check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 30

AUREN K'ADDARA
             ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 


30 «*****» da asuba dady ya tashi, sai da ya tada ita sannan yafice yaje b'angaren sa yay alwala yasaka jallabiya ya nufi masallaci, koda ya dawo b'angarensa ya wuce yay kwanciyar sa.

Munneerah ko da ta idar da sallah saita d'akko AL'KUR'ANI ta hau karatu, dan bata iya barcin safe ba,sai da agogo ya nuna 7:am sannan tai addu'a, ta tashi ta gyara d'akinta fes ta had'a masa book's d'insa da wayoyinsa waje d'aya ta adana masa, ta wanke bayinta, ta dawo falo ma ta gyara ta bad'e gidan da k'amshi, mai dad'i.

Kichin ta nufa tana nazarin mizata fara dafawa yau amatsayin ta na amarya,🤔 can tai murmushi da alama ta tuna,dan haka ta hau aikin girki.

Sai wajan karfe 08:30 am, ta kammala, tajere k'ayataccen break  d'inta, a inda aka tanada dan cin abinci, 
Bayan ta gama ta nufi d'aki dan yin wanka.

Wajan k'arfe 8:30am shima dady ya tashi, yay wanka, ya shirya cikin jar shadda d'inkin zamani yayi kyau sosai sumarnan da sajensa sunsha gyara sai walkiyar mai sukeyi, yasaka turarensa mai dad'in k'amshi,
Ya fito hannunsa rik'e da farara riga da likitoci kesakawa.
Kaitsaye b'angaren Munneerah yanufa......

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *