check your best novels here

Monday 20 February 2017

NI DA AMINIYATA!!! 47 to 51

[18/11/2016 12:08] bilyn Abdul: 18~November~2016




NI DA AMINIYATA!!



NA BILKISA IBRAHIM



47

..........wannan ranar tazoma Sopy cikin farin ciki, domin kallo d'aya zaka mata kagane tsantsar farin cikinta, har a dani (dinning) takasa b'oye farin cikinta.
    Uncle G! Yabita da kallo, cikin muryarsa mai taushi da amo ya ce, "Sopyna wai yau miya sakaki cikin farin ciki ne??
   Sopy tayi wani murmushi wanda yasa kuma tunta lotsawa ta ce, "hubbina ina farin ciki yau zan koma makaranta, ALLAH bazan iya misalta maka yanda nakeson karatuba.
    Ya murmusa, yana kallonta, sai kuma yad'an  had'e rai, cikin tsoro sopy ta ce, "uncle yaya dai, saida ya kurb'i tee sannan ya ce, "aii inaga sai sati nasama zaki koma, dan yau inada wani uzuri bazan shiga makaranta da wuriba.
   aii mutuniyar taku saita fashe da kuka kawai, uncle G! baisan sanda dariya ta kufce masaba, ganin haka sai sopy ta k'ara k'arfin kukanta.
    Uncle G! yataso yakama hannunta yana dariya, yad'an tsagaita da dariyar ya ce, "kinga nifa wasa nake miki sarkin shagwab'a, tashi mutafi danni na k'oshi ma, ya mik'ar da'ita yana fad'in tashi autar inna tashi karmu makara.
   Duk abunnan dasukeyi fareeda tana wajen, amma tayi kicin2 da rai, dan ita lamarin bai birgetaba.
   Sukace mata sai sun dawo, batareda sun jira amsartaba suka fice.
   Amota uncle G! ya ce, "Sopy!!.
  Ta ce, "na'am.
Ya ce, "inagafa yakamata mu maida fareeda gida dan su baba su san aurenta ya mutu, bai kamata mubarta annan ba batareda kowa ya saniba, kuma sainaga kwana biyunnan kamar bata cikin walwalarta.
   Sopy tad'an gyara zamanta, sannan tajuyo tana kallon uncle G! da idanunsa ke kan titi ta ce, "gsky kafad'a uncle, saidai wlhy ina fargabar zuwa gida nace fareeda tana wajenmu, dan bammanta yanada suka rabuda iyayentaba da 'yan uwanta.
   Ya d'an juyo ya kalleta tareda k'ara dafe sitiyari, ya maida kallonsa ga titi yana d'an murmushi, ya ce, " karki damu, insha ALLAHU babu abinda zai faru, kuma nasan zasuyi miki k'yak'yk'yawar fahimta.
   Sopy ta ce, "to ALLAH yasa.
  Ya danna kan motarsa cikin marantar yana fad'in amin.
   Tunda motar tashigo su Nadiya suka nufota, dan sun san harda sopy.
  Uncle G! ya juyo yana kallon sopy ya ce, "banda yawo, banda magana da maza inhar bata kama doleba.
   Sopy tayi murmushi tareda fad'in ALLAH ngd maka daka azurtani da samun miji mai tsananin kishina.
    Yay 'yar dariya shima ya ce, "ALLAH ngd maka daka bani mata mai jin maganata, suka tuntsure da dariya, a dai dai wannan lokacin ne kuma su Nadiya suka k'araso.
   Su Nadiya suka gaida uncle G! Ya amsa yana tambarsu ya gajiyar ranar, sukace aii babu wata gajiya.
   Ya ce, "to masha ALLAH, ya nuna musu sopy yana fad'in ga amanata nan nabaku, karku yarda wani abu ya tab'ata.
   Sukace to mun karb'a.
 Yay nufi office yana fad'in saikin jini.

Suma aji suka nufa, dayake sopy tasaka nik'af babu wanda yaganeta, sai wasu tsurari dasukaga sanda uncle G! ya ajiyeta amota.
    Ahaka wani malami ya shigo yay musu lecture, bayan fitarsa babu dad'ewa uncle G! yashigo, tunda yashigo idanunsa akan Sopy, wannan yasa wasu d'aliban suka zargi wani abu.
   Sopy kama duk kunya tarufeta yanda taga yawancin d'aliban sun zura mata idanu suna son su san wacece??,  dahaka yagama ya fice.
   Wad'anda suka kasa jurewa saida suka tambayi zaliha wacece? Itako ta ce, "musu matarsace safiyya.

   Bayan fitarsa yanufi office, wasu 'yammata uku dake zaune jikin wata bishiyya suka bishi da kallo, d'aya ta ce, "wai dan ALLAH khadija shi wannan malamin waye?, nakula yacika jin kansa dayawa.
    Wadda aka kira khadija ta ce, "sunansa malam youseef hussain Ahmad, amma ana kiransa uncle G!, wannan dakikeji dagani a kwai ilimi, sai girman kai, shiyyasa 'yammatan makarantar nan suka mutu akansa, shikuma yana wulak'antasu, akwai wata kairat 'yar mai kud'ice ina gaya miki, ga k'yau, ta mutu a sonsa, amma mutuminnan yayta wulak'antata, daga k'arshe ma babanta sai America ya maida ita take karatu.
   Wadda tayi tambayar ta tab'e baki, ince hala shima d'an masu kud'inne??.
   Khadija ta ce, "wlhy talakane tib'is, shegen girman kaine kawai yake d'awai niya dashi.
   D'ayar datak'i saka musu baki tun d'azu ta ce, "nikam wlhy ina son mutum mai ra"ayin kansa,  dan irin wannan auren na kwad'ayi bashida wata riba, saima raini daga dangin matar, yanzu bagashi yayi aurensaba.
    Zainab tai saurin cewa "o, dama yanada mata??.
   Khadija ta tab'e baki, yayi aure wata d'aya daya wuce, karkiga matar batada wani k'yau sosai, kullum cikin hijjabi kamar d'iyar limamai.
   Zuh'rah tayi dariya aii haka shine dai dai, dankuwa shine mutuncin d'iya mace, su wad'ancan masu ikirarin suna son nasa, dasun suturce jikinsu daya sosu, kuma aii ba k'yau bane abinda yakamata mace tayi alfahari dashi, k'yawun hali da tarbiya sune babban jigon rayuwa.
   Khadija da taji haushin maganar zuh'rah ta ce, "zainab tashi mutafi, dan nakula itama sonsa takeyi.
   Zuh'rah tayi dariya, aii uncle G! abin sone ga kowace 'ya mace, domin yahad'a dukkan abinda mace take buk'ata, kema kanki kinsha aika masa da wasik'ar soyayya, rashin amsa tayinkine yasa kikejin haushinsa, dan nasan har hotonki wlhy kin tab'a aika masa, kuma itama zainab d'in ta k'yasane shiyyasa ta tanbayi koshi waye??.
    Cikin jin haushi khadija ta ce, "banza kawai saiki saka lasifika ki fad'a, taja hannun zainab suka bar gurin.
    Zuh'rah ta tuntsure da dariya tana fad'in 'yan rainin wayo, ku k'yawunne daku?, kowacce fuska kamar d'uwawu.

Sopy suna zaune da Nadiya tanad'an nuna mata ayyukan da akayi bata nan, saitaji wayarta tana wringing, ta ciro a jaka ta duba, saitaga uncle G! ne, ta d'aga tana d'an murmushi.
   Ya ce, "ki sameni a office yanzu, kafin ta ce, "wani abu ya kashe.
   Nadiya ta ce, "yaya dai??.
 Sopy tad'an ya tsine fuska ta ce, "wai uncle G! ne yake kirana.
    Nadiya tayi dariya, aii sai atashi a amsa kiran mai gida.
  Sopy ta harareta Nadiya kema sokike ki koma teema ko??.
   Nadiya ta girgiza kai tana dariya.
   Sopy ta mik'e domin amsa kiran hubbin ta.
    Deexerh ta ce, "aunty bily! Badai soyayya zasu yimana a makarantaba.
   Naja hannununta ina fad'in taho mu bita dan kar abarmu abaya, sanda muka iso har sopy ta kwan kwasa k'ofar yabata izinin shiga, mukayi wuf muka shige muma.
   Uncle G! dake zaune yana rubuce2 ya d'ago yana kallon sopy, fuskarsa d'auke da murmushi, ya ce, "sama k'ofar key, muka kalli juna nida deexerh mukace asama k'ofa key kuma???.
   Sopy ta kulle k'ofar sannan ta nufeshi, deexerh ta ce, "aunty sopyn nanmafa 'yar duniyace, na d'an murmusa dan jin furucin deexerh.
   Har zata zauna a kujerar dake kallonsa ya ce, "zonan, ba musu ta je wajensa, saman cinyarsa ya jawota, yasa hannu ya d'aga nik'af d'in, ya ce, "nima da nik'af d'in za'azo wajena??.
    Sopy tayi farrr da idanu ta ce, "ba kaine kasaka dokarba, ya sumbaci lab'anta yana murmushi, to aii banda ni acikin dokar ko???.
    Sopy takai hannu ta shafa fuskarsa tana wani d'an murmushi ta ce, "to, ayi hak'uri.
    Yanda take masa maganar dakuma shafa fuskarsa saiyasa jikinsa yay sanyi, batareda yashirya ba ya had'e bakinsa da nata, yaukam ba'a bar sopy abayaba, dan itama maida murtani takeyi, wannan yasa suka d'au dogon lokaci suna kissing d'in juna, sopy ce tafara janye bakinta, suka kalli juna itadashi, idanunsa sun d'anyi jaa, tayi murmushi tareda sinne kanta a k'irjinsa.
    Ya kuma run gumeta yana murmushi, ya ce, "saida kika gama tsotseni sannan zakiji kunya?.
   Ta ce, "kai uncle kana bani kunya.
  Yayi dariya to nadaina baki kunya, dan kar gobe akasa sumbatata, ji sukayi ana kwankwasa k'ofa...
   Sopy ta tashi da sauri ta maida nik'af d'inta sannan taje ta bud'e, malam faruk ne, ta gaidashi sannan ta fice.
    Malam faruk yak'araso yana fad'in kaida waye haka??.
   Uncle G! ya kwantar da bayansa jikin kujera yana fad'in kai atunaninka nida wa zaka gani a office a rufe??.
    Malam faruk ya zauna yana dariya, ya ce, "ito, sai dai kaida safiyya amarya.
   Uncle G! ya ce, "to itace.
Malam faruk ya tuntsure da dariya, amma mutumina ALLAH ya shiryaka, soyayya har a makaranta, to mima kukeyi a office.
    Uncle G! ya ce, "duk abinda zuciyarka tabaka, to shi mukeyi d'an sa ido.
   Malam faruk yay dariya ya ce, "ALLAH dai ya shiryaka youseef amma aii kayi hak'uri dai ku koma gida.
   Uncle G! ya ce, "kai d'an iska idan babu abinda yakawoka tashi kakama gabanka, dama kazo ka katse mini jin dad'i.
    "O, wai da gsk ne??, malam faruk yafad'a.
   Suka tun tsure da dariya suduka, uncle G ya ce, "faruk kananan baka canjaba wlhy ka iya gulma kamar mace.................    ........




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[19/11/2016 15:09] bilyn Abdul: 19~November~2016




NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM



48

...........Akwana atashi babu wuya gurin ALLAH, yau satin Sopy d'aya da komawa makaranata, kullum takan tashi kamar yanda ta saba ta had'a musu break, idan tana da lectures d'in safe sai su tafi tareda uncle, idan kuma batada shi sai yatafi, daga baya ta bishi.
    A b'angaren fareeda kuwa tana nan tana shirya abubuwa masu yawa akan uncle G! Dan kullum tana yaudarar zuciyarta akana wataran zata iya mallakarsa amatsayin miji, na ce, "lallai kina da aiki 'yammata.
    Yauma sopy ita kad'ai ta girka abincin rana, dan fareeda ta tsiri barcin rana, Sopy bata damu da hakanba, dan dama bataso fareeda tana tayata akan aikin gidanta, tagama tsaf tagyara gidan, yau kam a d'akin uncle G! tayi wanka, tadawo d'akinta ta shirya.
    Babu dad'ewa uncle G! yadawo, dan yad'an fita, ta taroshi kamar yanda tasaba, takawo masa ruwa yasha sannan tarakashi bayi yay wanka.
   Falo suka fito domin cin abincin rana, ya ce, "wai ina fareeda ne?.
   Sopy ta ce, "tana d'aki tana barci.
  Ya jin jina kai, badai tun barcin dana fita nabarta tanayiba?.
   Sopy ta ce, "wlhy tunshine.
Baice komaiba yaja kujera ya zauna, sopy tafara zuba masa abinci, fareeda ta fito kamar an jehota, tana wani murza idanu wai ita ta tashi daga barci.
   Uncle G! ya ce, "lallai yau kinsha barci, ALLAH yasa dai lafiya??.
   Fareeda tayi wani walay da idanu sannan ta ce, lafiya lau yaa youseef.
   Yanda tayi maganar sai ya k'ona ma sopy rai, wani abu yazo ya tokare mak'oshinta, da sauri ta d'auki ruwa tasha, uncle G! ya bita da kallon mamaki ya ce, "sopy yadai??.
   Ta girgiza kai alamar bakomai, ta tura masa filet d'in abinci gabansa.
    Fareeda tayi wani d'an murmushin samun nasa, taja kula tana zuba abincin.
    Laumar farko uncle G! ya had'e rai, yad'auki ruwa da sauri ya kora, ita dai sopy kallonsa kawai takeyi, ya ajiye cokalin ya dafe kai.
   sopy ta daure ta ce, "uncle lafiya??, yad'ago idanu cikin matuk'ar b'acin rai, ya ce, "kici abincin kiji mana.
   Jiki asanyaye sopy takai lomar abinci bakinta, wani irin aza babben yaji taji na fitar hankali, ko yarabawa dasuke shan yaji bazasu iya cin abincinba.
   Sopy ta dafe kai danjin ya sara mata, cikin masifa uncle G! ya ce, "to yau kuma miye sanadi?, ranar mun d'auka a matsayin kus kure, yau kuma amatsayin mi kikeso mu d'auka, duk maitarmu bazamu iya cin wannan yajin ba, wannan wace irin rayuwace, aii da ba haka kike girkinba ko.
   Sopy ta d'ago fuska shab'e2 da hawaye ta ce, "kayi hak'uri uncle G!, nidai nasan lafiya lau nayi girkina, wlhy bansan yanda akayi yajinnan yay yawa hakaba.
    Uncle G! yaja tsaki, ya ce, "to mikike nufi?, ko kina nufin wanine yazuba miki yajin?, naga dai gidannan mu ukune kawai,   a cikinmu waye zai zuba miki yaji a abinci? .
   Gaban fareeda ya fad'i rass.
 Sopy ta share hawaye, ta ce, "inma wani yake zubamin dan yahad'ani dakai tofa na barshi da ALLAH, tana kaiwa nan tatashi ta shige d'aki.
   Suduka binta sukai da kallo, shima saiya tashi ya shige d'akinsa cikin b'acin rai.
    Fareeda tayi 'yar dariya, tana fad'in 'yan rainin hankali kwadaiji dashi, tashi tayi tanufi d'akin sopy itama.
   Sopy tana kwance kan gado tanata rusar kuka, fareeda tashigo ta zauna gefenta, cikin sanyin murya ta ce, "sopy kiyi hak'uri, haka rayuwar aure ta ke, wani lokacin ayi farinciki, wani lokacin kuma kuka, sopy ta d'ago idanunta dasukayi jajur tana kallon fareeda, fareeda ta jin jina mata kai tana fad'in sopy gsky nake gaya miki, kuma nasan kema zaki fahim ceni.
    Batareda sopy tace komaiba ta maida kanta ta kwanta.
  Fareeda ta watsa mata harara harda gwalo.
   
Har dare gidan babu dad'i, sopy kuma tak'i dafa komai, tak'i shiga d'akin uncle G!, shima dai tunda ya shiga bai fitoba, fareeda ce kawai take cikin walwala.
   Sallar magribace ta fitarda uncle G! waje, saida akayi isha'i ya dawo, hannunsa rik'e da ledoji, fareeda ce kawai a falon, ya bata leda d'aya ya wuce da sauran d'akinsa, fareeda ta bud'e ledan tana wani murmun mugunta, namane ciki da kayan ciye2, tako bud'e tahau cin kayanta.
   Har wajen k'arfe goma sopy tana d'aki tak'i fitowa, uncle G! dake kwance bisa gado yanata juye2, yad'anja tsaki, azuciyarsa ya ce, "wai dama haka matan suke kamar zuma, ga zak'i ga harbi, ya tashi zaune yana bin d'akin da kallo, yay d'an murmushi yayinda idanunsa suka kai akan hoton su shida sopy, sunyi matuk'ar k'yau, kowannensu yana murmushi, atake yaji zuciyarsa ta huce, ya mik'e tsam yanufi d'akin sopy, har yanzu fareeda tana falon tana kallo, kallo d'aya yay mata ya d'auke kai, ya tura k'ofar yashiga, sopy tana kwance tana jinsa.
    Ya zauna kusada ita yana shafa fuskarta, itadai tana jinsa tayi shiru, ya duk'o da fuskarsa kusada tata har sunajin saukar numfashin juna, cikin taushin murya ya ce, "haba my sopy yau ba'ayi danine?.
   Ta janye fuskarta daga kusada tasa, tana turo baki gaba, ya kwanto ta bayanta, yana sassanyar dariya acikin kunnenta.
   Jitai tsigar jikinta ta tashi yarrr, ya sumbaci gefen kuma tunta, ta d'ago da sauri tana kallonsa, saita murgud'a masa baki, yayi murmushi yana fad'in nikike murgud'awa baki?.
   Tai masa shiru, sakkowa yayi daga gadon ya d'auketa cak, fareeda tayi saurin komawa saman kujera ta zauna, sopy kuwa sai watsal2 takeyi tana kukan shagwab'a wai ya sauketa bataso.
    Ya ce, "aii saimunje d'aki kin fad'amin wanda kika murgud'awa baki.
   Ta ce, "nifa bada kai nakeba, ya ce, "daga baya kenan.
   Fareeda ta rakasu da harara tareda jan wani mugun tsaki, dan bahaka tasoba.
   Uncle G! Ya jefa sopy saman gado, yay mata runfa da faffad'an k'irjinsa, bakinsa ya had'e da nata, yashiga nuna mata soyayya mai tsaftar gske, naja hannun hauwa'u, ina fad'in kinga zomuyi waje kafin uncle G ya koramu.
    Ta ce, kai bilki ki tsaya mud'an k'ara gani mana, na zaro idanu waje ina fad'in ALLAH ya shiryaki hauwa'u, daga samun lafiyarki, ko kinaso uncle G! ya maidaki gadon asibitine?, kijama janu d'an kuka.
    Sai da komai yalafa muka koma, tarar dasu mukai yana bata nama abaki suna ta hirarsu da dariya.
    Hauwa'u ta ce, "lallai bilki mai shiga tsakanin miji da mata yana tareda kunya.
   Na ce, "wlhy kuwa hauwa'u, hannunta naja muka nufi d'akin sopy dan mugano muku halin da fareeda take ciki.
     Saman gado muka tarar da ita, tana faman jan tsaki, na jin jina kai ina fad'in lallai wannan bata gajiba, dan na kula wani abu take k'ara shiryawa.
    Hauwa'u ta ce, " 'yar wahala, ni kinga mutafi muma wajan mazajenmu karmu lalace anan.


WASHE GARI
sopy ta had'a break tsaf, ta gara gidan, saidai yau na kula kamar akwai abinda take k'ullawa, dan sai murmushi takeyi, tana shiga wanka fareeda ta fito tanufi kichin d'in.
    Sopy suka gama shirinsu tsaf da uncle G! suka fito sunata zabga k'amshi, fareeda dake zaune afalon tun d'azu ta gaida uncle G!, suka gaisa da sopy, sannan suka nufi dini domin cin abinci, farida kuma saita nufi d'aki waizata d'akko abu.
    Sopy tagama had'ama uncle G! abinci ta tura gabansa, yako ja ya hauci, sopy tatattare kulolin datai amfani dasu tanufi kichin, nayi dariya, dan nakula sopy ta kwashe abincin sune itada uncle G! acikin wata kula daban, saita bar wani a d'ayar kular, tayi alamu kamar an d'iba.
   Tana dawowa ta tarar fareeda tafito, sai dai, sai kallon uncle G! take dayake cin abincinsa cikin kwanciyar han kali harma yana lumshe idanu.
   Taja kula itama tazu, ko kallon inda take sopy batayiba taja abincin ta ta hauci.
   Fareeda dai saicin abinci take tana matse idanu, gashi babu damar magana, tunda masu gidan basuce komaiba, saima hirarsu sukeyi, sai dai zuciyarta sai tunani take akan ya akayi basuji d'anbanzan sukarin data zuba a aciki abincin ba.
   Da haka suka gama, uncle G! yafita, sopy ma tatafi d'akinsa dan ta gyara, fareeda taja abincin da uncle G! yarage taci, saitaji lafiyarshi lau, tarike kugu tana fad'in wato matar nan boye musu abinci tayi kenan??.
   Sopy dake lab'e tana kallonta tayi murmushi kawai.
    Aka kwan kwasa k'ofa da sauri fareeda taje tabud'e azatonta uncle G! ne, amma saitaga su aunty Nafisa, da aunty hauwa'u, da aunty zainab yayarta, dakuma aunty Asiya matar uncle kabeer, cikin mamaki suke kallonta, itama dai cikin tsoro da fargaba take kallonsu.
   Tofa masu karatu,  koya zata kayane kuma, kukasance taredani danjin amsar tambayarku..........................
    



Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[20/11/2016 11:32] bilyn Abdul: 20~November~2016




NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM



49

..........Aunty zainab ta wankama fareeda mari, Wanda yasata zubewa awajan dafe da kumatu, cigaba tayi da dukanta tamkar uwarta, dak'yar su aunty Nafisa suka rik'eta, cikin matuk'ar b'acin rai aunty zainab ta ce, "kubarni naci uban wannan mara mutuncin, ita hartanada k'afafun zuwa gidan safiyya, saboda batada mutunci.
    Sopy tafito da sauri dan jin hayaniya, yayunta tagani tsai tsaye da alama babu lafiya.
    Aunty zainab ta tako har zuwa inda sopy take, tana fad'in wato sopy har kin farka daga magagin cin amana da yaudara irin na fareeda ko, tanuna fareeda da jini yake zuba ta hanci saboda dukan hancinta da aunty zainab d'in tayi, ta ce, "waccan dakike gani bom ce data tarwatsa rayuwarki abaya, kuma inada tabbacin yanzuma zata tarwatsa sabuwar rayuwar dakika kasance aciki, dan ita kaskace rab'u mai jini, data tsotse jinin jikinki saita barki da zallar ruwa, takama kafad'ar sopy ta girgiza tana kuka tana fad'in haba safiyya miyasa kika amince da wadda taci amanarki, miyasa kika amince da wadda tarabu da iyayenta akan d'ana miji, itace sanadin kamuwar mahaifinmu da ciyo mai muni, itace ta haddasa bak'in ciki a family namu wanda bazamu tab'a mantawa dashiba, itace tasa mutane sukema gidanmu kallon masu k'arancin tarbiya, miyasa kika yarda mak'iyyarki wadda bata sonki dan ALLAH, Aunty zainab ta durkushe awajen tana wani irin kuka mai ban tausayi, itama sopyn saita take mata baya, suka rungume juna suna kuka.
    Suma sauran sai matsar hawaye sukeyi, fareeda kam tana gefe tana jiyyar kanta, ahaka uncle G! yashigo yasamesu, ya tsaya turus yana kallonsu da mamaki.
    Dak'yar ya iya furta tambayar waye ya mutu????.
    Gaba d'ayansu suka d'ago kai suna kallonsa, sopy tazo da gudu ta shige jikinsa, ya rungemeta tsam yana lallashinta, bayan kamar minti biyar ya cirota daga jikinsa, ya ce, "Sopy miya farune wai??, ko wanine ya rasu??.
    Sopy ta girgiza kai tana hawaye, yasa hannu yana share mata hawayen yana fad'in kukan ya isa haka, fad'amin miyake faruwa??.
       Sopy ta nuna masa fareeda da hannu, fuska duk jini da alamun duka, kunsandai farin mutim, koyaya aka tab'ashi sai yanuna.
    Uncle G! yadawo da kallonsa wajen su aunty zainab, har yanzu kuka takeyi, aunty Nafisa taje ta d'agota ta rungume, tana bata hak'uri.
      
          Tsawon minti shabiyar, kowa ya nutsu, suna zazzaune a falo, harma Sopy tayi k'arfin halin kawo musu ruwa, fareeda kuma ta wanko fuskarta.
    Uncle G! yay musu sallama suka amsa, sannan yad'ora da tambayar abinda yafaru.
    Aunty Nafisa ce tasanar masa da komai, ta d'ora dafad'in, mukammu abin yabamu mamaki, dan bamuyi tunanin ganin fareeda ananba, dukda dai agida ana nemanta, saka makon mijinta yaje har gida yafad'ama iyayenmu cewa yasaketa har saki uku.
    Uncle G! yaja numfashi sanna ya d'ora da fad'a musu yanda ya samo fareeda har zuwanta gidan da zamanta, dakuma hukuncin dasuka yanke na maidata gida, amma sopy ta ce, "tana jin tsoron hakan, dan bataso akasa fahimtarta, yaci gaba da fad"in amma ina mai baku hak'uri akan kubar fareeda domin tayi nadamar abinda ta aikata, Sopy ta ce, "azuciyarta zadai tayi nan gaba, dan mai hali baya canja halinsa uncle.
   Uncle G! ya ce, "kutan bayi Safiyya tunda fareeda tazo gidannan bata tab'a aikata mana wani abu wanda bai daceba, dan haka ina rok'onku kuma ku yafe mata, kamar yanda Safiyya ta yafe mata, inada tabbacin hakan zai taimaka mata wajen k'ara samun gyaruwar halayenta, ku kuma zamo mana 'yan jagora wajen nema mata gafara gasu baba da mama.
    Aunty zainab ta ce, "ban katsekaba yaya youseef, amma nasan har yanzu fareeda batayi nadama ba, wlhy nasan tana nan tana k'ulla wasu sababbin makirce2n nata, nasan fareeda sosai, tun muna k'anana nake fuskantar mugun halinta, nasan fareeda tafi shak'uwa da Sopy fiye da kowa acikinmu, amma nafi Sopy sanin halin fareeda, dan Sopy ta yarda da fareeda, kuma batada yawan saka idanu akan d'abi'un fareedar.
    Aunty Nafisa ta ce, "A'a, zainab tunda ya ce, "tayi nadama bakuma ta tab'a aikata wani abu dazai shiga tsakaninsuba to yakamata muyafe mata, mukuma yimata addu'ar k'ara samun shiriya.
    Nandai sukaita rok'on aunty zainab har ta sakko, ta yafema fareeda, dan saida fareedar ta gurfana agabansu tana neman afuwa, Na ce, "shegiya kamar har zuciyarta.

Yaudai anan suka wuni, Sopy tayi musu abinci mai dad'i da gamsarwa, sukasha hirarsu ta yaushe gamo, sopy ta ce, "aunty Asiya yaushe zaki haihu?, Aunty Asiya tayi murmushi ta ce, "sai watan gobe Safiyya.
   Sopy ta marairaice fuska ta ce, "dan ALLAH ki lallab'i uncle kabeer yabar uncle yakaini naga su inna, dan ya ce, "wai saikin haihu zan fara fita.
    Aunty hauwa'u ta ce, "A'a bakin koma makarantaba??, Sopy ta zumb'uro baki gaba tana fad'in, to makarantar da ga ita ina nake zuwa,?.
    Dariya sosai tabasu, Aunty zainab ta ce, "aii ko autar inna saidai kiyi hak'uri, dan muma duk haka akaimana, ta ce, "tab nikam wlhy nagaji, aii zama guri d'aya tsautsayi inji kifi, suka tun tsure da dariya suna tsokanarta.
     Fareeda kuwa tana d'aki ta kume kanta, dan taji zafin dukan, zuciyarta ta ce, "karki damu fareeda dama abu mai daraja ba'a samunshi abanza, sai ansha wahala, inda zaki bini daki2 dana fad'a miki hanyoyin dazakibi ki mallaki uncle G!.
    Na ce, "hummm naga wannan 'yar akuyar har yanzu bata san inda duniya ta nufaba.
    Gani nai tana zuba murmushi, alamun karatun da zuciyar tata takaranta mata yayi mata dad'i, kuma ta karb'eshi hannu bibiyu.
    Lallai idan zaka gina ramin mugunta tofa ka ginashi gajere, dan idan aka samu kus kure tofa kaizaka fad'a ciki.

saida akayi la'asar sannan  suka tafi, tareda alkairi mai yawa daga uncle G!.
   Bayan tafiyarsu Sopy ta shiga d'akin uncle G! Yana zaune yana duba wasu books, ta zauna gefensa, ya d'ago manyan idanunsa farare tas yana kallonta, tayi masa sassanyan murmushi, ya kanne mata ido d'aya shima yana mayar mata da murtanin murmushin nata.
     Ya rufe littafin yajuyo gareta, ta ce, "hubbina ka daina karatunne??, ya jawota jikinsa yana fad'in ai idan kina guri sopyna banida lokacin komai sai naki, kin zamomin magana d'isun da kan kama zuciyata da matuk'ar sauri idan kika kusantota, idan kuma bak'ya kusa tofa zuciyata tana tareda ke, dan gangar jikina kaiwai kike barmini, yakama yatsun hannunta yana wasa dasu, yak'ara kashe murya ya ce, "Sopyna yaushe zaki bani magajinane??.
    Sopy tasaka hannu ta rufe fuska dan kunya.................




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[20/11/2016 13:06] bilyn Abdul: 20~November~2016



NI DA AMINIYATA!!!




NA BILKISA IBRAHIM


50

...........Uncle G! Yay murmushi yana fad'in Sopy sarkin kunya, daga tambayar baby sai aji kunya..
   Tayi k'ok'arin mik'ewa zata gudu uncle G! yakuma matseta, ta ce, hubbina aikifa zanje nayi, yaja hancinta yana fad'in ainanma aikin kikeyi, ta ce, "aikin mi nakeyi anan?, ya ce, "na bama youseef farin ciki mana.
    Sopy tayi murmushi, ta ce, "uncle wai yaushe zamuje Gurum??.
 ya ce, "kinaso mujene??.
 ta ce, "emana inaso naje na gaida su gwaggona.
   Yay murmushi to shikenan zamuje, amma kibari sainan gaba, dan su aunty hafsat sunce zasuzo ranar juma'a.
    Cikin matuk'ar farin ciki ta k'an k'ameshi, ta ce, uncle dgsk kakeyi dan ALLAH?.
    YA CE, dgsk Sopyna, sunce zasuzo suyimana kwana biyu, ta ce, harda Aysha?, ya ce, eh harda ita.
   Kai wlhy naji dad'i sosai, tatashi tana fad'in bari kaga naje nafara shiri.
   Ya bita da kallo yana murmushi, akullum tamkar k'ara masa son Sopy akeyi, yakanji kamar babu mata aduniya sai ita kad'ai, komai na yarinyar abin sone.

^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
Akwana atashi babu wuya gurun mai duka, komai yana tafiya yanda akeso, Sopy tana samun farin ciki awajen mijinta, takanji babu yashi a rayuwarta.
   To shima a b'anfarensa yakanji babu tankar Safiyyar, kullum burubsu su farantawa juba, takan tsara masa abinci mai gam sarwa dasaka nishad'i, kullum tana cikin kwalliya ta d'aukar hankali, ta bad'e gidanta da jikinta da k'amshi, kullum burunta tayaya zata farantawa mijinta.
   Bata wasa da samo hanyoyin rik'e miji, dan haka bily ta sakata a groups masu dama, takan tsinci abubuwan k'aruwa acikin HAUSA NOVELs masu yawa, dan kowa da irin baiwar rubutun da ALLAH yabashi, idan dare yayi su kashe junansu da soyayya itada HUBBIN ta.
    Uncle G! yana matuk'ar alfahari da ita.
    Matsala d'aya take fuskanta, itace fareeda, dan yanzu fareedar tafito dawasu salo2 na rainin hankali, sai lokacin data fuskanci sun kusa dawowa saita ci kwalliya ta zauna a tsakar gida, da sun dawo itace zata bud'e musu get tana kwar kwasa, suna shigowa falo zatayi saurin kawoma uncle G! ruwa ko lemo, da daddare kuwa tana nane dasu a falo, har saitaga sun shiga sannan take tashi, takan k'ir k'iri dafa wani abu takawoma uncle G! wai yaci, idan suna hira, taringa wata kwar kwasa da kwantar da murya kamar tana kusada mijinta,ko sopy ta gwaleta tofa bata nuna jin haushinta, wani rainin hankali kuma data d'auka shine datayi isha'i saitayi shiri cikin kayan barci tazo ta zauna falo suna hira.
   Wannan lamari yana k'ona zuciyar Safiyya.

    Yauma suna falo suna hira, uncle G! yana kwance saman doguwar kujera, yayinda sopy take zaune a k'asa saitin kansa tana cin tuffa (Apple), fareeda kuma tana saman kujera tana satar kallon uncle G!, wandashi bama ta isheshi kalloba, sopy tana kula da ita.
    Zuwa can sopy ta ce, "wayyo ALLAH hubbina??, uncle G! ya juyo da sauri yana kallonta, ya ce, "ya akayi Sopyna?, cikin shagwab'a ta ce, "jinayi kaina ya sara.
    Ya tashi zaune yana fad'in zona yimiki kamu, dan bana son kisha magani, saboda gudun ganganci, bansaniba ko nayi ajiyar baby.
    Sopy ta mike da nufin zama kusa dashi, amma saiya jawota saman cinyarsa, ta ce, "ngd hubbina.
   Yayi murmushi yana fad'in wannan aikinane, addu'a yafara yi yana tofa mata, bayan ya gama tawani kanne masa ido d'aya tareda d'aga masa gira.
   Aii sai jikin mutumin  naku yasaki, kwata2 ya manta da wata fareeda afalon, saiya had'e bakinsa da nata, yashiga sumba tarta cikin nuna kwarewa, Sopy saita bada kai bori yahau, sunkai tsawon lokaci suna abu d'aya, zuwa can yashiga shafata.
    Wani kududun bak'in ciki yatokare zuciya fareeda, ta had"iye wani mugun yawu wanda yasakata sark'ewa tafara tari.
    Sai a sanna uncle G! yatuna akwai wata halitta fareeda a falon, suduka suka d'ago suna kallonta, sopy tayi wani murmushi mugunta, tad'aga yatsun hannunta biyu tama fareeda sorry, cikin wani murmushin rainin hankali ta ce, "sorry fareedana, munata soyayya agabanki, kinsan hubbina ya iya mantar dani duniyar dana ke ciki, wlhy nama manta kinanan, ta sumbaci hannun uncle G! sukaima juna murmushi.
    Jin kalamun sopy na rainin wayo sai suka saka zuciyar fareeda kumburo wa, jita ke mar zata fashe, har fuskarta saida ta nuna alamun b'acinrai.
    Sopy ta ce, "hubbina?
Uncle G' ya ce, "na'am sopyna.
               Ta ce, "yakamata kasiyoma fareeda tv sai asaka mata a d'akina, dan bai kamata tana zama damu a falo muna tayar mata da hankaliba, kasan gwauro bai iya shiga matsalaba, gashi kuma babu mai taimaka mata.
    Uncle G! ya sumbaci bakin sopy ya ce, "gsky ne sopyna, insha ALLAHU zanyi k'ok'arin hakan, dan nima nakula tana shiga damuwa da takura.
     Fareeda tak'ara kumewa dajin kalamun sopy da uncle G!, ta kulama sun raina mata hankali, da sauri tatashi tana hawaye ta shige d'akin sopy.
   Sopy ta bita da kallo tana 'yar dariya, ta mik'e tana fad'in hubbina bari najiyo miye damuwar "AMINIYATA!!!!!;".
   Uncle G yabita da kallo yana murmushi, yasani sarai bak'ak'en magan ganu sopyn tagawa fareeda.
    A can kuwa sopy tana isa tabud'e d'akin ta shiga, agado ta tarar da fareeda tana kuka, sopy tad'an tab'e baki sannan ta k'arasa gaban gadon tana tafa hannuwa, ta ce, "fareeda kenan nakula ke har yanzu d'aukata kike amatsayin safiyya sakarai, fareeda!! Tabas abaya kinyi nasarar kwace Abdul daga hannuna, to ki d'auka awanna lokacin kece kikayi winning d'in game d'in, nikuma nasamu game over.
    Amma saidaifa awannan karon ta canja zani, domin nima da shirina nazo fagen famar, kisa azuciyarki uncle G! nawane nikad'ai, babu wata kucakar mace data isa naraba son youseef da ita, karki d'auka wani ban k'aro k'irjinki da saka kayan barci kizauna agabansa zai ja hankalinsa a kanki, 'yammatan dasuka fiki ilimi da wayewa ma sunyi abinda yafi haka amma basuci nasaraba.
   To kema inaso ki d'auka aranki bazaki tab'a yin nasaraba, tuni nasan kece kike zubamin gshiri, yaji, sukari acikin abinci, fareeda son gsky babu abinda yake rusashi, nida uncle G! son gsky mukema juna bana sha'awa ba, dan haka ki daina wahalar da kanki wajen hangen zaki iya rusa wannan soyayyar, bare harki samu damar mallakar mijina.
    Sopy tayi wata 'yar dariyar k'eta, ta ce, "lallai yau nayarda da batun aunty zainab, datace ke kaskace rab'u mai jini, kuma ke bom ce, tofa saidai ki d'auka awannan karon remote d'in bom d'inki yana hannuna, idan nagadama saina danna ki tarwatse, dan haka ki dawo da han kalinki jikinki, tun kafin kiyi asararsa, ki daina biyema shed'aniyar zuciyarki datake d'ora miki karatun da babu fassara, inko ba hakaba kina gab dashiga makarantar dana sani.
   Tana kaiwa nan tafice abinta.

Fareeda tana kwance kamar gunki, zuciyarta cike da mamakin kalam safiyya, wai yaushe sopyn ta waye?, ya akayima tagano sirrikan zuciyarta haka?, lallai yau sopy tagaya mata magan ganu masu ciwon gsk, irin wanda babu wani mahaluki daya tab'a gaya mata kwatan kwacinsu, ta dun k'ule hannu ta naushi iska, da sauri nafito ina tuntsura dariya, dan karta maujeni nima, tabar mijina da jinya.  
    D'akin uncle G! na nufa, amma saina tarar sun rufe k'ofa, dan haka na nufi hanyar fita, dan bazan koma wajen fareeda 'yar mahakaciya ba ta bibbigeni abanza, gobe nakasa kawo muku rahoto......................



Assalamu alaikum, ina mik'o d'umbin gaisuwa ga dandazon makaranta littafin ""NI DA AMINIYATA!!!,""  ina muku fatan alkairi a duk inda kuke, ina kuma gdy da k'aunar da kuke nuna mini,, ALLAH  yabarmu tare, ya had'amu a ALJANNARSA baki d'aya.

   acigaba da gashi!!!!!!!!!!!!!!!!...



Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[21/11/2016 15:01] bilyn Abdul: 21~November~2016




NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM

51

...........WASHE GARI. Fareeda kasa fitowa tayi, har sukayi break bata fitoba, Uncle G! ya ce, "Sopy yau kuwa lafiya naga fareeda bata fitoba??.
    Sopy tad'an murmusa tareda fad'in lafiyarta k'alau, k'ila ta k'oshine.
    Uncle G! yad'an tsura mata idanuwa, domin son gano wani abu, amma sai Sopy ta kauda kai tana dariya, shima saiyayi dariyar ya ce, "miya baki dariya sopyna?.
    Sopy ta ce, "kaine kabani dariya, dan naga ka kafeni da kallo kamar a kotu.
    Ya ce, "Sopyna baki da dama kema, nakula randa natashi k'ara aure zamusha fama, dan kinada kishi, ya k'arasa maganar cikin tsokana.
   Sopy ta d'aure fuska tamau.
    Uncle G! ya tuntsure da dariya, harda buga kai, yadawo kusada ita, yadafa kafad'ar ta kinga sopyna dawasa nake miki, ke kad'aice matar youseef daga ke babu k'ari.
    Sopy tad'an turo baki tana fad'in nidai ban yardaba.
   Ya jawota zuwa jikinsa ya ce, "mikike so nayi miki dan ki yarda??, ta d'ago tana kallonsa, ta ce, "kayimini alk'awari.
    Yad'an kafa mata idanu na tsawon minti biyu, saikuma ya lumshe idanunsa ya bud'e, ya jinjina kai yana fad'in ni youseef nayi alk'awarin kasancewa da safiyya har k'arshen rayuwata, kuma ita kad'ai amatsayin matata, saidai idan wata k'addara ko jarabawa takawo sab'anin haka a rayuwarmu.
    Sopy ta rungumeshi  tana murmushi, ta ce, "nima hakan take a gareni hubbina, ALLAH kuma yabamu ikon ruk'e junanamu da hak'uri da juriya.
   Uncle G! ya rungumeta yana fad'in amin ya Rabbi sopyna.

Zan iya cemuku dai ayanzu fareeda tad'an fara shiga hankalinta, dan tad'an rage aikata wasu abubuwan saidaifa har yanzu tanan akan bakanta nason mallakar uncle G! amatsayin miji, to itamadai safiyya tanan tana tanadar manya2 makaman yak'ar fareeda, dankuwa kulum tana tashi da shirin kota kwana.

Yaukam sai k'arfe biyu sopy tashiga makaranta, dan batada lecture d'in safe, sai sauri take dan tasan uncle G! yau zaimusu lecture karfe biyu da kwata, cikin sassarfa ta isa class, amma saidai ta makaro, domin kuwa har uncle G! ya shiga.
    Taja birki ak'ofar class d'in kamar yanda makararu suke tsaye, tofa saimuce kallon ya koma sama, sai hankalin 'yan class d'in da makararru suka dawo kanta, kowa yana so yaga ikon ALLAH, jiyayi k'amshin turarenta ya yawauta agurin dan haka yad'an juyo ya kalli inda yake zaton take, sukaima juna kallon ido cikin ido, amma sai uncle G! ya basar yacigaba da lecture d'insa.
    Wani k'ududun bak'in cikin ya tokare mak'ogwaron sopy, gashi gabad'aya hankalin d'aliban yana kanta.
    Uncle G! ya juyo ya kalleta yana wani d'an murmushin mugunta, dukada fuskarta tana yane da nikaf wannan bai hanata murgud'a masa bakiba, ya maida kallonsa ga d'alibai fuskarsa d'auke da murmushi.
     Bayan ya kammala lecture d'in ya fito, hannun sopy yakama batareda yayi mata maganaba, sopy tayi k'ok'arin kwace hannunta, amma saita kasa, dan ba rik'on wasa yay mataba.
    Har cikin office d'insa ya kaita, sannan yasaki hannunta yajiginna da k'ofar ya hard'e hannayensa a k'irji.
   Sopy ta kauda kai gefe dan haushi, hannu yasa ya yaye mata nik'af d'in fuskarta, ta galla masa harar tana murugud'a baki, yasa yatsu biyu ya kamo lab'b'anta, yad'an matsesu waje d'aya, ta rik'e hannunsa tana k'ara, dan taji zafi.
    Uncle G! ya ce, "o, autar inna da zafine??, ta harareshi da idanuwanta dasukayi jaa, yasaki bakinta yana murmushi, hannu yasa ya d'ago fuskarta suna kallon juna, ya ce, "wannan shine gargad'inki, daga yau idan kika sake makara tofa hukuncin yafi haka yawa.
    Ta lumshe idanunta, wasu hawaye suka zubo bisa kuma tunta, wani tsadadden murmushi yasaki tareda sumbatar bakinta, ta bud'e idanu da sauri, suka zubama juna ido, daka gansu kasan kallon k'auna sukema juna, suka lumshe idanu alokaci d'aya kum suka bud'e, uncle G! ya rungumeta tsam zuwa jikinsa.
    Sopy ta ce, "a zuciyarta, uncle G! Kenan,  zuma ga zak'i ga harbi.
   
  Yau takasance juma'a, yaune kuma su aunty Hafsat zasuzo, gaba d'aya sopy ta rikita kanta sai aiki takeyi, domin tarbar bak'inta, ita dai fareeda sai kallon ikon ALLAH takeyi, hakama uncle G! binta kawai yake da kallon mamaki, dan ganin yanda taketa hidima kamar wasu bak'ine daban zasuzo basu libabatu ba.
      Wajen k'arfe d'aya da rabi uncle G! yatafi tarosu a tasha..............





Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *