check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA page 14

AUREN  K'ADDARA
                ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim

14 «******»haka sukaita hirarsu da dariya dan sun saba dajuna,tare sukai karatu a America sudukan su,akwai shakuwa mai karfi atsakanin su gasu 'yan uwan juna,
Kafe 12:16 pm suka gama shirinsu cikin manyan kaya farare sunyi kyau sosai,sadiq ya kalli dady kai mutumina kafa had'u,kaganka kamar ango wallahi,
Dady dake taje sumarsa yace kaidai bari wannan duk aikin dad ne,wai dankar nasaka k'ananun kaya yad'inka mini wad'annan,nima dai abin yabani dariya,zansa ne kawai dan karyace banji maganarsaba.
         "Jafar yashigo yana d'aura agogo,kai malamai dan ALLAH kuyi sauri,guri yakure d'aya saura kar mu makara sallah,kunsan abba kuma yace ba African tame"
Cikin han zari kowa ya gama abinda yakeyi suka shirya tsaf,
Masallaci suka nufa, bayan an idar da SALLAH suka nufi wajan d'aurin auren,gaba d'aya akofar gidan abban su sadiq za a d'aura tunda shine babba,
Basuda tarkacen abokai,su hud'unnan sune abokan juna saidai abokan aiki da wad'anda ake gaisuwar mutinci, daku ma dangi sa'anninsu, d'aurin auren yatara manyan mutanan k'asarnan, dan alhaji el~mansur sanannen mutumne hakama abban sadiq,
An fara d'aura auren Safwan Ahmad Abdul~Aziz & Hafsat Muh'd Abdul~Aziz,sai Sadiq Muh'd  Abdul'~Aziz & Zainab Suraj  Abdul~Aziz,sai Jafar Sulaiman Abdul~AZiz. & Ni'ima Muh'd Abdul~Aziz,kamar daga sama yaji ance an d'aura auren Abdul~Aziz EL~Mansur Adam & Munneera Muh'd Abdul~Aziz, dasauri ya kalli su jafar suka d'aga  masa hannu alamar jinjina 🏻.
Shikam yay galala kamar soko yana  kallonsu, shikuma aka d'aurama aure, bayan gana gidan can sun gagaresa, kuma arasa da wadda za'a had'ashi sai wannan 'yar shilar yarinyar🏼, kai shikam yaga takansa, AUREN K'ADDARA ko BIYAYYA shikam baisan mizai kira aurarrakin nasaba,
Da sauri yajuyo danjin antab'ashi wasu abokan sune suke masa murna,haka ya daure ya amsawa cikin dariyar yak'e.
Su Sadiq suka k'araso suna dariya, run gumeshi sukayi suna fad'in brother muna tayaka murna,shidai dady bin kowa yake da kallo.......

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *