check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 41

AUREN  K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

41 «*****» bayan sundawo masallaci, Dr Anuwar ya biyoshi office d'insa, dady yazauna a kujerarsa, shikuma Dr Anuwar ya zauna akan d'aya daga kujerar dake gaban tebir d'in, Dr Anuwar ya tsurama dady idanu my friend dama ina son magana dakai??
   "Dady yay murmushi ina jinka my friend"
 Inason magana ne akan amaryarka?
 Karka damu my friend ina saurarenka
      "Abdul !!!, ince dai kayi bincike akan ciwon dake  damun ta kuma kaga sakamako??
    "Dady ya girgiza kai my friend bankai gayiba dai, amma inada shirin yi,
 Dr Anuwar ya jinjina kai toni nayi,
Ya fad'a yana kallonsa, dady ya gyara zama sosai, to my friend mi binciken ya nuna maka??
      "Abinda bincike ya nuna my friend matarka tana buk'atar tai makonka, domin ta wannan hanyar ne kawai mai sauk'i dazata rabu da wannan ciwon.

Dady yazaro idanu waje , my friend kasan mikake fad'a kuwa??
 Dr anuwar yay dariya nasani my friend, kuma nasan kaima kasan haka ne, saidai kawai dan kana kan wani ra ayinka ne na daban.

Bahaka bane my friend, abinda zaka duba shine yarinyarna tayi k'ank'anta dayawa, shekara 17 fa.
 Dr Anuwar yay murmushi oh kai aganinka 'yar shekara 17, bazata iya d'akar nauyin kaba, to ai itace ma daidai aure, ya mik'e kayi nazari abokina, ka tai maki matarka, dan muna buk'atar baby da wuri ya fita yana dariya.

Shima dady dariyar yakeyi, yana girgiza kai, my friend akwai sauran lokaci, yafad'a yana duba waya.

Kamar yanda yasaba, yauma ya tashi karfe 5:30 pm yanufi gidansa cikin irin wani nishad'i dashima bai san na miyeba,
  Amma sai mi yana dosar sashinsa saiyaga su husna zaune akan fararen kujeru sunata hira da dariya kowa taci kwalliya ta d'aukar hankali.

Dandanan ya had'e rai kamar bashiba, yadoshi b'angarensa batare daya sake kallonsuba,.

Da sauri suka taso suka biyosa, shikam ya cigaba da bud'e d'akinsa, ikileema tace haba dear, dan ALLAH kana ganinmu ka share??
Banza yay mata saida yagama bud'ewa ya shige, sukai saurin k'ok'arin biyoshi, yadaka musu tsawa kunsan ALLAH duk wadda ta shigo mini nan wallahi saina karyata, idan kuma kunji k'arya ku ahigo, ya fad'a cikin k'araji.
    "Sukai zugud'i suna kallonsa harya maida k'ofar ya rufe.

Zuciyarsa na zafi ya shiga bayi yama rasa kalar tunanin da zaiyi akan wad'annan yaran, bayan yagama ya shirya cikin farar jallabiyy,yanufi b'angaren Munneerah, tana kwance adoguwar kujera ya turo kofa, da sallama ya shigo, ta mik'e zimbur zaune, yabita da kallo, itakuma ta durkusa tana gaidashi, damasa sannu dazuwa, ya amsa fuska acinkushe, takawo masa ruwa ya sha, ya mik'e nibari naje masallaci, tace to adawo lafiya.

Bayan yadawo  suka ci abinci, amma harsannan fuskarsa babu walwalah.
Yauma ko.abincin kirki baiciba, wajan k'arfe 10:pm, Munneerah ta mik'e dan barci takeji, yaukuma tasan yayan nata yay mata nisa tunda anty nanta sundawo, yabita dakallo, bayan ta shige shima ya mik'e yanufi b'angarensa.

Shirin barci yayo ya dawo tana zaune tana addu'a ya shigo, tabishi da kallon mamaki, yazo bakin gadon ya zauna.
Dukda tana shakkar yimasa magana saboda ganin fuskarsa ahad'e amma ta daure tace yaya!!.
Yajuyo yana kallonta batare dayayi maganaba, ta daure tace su anty husna fa sundawo.
To insun dawo sai akai yaya?
Takuma daurewa tace ince acan zaka kwana?
   "Harara ya watsa mata sannan yace saiki d'aukeni ki kaini, yafad'a yana kwanciya.......

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *