check your best novels here

Sunday 26 February 2017

NAWAFF!!! 18 & 19

[14/12/2016 12:55] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆
 NAWAFF 
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM




Page 18

BAYAN KWANA BIYU 
       Najeria suka buga wasa da gini, sai dai wanan wasa baiyima Najiria dad'iba, dan antashi 1-1 amma yau ba Nawaf ya zura mana kwalloba.
   Dana kalli Nawaf d'inma sainaga baya cikin walwala, na ce, "yau miskilanci 'yan mazan ya motsa.
  
KANO
    faisal ma an sallamesa saidai har yanzu yana zuba sambatunsa, duk ya rame yayi ba'ki, sai ro'kon iyayensa yake akan subarshi yaje gidansu yasmeen, 'kila idan yabata ha'kuri ta ha'kura tadawo gareshi.
   Tun iyayen na d'aukar lamarin nasa wasa har suka koma tausayinsa, idan yana surutai hajiya jummai har kuka takeyi masa, gabad'aya sun rasa kansa, bayada wani zance saina yasmeen.
    Hajiya jummai ta ce, "Alhaji kodai zuwa zamuyi mu ro'ki iyayen yasmeen ne?, 'kila su tausayamana su warware wancan auren, subama faisal.
   Alhaji buba yay shiru yana nazarin maganarta, zuwa can ya ce, "kina ganin hakan zata faru?, kuma idan sun yarda shi wanda ya auri yasmeen d'in zai amince??.
   Hajiya jummai ta ce, "to Alhaji saimu gwada, kuma ko biyansa yakeso muyi ai sai mu biyasa ko nawane, indai zai saki yasmeen faisal ya aura, karmuzo d'anmu ya susuce akan abinda baifi 'karfin saba.
   Na ce, "hummm aikodai wannan tafi 'karfinsa, dan ba kowacce mace kud'i ke iya sayaba.
    
KIRA
    mu mata munada al'adar cewa sai mun auri mai kud'i, kuma hakan ba daidai bane, kedai amatsayinki na d'iya mace kamata yayi kiyi addu'a ALLAH yabaki miji nagari mai 'kaunarki da gsky.
    Wlhy masu kud'innan damuke hari ba kowane yadamu da fita ha'k'kin iyalinsaba.
   Musamman ma mazan hausawa, idan suna samun kud'i sunfi maida hankalinsu ga neman kud'in fiyeda 'ya'yansu da matansu.
   Wani saiya had'a wata uku zuwa hud'u baya 'kasar, yabar matar cikin damuwa da kewa, shikuma yanacan tareda karuwai a hotel, to dan ALLAH miye ribar auren irin wanan mai kud'in.
   Idan baki kai zuciya nesaba saiki fara bin mazan waje da aurenki, ALLAH ya kiyayemu.
   Idan kuwa kika auri talakannan daba kiso, duk inda yafita zuwa yamma yadawo, zai kula dake zai kula da 'ya'yanku, UBANGIJI ALLAH yasa mu gane amin.

   Yasmeen kuwa tana cikin damuwa, tanaso ta koma makaranta amma abba ya ce, "tabari mijinta yazo ta gaya masa, tayi kukan harta gaji dan tanaso takoma makaranta gashi anata wuceta a lectures.
   Yau suna zaune afalo harda umma da abba, sunata hirar gida, abba yana cewa lokaci kad'an yarage suje kwangwalan dansuga dangi dangi su gansu, yaseer yanata murna, amma yasmeen ko motsi batayiba.
   Abba ya ce, "mamana lafiya dai??, tai firgigit tana fad'in lafiya lao abba, ya ce, "inafa lafiya munata magana amma ba'kya tare damu, zonan mamana naji damuwarki kinji.
   Jiki a sanyaye yasmeen ta tashi taje kusada 'kafafun abba ta zauna, yadafa kanta yana fad'in mike damunki? fad'amin!.
   Saida ta matso hawaye sanan ta ce, "abba makaranta ta.
  Tofa, abba ya fad'a, yanzunan dama saboda bokonnan kika takuri kanki, to aii na ce, "ki bari mijinki yazo saikuyi magana.
   Babansa yakirani d'azu ya ce, "gobe zasuzo insha ALLAHU, dama baya nanane shiyyasa bai zoba.
   Cikin sigar lallashi ya ce, "kiyi ha'kuri kinji mamana, ki d'auki duk abinda ya sameki amtsayi 'kaddara.
   Yasmeen ta d'aga kai tana hawaye,. Abba ya ce, "yauwa mamana ALLAH yay muku albarka kunji, ya tsare mana ku.
   Umma da yaseer sukace amin.
 Daga nan yasmeen tad'an saki jikinta tana d'an saka baki a hirar tasu, amma ba sosaiba.

NAWAFF
   yau da yamma Nawaf ya iso kano, zaid'an kwana biyu ya koma abuja, kafin aci gaba da wasa.
   Sunyi murnan ganinsa, momcy ta shafa kansa cikin hausarta dabata gama nuna ba ta ce, "my dear duk ka rame wlhy, mike damunka haka??.
   Nawaf yad'an cije leb'ensa na 'kasa ya ce, "momcy wanan auren da papa yay min mana, ALLAH bazan 6oye mikiba bana son aurenan momcy, ya'karasa fad'a cikin raunin murya.
    Momcy ta kwanto dashi gefen kafad'arta ta ce, "kayi ha'kuri Abbuna ina ji ajikina wanan auren Alkairine a gareka, kuma yanda su Abdallah suke bani labarin matar taka da gidan data fito duk masu mutuncine, da tarbiyya.
   Banaso akan aurennan kabari sa6ani yashiga tsaka ninka da papan ku, ka danne zuciyarka ka koyi son matarka tunkafin tadawo hannunka.
   Zanta tayaku da addu'a insha ALLAHU, itama ALLAH yacusa mata sonka kaji, dukda nasa modeebbona abin sone ga kowacce mace, babu macen dazata gansa ta ce, "bataso, momcy ta 'karashe maganar da tsokana.
   hannu yasa ya rufe idanunsa don kunya.
   Momcy tayi dariya, ato idan kuma bakaso mutafi saudia kaza6a cikin dangi, gama ummuhabeba nan kullum damuwarta tana kanka, kaga sai kawai musha biki.
   Nawaf ya zaro idanu ya ce, "momcy yi shiru kar papa yaji, danni bana ra'ayin zama da mata biyu, kuma ma bana son ummuhabeeba tacika 'kyau dayawa nikuma bana son macen data cika 'kyau gsky.
    Tofa, momcy tafad'a, wanan kuma wani sabon idea ne na rashin son auren 'kya'ky'kyawar mace??.
   Nawaf yay murmushi har fararen ha'koransa suka fito, ya ce, "A'a my sweet mom ra'ayina ne nidai!!!....
   Abdallah ya shigo da sallama, Nawaf ya ce, "ka amso mini?, eh yaya na amso, na kaimaka d'akinka banyi zaton kana nanba aii.
  Okey babu damuwa, amma yau miya hanaka zuwa islamiyya ne??, Abdallah yad'an sosai gefen wuyansa yagyara zama zai shararo 'karya.......Nawaf ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu kaga basai kafad'aba, dan nasa 'karya zakamin.
   Momcy ta ce, "aii dama jira nake kadawo na sanar maka kwata2 Abdallah baya son zuwa islamiyya, danshi bai biyo halinkaba, tun kana shekara sha biyar ka sauke ALKUR'ANI, amma Abdallah har yanzu baikai ko izufi 50 ba nakula Anwar ma yakusa kamosa.
    Harara Nawaf ya watsa masa, ya ce, "wato kai nakula kaine mara ji d'in gidanan ko?, wlhy ka maida hankalinka kajiko, ku a tunaninku karatun boko shine wayewa ko??, amma ai baka ta6a fashin makarantar bokoba ko??.
  Kun manta karatun bokon iyakarsa nan duniys, karatun islamiyyar dabaku basa muhimman cinba shine zai zame mana tudun dafawa awata rana mai cike da rud'ani.
   Wlhy daga yau nasake jin bakaje islamiyyaba sai ranka yayi matu'kar 6aci, tashi kabani waje sakarai kawai.
  sum sum Abdallah yatashi yashige d'akinsa yana zum6ura baki.

WASHE GARI
    Tunda wuri umma da ameena suke hidimar had'a abubuwan tarbar ba'ki amma banda yasmeen data shige d'aki wai batada lfy.
   Dan haka umma taje ta nemo Ameena 'kawar yasmeen d'in dan ta tayata.
   Yasmeen kuwa tana d'aki cikin fargaba da damuwa, wai yau zataga mijinta, ko zaizo mata da mutuncine?, kokuma sa6anin hakan??.
    Har zuwa azahar tana d'aki tana kullawa da kwancewa, dakuma fad'uwar gaba.

a wannan lokacin kuwa Nawaf yanacan anci kwalliya cikin 'kananun kaya, ya fito shida mas'ud sai zabga 'kamshi suke, 6an garen su momcy suka nufa, afalo suka iske momcy da papa dasu Anwar.
   Papa ya ce, "kunyi 'kyau sai dai modeebbo koma ka canjo kaya wad'anan basu yiba.
   Nawaf yabi jikinsa da kallo, papa miye aibun wad'anan kayan yafad'a cikin shagwa6a.
  Papa ya ce, "aibunsu dasuka kasance 'kananun kaya, kai bakaga shigar da d'an uwanka yayi ba mas'ud.
   Gidan surukai zakujefa, kuma yau zasu fara ganinka, sai kaiwai suganka da 'kananun kaya kamar d'an yahudawa, maza kaje ka canjo shadda ina nan ina jiranka, dan kuna 'kara 6ata lokaci.
   Badan Nawaf yasoba yakoma ya sako farar shadda 'kal d'inkin zamani, harda saka hula, kai yayi 'kau wlhy, saiya fito asalin balarabensa, dan dakaga Nawaf dole ka kirashi ci kakken balarabe.
   Nawaf dogone sosai yanafa jikin 'karfi sabida training dayakeyi, yana da suffa irinta kosashshen xaki, daga sama 'ka'k'karfane sosai cikinsa ad'ame tamkar baya cin abinci, farine amma ba tas ba, kalar fatarsa irinta larabawace jaa kenan zamuce, yanada suma mai yawan gske mai kuma laushi d 'kalli dukda tanashan gyara da mayuka masu tsada, yanada d'an saje wanda ya tsaya iya kumatinsa dai dai kunne, ida nunsa masu 'kyau da haske ga girar ido zara zara, kai komaidai yaji d'ammmmm.
     Papa yay murmushi yauwa ko kaifa modeebbo, yanzu kaga shine mutuntawa, sai kuje banaso naji wani abinda zai 6ata mini rai, kuma ku sayi wani abu akai mata kar aje hannu rabbana, ku gashe mana dasu.
   Mas'ud ne kawai ya amsa.
Abdallah ya  ce, "yaya dan ALLAH zanje.
   Harara Nawaf ya watsa masa wadda tasakashi saurin rufe baki.
   Sukuma suka fice.
Papa ya ce, "huum d'an yanzu saka barsa da halinsa kawai.

Amota mas'ud ya ce, "mutumina baka ta6a kwalliya irin ta yauba wlhy, gashi yau ranar shan mamakice.
   Nawaf ya ce, "wane irin mamaki kuma bro's??, wani murmushi mas'ud yayi, ya ce, "sai munje zaka gani!".
    Baki Nawaf yad'an ta6e yana fad'in ni babu wani abin mamaki dazan gani malam.
   Mas'ud ya tuntsure da dariya   , banza Nawaf yay masa.
       Sun isa 'kofar gidansu yasmeen, mas'ud ya ce, "ka kirata kace mun iso mana.
   Harara Nawaf ya sakar masa, ya ce, "lallai ashe zamu kwana anan kuwa, indai har saina kirata ne.
   Girgixa kai kawai mas'ud yayi yad'akko wayarsa ya kira yaseer ya ce, "yaseer gamu munzo.
   Yaseer ya ce, "to yaya ku shigo falon Abba.
  Mas'ud ya kalli Nawaf bayan ya gama wayar, ya ce, "to saika fito ance mu shiga, baki Nawaf ya ta6e ya bud'e motar yafito.
   Cikin gidan suka danna kai, har zuwa 'kofar falon abba dake harabar gidan ta baya, babu yanda za ayi kaga masu gidan dan 'kofar falonsu tana can cikin lungu, Tunda suka shigo 'kamshin turare falon da abinci yake dukan hancinsu, suka zazzauna.
    Babu dad'ewa yaseer ya shigo da sallam suka amsa, idanu ya zaro waje dan mamaki, ya 'kara murza idaninsa, yagadai kwarai dgsk modeebbo ne, ya ce, "yaya mas'ud dan ALLAH dgske ida nuna sukeyi??.
   Murmushi mas'ud yayi dan yagane me yaseer yake nufi, ya ce, "gsky suka nuna maka yaseer, modebbone dai daga kasani yana gara mana kwallo a afili.
   Nawaf yay murmushi shima ya ce, "zonan 'kanina!, jiki a sanyaye yaseer ya 'karasa wajensa, hannunsa yakama ya zaunar dashi kusadashi, kasannine??, yaseer yay dariya, aiko shekaran jiya saidanaga wasanka, wlhy narasa irin murnar dazanyi danna burge kaina, amma ALLAH ngd maka daka nuna min wanda nake 'kauna ido da ido.
   Nawaf yaji dad'i sosai, danhaka ya rungume yaseer shima.
   mas'ud ya ce, "yaseer sisto d'inkafa?.
  Yaseer yami'ke yana fad'in kuyi ha'kuri farinciki ne ya mantar dani bari na kirata!!.
  Mas'ud ya ce, "to karka gaya mata abinda kagani fa.
   Cikin dariya yaseer ya ce, "bazan fad'aba ALLAH.
       yasmeen zaune afalo tana jiran yaseer yazo yakirata, tayi 'kyau cikin les green ta d'ora farin mayafi dukda ba kwalliya tayiba amma tayi bala'in 'kyau.
   Muskarsa cike da fara'a ya ce, "sisto kije suna jiranki, bai jira amsartaba yashige d'akin umma domin kai mata rahoton farin ciki.
    Jiki a sanyaye ta tashi tanufi falon, tad'an dad'e a 'kofar falon 'kirjinta yana dukan tara2, daga 'karshe tayi kundun bala tashiga da sallama, cikin siririyar muryarta.
   Mas'ud ne kawai ya amsa, dan Nawaf yana wayane.
   Ta zauna suka gaisa da mas'ud yabata ha'kuri akan kwana biyu basu zoba, tayi d'an mumushi tana fad'in babu damuwa aii.
  Mas'ud sai dariyar mugunta ya ke k'asa2, ya'kagara yaga yanda za'a had'u.
    To nimadai 'yar rahoto abinda nake jira kenan.
   Bayan Nawaf yagama waya ya juwyo yana kallon mas'ud, mas'ud ya ce, "lafiya dai ko??.
   Harar sa Nawaf yayi ya ce, "ban saniba.
    Mas'ud ya tuntsure da dariya, cikin dariya ya ce, "Amarya ga angonki na kawo miki yau dai.
  Kan yasmeen a'kasa ta ce, "ina yini?, 
   Lafiya. kawai Nawaf yafad'a yana wani yatsine fuska.
   Yasmeen ta mi'ke domin ta basu ko ruwane dan takula ko bud'e abincin basu yiba.
   Ta 'karaso kanta a'kasa, shi Nawaf ma waya yake latsawa, gabansu ta dur'kusa ta tsiyaya lemon kwakwa ta mi'kawa mas'ud.
   Ta zuba wani ta mi'kawa Nawaf dake latsa waya abinsa.
  Mas'ud ya ce, "malam ana baka abufa, ayatsine Nawaf yad'ago zaiyi magana, saiya daskare a gurin.
   Cikin in ina ya ce, "kai ba dai ke ba ce.....
   Itama cikin tsoro take kallonsa, sudukansu 'kirjinsu yana bugawa da tsananin 'karfi, hannun yasmeen sai rawa yake, gashi takasa ajiye lemon.
   Shima Nawaf cikin rawar hannu da baki yake nuna yasmeenamma yakasa cigaba da furta komai.
    Shiko mas'ud sai dariya yakeyi yana tafa hannaye.....................








©2016


Bilyn Abdul
     Mrs Abdus'salam
         Luv u oll my fan's
[14/12/2016 20:02] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆
 NAWAFF 
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM



Page 19

....Lokaci d'aya suka mi'ke kowa yana kallon kowa, idan kagansu saika d'auka kallon soyayya sukema juna, yasmeen ce tafara janye idanunta tana zubar da hawaye, saikuma tad'ago da sauri tana kallonsa.
   Nawaf yagyara tsayuwarsa tareda 'kara d'aure fuska ya ce, "lallai yarinya dama kece papa ya 'ka'kaba mini, tofa ina mai baki shawara 'yammata tun wuri ki hanzarta fad'a musu su warware wanan auren ankuwa ba hakaba wlhy zaki gwammace kid'a da karatu, ya 'kare fad'a yana huci, kamar wanda yake afilin danbe.
    Cikin tsiwa yasmeen ta harareshi ga hawaye share2 a fuska, ta ce, "ai basai nasha wahalar sanar dasuba malam, wannan damar tana hannunka, idan kaso nanda minti d'aya saika datse igiyar da aka d'auramini ta 'kaddara dakai, tsowww... taja tsaki.
   Wani 'kududun ba'kin ciki ya tokare ma'koshin Nawaf, wlhy badan yanajin tsoron fushin mahaifansaba da agurinnan zai saki yarinyarnan, ya had'iye wani mugun yawu jikake 'kudddd.
  Idanunsa sun kad'a sunyi jajur,, yasmeen ta ce, "aikin banza ashema kai matsoracine??..........kafin tarufe baki ya dam'ki hannunta na dama ya murd'e tabaya, tako kware baki zatayi ihu dan azaba, da sauri yasa d'ayan hannunsa ya toshe mata baki, saida ya tabbatar hannun ya murd'u sanan ya saketa yana dariyar mugunta, ya ce, "nida ke za'a tantance matsoraci.
   Yasmeen ta durkushe tana zubar da hawaye, jitake kamar hannunta baya jikinta, kwatakwata takasa d'agashi.
   Mus'ud yale'ko dan yaga wainar da ake toyawa tunda yasan ba shiri sukeyiba.dan tund'azu yafita yabarsu su biyu kawai.
  Da sauri ya'karaso ganin yasmeen tsugunne tana rusar kuka, a hanxarce ya ce, "Nawaf!! mikayi matane??.
   Banza Nawaf yay masa ya koma saman kujera ya zauna yana shan lemon kwakwarsa wanda yayi masa dad'i.
   Ran mas'ud ya6aci sosai ya ce, "waikai Nawaf wane irin mugun mutumne yau kuma mizakace tayi maka??.
   Nawaf ya yatsine fuska, katanbayeta abinda taimin sai nikuma nagaya maka abinda nayi mata, kawani d'ora mini laifi ni kad'ai, tsowwww ya 'karashe maganar da tsaki.
    Mas'ud ya ce, "kiyi hakuri yasmeen ALLAH zai saka miki,, yasmeen tad'ago jajayen ida nunta ta ce, "karka damu mas'ud nima dakaina zan rama, dan wlhy bana barin bashi, karya d'auka dan yayi mini wanan muguntar zan barsa, shima ya saurari ranar ramuwa..
   Tana kaiwanan ta mi'ke zata tafi, mas'ud ya ce, "plz karki tafi ki dawo, kinga su umma bazasuji dad'iba.
   Batayi musuba tadawo ta zauna dan tana ganin darajar mas'ud.
   Nawaf kam ko kallo basu isheshiba, yanata danne2 awaya hankalinsa kwance, yana kora lemon kwakwa.
   Na ce, ji 'kafin hali azo gidanku a cuceka. 

Afalon umma kuwa faisal ne da hajiya jummai da alhaji buba, zuwansu kenan suma, umma bata nuna musu komaiba ta tarbesu da mutunci, harda ruwa ta zauna suka gaisa sanan ta ce, "gashi kunzo malam baya nan amma yana hanya, dama jiya yake magana akan akwatuna, ya ce, "azo akai muku kafin ku biyo.
   Hajiya jummai tayi dariya, A'a mu ba kar6ar akwatuna muka zoba, munzo mu baku ha'kuri akan abinda yafarune, wlhy makircin wani abokin faisal ne, shikuma babu bincike yaje ya aikata wanan aika aikar, amma wlhy tunda aka gane makircine hankalinsa ya tashi, nan dai hajiya jummai ta labartawa umma komai daya faru.
   Umma ta ce, "ALLAH sarki ai bamu saniba damunzo mun dubashi, ALLAH yasa kaffarane faisal.
  faisal ya ce, "amin umma, yafad'a yana wani sissinkuyar dakai 'kasa, adole shi mai kunya.
   Hajiya jummai ta ce, "nibanga 'yar tawaba.
   Umma ta ce, "tana nan wlhy, tayi ba'kine, ALLAH sarki d'iyar albarka.
   Alhaji buba yaga hajiya jummai tanata wani kewaye2 takasa furta komai, sai kawai ya wage baki yashiga bayanai.
   Maman yaseer dama abinda yakawomu shine dan ALLAH ayi ha'kuri da abinda yafaru baya, tunda faisal yayi nadama ayi ha'ku amayar masa matarsa, munyi muku al'kawari hakan bazai sake faruwaba.
   Cikin mamaki umma take kallonsu, ta ce, "alhaji ai yasmeen yanzu tanada aure, ko baku saniba??.
   Hajiya jummai ta kar6e, munsani mmn yaseer, abinda dama mukeso muce shine dan ALLAH abama wancan mijin ha'kuri sai a war ware adawoma da faisal matarsa.....

Da sauri yaseer ya shige falon abba, batareda yaji furicin ummaba, kai tsaye wajen Nawaf yanufa, yayinda mas'ud da yasmeen suke d'an ta6a hira.
  Akunne yaseer ya gwargwad'ama Nawaf abinda yajiyo.
   Idanu naga Nawaf yazaro ya ce 'kanina da gsk, yaseer ya kad'a kai tareda fad'in sunama falon umma,, kafad'ar yaseer Nawaf yadafa ya ce, "karka damu bazamu barima Mafita ba  ka kwantar da hankalinka, yaseer ya ce, "to bara naje naji yanzu mi ake tattaunawa.
   To Nawaf ya cema yaseer.
  Maganar ta girgiza Nawaff, amma shi atunaninsa yasmeen tana son failal ne, yazata makircinne da gsk.
   Dan haka yake ganin ai bama saiya saketaba yasamu hanyar yima yasmeen abinda yaso kenan.
     
Awajen su umma kuwa, umma ta ce, "musu to wanan ba maganarta bace sai abba yadawo zasuyi shawara.
   Alhaji buba ya ce, "to bari suje suna saurarensu idan sunyi shawarar.
   Umma ta ce, "to mungode ku gaida gida.
   Har ga ALLAH faisal yaso ganin yasmeen amma babu dama, danko mai kama da'ita bai ganiba,, jiki a sanyaye yatashi yabisu hajiya jummai yanata raba idanu dan son ganin yasmeen.

    Tafiyarsu babu dad'ewa abba yadawo, bayan ya huta yasha ruwa yashiga suka gaisa da su Nawaf, har 'kasa suka tsugunna suka gaidashi, Nawaf sai wani sisinkuyar dakai yakeyi.
   Yasmeen ta ce, "munafinci banza, wlhy indai nice zaka gane kurenka.
   Sun d'an dad'e suna hira da abba, daga nan umma tashigo suka gaisa, su duka sun yaba da hankalin surikin nasu, gashi 'kya'ky'kyawa laillai d'iyarsu ta more saidai subita da fatan alkairi, dan auren miji nagari bababar ribace.
    Sai gab da magriba suka tafi, abba yamatsa saita yimusu rakiya.
  A 'kofar gida mas'ud ya ce, "yasmeen yakamata nima ki samar min mata a anguwarnan gsky.
   Yasmeen tad'anyi murmushi, ai indai wannan ne takwana gidan sau'ki, nabaka ameena.
   Ya ce, "woow!! Kice harna samu?, yasmeen ta ce, insha ALLAH.
   to yakamata afara yimini kamfen daga yau.
   Nawaf yaja tsaki yana fad'in malam nifa kana 6ata mini lokaci kaji,  tsaki mas'ud yaja, ya ce, "matsalarka ce kuma wannan, d'an rainin wayo kodan kaga ka kama taka a hannu, to nima tawa nake nema.
   Baki Nawaf ya ta6e ya ce, "kaine mata ke gabanka aii.
     Maganar tayi mugun 6atawa yasmeen rai, dan haka taja wani dogon tsaki tana fad'in wandama ya ce, "basa gabansa munafinci ne kawai...
    Da sauri Nawaf ya ce, "ke waye munafikin??, saida ta murgud'a baki sanan ta ce, "damai aikatawa nake.
    Nawaf yay wata 'yar dariya, yarinya kin taimaki kanki dakika kauce, wlhy dasai na ida 6alla wananan hannun mai kamada sillen kara.
   Masha ALLAH yasmeen tafad'a tana murgud'a masa baki, ta ce, "basai kazo ka 6allaba, kuma dakai ake zaka kashe nine???.
    tana ganin Nawaf ya biyota ta tsillara da gudu cikin gida.
  Nawaf ya ce, "'karamar 'yar marakunya daki tsaya mana kiga hauka.
    Mas'ud ya ce, "wlhy tunda nake ban ta6a kallon film mai dad'in kamar nakuba, gsky kuna wuta alhaji.
   Harara Nawaf yasakar masa, ya ce, "kaifa d'an iskane wlhy    mas'ud ya ce, "iskan cin menayi maka malam??.
    Nawaf ya ce, "wai mas'ud ya akayi haka, kodai kaine kayi wanan had'in yama za'ayi wanan yarinyar tazama matata, aii da sake.
   Babu wani sake malam aii ka d'auka an wuce gurin kawai, domin wannan wata hikima ce daga cikin hikimomin ubangiji.
  Wai mikayi mata d'azu naga tana kuka??, ko har an fara soye wane??.
   Duka Nawaf ya d'akama mas'ud ya ce, "a 'konewa aka fara ba soyewa ba, rashin kunya tamin na hukuntata.
    Hhhhh kaidai wlhy mugune nakula.
  Koda yake wasan yana 'kyau dan nasan saita rama.
   Lallai kam kokuma ta rame ba, dan wlhy yanzu ta ce, "zatamin hauka wahala zatasha ba 'karamaba, garama ka bata shawara ta kiyayeni.
   Hhhhh kadaiji dashi malam, dahaka suka 'karasa wani masallaci domin yin sallahr magriba.

Yasmeen kuwa da gudi tashiga gida, a falo suka had'u da umma ta ce, "k irin wannan gudu haka lafiya?.
   Gefen wuyanta ta sosa ta ce, "babu komai umma.
   Girgiza kai kawai umma tayi tashige d'aki domin yin sallah.
   Itama yasmeen d'aki ta shige ta kwanta domin tana fashin sallah, dan danan tashiga duniyar tunani, lallai saita dage tunda har ALLAH ya 'kaddara mata zaman aure da wanan d'an haya'ki, saidai kuma tayi farin cikin rabuwada faisal d'an is......takumayi ba'kin cikin kasancewa da Nawaf d'an kwallo, wai itace matar d'an kwallo kai lamarin tamkar almara wlhy, gsky bata moreba dan ita kwallo bata burgeta bare mai yinta, amma gashi ALLAH ya jarabceta da auren d'an kwallon.
    Ta kalli hannunta da har yanzu ciwo yakemata ta ce, "mugu ALLAH yasaka mini, kuma wlhy ka rubuta ka ajiye saina rama, 'kilama yayi mani targad'e azzalumin.
   Haka tai ta tuna abinda yafaru d'azu tamkar a mafarki.

FAISAL
    faisal kuwa koda suka tafi saiya sakama iyayenasa kuka, hajiya jummai ta hau rarrashinsa haba faisal d'in dady kayi ha'kuri, kobakaga 'ko'karin da mukeyi akanka bane, ka d'auka yasmeen tama rigada tadawo hannunka nan bada dad'ewa ba.
   Alhaji buba ya ce, "bana son ganin kukanka my son dan ALLAH kabari indai yasmeen ce dan kai aka halicceta kaji.
   Kai kawai yad'aga yana share hawaye.
   Wlhy ni dariyama yabani.

BAYAN KWANA BIYU.
    yasmeen tasake yima abba maganar makarantar ta, abba ya ce, "banace ki fad'ama mijinki idan yazoba.
   Ta ce, "abba ai na manta ban fad'a masaba.
   Aii wanan mai sau'kine tashi kije ki fad'a masa ta waya yanzu, idan ya yarda saiki fara zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.
    Jiki asanyaye yasmeen ta mi'ke, ita yanzu idan ta kirashi mizatace masa, 'kilama yay mata wula 'kancin daya saba mata, itako wlhy ba 'kyaleshi zatayiba.
   Tadad'e tana kullawa da kwancewa, daga baya ta d'auki wayar tafara kiransa cikin fad'uwar gaba, har wayar ta tsinke bai d'aukaba.
   Ta kai dubanta akan agogo 'karfe 9:56pm, wata zuciya ta ce, "ki 'kara kira, maso d'an tsuntsu aishi ke binshi da jifa.
    Ta sake kira har sau biyu bai d'agaba, jiki asanyaye tazame ta kwanta tana hawaye, shike nan an hanata zuwa makaranta tanaji tana gani.
   
^^^^^^^^^^^^^^^^
    Alokacin da yasmeen take kiran Nawaf yana wanka, yanajin wayar tana wringing, gashi yana dad'ewa awajen wanka, saida yagama komai na al'adar rayuwarsa kamar shafa'i da wutiri, karatun alkur'ani, (dan duk dare saiya karanta littafi amai tsarki,) san shayi, sannan ya haye gado ya kwanta, wayoyinsa yajawo, yafara duba missed calls, ya kira wad'anda suke da muhimmanci sanan, wayar da yasmeen takira itace 'karshe, 3missed call yagani saidai kuma ba'kuwar number ce, shikuma baya kiran ba'kuwar number.
   Harya kwanta sai kuma zuciyarsa ta kwad'aita masa yakira, dan baisan dalilin dayasa mai number yay masa 3missedcall ba.
    Lokacin har yasmeen tagama kukanta tayi barci, dayake barcin baiyi nisaba saitaji phone d'inta na wringing, sanda ta d'auka harta kusa tsinkewama.
   Cikin muryar barci ta ce, "assalamu alaikum.
    saida yaja ajiyar zuciya wadda shi kansa basan yayiba, ya ce, "wa'alaikissalam wacece??.
    Tuni yasmeen ta watstsake domin jin muryar Nawaf, dan da farko bata duba number da aka kirata dashiba, ta tashi zaune, cikin rawar murya ta ce, "yasmeen ce!!.
    Yad'an ta b'e baki dan tunda tayi sallama yagane muryarta, ya ce, "ban ganekiba, kinga kimin bayani yanda zan gane banason inda2, inba hakaba zan kashe wayata.
    Saidata murgud'a baki tamkar tana gabansa, ta ce, "toni wane bayani zan maka tunda nafad'i sunana baka ganeba, ni dama sonake na koma makaranta kuma abba ya ce, "saina sanar maka shiyyasama nakiraka, inba hakaba mizaisa nakiraka, ta 'kare maganar cikin mugud'a baki.
    Tamkar yaganta ya ce, "mara kunyar banza, to ban aminceba inkuma kikaje ban saniba ALLAH ya isa, d'if ya yanke wayar.
   Wasu hawaye suka zubo mata masu zafi, zuciyarta taita zugata akan takirashi ta ro'keshi 'kila yabarta.
   Haka ta daure ta kirashi, yay buris da wayar, saida ta sake kira sanan ya d'auka, wani lallausan murmushi yasaki na mugunta kafin yad'aga, yana d'agawa ya ce, "k nifa kin dameni barci zanyi.
   Ta matse hawaye ta ce, "plz dan ALLAH kabarni, kaga zamu fara EXAM ne kwanan.
   Saida yagyara kwanciya sanan ya ce, "toni ina ruwana, nidai nace ALLAH ya isa ko, kuma zan kira abba na ce, "na hanaki, dan haka karki sake kirana zanyi barcine, bata ankaraba ya kashe wayar.
   Dariya yashiga tuntsurawa harda hawaye, yarinya baki sanni bane, inada hanyoyin maga ninki wlhy, yafad'a yana kwanciya.
   Itako yasmeen kuka tashiga rerawa kamar uwarta ta mutu, saida tayi mai isarta sanan tayi shiru, har barci ya kwasheta..
   Na ce, "yasmeen asuba tagari..................


Assalamu alaikum
  Ina mi'ko d'unbin gaisuwa ga masoyana, nagode kuna 'karamin 'karfin guywa gsky, ngd ALLAH yabar zuminci.
   Luv u oll!!!!!!.

Acigaba da gashi!!!!!!!!!!.






©2016

Bilyn Abdul
    Mrs Abdus'salam
        Luv u oll my fan's
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *