check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 27

AUREN  K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 


27 «******» daga nan gidan dady sabon gidan da dad yabashi ya nufa, lallai gidan ya had'u🏘, idan natsaya baku labarin gidan sai mu b'ata lokaci, amma gidan b'angare hud'une kowa danasa baruwan wata da wata, yagama zagaye gidan ya koma gida.

Gado ya haye yay barcinsa tunda yau babu karnika agidan.

Su ikileema kuwa suna zuwa kowa gidansu ta wuce, suka zayyane ma iyayensu abinda ya faru k'arya da gaskiya, suka d'aure musu gindi wai su zauna har sai dady  yazo.

Da daddare dad ya shirya ya nufi gidan umma, acan yasamu yayyenasa, abban ikileema da abban husna, ya gaishesu kowa ya amsa fuska acinkushe, baibi takansuba yafara basu hak'uri akan yaran da abinda ya faru, yace kuma suyi hakuri abashi yaran ya maidasu yanzu.

Umma ta watsa masa harara to ubanmu Mansur ba dole abaka yara katafi dasuba tunda yaran wasane su, agabana yaron yaci mutincinsu ya had'a dani sannan kawai dan karainamu, kai mai d'a da kud'i kazo kace abaka yaran ka maida masa, in kaga sun koma sai yazo dakansa gidannan ya basu hakuri, yakuma saki wacan farar koman dannasan farintane  yake d'ibarsa ba wata tsiyaba.

Dad yace umma kiyi hakuri saboda yarannan duk d'ayane awajanmu  bashi da damar sakin wata yabar wata, dan hakan zai iya b'ata mana zuminci gabad'aya, dan haka kuyi hak'uri kawai sukoma.

Abban husna yace kai Mansur kaje  kawai inhar kun yarda da sharad'in umma to yasaki wadda kuka auro masa agobe adawo masa da 'yan uwansa d'akinsu.

Dad ya mike.yana fad'in kudaiyi tunanin mai yuwu wa, duk shawarar dakuka yanke muna jira ya fice abinsa batare dayabi takan kiran da abban ikileema yake masaba...


billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *