check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 32

AUREN  K'ADDARA
               ko  BIYAYYA

Na billkisa ibrahim 

32 «******»saida ya fice ta koma cikin gida, ta d'auki waya ta kira 'yan biyu wai dan ALLAH suzo su tayata hira,

Shikam gogan naku koda yafita gidansu ya nufa, zuciyar sa fal tunanin wannan 'yar shilar yarinyar da ya raina, dukkanin abinda tai masa yau ya d'aure masa kai da kwanya, idan ya tuna su husna da ayyukansu,a tsawon shekara d'aya d'auka tare dasu amma ko maka mancin abinda yarin yarnan tai masa yau, basu tab'a yimasa ba, dai dai da d'akinsa sai dai shiya gyara, to bare girki, koda yake nasu d'akunan ma bagyarawa sukeyiba saidai masu aiki su gyara musu, yay hon mai gadi ya bud'e masa get, saida suka gaisa ya k'arasa cikin gidan.

Da sallama ya shiga falon, suna zaune a darning table, suna break, ya gaida iyayensa su kairat suka gaisheshi,
      "Babana taso kayi break mana !!
 Dady yay dariya dad nida abinci kuma ai sai na rana, yanzu kam akoshe nake.
Shima yay dariyar,  babana ina kasamu abinci??
yanzufa naji mom d'inku tanacewa su kairat suzo sukai muku break.

  A'a wlh mun hutash sheki mom ba sai an rik'a kaiwaba.
       "Matata ta iya girki"
Dad a tanbayi mai mata a ina yaci abinci, ya fad'a yana dariya
 Suma gaba d'aya suka tun tsire da dariya, ya mike shima yana dariyar kunga sai anjiman ku ni zan makara.

Dad yarage dariyarsa to kayi k'ok'ari idan aiki yayimaka sauk'i ko zuwa yamma ne kasa meni a office.
      "Yace to sai nazo"
"Mom sai anjima"
"To babana adawo lafiya" 
       Su kairat sukace yaya yanzufa zamu gidanka
 To sai kunje, kuna can har dare ko??
    "Eh har sai kadawo ma"
To shikenan ya fad'a yana fita

Yana isa asibitin ya fara shirin shiga tiyata bayan ya gama zagaya marasa lafiyar yana musu sannu da tanbayar su ya jiki, wanna kyawawan halayen nasa ya sashi yin fice asibitin, koya kake dady baya wulak'antaka ya iya tattalin mara lafiya da kwantar masa da hankali, in har baka da k'arfi, zai taimaka maka da aljihunsa da basirar sa, duk sanda ya iso asibiti sai ya zagaya marasa lafiya, yay musu sannu, mai buk'ar wani abu yay masa sannan ya dawo office yacigaba da duba marasa lafiya
Shidai barahi da shegen miskilanci kuma abun ajininsa yake.

To yauma bayan yagama zaga yensa ya shiga tiyata bakin sa da addu'oin neman nasara.......

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *