji sai ihu da ashariyar da fareeda take kutun tumawa.
     Tabas fareeda tana shan duka, dan tun tana iya karewa harta fara gazawa, uncle G! ya d'auki waya yakira uncle kabeer, ya ce, "kabeer kataimakeni wlhy za'ayi kisa agidana, ka gaggauta zuwa, nakasa tab'uka komai saboda tashin hankali.
     Cikin rud'u uncle kabeer ya ce, "lfy? ??, kai dai kazo uncle G! yafad'a tareda kashe wayar yanufo falo.
    Fareeda ta rarumi wuk'a wai zata kashe sopy, uncle G! duk yarikice sai hak'uri yake bama fareeda.
   Amma sopy ko'a jikinta dan fuskarta bata nuna alamar tsoroba, sopy tad'auki filawa ta jefama fareeda jikake dauuuuuu agoshi, dan danan goshin fareeda ya fashe jini yafara ambaliya a fuskarta, dama duk anjimata ciwo a hannuwa da jiki.
    Fareeda tayi wata k'ara mai razanar wa, amma ko ajikin sopy, taje ta tad'e fareeda ta fad'i akan tayils takara fasa kai, da alama kafarta ta karye kokuma targad'e, hakan bai ishi sopy ba, ta hau kan ruwan cikin fareeda tacigaba da ribd'a, gaba d'aya hankalin uncle G! yatashi, gashi yakasa d'aga sopy daga saman fareeda, ga fareeda tanata kakarin mutuwa, da gudu uncle kabeer yak'aso, dak'yar suka iya d'aga sopy daga saman cikin fareeda.
    Sopy saijan ajiyar zuciya take kamar zata mutu, uncle kabeer yasan sopy idan tayi zuciya zata iya aikata komai, kuma tana samun k'arfi na musamman awannan lokacin, dan haka bai zargi uncle G! da sakakin hana sopy dukan fareeda ba.
    Ta kuma yun kurowa zata damki fareeda, unlce kabeer ya ce, "youseef kariketa, dan yanzu sopy bata cikin han kalinta.
      Ruk'o sosai uncle G! yayma sopy, amma sai fige2 takeyi tana fad'in ya saketa ta kashe fareeda kowama yahuta.
    Data kasa kufcewa saita fashe da kuka mai ban tasayi, acan kuma uncle kabeer yana k'ok'arin far fad'o da fareeda dan ta suma, tad'an dad'e kafin ta kawo numfashi, dak'ar uncle kabeer ya d'agata ya d'ora saman kujera.
    Kamar daga sama sukaji ana buga k"ofa, uncle kabeer yaje ya bud'e dan yasan ko su waye.

Suduka suka shigo, uncle G! yana binsu da kallo, akwai baban farida da mamarta sai k'anin babanta sai  yayyaenta maza biyu, sai zainab, sai baban sopy da inna saikuma aunty Nafisa da aunty hauwa'u da aunty asiya matar uncle kabeer, suduka kallon falon suke, dan kuwa ya hargitsu, lallai sun tabbata ansha gumurzu agidan.
     Suka kai dubansu akan fareeda dake kwance jina jina, sai kuma sopy da uncle G! yasaketa ganin iyayenta, yazata tahak'ura tunda taga iyayensu, amma ina baisan zuciyar sopy idan tab'aci akwai matsalaba.
     Yana sakinta kan fareeda tayi, tacigaba da jibga, baban tane ya wanka mata mari, wanda yasa tashiga hankalinta, ta zube a k'asa tana gunjin kuka, dan an hanata koyama fareeda darasi, mamar fareeda tazo ta rungume sopy tana lallashi, saida kowa ya natsa, aka zazzauna falon yayi ahiru, babu abinda kakeji sai shashshekar kukan sopy, wanan kuma sunsan bazata dainaba har sai ta huce, ko kuma an tofa addu'a acikin ruwa an bata tasha sannan.
    Wani mai kyamis dake bayansu uncle kabeer yakira, yazo yay musu diresin d'in wajajen dasukaji ciwo, na sopy kad'an ne, amma fareeda abin sai wanda yagani, ma gunguna yabasu sannan ya gice.
      Palon yay tsit kamar ruwa ya cinyesu, har tsawon minti goma babu wanda ya ce, "uffan.
     Sai can k'anin baban fareeda yay gyaran murya, tareda sallama suka amsa, ya ce, "yusufa miya kawo wannan d'anyen aikin a gidanka, kuma a ina kuka samo fareedatu???.
            Uncle G! ya sassauta murya cikin ladabi, yashiga basu labari tundaga zuwan fareeda gidan har zuwa abinda ya faru yau, baba yadawo kan fareeda ya ce,  "fareeda haka akayi, ta ce, "tunda taji uncle G! bai fad'i tsiyatakun datayiba, yadawo kan sopy wadda har yanzu tana ajiyar zuciya ya ce, "ke kuma mikika sani gameda hakan safiyya??.
    Sopy saitayi shiru, kowa yasan idan tayi zuciya batason magana, dan haka uncle G! yay saurin  ce wa, "a k'yaleta kawai wanda suka fad'a shida fareeda ya isa,  Dan baya so sopy  tab'aro komai.
      Baban fareeda  ya ce, "dolene itama tayi magana dan kar a tauyeta, uncle kabeer ya mika mata kofin ruwan addu'a takarb'a tasha, bayan "yan muntuna tadawo hayyacinta.
     Ta zauna ta zayyano duk abinda ya ke fatuwa tsaka ninta da fareeda, har abinda yasa Abdul ya koma kan fareeda, dan fareedar tafad'ama sopy komai da bakinta, tafad'i zuba mata gishiri da yaji da suga cikin abinci da fareeda tayi, har saka kayan barci tazo falo ta zauna saida sopy tafad'i, tafad'i gargadin data yima fareedar dan takiyayeta, dakuma abinda yafaru a yau.
    Sopy bata rage komaiba.
  Maman fareeda ta dakawa fareeda tsawa ta ce, "koki warware tuggun dakika kulla yau kokuma na tsine miki, nakuma kasheki da hannuna, yayanta ya zazzare mata idanu ya ce, "bazaki fad'aba muna fuka annamimiya.
    Fareeda dataga babu sarki sai ALLAH saita fad'i gskyr abinda yafaru yau, takuma wanke uncle G! daga zargi, danshi yak'i fad'ar komai.
    Uncle G! yaja ajiyar zuciya danjin ALLAH mai komai mai kowa ya kub'utsr dashi.
     Maman fareeda ta fashe da kuka danjin abinda d'iyar tata ta aikata, abin kunya da kazanta.
     Dak'ar aka lallasheta, ta ce, "kuma bazasu sake zama da fareedaba, saidai tanemi wasu iyayen badai suba.
     Nakula yau fareeda tayi nadama ta gsky, dan kallo d'aya zakai mata ka sheda hakan, kuka tashiga rerawa tana basu hakuri, da fadin tayi nadama walhy tayi nadamar aikata duk abinda yafaru abaya da yanzu, takumayi alkawarin canja halayenta.
    Baban ya daka mata tsawa ya ce, "makaryaciyar banza da wofi, ba haka kika cema su yufan ba yayinda ya tsuntoki, kekam inaga wutar ALLAH ce kawai zata sakaki nadama.
     Da sauri baban sopy ya karb'e da fad'in A'a bama fata, kuma ni na yarda da tubanta, dan haka zata koma gidana da zama, kafin ALLAH yabata miji tayi aure, sai dai ina nemar mata gafara daga gareku,, kuyi hakuri ku yafe mata, bakinku kawai zai iya hana dawwamar tubanta, zai kara jefata wajen aikata wani kuskuren, ku yafe mata dan ALLAH.
    da k'yar uncle G! da uncle kabeer da inna  suka saka baki, iyayen fareeda suka yafe mata, aka dawo kan 'yan uwa suma ansha fama kafin su yafe, sopy kuwa duk'ar dakai tayi dan baxata iya yafe waba, sunsan halinta sarai yanzu tana kan dokin zuciya, dan haka uncle kabeer ya ce, "su barta sai nan gaba, idan ta huce, dan ba'a tursasa mutum ya yafe zalincin da'akai masa.
    Haka aka hak'ura aka bar sopy, suka tusa k'eyar fareeda suka tafi, akabarsu aunty zainab suna gyara gidan sopy, dan yayi kaca2 kamar filin sukuwa.
    Gyara sosai sukai mata aka maida komai mazauninsa, wadanda suka fashe aka zubar, sai bayan isha'i suka tafi, bayan sun yimusu girki sunsaka sopy ta gasa jikinta da ruwa mai zafi, saboda tsamin jiki.

Suka tafi gidan shiru, dan uncle G! yana masallaci, tazuba abinci taci batareda tajirashiba, ta sha magani tashige d'akinta ta kwanta.
     Uncle G! ya dawo yaga bata falo saiya lek'a d'akinta, tana kwance akan gado amma da alama idanunta biyu, dan yaga tana karkad'a k'afafuwa, alamar har yanzu asama take, dazata samu wani dasaita ruburbud'a, kamar yanda ta suburbud'i fareeda.
     Uncle G! yashigo jiki asanyaye, yak'araso kusa da gadon ya tsura mata idanu, kallo d'aya tayi masa ta kauda kai gefe, yad'an murmusa,  ya zauna kusada ita, yakamo hannunta dake saman ruwan cikinta, yad'an matsasu, tayi burus dashi, ya matso ya juyo da fuskarta gefen dayake, saita runtse idanu.
    Ahankali ya furta wai laifin mi nayi sopyna, idan nayi laifine sai asanar dani, wasu zafafan hawaye suka shiga zubowa daga kumatun sopy.
     Uncle G! ya jin jina kai, lallai ya yarda da batun uncle kabeer dayace fushin sopy bala'ine, shikam ya shaida yau,  yasa hannu yana share mata hawaye, ya dawo da kanta saman cin yarsa yana cigaba da lallashi, amma tak'i saurarensa.
    Dole yahakura yaje yaci abinci yay wanka, yayo shirin barci yazo yakwanta kusada ita, yay musu addua dan ita harma tayi barci.
     Shiko saiya kasa barcin dan abubuwan dasuka faru d'azune suka shiga dawo masa, gani yake kamar alabarin littafi ko film, ya dad'e bai barciba, saidaga baya ya saceshi shima. .............





Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[25/11/2016 14:31] bilyn Abdul: 25~November~2016




NI DA AMINIYATA!!! 





NA BILKISA IBRAHIM




55

...............Tsawon kwana uku kenan amma Sopy tak'i sakin jikinta, kwatata ta daina fara'a, bata shiga d'akin uncle G!, dan idan ta tuno da yanda tasamesu ad'akin shida fareeda sai taji hawaye na kwaranya a idaniyarta, lallai tana ji aranta da uncle G! da fareeda sunyi tarayya tofa da har abada ta barmata uncle G!.
     Gaba d'aya uncle G! yarasa kanta, tun yana lallashi har yabari dan yafara jin haushinta shima, yayi fushinsa na kwana d'aya ya sakko dan dole yakoma lallashinta.
     Yauma tana zaune afalo ita kad'ai ta kurama tv ido,saidai azahiri ba kallon takeyiba tana duniyar tunanine, uncle G! yashigo hannunsa nik'i2 da kaya, kwata2 sopy batasan ya shigoba, dan tunaninta baya tareda duniyarta.
   Ya dire kayan a tsakkiyar falon, ya nufo gareta, ahankali ya zauna kusada ita, yajawota zuwa jikinsa, tai figigit alamar dawowa, cikin d'an rikicewa ta ce, "sannu dazuwa, ALLAH bansan ka dawoba.
    Uncle G! yay d'an murmushi tareda shafa gashinta ya ce, "yaza'ayi kisan nashigo bayan kina duniyar tunani, ya kuma mayseta ajikinsa yana fad'in sopyna plz yakamata komai ya wuce, ki d'ebi abinda yafaru ki watsashi baya, muci haba da gina sabuwar rayuwa, ki d'auki hakan a matsayin k'addararki ta rayuwa.
    Sopy ta zubo da hawaye tak'ara kwanciya luf ajinkin uncle G!, shikuma yana shafata kamar mage, ta ce, "nakan dad'e ban damu da abuba koda yafaru a garenine, amma daga lokacin da'aka kaini mak'ura nakan shiga rud'ani da gushewar farin ciki, tad'ago tana kallon fuskar sa, ta ce, "uncle!! plz ka kaini wajen dazanyi kamar sati biyu, wannan ce kad'ai mafitar dazata mantar dani, rud'anin danake ciki a yanzu.
    Uncle G! yay murmushi ya ce, "indai hakan zai sakaki farin ciki tofa zan miki, dama na shirya mana tafiya Gurum tunda makarantarmu mun shiga yajin aiki,  tad'ago da sauri tana kallonsa tai saurin fad'in dgsk??.
   Ya jin jina kai alamar eh.
  Ta ce, "amma baka fad'a mini ba.
  Yashafa kanta ya ce, "naga kina cikin rud'anine", yad'ora da fad'in idan kuma bak'ya son Gurum toki fad'i inda kike so sai muje, domin samun farincikin ki.
    ta murmusa tareda murza tafin hannunsa, tad'ago tana kallon k'yak'yk'yawar fuskarsa ta ce, "aii nafison Gurum fiye da ko ina.
     Shima murmusawa yayi ya ce, "ngd da k'aunar dakikema garina.
   Tad'an harareshi oh, garinka mane kai kad'ai?.
   Yay 'yar dariya ya ce, "sorry garinmu.
    Yaudai babu laifi sund'anyi hira, har aka ci soyayya a wajen barci.
   Na girgiza kai ina fad'in mata da miji sai ALLAH.

 Bayan kwana biyu suka shirya, zuwa Gurum, babu yanda baiyi da'itaba akan suje su gaida su inna ba, amma ta ce, "bazata jeba, har k'ararta yakai wajen uncle kabeer.
    Uncle kabeer ya ce, "ya k'yaleta, yasan saboda fareeda ta ce, "baza tajeba", kuma hakan yayi, inko taje tofa sabon fad'a zai tashine.
    Uncle G ya ce, "haba aii ta hak'ura, uncle Kabeer yay dariya ya ce, "lallai nakula har yanzu bakasan halin sopy ba, ta hakura ne dan bata ganinta, amma sopy tafi kurma naci awajen fad'a.
   Uncle G! yay dariya yana f'ad'in ga k'arfin tsiya, dariya sukayi suduka suka kashe wayar uncle kabeer yana fad'in nidai babu ruwana, kunfi kusa,  .

   Yaukam tunda safe Gurum tai d'iba, shabiyu a Gurum tayi musu, su gwaggo sunyi farin cikin ganinsu, anmusu tarba mai k'yau, abinci har sopy ta rasa wanda zata ci.
    Aysha ta gyara musu b'an garensu.
    Da yamma baba yadawo daga gona shima yayi matuk'ar farin cikin ganinsu, yay musu godiyar hidimar dasuka sha da su Libabatu, yasa musu albarka sosai, itadai sopy saijin kunya takeyi.
     To haka rayuwa tacigaba da tafiya mai tarin farinciki, dan Gurum tayi musu dad'i, gashi kullum sai aysha ta raka sopy gidajen 'yan uwa da abokan arzik'i, tun uncle G! yana nuna baya so har ya hak'ura.
     Yau kwanansu hud'u da zuwa, sopy ta yashi da matsanancin zazzab'i, tun dare take zuba amai, har zuwa safiya, duk jikinta yasaki, saida safe uncle G! ya sanar da su gwaggo.
     Cikin hanzari gwaggo tazo b'an garensu, ta iske sopy tanata shek'a amai, ta kalli uncle G! ta ce, "yusufa yakamata kakira mas'ud abokinka yazo ya dubata ko?.
     Uncle G! ya ce, "to gwaggo, bari naje naga idan yana nan, gwaggo ta ce, "to ALLAH yasa adace.
   Ya fice yana fad'in amin, babu dad'ewa suka dawo tareda mas'ud shima d'an Gurum ne, tare sukai piramary da secondary, ya duba sopy sosai, saiya saka mata k'arin ruwa yatafi dan ya bincika abinda ke damunta.
     Karin ruwan da aka saka mata yasatayi barci, gwaggo da uncle G! zaune sun saka sopy Gaba sun zabga tagumi, baba kuma yana daga k'ofar d'aki zaune akan dankari, shimadai yayi shirun, aysha kuwa ta garzaya domin sanar da su aunty hafsat halin da'ake ciki.
    Sai wajen karfe d'aya mas'ud yadawo, sannan su gwaggo sun fito, ya mik'ama uncle G! hannu yana murmushi.
    Jiki a sanyaye uncle G! yabashi sukayi musabaha, mas'ud ya ce, "my Brother congratulation on your success!".
    Cikin rashin fahimta uncle G! yake kallonsa, ya daure ya ce, "d'an uwa ni wane arzik'i nasamu da har zaka tayani murna.
   Mas'ud yay murmushi ya ce, "kasamu babban arzik'i wanda wasu da yawa suke nema, harma dani aciki,kasamu k'yauta wadda ALLAH kad'aine yake badawa,kasamu arzik'i mai tarin ni'ima, na samun d'a daga matarka Safiyya!.
    Cikin matuk'ar farin ciki ya rungume mas'ud, yana fad'in "Alhmdllhi ALA kulli halin", lallai nayi maraba da samun wannan d'ingimemiyar k'yauta, ina kuma godiya ga sarkin sarakuna, mai so dak'aunar bayinsa.
   Uncle G! Yadawo da kallonsa ga sopy yana murmushi, lallai ALLAH yasoshi daba'a zubarmasa da d'a ba  wajen dambe.
   Sun dad'e suna murna kafin gwaggo ta shigo, itama mas'ud ya fad'a mata, dan uncle G! yakasa saboda kunya.
    Dan danan gida ya kaure da murna, harsu aunty hafsat ma sunzo tun d'azu, kowa farin ciki yake zasuga d'an uncle G! Aduniya, gwaggo da baba jisuke kamar yau suka fara samun jika, bare kuma uban ginsami uncle G!, aii jiyake yafi kowa sa'a a wannan rana.
    ""wannan na sopy ne da uncle G!!!!"".......................






Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[26/11/2016 18:05] bilyn Abdul: 26~November~2016





NI DA AMINIYATA!!!




NA BILKISA IBRAHIM




56

.............Sopy bata farkaba sai la'asar bayan ruwan da'aka saka mata ya k'are, uncle G! ya taimaka mata tayi wanka dan taji k'arfin jikinta.
     Su aunty hafsat suka shigo suna mata sannu, gwaggo takawo mata Abinci da Awara da fura wadda tasha nono mai k"yau.
     Aunty hafsat ta ce, "k'anwata azuba miki abincin ko? kici.
   Sopy tad'an yatsine fuska ta ce, "aunty nak'oshi, uncle G! ya harareta ya ce, "mikike nufi da kin k'oshi, haka kikeso ki zauna da yunwa?, tun jiyafa rabonki da cin abinci.
    Gwaggo ta ce, "A'a yusufa abita ahankali, gwaggo ta matso kusada ita, ta ce, "d'iyata daure kici koda awararce, ko fura, fad'a min wanne kikeso, inkuma bak'ya sonsu a sake miki wasu.
     Sopy ta ce, A'a Gwaggo zanci awarar, to shikenan gwaggo ta fad'a, Libabatu ta zuba mata awarar ta mik'a ma uncle G! dake kusada ita.
    Ya d'auka yakai bakin sopy, sopy tayi k'asa da kai dan kunya, ahankali ta furta uncle kabarsa zan iya ci dakaina.
     Ya ce, "karb'a kici kinga hannunki akwai datti gashi kuma jikinki babu k'arfi.
     Gwaggo dake jinsu ta ce, "in bata son naka, bari ni nabata, da sauri sopy ta bud'e baki uncke G! ya saka mata awarar.
     Abun yabasu dariya, dan haka suka tuntsure da dariya suduka d'akin, aunty hafsat ta ce, "k'anwata kunyarki tayi yawa.
     Gwaggo ta ce, "aii haka akeson mace takasance mai kunya, Dan kunya adon mace .
   Sopy tad'anci Awarar, dan tayi mata dad'i sosai, bayan tagama ta k'ara kwanciya, uncke G! ya ce, "tashi kid'an zauna ki huta, kar kwanciyar tayi yawa.
     Gwaggo ta ce, "A'a kabarta ta kwanta, k'ila tafi jin dad'in kwan ciyar.
    Ya ce, "to.

Sai dare su aunty hafsat suka tafi.
    Baba ya sissiyoma sopy abubuwan kwad'ayi ya ce, "abata taci, bayan yai mata sannu suka tafi b'an garensu.
    Uncle G! ya kalleta yana murmushi, ya ce, "lallai ke 'yar gata ce, kowa jiyake dake, tayi murmushi tana fad'in kokana kishine?.
     Ya murmusa tareda d'ora hannunsa akan cikinta, ya ce, "bawani kishi, kema aii gamasu kwace miki fada nan sun kusa zuwa.
    Cikin rashin fahimta sopy ta ke kallonsa, ta daure ta ce, "ban gane abinda kake nufiba??, ya kanne mata ido d'aya ya ce, "zaki gane, alokacin da yarona ko yarinya suka fara aikin 'yan kwallo acikinki.
    Sopy ta zaro idanu waje ta ce, "kamar ya ya?, ya kwanto da kanta bisa cinyarsa, yad'ora hannunsa saman cikinta, d'ayan hannunsa yana shafa gashin kanta, ya ce, "Inada babbar ajiya awannan cikin, ma'ana saka makon ciyonki na bayyanar yarona ne.
     Sopy tasaka hannu ta rufe fuska dan tagane miyake nufi, yay 'yar dariya, lallai yarinya kardai kice yarona d'an farin k'auye za'a maidashi?, to wlhy ban yardaba, garama tun yanzu na fad'a miki, dan banyarda a b'oyema yarinyata ko yarona suna ba, banyarda atureshi saboda yazo a matsayin d'an fariba, yasa hannu ya cire hannunta data rufe fuska dashi.
      Saita rintse idanuwa, yakai bakinsa kan nata, yafara al'amura.
   Na ce, "hummmm shidai uncle G! baya gajiya dayin kiss, bare kwana biyu ba'a had'uba.

Haka al'amura suka cigaba da tafiya a gurum, sopy tana shan tarairaya, duk abinda ta ce, "tana so sai an nemamata, koda awajen gurum yake kuwa, gwaggo ta hanata aikin komai, d'akinsuma Aysha ce take gyarawa kullum, a b'an garen uncle G! kuwa abin ba'a magana, suma su lubabatu suna bada gudummawa, dahaka sati biyun dasuka d'ebo tacika.
      Amma baba da gwaggo sun hana tafiya, sunce tunda ba'a koma makarantar ba to bazasu tafiba sai sopy ta k'ara samun sauk'i, badan uncle G! yasoba dole ya hak'ura.
     Shikam yana so su tafine dan yana cikin takura, gashi kuma wata sa'inma sopy a d'akin gwaggo take kwana idan jikin yay tsanani, itama kanta sopyn ya lura yanzu gudunshi takeyi.
    Itako sopy bataso uncle G! yazo mata da buk'ata ne, shiyyasa take baya2 dashi, dan bata so yacika takura mata.
    Kunsan wani cikin yana faruwa haka.

In tak'aice mu dai saida sukayi wata d'aya dawasu kwanaki, dan saida aka sanar an koma yajin aiki sannan baba yabarsu suka dawo kano.
     Sun dawo cike da kewar muta nen gurum, yayinda suma suka barosu da kewarsu.
     Tsaf suka tarar da gidansu an gyara, wananan duk aikin aunty Asiyane, sunji dad'i sosai, suna zuwa sai wanka da cin abincin da aunty asiyar ta aiko musu.
    Bayan sun gana suka kwanta dan su huta.

A b'an garen fareeda kuwa al'amira sai ahan kali, dan ba komai take nema ta samuba, sauk'in tama tana agidan su sopyne, amma tayi bak'i ta rame kamar ba'itaba,  kullum sai inna ta ce, "taje ta gaidasu mama.
    Badan tasoba take zuwa, dan idan taje gidan sai mama ta had'e mata rai, daga ita har baba basa sakar mata fuska, lamuran suna damunta, amma tasan laifintane.
    Yau ma tana zaune ad'akin sopy nada, ta had'a kai da guywa, hawaye suna kwaranya a idanunta, tana tuna rayuwa irin ta gidan sopy, duk da uncle G! bamai kud'i bane, amma yana k'ok'ari akan iyalinsa, yana wadatasu da cima mai dad'i, amma nan daga tuwo sai shinkafa, tarik'e kai tana hawaye.
    Araina ne ce, "su fareeda anji jiki, an shiryu badan ALLAH ba.....................





Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *