check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 29

AUREN  K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim

29 «******»  yasa key d'in ya bud'e d'akin, ya kwashi kayansa yay ciki.
Ta mik'e zumbur zaune tana kallonsa cikin mamaki, kallo d'aya yay mata ya kauda kai, kujerar dake d'akin yanufa ya zube kayansa bisa tebir d'in gaban kujeran ya zauna.

Ya kalli Munneerah dake ta faman kallonsa, sai kuma ya mik'e ya nufi wajan gadon, shima yana kallon ta, ya kauda kai, kinci abinci ya fad'a yana bud'e kulolin dake gefenta??
     "Tace na k'oshi"
"Ya d'aure fuska mekika ci??
 "Ba komai"
Oya sakko kici abinci kafin na b'ata miki rai.
Ganin ya tamke fuska yasata sakkowa da sauri, dan dady yanada kwarjini sosai duk fitsarar ka in ya had'e fuska sai kaji shakkarsa.

Ya kalle ta tana cikin doguwar riga ta barci, amma bata kai k'asa ba,tayi mata kyau sosai, ya zauna bakin gadon, ita kuma ta zauna k'asa tana zuba masa abincin, ta gama ta jawo wani filet d'in zata zuba, yace karki zuba wannan ma ya ishemu.

Ya sakko ya zauna saman kafet d'in, ya fara cin abincin, itako ta kasa ci sai wasa take da zoben hannunta.
Ya d'an buga cokalin ajikin filet d'in, ta d'ago tana kallonsa,bana son yawan magana fa kici abinci,ba yanda zatayi dole ta d'auki cokali tafara ci, bai kuma bi takanta ba ya ci abincinsa da dukkan kayan abincin ya mik'e ya koma saman kujera, ya bud'e jakkar aikinsa, ya d'akko wasu book's yana dubawa.
Ta d'an ci abincin ta tattare kayan takai kichin,
Ta dawo ta haye gado ta kwanta, shikam yanata bin cikensa har wajan kar fe 2:pm sannan ya mik'e yaje kan gadon daga gefenta ya kwanta yay addu'a sai barci.....


billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *