check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA page 10

AUREN K'ADDARA
                Ko BIYAYYA


Na billkisa ibrahim

10 «*****» tsaki taja amma baijiba dan tasan inhar yaji sai yaci k'aniyarta, duk iskancinsu saidai suyi iyasu kad'ai amma basa sakashi ciki,suna mugun jin tsoronsa,
      "Yau dai antashi da ruwan safe, dan haka garin ya d'au sanyi, dady yana cikin bargo ad'akinsa saboda ruwa baije aikiba ,barci yake mai dad'i,saiya jiyo hayaniyar su husna yaja tsaki yagyara kwanciyarsa, jin abun bana k'arewa bane ya tashi cikin fushi yanufi falon,ikileema ce ta shak'e husna tanata jibga,kamar uwarta,
 "Dady yadaka musu tsawa kunsan ALLAH in har baku bariba zan zaneku,dukda dukan mace baya cikin tsarina,kainifa na gaji da iskancin nan naku wallahi gab nake da kora ko waCce gidan ubanta idan kuma kunji karya kuci gaba ya fad'a yana nufar d'akinsa"
   "Kan gado yafad'a rubda ciki,yadafe kai ni ABDUL~AZIZ naga takaina wannan wace irin rayuwace, AUREN KADDARA ko BIYAYYA za a kira aurena,
    Hayaniyar su ikileema yaji sun cigaba da fad'an,yace nidai shike nan an aura mini jaraba,
Mikewa yayi yacanza kaya ko wanka baiyiba,ya d'auki key d'in mota da wayoyinsa ya fito,ko kallo basu isheshiba ya wucesu afalo suna danbe,
Gindansu yanufa su mom suna falo harda 'yan biyu sunata hirarsu,sallamarsa sukaji 'yan biyu suka mik'e da gudu suka rungumesa.
"Yace oh ku waibakusan kun girmaba??
Sukai dariya yaya mubamu wani girma ba sai nan gaba,
Ya zauna yana gaishe da iyayensa, suka amsa masa cikin fara'a,
Mom tace babana inji dai lafiya naga  kamar da damuwa atare dakai,
"Yay d'an tsaki mom barci nakeji wallahi, to miya hanaka yi? Kataho nan acikin ruwannan,🌧🌧 baka tsoron mura? 
To mom ina tare da karnuka🐕🐕 yaza'ayi subarni nayi barci,
Ya mik'e ransa a b'ace yanufi d'akin mom,
Binsa sukai da kallo cikin tausayi duk yarame sai fari da dogon hanci, dad yakalli mom dolene munema ma yaronnan mafita Bilkisu, mom tace gaskiya kam alhaji nima lamarinsa ya fara bani tsoro,
 Kairat tace ALLAH dad kubar mu muje mu koya musu hankali, dan wallahi baza mubari su kashemana  d'an uwa ba,mom tace a'a bamu aikekuba.
 Gadon mom ya haye abinsa cikin minti  goma barci yay awan gaba dashi....

billy
{Mrs abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *