check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA page 5

AUREN KADDARA
              ko BIYAYYA


Na bilkisa ibrahim

 5 «******» ranar akawayi gari kawun alhaji el~mansur yarasu, mutuwar ta girgiza shi sosai dan kallon mahaifi yake masa, ga shi bai taba haihuwa ba, inna matarsa kuma tace zata koma yola, ba lallashin da baimataba taki, tace bazata iya zamaba inhar ba malam, suyi hakuri zata rinka zuwa akai akai, dubasu haka ya hakura ta tafi tabarsu da kewarta

   ******* rayuwa taci gaba da gudu tamkar yanda ruwa ke gudana ahanyarsa, dady ya kammala karatusa a kasar amuruka {American} yazama cikakken likeetan mata, tare da jabir aka kaisu amma shiyya ki maida hankali akan karatun sai neman mata kamar bunsuru, ga shaye shaye, acan dady yabarosa shi sainan da wata uku zai dawo,
Badiyya, da nuwaira, da nafisa duk sunyi aure, harma da yara,
Ikileema da husna sune 'yan mata yanzun suna karatu a kunbotso [SA'ADATU  RIMI COLLEGE] bama wani kokarine da suba sai girman kan tsiya da iyayi su adole 'ya 'yan masu kudi, yanzuma shawarar da iyayen sukeyi wai zasu kaisu gana suci gaba da karatu.
ABDUL'AZIZ  EL~MANSUR ADAM  ya zama cikakken namiji kyakkawa ajin farko, dole duk mace mai lafiya ta gansa ta kyasa, sai dai miskiline, amma yanada saukin kai da son mutane, sai dai baya kula mata,dan basa cikin 'yan kayansa, hasalima baya dariya agaban mace,yace yawan yima mace dariya yana kawo su rainaka, shikuma baya son raini.
'Yan biyu ma anzama 'yan mata suna (ss 3 )a school sune ke kokarin zana (s,s,c,e)awannan shekaran 
Ayau dady ya sauka kasarsa ta haihuwa kowa yayi murna da dawowarsa, barema kannansa 
Bayan yahuta suna zaune a palo shida iyayensa da kannansa suna hira 
Dady ya kalli dad, yace dad 'yanmatan kafa sunyi girma mikake basu kaida mom haka?? 
Dad yay murmushi yace babana kaima baga yanda ka komaba, kazama handsome,komai naka ya canja. Gaba daya suka saka dariya, kairat tace wallahi kuwa yaya ka kara kyau sosai, turai ta karbeka, dama muma mom tayarda dad ya kaimu muyi karatunmu acan wallahi, yaya dan allah kasa baki.
Dady yace a'a wlh koni ban yarda, akaikuba yanda ake lalata yaran mutane, ana koya musu rashin tarbiyya, ai bazan yarda akaimini kanne canba.
  Kausar tace yaya baka yarda damuba ne,yace nayarda daku, saidai kinga ku matane kunada rauni, yaci gaba ku gane abinda nake nufi, kuyi hakuri kuyi karatunku anan gida najeria kunji.
{An expert drier can also last long my dear sister's}
Sukace hakane yaya dama danmuga su husna zasune shiyyasa,yace to ina ruwan ku dasu,kuyi harkar gabanku kudai mana,to ko sudin ma wazai kaisu?? 
Kausar tace abban gidan su husna mana.yace to allah ya kiyaye hanya,ku dai kuyi zamanku akasarku  kuyi karatunku,duk inda mutum yake indai yasa kansa karatu to zaiyishi kunji.
Mom tace ato gaya musu dai, kila kai suji maganarka, danmu gani sukeyi bamuyi dai daiba.
Dady yace wlh kunyi dai dai mom, su wadannan mi suka sanine, game da duniya da yanda take tafiya. Haka suka cigaba da hirarsu cikin fahimtar juna.......

billy
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *