check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 34

AUREN  K'ADDARA
               ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

34 «*****» to kinjifa mama dama kinsan wannan amma kika barni agida ita waccan sarkin iyayin husna uwarta tace ba yanzuba, to nidai duk ma yanda za'ayi kiyi nakoma d'akina awannan satin,
   Gaakiyarki ikileema in ALLAH ya yarda yau da abban ku ya dawo zan masa magana gara ki koma d'akinki.
    "Ta tashi cikin murna ta rungume uwar tata tana godiya.


To ab'angaren husnama haka abin yake ita babanta ma tasanar tanason komawa d'akinta, yace karta damu zaije yasamu umma da yaya da maganar yau da daddare.
    "Tace to"


Agidan dady kuwa zama akeyi irin na k'anwa mai girmama yayan ta, da yaya mai kula da k'anwarsa amma babu wata shakuwa data wuce gaisuwa da safe, ta had'a masa break, ta rakashi wajan motarsa in zai tafi aiki, tadawo ta gyara masa d'akinsa, ta wanke kayansa daya cire, tayi girki da rana mai dad'i da gamsarwa akai masa asibiti,inya dawo ta taroshi tarakasa har b'angarensa, ta basa ruwa yasha, dama ta had'a masa ruwan wanka, da dadare ta dafa musu abinci mara nauyi suci, koda ba wata hira mai tsawo ke had'asuba sukan zauna apalo d'aya suna kallo, koyana bincikensa akan aikinsa, ita kuma tana kallo, duk abinda yasakata zatayi babu fushi bare canja fuska kota nuna gajiya warta.
Wannan ne yakansa kan dady girma dajinfa shima fa ya isa maigida, shima yana kyautata mata indai yafita yaga wani abida ya birgeshi zai siyo mata,

TUNA TARWA :- 'yan uwana mata bamu cika san yiwa mai gida wankiba, bare idan ALLAH yad'an bashi karfen nasara ahannu (kud'i) masu d'an k'ok'ari a cikinmu sune masu wanke singlet da gajeren wando, kina zaune mai gida zai had'a wanki ya bayar, sai kiji muna fad'in bazamu iyaba gana yara ganashi kai wallahi aiki yay mini yawa, a'a uwar gida tsarama kanki yanda zaki zauna agidan miji kinji, kula dashi da dukiyarsa sutturarsa, tsara wani d'an lokaci kina yima mai gida wanki yanasa farin ciki da kaunarki azuciyarsa, zaki k'ara samun fada a cikin zuciyarsa,....kudai biyoni 'yan uwa........

billy 
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *