check your best novels here

Wednesday 1 March 2017

NAWAFF! !! 39/42

[26/02 15:13] Abba Gana: ☆☆☆☆☆☆☆
 NAWAFF 
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞





Page39 & 40


....da 'kyar ta tashi tai sallah da asuba, ta kuma komawa barci, sai 'karfe goma ta tashi na safe, shima saida momcy ta tada ita, ta tashi tayi wanka tayi shirinta cikin doguwa riga ba'ka, ta naďe kanta da farin gyale, tayi 'kyau sosai, ko abincin da'aka kawo mata bata tsaya ciba tafito dan su momcy suna jiranta.
   Ta tsugunna har 'kasa ta gaishesu, cikin fara'a suka amsa, har papa na tsokanarta da faďin, gara muje da wuri kafin mijinki yafa kiran wayoyinmu, yasmeen tayi ďan murmushi cikin jin kunya.
   Momcy takama hannunta ta mi'kar da ita.
   Ahmad ne yazo ya ďaukesu, momcy da papa suna baya yasmeen kuma agaba kusada Ahmad.
    Asibitin cike yake da 'yan kwallo, Ahmad ya ce, "sunzo duba marasa lafiyane, su papa suka nemi guri suka zauna,  Ahmad ya ce, "yasmeen mushiga ke saiki gaisa da abokanmu, suma suga matar modebbo ko??, momcy ta ce, "eh yakamata hakan, tashi kuje yasmeen.
   Yasmeen tami'ke tana faďin to momy,   Ahmad da yasmeen suka nufi ďakin da Nawaf yake kwance, cike yake da abokansu, wasu azaune wasu atsaye, yasmeen tayi tsaye takasa shiga saboda kunya, Ahmad ya ce, "shigo mana.
    Yasmeen tashigo kanta a'kasa, sukam sai kallonta sukeyi, yau dai Nawaf azaune yake, yajingina da filo a bayansa, kuma kumburin 'kafar da sau'ki, ya mi'kama yasmeen hannu alamar wai tazo, ta no'ke kafaďa, alamar A'a.
   Yay murmushi yana faďin to zoki zauna nan, dan kinga nan duk abokainane, karsu ďauka 'kanwatace ba matataba.
    Yasmeen ta'karasa ta zauna kusada 'kafafunsa, yakamo hannunta ya rumtse anasa, sannan ya maida kansa ga abokan nasa dasuketa kallon yasmeen, ya ce, "friend ga matana, sunanta fateema xarah.
   Cikin harshen turanci yake maganar, sukace wow!! Beautiful Sannu dazuwa.
   Itama cikin harshen turancin ta gaidasu, suka shiga mi'ka mata hannu wai su gaisa, Nawaf ya girgiza kai tareda sake ru'ko đanyan hannun nata, ya ce, "koda wasa karma ki fara, amma da hausa yafaďa.
   Wani bature acikinsu ya ce, modebbo miyasa zaka hanata, aii gaisuwa zamuyi ko??, ya girgiza kai yana faďin no ita bata gaisuwa da maza, saidai zaku iya gaisawa da baki.
    Sai koďata sukeyi, wani harda faďin wai zaizo 9ja abashi mata.
   Na ce, "aiko yazo yaza6a a group ďina duk wadda tayi masa nabasa, kai ni harma na za6ar masa, ku kawo kunnanku nagaya muku,, nabashi kai............baridai nayi shiru, kar wasu suce ban za6esuba.
     Bayan sun gama gaisawa suka fice, har yanzu Nawaf yana ri'ke da hannun yasmeen yana murzawa ahankali, ta ce, "plz ka sakeni su momcy suna zuwafa, yaja numfashi, to sarkin tsoro, kedai ba'a ta6a jikinki ko?, kodayake ba'kya bu'katar hakanne?,  tazare hannunta ďaya daga nasa tana ta6e baki.
   Ahankali ya ce, "kina nandai baki canjaba ko?, ta ce, "kaima ai baka canjaba,.
   Ya ce, "ko??, taďan murguďa baki, tana faďin kaima kasani aii.
     Ya ce, "nasan mi??
      Ta gyara zamanta tana faďin kasan baka canjaba ďinba.
   Fatar hannunta yakama yamirďe.
   Tari'ke hannunsa kam, wayyo ALLAH da zafi fa??.
    Yay 'yar dariya aii dama dankiji zafin nayi, yafaďa ahankali.
    Ta ce, " mutum yana hannun ALLAH amma bai daina muguntaba, wawura yakaimata tai saurin kaucewa ta ce, "aikuma kayi na 'karshe malam.  
   Momcy da papa suka shigo, yasmeen ta fisge hannunta tana gyara zama, su momcy suka zauna suna mai yaba yanda jikin Nawaf yay 'kyau.
   Papa ya ce, "masha ALLAHU lallai jiki yayi 'kyau modebbo, yau harda zama.
   Nawaf ya ce, wlhy kuwa papa harma ji nake zan iya taka 'kafar, papa yay dariya, A'a modebbo wannan da sauran lokaci aii.
     Alhmdllh momcy tafaďa, aii haka muke fata muma muga ka taka, dama su Anwar sun damemu dakira, wai ykk??,
    Ayya 'yan 'kannina nayi missing nasu nima, su kwantar da hankalinsu, ina samun sau'ki, bari Ahmad yazo ya kwaso mini wayoyina, nasan mutane sunata nemana.
    Papa ya ce, "yakamata ka kunna kuwa, kodan gaisawa da 'yan uwa da abokan arxi'ki, dukda muma sunata kiranmu, kaga kuma bakoda yaushe muke tare da kaiba, indan kuwa ka kunna kowa zai dunga samunka, aduk lokacin daya kira.
    Nawaf ya ce, "to papa bari muga yazo saiya ďakkomin.
    Nan dai sukaita 'yar hirarsu, suna yaba 'ko'karin Ahmad.      Nawaf ya shagwa6e fuska wai yunwa yakeji, momcy tayi dariya itada papa, kai modebbo shagwa6a kuma??, kafa girma abbunmu.
   Nawaf yay ďan murmushi yana faďin papa aini idan ina gabanku jina nake yaro 'karami wlhy.
   Nanma dariya sukayi, momcy ta ce, "to matarka tabaka abincin ko?, yasmeen tai saurin kallon Nawaf saiya ďaga mata gira, ita kuma ta murguďa masa baki, ya nuna kansa alamar wai shi.
   Su momcy suna kallonsu, yasmeen ta haďa abinci ta matso kusada shi tana wani zuzzun6ura baki.
   Ta ďiba a cokali ta mi'ka masa, saida ya harareta sannan ya kar6a, yaďan kalli gefen dasu momcy suke yaga hankalinsu baya kansu, suma hirarsu sukeyi, yay 'kasa da murya yanda bazasujiba ya ce, "ki ajiye rashin kunuarki yarinya, dan wannan karan inada hanyoyin maganinki dayawa.
    Yasmeen ta ta6e baki ta ce, "aii nasaba jin wanan, hannunta yakamo ya sumbata, saida taďan girgiza dan sumbar tashigeta, Nawaf yay saurin ri'ke filet ďin dake hannunta ya ce, " 'yammata harda wannan??.
    Yasmeen tai 'kasa da idanu dan yauce rana tafarko dataji tana jin kunyar Nawaf,, cikin shagwa6a ya ce, " momcy kinga ta daina bani abincin ko??.
   Yasmeen tazaro ido itama cikin tata shagwa6ar ta ce, "mom ALLAH ina bashi shine baya ci, dama babu wata yunwa dayakeji, su  momcy dariyama suka basu, dan haka suduka sukayi murmushi, papa ya ce, "to yanzu mu yazamu gane mai gsky??.
    Nawaf ya harareta ALLAH papa nine mai gsky, yasmeen ta ce, "bawani nice mai gsky, Nawaf ya ce, "to nidai yunwa nakeji dan haka kibani abinci, filet ďin hannunsa ta kar6a tana hararar sa, yasaki murmushin mugunta.
    Haka Nawaf yacigaba da jinyar jikinsa, Alhmdllh kuma jikin yana 'kyau, saidai tundaga ranar yasmeen take baya2 dashi, dan takula yana neman yarin'ka bata kunya agaban su papa.
    Amma soyayyarsa kullum 'kara ruruwa take azuciyarta, to shima dai hakane jiyake kamar ya haďiye matar tasa, amma jin kai yahashi faďa mata yana sonta, dan haka kullum take ganin kamar tana dakon son wanda baya sontane.
    Shima Nawaf yanama soyayyar dayakema yasmeen kallon son maso wani, danshi atunaninsa har yanzu yasmeen tana son tsohon mijintane, baisan bata ta6a son faisalba ko a bayaba, bare yanzu.
      
   A yaune su mas'ud suka iso shida Anwar da Abdallah, Nawaf yayi matu'kar farin cikin zuwansu, haka suma sunyi farincikin ganin yafara samun lafiya, dan zamu iya cewa saura kaďan, yausu anan suka wuni yasmeen ma no'kewa tayi ta'ki zuwa wai kanta yana ciwo.
    Suma a hotel ďin dasu yasmeen suke anan aka musu masuki, da daddare suka haďu akasha hirar 9ja, saidai papa ya ce, "kowa yaje yakwanta sanan.
   Nawaf yakira Anwar ya ce, "yakaima yasmeen wayar, tana 'ko'karin kwanciya taji an buga 'kofar, saida ta le'ka taga Anwarne sanan ta buďe, Anwar lafiya dai ko??, ya mi'ka mata wayar yana faďin yayane ya ce, "nakawo miki wayar, yana bata yajuya yana faďin mu kwana lafiya.
    Ta maida 'kofar asanyaye tarufe ta ce, "to ALLAH yakaimu, saman gado tafaďa ta kwanta, tayi addu'ar barci dan Nawaf bai kiraba ita kuma wlhy bazata kirashiba.
   Ta kammala addau'ar ta lumshe idanu amma badan barciba, dan tana bu'katar jin muryar Nawaf, kamar daga sama wayar tafara 'kara alamar kira, tayi Burus da wayar harta tsinke, yasake kira, saida yakira sau uku, nanma ta'ki ďauka, sai ana huďu ta ďauka zuwa sanan Nawaf yacika fam da haushi.
    Ta ďauka kuma tayi shiru, shima shiru yayi sai huci yake kamar yana gabanta, cikin masifa ya ce, "waike wace irin "'yar rainin wayoce, dan wula 'kanci tunďazu nake kiran wayarnan kika 'ki ďauka kuma nasan kina kallonta.
     Yasmeen ta ta ta6e baki, tayi shiru kuma, wannan yasa Nawaf 'kara hawa sama, yacigaba da masifa, "k wlhy kishiga hankalinki dani, karkiga ina kwance a gadon asibiti kice zaki raina mini wayo, kinsanni kinsan halina, kodan kinga ina kulaki shine zaki min hauka, daga yanzu idan kinga na sake shiga harkarki kiyimini abinda kika ga dama, tsowww yaja tsaki tareda yanke wayar.
    Yasmeen ta dafe kai tana hawaye, wai ita miyasama ta 6atama Nawaf rai, miyasa bata ďagaba tun akiran farko, gashinan wajen jan aji ta 6ata komai, itada take fata tajawo hankalinsa gareta, gashi nan ta na 'ko'karin nisantasu da juna, sai kawai tahau kuka.
   Na ce, "tofa kaga wani ďigimi, wai dukan sauro da 'kota.
   Shikam Nawaf wurgi yayi da wayar ta fashe, yamaida kansa ya kwanta yana hargitsa sumarsa, zuciyarsa cike da ba'kin ciki, yarasa wane irrin 'kiyayya yasmeen take masa haka, wace irin tsana take masa wai, ya rintse idununsa yana fitar da huci, dolene yaďauki mataki akan yarinyarnan, yakamata yafita harkarta gaba ďaya, dan yakula 'yar kulawar dayake bata ta kwana biyunnan ce takeson jawo masa raini a wajenta.
    Zai tureta daga zuciyarsa yacigaba da harkokinsa, inyaso yamutu da sonta azuciyarsa mana, ahaka doctor yazo yasameshi.
    Bayan yaďan dubashi ya ce, "yana bu'katar ya kwanta yahuta, dan haka allurar barci zai masa.
    Nawaf ya ce, "A'a baya so.
    Doctor ya ce, "aii tazama dole, babu 6ata lokaci ya zurkuďa masa, barci kuwa yay awon gaba dashi.
    To itamadai yasmeen barcin ne ya saceta bayan tagama koke kokenta.
_________________________________        a yau aka fara koyama Nawaf tafiya, yana ri'ke da sanda guda biyu likitoci guda biyu suna gabansa saikuma wasu ma'aikatan abayansa, a harabar asibitin suke, dan haka su yasmeen suna gefe suna kallo.
    Nawaf sai matse idanu yakeyi yana dogara sanduna, ga zufa daketa tsatstsafo masa, sunďanyi nisa da tafiya, aka kar6e sanda ďaya, to dagananfa Nawaf ya 'kara shan wahala, zufa kuwa aii kamar ana kwara masa ruwa.
    Yasmeen tai 'kasa da akai tana hawaye, suma su Anwar haka, aka 'kara kar6e ďayar sandar, yafara tafiya da 'kafafunsa, daganan jikinsa yafara rawa, dauriyarsa ta 'kare, hawaye suka fara ambaliya a fiskar Nawaf, gsky koni yabani tausayi, gashi mugaye likitocinnan sun'ki cewa ya zauna.
   Tun yana daurewa yana ďaga 'kafar har yakoma janta, daga bayama saiya faďi, daga nan suka ďaukesa aka maidashi ďakin dayake, zuwa sanan yafita hayyacinsa.
    Momcy ta rungume yasmeen tana rarrashi, dukda itama hawayen takeyi.
    Harzuwa dare an hana kowa ganinsa, sai ha'kura sukayi suka koma masauki.
    Washe garima dasukaje basu ganshiba, sai lokacin da aka fito dashi domin motsa jiki, yaukam yamafi jiya shan wahala, saboda 'kafar tayi tsami jiya, haka suka kwasheshi suka maida.
    To ayau rana ta uku sai ya kasance da sau'ki, dan yau baisha wahalarba, dakansama ya koma ďaki.
   haka rayuwar tacigaba da tafiya, Nawaf yana samun sau'ki, kuma kullum ana fita dashi dan motsa jiki safe da yamma, saidai yafita harkar yasmeen gaba ďaya, ko zuwa sukayi dubashi daga gaisuwa babu abinda yake shiga tsakaninsu, saima 'yar harara da murguďa baki, amma kowa yana ma'kale da son ďan uwansa, babu wanda yafahimci halin dasuke ciki sai mas'ud, dan basayi gaban su papa, da su Abdallah, amma gaban mas'ud yin abunsu sukeyi.
     To yaudai an sallami Nawaf, gidan dayake zaune suka nufa, ya haďa duk abinda zai bu'kata suka koma hotel ďin inda su momcy suke.
    Papa ya ce, "akai masa kayansa inda matarsa take, gaban yasmeen yashiga faďuwa, miyasa baza'a kama masa ďakiba, kosu zauna da mas'ud, itako batason su kasance đaki đaya da Nawaf, bare yanzu daya tsaneta, ta lura ko ganinta baya sonyi, amma babu yanda zatayi tunda umarnin papa ne.
   Nawaf ya mi'ke yana dogara sanda yanufi ďakin yasmeen yana faďin bari naje nayi wanka saida safenku, kowa ya ce, "ALLAH yakaimu, momcy ta ce, "yasmeen tashi kema kije saida safe.
    Badan tasoba ta mi'ke  dan cika umarnin momcy.
  Ta tura 'kofar tashiga jiki a sanyaye kamar wadda kwai yafashemawa aciki, Nawaf yana zaune bakin gado yana cire kaya, kallo ďaya yasmeen tayi masa ta kawauda kai.
   Shiko aii ko kallon inda take bayyiba, tayi tsaye a tsakkiyar ďakin tana wasa da yatsun hannunta.
   Ya mi'ke yanufo inda take dagashi sai ďaurin guntun tawul, ahankali takeja baya azatonta wajenta yataho, daya matso saita matsa,  yamatso ta matsa, haka sukaitayi har zuwa jikin 'kofa, ta rintse idanu dan sunje 'karshe, ta manne da 'kofa sosai ga idanunta a runtse, ya'karasa takowa ahankali gurinta yakai jikinsa kusada ita kamar zai ringumeta fuskarnan murtuk ya tsare gida...........................



Assalamu alaikum 
Nagode da sakwannin gaisawa da addu'ar samun lafiya dakuketa ďawai niyar turomini,  harma dama su kirana, , Nagode kwarai da 'kaunarku gareni,  nima ina 'kaunarku a duk inda kuke,  ALLAH ya barmu tare, ya bar mana zuminci𷁬uv u oll!!!!!!!

©2016



bilyn Abdul
     Mrs Abdus'salam
         luv u oll my fan's
[26/02 15:13] Abba Gana: ☆☆☆☆☆☆☆
 NAWAFF 
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM




Page41 & 42

.....Yasmeen ta ďauke numfashi, sai 'kirjinta ke dukan tara2, ga jikinta yana rawa, tamaba Nawaf dariya kwarai da gsk, amma saiya gimtse.
    Kaďan yara6u da jikinta, yakai hannu bisa key ďin dake 'kofar ya kulle.
    Tanaji yana sakama 'kofa key sai rawar jikinta ta 'karu, tazame 'kasa ta zauna da6as, ta tura kanta tsakiyar cinyoyinta, tana ambatar sunan ALLAH.
    Ya bita da kallo bayan yagama kulle 'kofar, kai ya girgiza yan ta6e baki, kamar wanda yaga wani abin daba'a so.
   Bayi yashige domin yin wanka abinsa.
   Bayan wasu 'yan mintina taji motsin ruwa, amma tsoro yahanata tashi daga wajen, tama kasa ďago kanta, itafa har yanzu ta zata Nawaf yana awajen tsaye.
    Shima yana wanka yana murmushi, ashema yarinyar nan matsoraciya ce?, to ita da mitake tunanin zan mata ne?, yay wata 'yar dariya, ashedai ana tsoron iya iya inji 'yar mayya, yarinya kamar farar kura, ga tsoro ga jan faďa, dahaka yagama wankan yana zancen zuci, yafito
   Abin yabashi mamaki daya ganta a inda yabarta, kuma kanta a6oye har yanzu, ya murmusa yana dogara 'yar sandarsa, abakin gado yazauna yana cije le6e dan har yanzu 'kafar tana ďan masa zafi, tunda bata gama sakiba gaba ďaya, ya shafa mai tareda shirin barci, harkokinsa yaketayi batareda ya'karabi takan yasmeen ba, yagama shirinsa tsaf, ya haďa shayi yasha da magungunan sa.
    Saida ya kwanta sannan ya ce, "k anan zaki kwana ne??, tayi shiru babu amsa, yay tsaki waike ba'kya jina ne?, yay maganar cikin tsawa.
   Da sauri yasmeen ta ďago tana kallonsa baiwar ALLAH ashe barci takeyi ahaka, ya ce, "bazaki tashi a 'kofar nanba nane??.
  Yanda yay maganar yana zaro idanu  gashi ya haďe girar sama data 'kasa, saitaji bazata iya maida masaba, dan Nawaf yanada kwarjini, idan ya haďe fiska ko kai waye dole kaji tsoronsa, ta mi'ke jiki na rawa ta shige bathroom.
   Nawaf ya girgiza kai yana lumshe fararen idanunsa, gaba đaya kansa a kulle yake, yakamata yanemi shawarar mas'ud, amma kuma bayaso kowa yasan sirrinsa, to kenan zai cigaba da zama da damuwa azuciyarsa, gashi wadda yakeyi dan ita batasan yana yibama, yafitar da huci maizafi daga bakinsa,, lallai lokaci yayi dazai gwada karfinsa yacije le6ensa na 'kasa, yakai hannu bisa 'kafarsa mai ciwo yana girgiza kai, afili ya furta akwai sauran lokaci!!!.
    Tadaďe a bayin zaune dan babu abinda takeyi, saima duniyar tunani data lula, ta manta da inda take zaune.
   Nawaf sarkin saurin jin haushi har ya sha'ka, ya mi'ke yana masafa, yaja sandarsa zuwa 'kofar bayin, da 'karfi ya buga 'kofar bathroom ďin, "k wai wane irin iskancine wannan?, mikikeyi a cikin bathroom ďin??.
   Yasmeen ta ce, "wankafa nakeyi.
   Yaja tsaki yana faďin A'a iyo kikeyi 'karewar wanka, wlhy idan baki baki fitoba saina 6alle 'kofarnan, kuma jikinki saiya gaya miki.
    Ta murguďa baki kamar tana gabansa, a zuciyarta ta ce, "wlhy idanma wani abu kake 'kullawa to kama kwance sa, dan ALLAH bazai ta6a baka sa'a a kainaba, mugu kawai, amma afili sai ta ce, "aii dai ganinan fitowa ko. 
   Kwafa Nawaf yayi yakoma kan gadon yakwanta yana jan 'kafa, yana mamakin miskilanci irin na yasmeen.
   Na ce, " kunji wani 'karfin hali, tomiye na damuwa da fitowarta, kuma shi ya manta da nasa miskilancinne??,
   Yakai kusan minti goma da kwanciya sannan yasmeen ta buďe 'kofar ta fito, babu wani alamar wanka datayi, zuwa sanan Nawaf ya daďe dayin barci, saboda magungunan daya sha.
   Ta bishi da harara tana 'kun'kunai, saman kujera ta zauna, ta tsurama 'kya'ky'kyawar fuskarsa idanu, barci yake amma tamkar yana murmushi, ko afili bazakaga fuskarsa hakaba, lalle tayarda mijinta handsome ne, kuma Gentle man ne, domin komai nasa mai ajine, tafiyarsa, maganarsa, bare idan yana 'kayataccen murmushinsa mai kashe zuciyar 'yammata.
   Yanada kwarjini na musamman wanda dole ma'abota tarayya dashi su girmamashi,  gashi da tausayi da son jama'a, tunda take tareda shi bata ta6a ganin ya wula'kanta waniba dukda ďaukaka da ALLAH ya bashi, jarumi wanda duniya tasani, kuma take alfahari dashi, tunda yasamu ciwonnan gidan radio da tv mujallu da jaridu suketa yayatama duniya, yanzu ta'kara tabbatarwa Nawaf sananne ne a duniya, yakan girmama masoyansa, gashida 'kyauta, yakan taimakawa na 'kasa dashi bashida rowa ko kaďan, tasaki wani lallausan murmushi yayinda taga fuskar Nawaf ma tana bayyana murmushin. Yajuya kwanciyarsa zuwa ďayan 6angaren.
   Tazame ta kwanta saman kujerar dan ganin ya 6oyema ganinta, babu daďewa barci yay awon gaba da'ita.
  Na ce, "mukwana lafiya.

Da asuba yarigata tashi kona ce, "tare suka tashi, badai ta nuna ta farka bane, tana kallonsa yami'ke yana dogara sandarsa zuwa bayi, alwala yayo yafito, ya canja kayan barcinsa zuwa jallabiya fara, ya ďauki abun sallah ya shinfiďa, saida taga ya kabbara sallah sannan ta tashi ahankali itama tayo alwalar, abayansa ta kabbara tata sallar.
   Bayan sun idar kowa ya zauna yana addu'a, Nawaf yajuyo da zummar tada yasmeen tayi sallah, sai kuma yaganta abayansa, ya ďauke kai tamkar bai gantaba, itama tayi burus dashi kamar batasan da zaman wani ďan adam a wajenba.
   Ya tashi ahankali yana dogara sandarsa, yafice batareda yabi takanta ba, murmushi yasmeen tayi tatashi ta haye gado ta kwanta abinta.
   Shikam wajan motsa jiki yanufa dake a hotel ďin.
   Yasmeen tasha barcinta sosai, dan Nawaf bai dawoba, yanacan wajen motsa jiki, har saida ma'aikaciya tashigo, yasmeen ta fito waje dan bata damar gyara ďakin, saida tagama sannan tadawo tashiga wanka.
   Tafito ta shirya tsaf cikin siket da riga na golden brown ďin material, ta naďa ďaurin ďankwali mai tsari, dukda bawata kwalliya tayiba tayi 'kyau sosai, tana fesa turare Nawaf yashigo sai hura hanci yakeyi daka gansa kasan yagaji matu'ka.
   Momcy tashigo itama, da sauri yasmeen ta tsugunna tana gaisheta, momcy ta amsa cikin fara'a, ta ďora da faďin ďiyata, ga mijinki nan nakula yagaji matu'ka, daga wajen motsa jiki yake, kisamu ruwa mai zafi ki gasa masa jikinsa danya samu ďan'karfi kinji.
  Yasmeen taďaga kai atsorace kuma cikin kunya, momcy tadafa kan Nawaf tana masa sannu, ya amsa yana ďan murmushi, karki damu momcyna komai zai dawo normal insha ALLAH, wannan motsa jikin shine zai taimaka mini sosai.
   Momcy ta ce, "to shikenan abu na ALLAH ya'kara lafiya kaji, amin my dear mom, momcy ta ce, "bari naje, ďiyata agasa 'kafarnan sosai, dan ya ce, "jiya da daddare ba'ayiba.
   Yasmeen ta ce, "to mom.
Momcy tafice taja musu ďakin.
    
   Yasmeen tana tsaye inda momcy tabarta ko motsawa batayiba, shikuma Nawaf yana zaune a kujera yana mata kallo kasa2, tayi masa 'kyau sosai yau, kayan sun dace da jikinta, jiyyake tamkar yaje ya rungumeta.
    Yaďan gyara zamansa yana faďin wash ALLAHNA!!.
   da sauri yasmeen taďago tana kallonsa, ya haďe fuska kamar bashiba, ya ce, "kije ki haďa ruwan mana.
   Ta ďan hararesa kafin tawuce bayi, ta haďa ruwa mai zafi sosai, wanda nakula harda mugunta, dan da alama zaiyi zafi sosai.
   Tafito tana goge hannu da 'karamin tawul, kallo ďaya tamasa ta ce, "na haďa, ya kalleta yana ta6e baki to dakika haďa sai akayi yaya?, itama bakin ta ta6e sanan ta ce, "idan kana bu'kata saikaje kayi wankan.
   Yami'ke yana kwafa, gabanta yaje ya tsaya kerere, ta ce, "lafiya?, ya ce, "ita takawo haka, hannunta yaja kawai suka nufi hanyar bayi, ta ce, "wai miye haka ne??.
   Bai tanka mataba har saida sukaje cikin bathroom ďin sannan ya ce, "bakiji mi momcy tace mikiba kenan??, catayi ki gasa mini jiki.
   Yasmeen ta zaro idanu waje, tokai saika amince nagasa maka jiki ďin??, yay wani bazawarin murmushi yana faďin toke ba matata bace, miye aciki??.
   Yasmeen tajuya zata fice tana faďin nikam bada niba wlhy.
   Da sauri ya dam'ke hannunta, "k momcy kika raina kenan??.
   Yasmeen ta ce, "kata6a ganin mutum ya raina mahaifiyarsa, kodawasa bazan raina mahaifiyataba aii.
   Nawaf yaji daďin furicinta, yakaďa manyan idanunsa cikin muryarsa mai daďi, ya ce, "to saiki cika umarninta aii ko, yasmeen ta girgiza kai, kaima kasan bazai yuwuba 'kato dakai ka tu..............saikuma tayi shiru.
   ya matsa hannunta daya ri'ke da 'karfi, nine 'katon???, jin zai murmushe mata kashin hannu abanza ta girgiza kai, nifa badakai nakeba, ya ce, "dawa kike to???.
    Tuni tafara hawaye, kasakar mini hannu to zan faďa.
   Bayason ganin kukanta dan haka yasaketa, amma yakoma 'kofar bayin ya tsaya, babu damar guduwa kenan.
    Ta ce, "plz kayi ha'kuri wlhy bazan iyaba, inajin kunya.
   Hummm dama kinada kunya 'yammata??, yasmeen ta harareshi A'a banida ita, ya murmusa ke dai bakinki baya mutuwa ko??, ta murguďa baki, ya ce, "yayi 'kyau 'yammata, yafaďa yana nufota, ita kuma taja baya har suka kai 'karshen bango.
   Yay wata dariya yarinya ai anzo wajen kuma, ta manne da jikin bango tana mazurai.
  Ahankali ya'karasa gareta, har suna jin numfashin juna, ta runtse idanu kam kamar wadda taga ba'kin aljani, yadafe bango da hannayensa biyu, itakuma tana tsakkiya har jikinta yana gogar nasa, yakai fukarsa jikin wuyanta yana shinshina.
    Ta kauda kai gefe tana faďin wai miye haka??, yacigaba da shinshinar wuyanta batareda ya tankataba, tasa hannu tana ture fuskarsa.
    Cikin sar'kewar murya ya ce, zanyi maganinki ne 'yammata, dan na kula kin rainani dayawan gsk, ya ďago yana kollonta, sai kauda fuska takeyi harda 'yan kwallanta, itadai aduniya ta tsani namiji yazo kusada ita, tun abinda yaso faruwa da ita a kwangwalan da wanda Faisal yaso aikata mata yasa takasa mancewa har yanzu, wasu hawaye masu zafi suka zubo akumatunta.
    Nawaf yasa yatsu biyo yadawo da fuskarta tana kallon tasa, sukaima juna kallon ido cikin ido, tai saurin lumshe nata idanun dan ganin yanda nasa suka canja launi zuwa jaa, ya tsura mata idanunsa masu kalar jaa ayanzu, ahankali yakai bakinsa kan nata, shima ya lumshe nasa idanu.
   Yasmeen tashiga turesa tana kuka, ganin zata iya sakawa yafaďi saboda 'kafarsa babu kwari, saiyasaka hannuwansa biyu yakamo kumatunta ya ri'ke sosai atafin hannunsa.
   Sumbatarta yake kamar zaicire mata la66a, duk duka da mintsini datake masa baisa yasaketa ba, saida yayi mai isarsa ya saketa dan kansa yana fitar da numfashi, dagudu tafito ALLAH yasota bai rufe 'kofar bayinba.
   Shikuma yay saurin zaunawa danjin zai faďi, yadafe kai yana jijjuyawa, yadaďe ahaka, daga bisani yasakarma kansa ruwa, yakai tsawon minti20 ahaka, saida yaji ya dai daita sannan yahaďa ruwa mai zafi yashiga ciki, dan wanda yasmeen ta haďa ya huce.
   Yay lamo aciki idanunsa alumshe ruwan yana shiga dukkan sassan jikinsa musamman ma 'kafarsa mai ciwo, yadaďe ahaka sannan yay wankan sabulu yafito yana goge sumar kansa da 'karamin tawul.
   Abakin gado ya tarar da yasmeen zaune ta rabga uban tagumi fuska sha6e2 da hawaye, da'alama tana duniyar tunani.
    Ya zauna yana faďin "k!, shiru tayi masa, yadaka mata tsawa "k!!! Ba'kya jina?.
    Afirgice ta kalleshi, ya haďe fuska kamar bashiba, cikin faďa ya ce, "nabaki minti3 kije yanzunnan ki wanke fukarki, tun kafin nayi miki abinda yafi na ďazu, 'yar rainin hankali idan momcy tashigofa basai ta zata wani abu nayi mikiba.
   Itadai yasmeen ta mi'ke taje ta wanko fuska, dan bataso ya ce, "zai rin'ka mata irin haka, zata tsaneshine, duk wanda zai nuna yana son jikinta tofa yana zama ma'kiyintane.
   Tafito tana wani rarra6ewa ajikin bango, ya ce, "maza ki shafa fauda a fuskarki kamar ďazu, jiki yana 6ari tayi abinda yace, ta gyara ďaurin ďan kwalinta.
   Fuska aďaure ya ce, "kizo ki shafa mini mai, ta bishi da kallo tana mazurai, ta daure ta ce, "bafa hannunka bane mai ciwon?, cikin rawar murya tafaďa.
    Idanunsa alumshe ya ce, "nasani, koban isa nasakaki aiki bane??.
   Ta ce, "ni ba haka nake nufiba, amma.......
    Yay saurin katseta da faďin amma mi???, tai shiru tana shirin yin kuka, yay sauri faďin karki yarda waďan nan hawayen su zubo, idan kuma ba hakaba zan aikata miki abinda ba'kya so,, kuma kiyi maza kizo ki shafa mini mai idan ba hakaba hummmmyim ya 'kare maganar dayin kwafa.
    Da sauri tazo ta zauna gefensa, ta ďibi mai ahannunta tana murzawa, amma takasa shafa masa, sai mulmulashi take ahannu, yagaji da mi'ka mata hannu ya buďe idanunsa dasuke lumshe akanta.
   Tai 'kasa da idanunta, ya ce, "kin za6i komai yafaru kenan........? kafin yarufe baki ta kama hannun tafara shafa masa mai, ya lumshe idanu yana murmushi jiyake kamar tana masa susa, tagama ya mi'ka mata ďayan hannun, dahaka dai aka gama shafa man, ya ce, "saura kaya.
    Ta marairaice fuska tana faďin dan ALLAH kayi ha'kuri wlhy bazan iyaba ka tausaya mini.
    Yami'ke yana murmushi bataredaya tanka mataba, cikin 'kananun kaya yashirya, yagama ya ďauki waya yay musu odar abinda zasuci, itadai tana zaune tana kallonsa.
    Babu daďewa aka kwankwasa 'kofar yabada izinin shigowa, mai kawo abincine, ya ajiye yafita.
    Ya ďauki nasa ya tura mata nata gabanta yana faďin minti20 nabaki kiyi maza kici abincin nan, daga nan ya hau cin nasa batareda ya sake bi takantaba.
    Itama saitaja abincin taci, dan dama yunwa takeji, kusan tare suka gama, ya ďauki magungunan sa yasha, yana gamawa yatashi yadawo kujerar datake zaune, kusada ita yazauna, itakuma taďan matse jikinta kamar tana jinsanyi.
    Yaďan murmusa tareda zamewa ya kwanta yaďora kansa bisa cinyarta yana faďin matsoraciya kawai, ya lumshe idanunsa tamkar zaiyi marci.
    Aka kwankwasa 'kofar yasmeen tayi shiru kamar batajiba, Nawaf ya ce, "kowaye yashigo.
    Abdallah da mas'ud da Anwar ne, suka shigo da sallama, yasmeen tashiga ture kan Nawaf, amma ko motsi baiyiba,  suka zauna mas'ud ya ce, "a lallai mara lafiya ansamu harda so............, da sauri Nawaf ya buďe ido yana harararsa, kaifa mas'ud ďan iskane wlhy zaka fara ko??, mas'ud yay dariya to nabari bro's.
    Su Anwar suka gaisheshi da tambayar yajiki??, ya ce, "musu da sau'ki, suka gaisa da yasmeen, itadai duk kunya ta isheta amma Nawaf ko ajikinsa,  hirarsa yaketa zubawa.
    Ana haka momcy da papa suka shigo, azatonta Nawaf zai tashi, amma saitaga ya 'kara gyara kwanciyama, yasmeen ta rissina tana gaishesu, Nawaf ma ya gaishesu, suka tanbayeshi ya 'karfin jikin ya ce, "da sau'ki, Papa ya ce, "to ALLAH ya'kara afuwa, mu bari muje wani wuri saimun dawo..
   Suka ce, "to adawo lafiya", Anwar ya ce, "papa dan ALLAH zanje.
   Papa ya ce, "A'a kabari zuwa jibi zamuje tareda ku, saimun dawo, suka fice.
      Abdallah yashiga tuntsura dariyar mugunta, Anwar ya fashe da kukan shagwa6a, yana faďin yaya kagansa ko.
    Nawaf yadakama Abdallah tsawa dallah malam yima mutane shiru, ubanmiye abin dariya anan, Abdallah ya tsaya da dariyar yan toshe baki, wayar mas'ud tayi wringing yami'ke yana faďin ina zuwa.
    Nawaf ya ce, "malam babu wani kana zuwa kace kawai katafi soyayya.
   Mas'ud ya fice yana dariya, aii dai ba haramun zanyiba, kuma na fika, Nawaf ya murmusa azuciyarsa ya ce, "nima ina hanya, afili kuma sauya kalli yasmeen, suka haďa ido, tayi saurin janye idanunta daga kallonsa.
    Shima saiya kauda fuska yana murmushi.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya da sauri, jikin Nawaf yana sau'ki yanda yakamata, sannan agefe ga son yasmeen yana ďauwainiya dashi, saidai yakasa furta mata, dukda kwayar idanunsa da aiyukansa suna 'ko'karin fallasa asirin zuciyar tasa.
    Mas'ud ne kawai ya fahimci halin dayake ciki, amma shima bai nuna masaba tunda bai fito fili ya sanar masaba.
    Itakuma yasmeen dayakeyi dan ita takasa fahimtar ainahin gskyar sa, saboda kallon maza datakeyi abai bai, saka makon hare2 dasuka kawoma rayuwarta abaya, sai take kallon kowane namiji da irin wannan sigar yake kallon mace, dukda itama tana fama da dakon soyayyar tasa azuciyarta, amma ita takan gwada 'ko'kari, konace jarumtar 6oyewa, wannan yasa gwarzon nata yakasa fahimtarta yake mata kallon kitse afannin san maso wani, (wato yana sonta tana son faisal) wannan yasa yake kasa fallasa sirrin zuciyar tasa saboda tu'ku'kin ba'kin cikin kishi dakanyi ďawauniya dashi aduk lokacin da kwarin gwuywar faďa matan ya iso kwakwalwarsa.
    Shaiďan yakan kawo masa taswurar bazata amshi soyayyarsaba, dan tanada wanda takeso, 'kaddarace kawai tarabasu, shikuma ta haďasu.
   Aduk lokacin da shaiďan yagama masa wannan karatun yakanji baya son ganin yasmeen akusadashi, shikansa yakanji haushin kansa yanda yabari sonta da 'kaunarta suka yimasa kamun kaxar kuku, shikam ya yarda ALLAH ne ya yanka masa kazar wahala, shiyyasa yaketa faman figarta, gashi kuma gashinta yagaza 'karewa, yarintse ido yana fitar da huci mai zafi daga bakinsa. A haka yasmeen tafito daga bayi tasamesa.
   Tabishi da kallon mamaki, wannan irin huci haka kamar wanda yake filin gwada 'kwanji.
   Yajuwyo yana kallonta shima, taďan kauda idonta daga kansa, cikin sar'kewar murya ya ce, "lafiya dai?", yasmeen ta ce, "'kalau mika gani??, ya girgiza kai yana faďin babu komai.
   Ta juya tana linke kayansa daya cire yabajesu akan gadon, wayarsa dake bisa dirowar gefen gadon tahau kara alamar kira, ta ďauka tanufi inda yake ta mi'ka masa, ya ce, "waye?, batareda ya kar6aba.
    Ta kalli fuskar wayar sannan ta kalleshi ta ce, "number ce babu suna,, yaďan ďaga kafaďa shikenan kowaye bazan ďaukaba.
    Cikin mamaki yasmeen ta ce, "saboda mi??, yaďan tsura mata idanu, ya ce, "saboda bana ďaga ba'kuwar number, kuma wanan layin nawa kowa zai iya samunsa, dan shine number gama gari,, yasmeen ta ta6e baki, to kasan bazaka rin'ka ďagawaba miyasa karin'ka bada number??.
    Nawaf yaďan zaro ido waje tofa 'yar jarida akaina zaki fara aikin nakine??, A'a ALLAH yabaka ha'kuri malam niba faďa nake nemaba.
    Nawaf ya murmusa, ainima ba faďan nake nemaba, ni dan ALLAH ma zokimin tausa.
   Tausa kuma?, aiini idan zaka saka bindiga akaina bansan yanda aikeyin tausaba.
   Nawaf ya ce, "hummyimm aiko dole ki koya, dan ni mutumne maison idan yagaji amin tausa, ya 'kare maganar yana wani kanne ido ďaya, yasmeen ta kauda kai tana ta6e baki, ta ce, "dan kuma kanaso sai akace dole nice zan maka.
   Yay wata sassanyar dariya yana faďin, yarinyarnan nakula har yanzu 'kuruciya tana damunki wlhy, amma karki damu, nakusa kaiki makarantar hankali, kuma nine malamin.......bai gama rufe bakiba aka 'kara kiran wayar.
    Yasmeen ta ce, "babu 'kyau wula'kanta mutanedai.
   Yay murmushi nima ba wula'kantasu nakeyiba, inada hujjar 'kin ďagawa, duk inda mutum yaga wannan no ďin ya ďauka to yaga dokokin dana kafa, na ce, "kafin ka kirani ka tabbatar katuro mini sa'kon dazan gamsu dakai, idan naso zan iya kirankama da kaina, amma haka kawai daga kirana da number saina kama ďagawa, bakisan mu sanannu anada hanyoyin cutar damuba iri2, karki manta bakowa yake sonmu dan ALLAH ba.
    Yasmeen ta ďan jinjina kai tana ta ce, "hakane kuma, amma kabari ni naďaga wanan.
    Da sauri ya harareta, ya ce, "wlhy koda wasa karki fara, angaya miki kowane shara ya isa yaji muryan matata ne, ALLAH kobanan kika aikata saina gane, kuma zan miki kwakwkwaran hukunci.
    Yanda yake maganar cikin faďa sai abin yabama yasmeen mamaki, a zuciyarta ta ce, "badai kishina yafarayiba??, ta tuna randa ya sha'keta akan faisal, da fasa mata waya dayayi, wata zuciya ta ce, "babu wani kishi yana kare martabar igiyoyin aurensane kawai.
   Ahankali tajuya tacigaba da aikinta,, yabita da manyan idanunsa farare tas, ji yake zuciyarsa tana ambaliya akogin 'kaunarta wadda shi kansa baisan lokacin daya afkaba, ya lumshe idanunsa ahankali.

Bayan kwana huďu.
     Suka fara shirin komawa Najeria harda Nawaf, dan yaďauki hutu domin yin jiyya, daganan zai zarce da hutun 'karshen shekara,, suka shirya tsaf, Nawaf da Mas'ud suka shiga gari sukayo tsaraba, Nawaf ya ce, "malam wai lafiya naga tsarabarka ta 'kare akayan baby?.
     Mas'ud yay murmushi, ya ce, "malam aika kusa zama dadyne.
    Nawaf yazaro ido waje bro's dgsk kakeyi??, mas'ud ya sakeyin dariya, hakane wlhy bakai kana mana rowaba konace kana mana ba'kin cikin ganin baby,, Nawaf ya ce, "kai nayi farinciki ALLAH ya inganta mana, amma ni babu wani rowar baby danake muku dasauran lokacine kawai.
      Mas'ud ya ce, "shikenan muna nan muna jiran lokacin, amma gsky muna bu'katar baby, dan haka ku ajiye wani girman kanku ku bamu.
    Nawaf yakaima mas'ud duka, oh munema zamu baku babyn ba ALLAH ba??.
    A'a ALLAH ne zai bamu amma fa da taimakonku, Nawaf ya ce, "to saika bari saina 'kara aure,, hhhhhh su aure manya, malam tuni nafara harbo jirginka, saiya faďo zan maida yanda akayi, shiru Nawaf yayi dan yasan halin mas'ud sarai.
    'Kananun kaya yaďebo sosai, wanda duk azuciyarsa na yasmeen ne, dan ita kaďai yay ma tsaraba, yabama su Abdallah kuďi suyi tasu, hakama su momcy, saikuma 'kannen mas'ud daya siyomawa, daga nan suka dawo hotel ďin, ya tarar har yasmeen tagama haďa musu komai nasu.
      'Karfe bakwai na dare jirginsu yataso zuwa 9ja................





Assalamu alaikum
Ina muku barka da sabuwar shekara, amma ina kira gareku 'yan uwana akan mu gyara wani abu, damuke aikatawa a tsarin rayuwarmu.
    Idan ban mantaba munshiga shikarar musulunci wata biyu daya wuce baya, amma banga mutane suna posting sosai akan farin cikin shigarmu sabuwar shekaraba,,  wasuma basu san munshigaba,, amma abin haushi da ba'kin ciki kowa yasan anshiga sabuwar shekarar 2017, harma yana 'ko'karin yin posting ďin taya murna.
    'Yan uwana mu gyara, muringa girmama addininmu da aldarmu, mudaina fifita addinin wasu akan namu, dansu basu damu da abinda muke cikiba, koda sun sani sukan nuna basu fahimtaba,, tofa lokaci yayi dazamu fara gane karatun kurma wlhy,, ALLAH yasa mugane amin..



©2017


bilyn Abdul
     Mrs Abdus'salam
         luv u oll my fan's
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *