check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 46

AUREN  K'ADDARA
              ko  BIYAYYA

Na billkisa ibrahim 

46 «******» husna tatashi abarci tafito falo tana mik'ar tashi da hammar yunwa, karaf idonta akan tiren abincin da Munneerah ta ajiye, ta k'arasa da sauri wajan tana bubbud'e kwanikan abinci wani k'amshi mai dad'i yadaki hanacinta, tace "wow" waya ajiye abincinnan??
   Tanana tsaye ikileema ta shigo, ta k'araso da sauri husna a'ina kika samu abinci??
       "Kedai bari wallahi nima yanzu nake jajen wanda ya ajiye"
Munnerah ta shigo da sallama, suduka suka bita da kallo a wulak'ance, tace ina kwanan ku??
Ba wadda ta amsa mata saima tsaki da ikileema taja, husna tace to 'yar shishahigi miya kawoki b'angarena??
      "Munneerah ta raunana murya kiyi jakuri anty husna dama cazan muku ga abincinan"
    "Gabad'ayansu sai jikinsu yay sanyi, amma dan karta ganosu sai husna tace to munji ga hanya nan, tafad'a tana nuna hanyar fita.
     Munnerah tafito tana murmushi, nace baiwar ALLAH kenan.
 Muta nan naku kuwa sai suka zauna suna kwasar gara suna santi dayaba girki ko dad'in abincinne yasasu mance wacece ta dafa.

Darana takuma dafa wani lafiyayan abincin akakaiwa dady office, bata yi zuciyaba ta kaimaau ikileema suma.
~~~~~~~~~~
Dady yay hon maigadi ya bud'e masa k'aton get d'in ya shigo saida suka gaisa da mai gadi sannan ya ida shigowa.
 6an garensa yanufa, yarage kayan jikinsa, kamar yanda tasaba yauma ta had'a masa ruwan wanka daketa tashin k'amshi, yashiga yay wanka yana maijin dad'in ruwa, yaudai koda ya shirya sai yanufi masallaci dan yaji anakiran sallah.

Saida akai isha'i yadawo gida, 6angaren Munneerah ya wuce, su husna dake zaune  suna jirnsa afalon Munneerah, bayan sun gama zaginta da cimata mutunci, tanata kuka amma tanaji sallamar dady cikin  dabara ta goge hawayen, lokaci d'aya suka mik'e, ita tana masa sannu dazuwa, sukuma suna aikin kallonsa............


billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *