check your best novels here

Monday 20 February 2017

NI DA AMINIYATA!!! 57 to 60

[26/11/2016 21:46] bilyn Abdul: 27~November~2016





NI DA AMINIYATA!!!




NA BILKISA IBRAHIM



57


BAYAN WATA TAKWAS
...........Rayuwa mai gudu da sauri, daga safiya tayi sai gari ya waye, fareeda dai an shiryu da gsk, dan takoma makarantar islamiyya, gashi takoma wata shiru2, batada burin daya yuce tasamu miji tayi aure itama ta zauna agidanta, kullum kuma tana cikin yin istigifari, takan shiga gidansu ta taya mama aiki, dukda har yanzu mama bata sakar mata fuska, haka aikin inna duk ita takeyi, damuwar ta d'aya sopy, dan har yanzu sopy bata yafe mataba, ko gidan tazo bata kulata, gaisuwama sama2 sukeyi, kullum burinta ALLAH yakawo randa sopy zata yafe mata sukoma yanda suke da.
    Inna tana k'ok'ari wajen yiwa sopy nasiha akan tayafema fareeda tunda ta shiyu, duk sanda tazo gidan saita yimata irin wannan nasihar.
    To itama sopyn tayarda fareeda ta canja, amma tanaso tak'ara shiryuwane kafin ta ce,  " ta yafe mata, dan tuni ta yafema fareedar batadai furta bane kawai.   

GIDAN SOPY
Sopy anata fama da k'aton ciki, wanda da'alama ranar haihuwa kawai ake jira, dan tama daina zuwa makaranta.
    Afalo na isketa itada uncle G!, tana zaune a saman kafet ta mimmik'e kafafuwa, tasaka filet d'in kankana a tsakkiya tana sha, uncle G! Yana gefenta kwance a doguwar kujera.
    Ya kalleta ya tuntsure da dariya, sopy tajuyo tana kallonsa, ta ce, "miya baka dariya? hubbina!.
   Cikin dariya uncle G! Ya ce, "wlhy ke kika bani dariya sopyna, jibi yanda kika mik'e kafafu kina shan kankana, ALLAH kirage ci, nakula aranafa saikici abinci sau biyar.
    Sopy ta murgud'a baki tana fad'in to waye yaja mini?, aii dai kowa yasan da bahaka nake da ci kamar jakaba ko?.
    Uncle G! Ya kwashe da dariya, ya ce, "aina kusa kad'a miki tanbarin acici kazar gona.
   Sopy ta watsa masa harara, saikuma ta shagwab'e fuska tafara kukan shagwab'a, ya sakko yana gintse dariya, kusada ita ya zauna yana shafa bayanta ahankali, acikin kunnenta ya ce, "yakamata kibar shagwab'a, dan kinkusa zama momy.
    Yasa hannu ya share mata hawayen fuskarta.
  Ta ce, "to ba kaibane kake tsokanata, ya sumbaci kuma tunta yana fad'in to yi hakuri na bari maman baby.
   Yanzu mikikeso nayi miki danki huce, ta nuna masa k'afafunta da sukayi d'an fushi.
   Yay murmushi dan yasan mitake nufi, ahankali yafara mammatsa mata kafafun, ita kuma tafara lumshe idanu, ya ce, "karfa kiyi mini barci 'yammata!!.
     Sopy tad'an bud'e idanu tana murmushi, ta ce, "kasan kuwa harna fara jin barcin wlhy.
    Ya ce, "aii ke yanzu kin zama kasa, dan ko fira bak'ya barinmu muyi, b'urun2 saikice aje akwanta, ta ce, "to yazanyi hubbina!, nima ba laifina bane, ya ce, "gsky ne laifin babynane, yafad'a yana kanne mata ido d'aya.
     Ta ce, "yauwa hubbina wai yaushe kacema Aysha zata zo?, ya ce, "sai ranar juma'a, tunda ta ce, "Al'hamis za'ayi musu hutu.
    Sopy ta ce, "ALLAH ya kaimu, yakuma kawo mana ita lfy.
  "Amin uncle G! Yafad'a yana murmushi.


   Yau dawuri uncle G! yafita dan zaiyi lectures d'in safe.
    Sopy ta tashi tad'an gyara gidan iya inda zata iya, dan yau bata jin dad'in jikinta kwata2, tana dai daurewane dan bataso tahana uncle G! fita aiki, tad'an cije leb'e ta rik'e bayanta da hannu d'aya, tadafe kujera da d'ayan.
    Tad'an dad'e tsaye tana shan azabar ciyo, daga bisani yalafa, ta rarrafa dak'yar takoma bedroom.
    Tana zuwa tazube agado, tanata murkususu, saidaga baya wani bacci mai dad'i ya saceta.
                Agigice ta farka domin jin wani azababben ciyo, mai kamada na fitar rai, ai bata san sanda ta silmiyo daga gadoba, babu abinda takeyi sai salati da kiran sunan ALLAH, dak'yar ta iya d'aukar wayarta, batare da tasan nomber ko wayeba takira kawai, ALLAH yasota aunty Asiya takira, dak'yar ta ce, "plz kowaye yazo ya taimakeni zan mutu.
    Aunty asiya bata jira ta karasa ba, ta fito da sauri daga gida, gidansu ummy ta mik'a khalil, agurguje tazo gidan, sanda ta iso sopy harta fita hayyacinta, dan kuwa haihuwa ce gadan2.
    Aunty asiya ta rik'eta tana mata sannu.
    Ita dai sopy babu abinda takeyi sai ambatar sunan ALLAH, da duk addu'ar datazo bakinta, zuwa can tasaki wani uban nishi, jikake wani kacam, d'a yafad'o, yana tsanyara ihu.
   Aunty Asiya ta ce, "masha ALLAH, sopy sannu da aiki.
   Aunty asiya takira ummy ta ce, "ta turo mata mamarsu.
   Babu dad'ewa mamarsu ummy tazo, aka yanke cibiya, tareda d'auke sargad'ed'iyar yarinya maikama da babanta, maman ummy ta ce, "masha ALLAHU, da zuwan wannan k'yak'yk'awar yarinya duniya gidan gwa gwarmaya.................






Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[26/11/2016 23:18] bilyn Abdul: 27~November~2016




NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM



57

...........tsaf suka gyara jaririya da sopy, Aunty Asiya takira uncle kabeer ta sanar masa, shikuma yasanar da uncle G!, dan danan labari ya karad'e dangi, har muta nen Gurum labari yakai musu, acanma murna ce ta kaure, da addu'oin fatan alkairi ga jaririya, bak'uwar duniya.
        Uncle G! ya iso cikin murnarsa, bai damu da makwaftan dasuke zaune afaloba, suka gaidashi tareda yimasa barka.
      D'akin sopy ya isa cikin matuk'ar zumud'in son ganin jaririyarsa, yana shiga ya rungume sopy dake bakin gado tana shafa mai, dan batajin ciwon komai, saidai aunty asiya ta ce, "ta shirya suje asibiti aduba lafiyarta itada baby.
    Sopy tad'ago tana kallonsa, suka sakarwa juna murmushi, ya ce, "sannu sopyna, ya jikinki??, sopy ta ce, "komai nomal hubbina.
    Ya ce, "masha ALLAH, aunty asiya tashigo da sallama, suka amsa, ta mik'a masa jaririyar da'aka shirya cikin fararen kayan sanyi masu laushi.
    Yasa hannu biyu yakarb'a, ya tsura ma  jaririyar ido kamar zai cinyeta, yad'an mannata da jikinsa tareda lumshe idanu yana zubar da hawayen farinciki.
     Sopy tasaka hannu tana share masa, yad'an dad'e ahaka sannan ya bud'e idanu, ya sauke akan jaririyarsa, mai tsananin kama dashi, tanata barcin ta. 
    Tad'an motsa kad'an, yay saurin fad'in sorry my dear, yad'an jijjigata kad'an, takoma barcinta.
    Sopy ta ce, "hubbina santin baby ya hanaka magana ko??, yad'ago yana murmushi, ya ce, "sopyna k'yautar d'a!! dabance, bazan iya misalta miki irin farincikin danake cikiba yau wlhy.
     Sopy ta ce, "aii naga alama, dadyn baby!!.
    Uncle G! ya ce, "haka zancen yake, amma zonabaki sunan babyna, sopy ta mik'ama uncle G! kunnenta, ya gwargwad'a mata, tayi wani murmushi tana fad'in inko haka ta kasance to kayi halacci hubbina!.
    Ya ce, "ko? Sopyna!.
     Ta ce, "ALLAH kuwa.
Ya ce, "anyi an gama, barima kiga nayi maya hud'uba.
    Uncle G! yay mata hud'uba sannan suka tafi asibiti dan aduba lafiyarsu.
    Haka akayita hidima, koda yaushe gida cike da 'yan barka, su aunty Nafisa kuwa kullum sai sunzo, fareedama tazo saidai sopy bata sakar mata fuskaba sosai, itako fareeda bata damuba tanata rungume jaririya danji take wata irin k'aunar yarinyar tana shigarta.

   Yau muta nen gurum sukazo mota guda, aka had'a musu cima masu dad'i, sukaci sunata santi, sai yamma suka tafi akabar su aunty hafsat da libabatu da aysha anan, komai yana tafiya yanda akeson gwaggo ta had'o ma sopy kayan barka sosai, mutane sunata santi kayan, dan gwaggo ta taka rawar gani.
    Yau kuma aka kawo naman k'auri daga gidansu sopy, suma sunyi k'ok'ari, dan d'an akuya guda uncle kabeer ya siyo aka gyara, suma sunyi rawar gani wajen had'o kayan barka, ayau kuma shima uncle G! ya kawo nasa kayan barkar, abindai sai wanda yagani, komai dai2 saidai mak'yi zai kushe.

RANAR SUNA.
  yaune akasha sunan baby wadda taci sunan BILKISU MAI GADON ZINARI", lallai uncle G! yay mini halacci kuma nagode.
    Bayyana muku yanda taron suna yakasance b'ata lokacine saidai fa, ansha shagali na ban mamaki, groups dayawa sun halacci taron sunan baby Bilkisu!, irinsu.
PROFESSIONAL WRITER
ZUMUNTA GROUP 
HAUSA NOVELS
 MANSHAT NOVELS
PRECIOUS WRITER' FORUM
IKKIAM'S NOVELS
HAUSE OF NOVELS
SO DA K'AUNA GROUP 
FASHION & NOVELS
BEST FRIEND'S 
LABARUN LITTATAFAI
HAUSA NOVEL BOOKS
 MACE MUTUM GROUP, ma sun halacci wannan taron suna, harma da groups d'in daban fad'aba, suyi hak'uri amma suma duk mun gansu.
     Dahaka taron suna yatashi lafiya, akabar  mai jego da jaririya Bilkisa, tareda dadynta uncle G!!!.
    An kawo musu tsohuwar dazata kula dasu, har suyi arba'in, AYSHA ma ta nan anbarta, saboda wasu ayyukan.

Bayan arba'in, baby Bilkisu tayi b'ul2 da'ita gwanin sha'awa, tana shan tarairayar iyayenta, dan uncle G! yana dawowa aiki zai d"auketa sallah ce kawai takesawa ya ajiyeta, ranar weekend kuwa ai ahannunsa take wuni, yayta mata wasa tana b'angale baki, sunje Gurum yawon arba'in, an kaiwa gwaggo da baba sunga jikarsu, takosha addu'oi, awajen kakanninta.
    Ananma kano sun zagaya gidajen 'yan uwa da abokan arzik'i, daga baya sopy ta tattara takoma makaranta itama..................



WASA KWAKWALWA.
     wannan sak'one daga gareni, inaso ku fad'i abinda yake ranku game da wannan littafi mai suna NI DA AMINIYATA!!!.
      SHIN WA
☆WAKUKAFI TAUSAYI??.
☆WAKUKAFI JIN HAUSHI??.
☆WAKUKAFI SO???.
☆ WAYAFI BIRGEKU??.
        Karki bari ayi babu ke, fad'i ra'ayinki, ko gyara gareni agun danayi kuskure.
   Idan kuntashi, kusaka sunanku, da gruop d'in dakuke, dakuma ra'ayinku.
   Inanan ina jiran sak'wanninku, ta hanyar gruop gruop d'inku, dan saikun rubuta ra'ayoyinku kafin mu kalmashe bakin wannan labari, daga nan zuwa ranar litinin.
    Plz karkuyi sanya, nagode sosai da k'yaunarku gareni.
   SAINA JIKU!!!!!!!!!!!!!.





Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[28/11/2016 18:53] bilyn Abdul: 28~November~2016





NI DA AMINIYATA!!!




NA BILKISA IBRAHIM



59&56

.............haka rayuwa tacigaba da tafiya, su sopy suna rainon baby bilkisu, yanzu haka tafara zama, uncle yadawo da Aysha wajensa, an nema mata makaranta tana yi anan, haka sopy tana zuwa makaranta kuma tana fahimta, abunda bata ganeba uncle G! yana nuna mata.
     Adai2 wannan lokacinne kuma aka sha bikin fareeda da wani d'an anguwarsu salmanu, yanada mata d'aya da yara uku, fareeda ta aureshine kawai amma badan yayi mataba, dole ta aureshi dan zaman gidan ya isheta, gasu baba sun dameta akan tafito da miji, to hakadai aka rurrumata aka kaita, indama ALLAH yasota ba gidansu d'aya da kishiyarta ba, gidan hayane d'aki d'aya ya kama mata, suna had'akar bayi da kichin da sauran 'yan hayar gidan, bawata cimar arzik'i, shinkaface fara da mai da rana da safe kuwa koko da k'osai shima idan kin samu, da daddare tuwo, dan haka fareeda duk tafita hayya cinta ga wani uban bak'i datayi kamar ba itaba, shiyyasa kullum cikin kuka take da nadamar abinda ta aikata abaya, ALLAH yasotama sopy tayafe mata harda uncle G!.
       Agidan sopy kuwa abun su d'anas komai yana tafiya yanda suke so, ga mijinta yana nuna mata soyayya mai tsafta, koda yaushe k'ara tattalinta yake, itama k'ara sonshi take kullum, ga 'yar d'iyarsu abin sha'awa da burgewa.
     Aunty asiyama ta sake haihuwar mace, itama suna cin soyayyarsu da uncle kabeer, komai yana tafiya musu dai2.
     Haka yayun sopy sumadai Alhmdllh, komai dai2.
    Mutan gurum ma a b'angarensu komai nomal masha ALLAH.


BAYAN SHEKARA TAKWAS.
       Nayi shiri nida 'yan kazagina su madina, gidan uncle G muka nufa dan mu gano muku halin da suke ciki, tun a tsakar gida nafara gamo da yara biyu duk maza, 'yan kimanin shekara 6, d'aya ya ce, "mas'ud mima momy ta ce, "mukarb'o mata?.
     Ya ce, "kaji mus'ab d'innan bakai ta gaya mawaba, zaka wani tambayeni?.
   Mas'ud ya ce, "to mukoma mu tambayo?, tafd'i mus'ab yafad'a yana kallon mas'ud, ya ce, "wlhy bazan komaba kana ganin aunty bilkisu tana nemana ta daka saboda na d'aukar mata sweet d'azu, idan zakaje  keje ina nan ina jiranka, dan baxan shiga cikin gidaba harsai dady yadawo.
     Madina ta kalleni ta ce, "da'alam yarannan fa yaran sopy ne, bakiga kamabane??, na ce, "nagani madee kuma inaga tagwaye ne.
     Ana cikin haka saiga uncle G! Yadawo, dagu su mas'ud sukaje suka rungumeshi, shima yataresu da murna, d'ai2 ya d'aukesu yana d'agawa, ya ce, "yaran dady sai ina??.
     Mus'ab ya ce, "momy ce ta aikenmu kuma mun manta, uncle G ya ce, "to kumuje ciki.
    Mus'ab ya ce, "dady ALLAH aunty bilkisu zata dakeni, uncle G ya ce, "kamata laifine ko??, mas'ud yay saurin fad'in dady sweet ya d'aukar mata, uncle G ya ce, "lallai kayima aunty bily babbab laifi, yafad'a yana jan hannunsu.
     Muka gaidashi muma, sai asannan ya gammu, cikin murmushi ya ce, "lallai yau munada babbar bak'uwa, bily kece agidanmu?.
    Nayi dariya na ce, "nice uncle G!, kuna nan lafiya?, ya ce, "lafiya k'alau muke, kushiga mana, aii sopyn tana ciki, mukace to.
     A falo muka tarar da bilkisu rik'e da wata 'yar k'yak'yk'yawar yarinya, wadda zata kai shekara d'aya.
    Bilkisu tazo ta rungume dadynta, yashafa kanta yana fad'in aunty bily ga takwararki, ta ce, "dady wace takwarata??, ya nuna mata ni, da sauri tazo ta rungumeni tana gaisheni, naja hannunta muka zauna saman kujera, su madinama suka zauna.
     Uncle G! Yad'auki karamar yana fad'in little sopy ykk??, yarinya ta shiga tsalle tana dariya da alam tasan dadynta,   ya ce, "aunty bily jeki kira momy kice tayi bak'i.
    Bily ta ce, " to dady.

Babu dad'ewa suka fito tareda sopy, sopy ta zaro ido dan mamaki, ta ce, "bily kece yau agidanmu, dama baki manta damuba??.
    Nayi dariya ina fad'in yazan manta daku, abubuwane kawai sukayimin yawa.
   Sopy tayi dariya tana fad'in lallai dadyn bily yau kayi mana babban kamu, aina kasamo mana bily??.
   Ya ce, "wlhy anan na had'u da'isu a tsakar gida.
   Sopy ta ce, "lallai kam sannunku dazuwa, mukace yauwa, dan danan aka cika mana gaba da kayan ciye2, aka shiga firar yaushe gamo, ananma nakejin fareeda ta haihu harma gobe suna, na ce, "yaranta nawa yanzu, sopy ta ce d'ayace mai sunana safiyya saikuma yanzu ta haifi namiji.
     Nace ALLAH sarki ALLAH yaraya, kema ai naga kun had'a family keda uncle G!, sukayi dariya, uncle G ya ce, "hud'une kawai, bilkisu takwararki sai 'yan biyu mus'ab da mas'ud sai auta safiyya k'arama.
    Na ce, "masha ALLAH, ALLAH ya raya mana su.
  Suka ce amin.
   Sopy ta ce, "mus'ab ina aiken dana yimuku??, mas'ud ya ce, "momy mun manta shine muka dawo danmu tanbaya.
    Sopy ta dafe kai tana fad'in naga takaina, waiku wad'anne irin mashiriritane, aunty bily tashi kije gidan aunty asiya kice nace tabani sak'on.
   Bily ta ce, "to momy, intafi da pretty??, eh kitafi da ita amma samo zani ki goyata kuma   kudawo da yanzun nan.
    Ta ce, "to.
Yau wuni guda agidan uncle G mukayi, da yamma sopy tarakamu gidan Aysha dan itama tayi aure tana nan kusa dasu, sai daredai muka dawo gida cikeda kewar yaransu masu wayo da son mutane kamar iyayensu.
      TAMMAT BI HAMDULLAH.
   
anan nakawo k'arshen littafin  NI DA AMINIYATA, kuskuren danayi ALLAH ya yafe mini, abinda na fad'a dai2 ALLAH yabani lada.

Ina k'yaunar masoyana aduk inda suke, kuma bazan manta dakuba, ALLAH yabarmu tare.


WASA KWAKWALWA.

       UMMIEE KHALEEL
daga PRECIOUS WRITERS FORUM.
      Agaskiya naji dad'in novel d'inki ba k'aramin.............shhhh bari inyi shiru ki saikin k'arasa zanyi comment.

Toni banjin tausayin ko, amma bari dai in dan tausayawa fareeda, badan halintaba, amma dan ALLAH, gashi duk ta wulak'antu, da wahala, tarasa farin ciki a rayuwar ta, ba iyaye ba miji ba AMINIYA, gata nan dai da halinta, nad'an tausaya mata dan duk bata cimma burinta ba.
     Kuma ta k'as k'antu, hak'ik'a duniya budurwar wawace kuma makaranta ce, ba sai lallai abinda wani ka yasamu kaima dole sai ka samu ba, kowa da yanda ALLAH ya tsara masa rayuwarsa.
  Rayuwa same our finger nails are not equaltausayine gare ta da bata san wannan ba.

Fareeda tafi bani haushi a cikin character wlhy kamar in kasheta .......ALLAH ya raba mu da irin kawaye mai halinta ko sama da nata.

Sopy da hubbinta nafi so, sun dace da juna kawai ba abin kad'i.

Gsky uncle G yafi burgeni his life care 2 wife, salon soyayyan shi daban yake dana sauran mazan, hakika fatan kowace 'ya mace ta samu miji mai hali irin na uncle G, nima sai da na d'an fola mashi.

Kada ki fada wa sopy dan ALLAH kamin ta saekeni ta sambad'a ni.

Bily saina fad'a mata kuwa .

MOMYN HUNAINA
    daga HAUSA NOVELS.
         Fareeda abin tausayi kuma abin haushi, wanda yafi burgeni dangin uncle G dasu kabeer, sai tauraruwa sopy.

RUKY B GEGAS.
     Daga PROFESSIONAL WRITER.
     Sopy tafi burgeni, fareeda kuma tafi bani tausayi, uncle G nafi so.

RUKAYYA MUH'MD daga BEST FRIEND.
    nafi tausayin sopy, nafijin haushin careers..., nafi son sopy da uncle G, sopy da uncle G da baby bilkisu sunfi birgeni.

SALAMATU B BAGAYA daga PROFESAIONAL WRITER.
      ni nafi son sopy, fareeda tafi bani tausayi, iyayen sopy kuma sunfi burgeni, saboda hakuri da sukayi da fareeda, aunty bily ALLAH yabiyaki da gidan ALJANNA da MUSLMAI.

bily....Amin salamatu ngd.

DEEXERH daga ZUMUNTA.
      babu wanda nake tausayi aunty bily, duk nafi son sopy, kuma uncle G yafi burgeni, nafi jin haushin fareeda.

TEEMA daga PROFESSIONAL WRITER.
       Assalamu alaikum, sunana teema adamawa daga pro........fareeda. Wacce na fiso sopy, team sopy, wadda yafi burgeni uncle G, aunty bily saura kicce sonshi nake.

Bily.... aii saina fad'awa sopy

HAUWA LELE daga PRESIOUS WRITERS FORUM.
     Nafi tausayin sopy, nafi jin haushin fareeda , nafi son sopy,  sopy tafi burgeni.
    A gsky kinyi k'ok'ari bily, sai dai gdy, ALLAH ya k'ara basira, nidai banida tacewa sai dai ALLAH ya kara basira, yakuma baki ladan wannan kokari naki.
     Taki har kullum 
Hauwa lele

Bily .... ngd hauwa'u, amin.


HYSH JAHUN daga SO DA K'AUNA GROUP.
     Sopy nafi so, fareeda nafijin haushi, uncle G yafi burgeni, sopy tafi bani tausayi.
      Hysh jigawa state.


FASTIMA MAMMAN daga SO DA K'AUNA GROUP.
     Nima nafi son sopy, na tsani fareeda, uncle G da sopy sunfi burgeni, nafi tausayin sopy.


MURJANATU SULAIMAN daga FASHION & NOVEL GROUP.
      Nafi son sopy, wanda yafi burgeni uncle G, nafi jin haushin fareeda.

AMINA SALEH love u, daga HAUSA NOVELS.
    sopy tafi bani tausayi, fareeda tafi bani haushi, uncle G nafi so, dan yafi son sopy.


UMMUNASS daga HAUSE OF NOVEL.
    nidai sopy nafi so, kuma nafijin haushin fareeda, kuma fareeda takan bani tausayi wani lkcn.


SA'ADATU SA'AD daga HAUSE OF NOVELS.
    Nafison sopy da uncle G, gsky nafi jin haushin fareeda domin batada kirki, sannan sopy tabani tausayi lokacin da aka rabata da Abdul.


KULSUM daga HAUSE OF NOVELS.
    Nima sopy nakeso da uncle G.

NANERH daga PROFESSIONAL WRITER.
     nafi son sopy, nafi jin haushin Abdul, uncle G da uncle kabeer sunfi burgeni, fareeda tafi bani tausayi.


SAKINA GEGAS daga LEDIES FORUM.
      nafi son sopy, nafi jin haushin fareeda, uncle G yafi burgeni, fareeda tafi bani tausayi.


 UMMU MASAKEEN daga HAUSA NOVELS.
    gsky fareeda tafi bani tausayi, sannan nafi son sopy, uncle G yafi burgeni.

RUKY daga PROFESSIONAL WRITER.
      nafi son sopy, nafi jin haushin fareeda, iyayen sopy sunfi burgeni, fareeda nafi jin haushi.

ALHAMDULILLAH ina farincikin kammala wannan littafi nawa.

Ina godiya ga d'umbin masoyana, dawanda suka turomin sak'wanni da wad'andama basu sami damar turowaba, nagode da k'aunarku gareni.

Saikuma ALLAH yak'ara had'amu a sabon littafina mai suna NAWAFF DA KUKAN KURCIYA suna nan zuwa gareku nan bada dad'ewaba.


Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's


Luv u oll
 ©2016
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *