check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA?? page 16

AUREN K'ADDARA
                Ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim


16 «*****» sun fito zasu tafi saiga mom ta kallesu tana dariya, yarana kunga yanda kuka yi kyau kuwa,suma dariyar sukeyi banda dady daya tsurama mom idanu, mom tace a'a babana ya haka ai yau ranar murnace da farin ciki ba ranar fushiba,
Safwan yace ki kyalesa mom dan ya gankine, amma d'azu da akace an d'aura auren bakiga tsallen da yayiba, gaba d'aya suka tun tsure da dariya, dady yakaima safwan duka, safwan ya kauce yana dariya, mom tace to kuyi k'ok'ari kushiga babban falo ku gaida iyayenku kunjiko.
  "Sukace to"
"Mom tawuce tana dariya dan tasan d'an nata yau yana cikin wani yanayi"

"Sun shiga kamar yanda mom tace suka gaishe da iyaye da yayye"

Bayan sun fito jafar yace kai nifa wlh amaryata nake son gani, Sadiq yace ai duk tafiyar d'ayace muma sumuke son gani, to aina zamu gansu kodan ma muyi hotuna ce war safwan,
Amma dady yiyai kamar ma baisan abinda sukeyiba, jafar ya tab'ashi kaifa dady banji ka amsaba, harara yasakar masa kaga malam idan zaka kabar tsayani inkuma kaje kabar tunawa dani, nidaga nanma sai kano dan yau zan koma.
     "Cikin mamaki suka kallesa,
 "Sadiq yace tafiya fa kace??
 "Ashe kaji abinda nace kake kuma tan bayata"
  Safwan ya dafa kafad'arsa kaga d'an uwa kayi hakuri muje ayi hotunan nan sai mu tattauna matslarka amma dan ALLAH karka bari wani ya fahimci matsalarka har yarinyar, ko ba hakaba 'yan uwa?
" Su Sadiq sukace gaskiyane"
Dole haka dady yahakura yabi su amma fuskarsa ba walwala,
 Jafar ne yakira Ni'ima yatan bayeta suna ina? Tagaya masa,
Kai tsaye cikin gidan suka shiga,amaran duk suna nan tare da k'awayensu,
Suka cikaro da anty lubna da anty nafisa suna yima Munneerah kwalliya, kallo d'aya zakai mata kagane tana cikin damuwa,
 Sauran amaren kuwa suna gefe zaune da k'awayensu anata hira da raha irinta amare da k'awayensu,
  "Dady ya tsurama Munneerah idanu👁👁wai wannan 'yar yarinyarce matarsa, yarinyar dasuka gama d'auka kwanan nan, jibima k'irjin bakomai dukda dai akwai gyale ajikinta.
 Sadiq ya tab'ashi please oga in kayi hakuri jibi iyanzu tana gidanka.
 Banza yay masa kamar bai jiba
 " anty lubna tataso tana fad'in kai 'yan kannena kunyi kyau sosai, takama hannun dady d'an k'anina please zokayi lallashi, k'ila idan kaine tayi shiru, tun d'azu take kuka yanzu haka zazzab'ine ajikinta da k'ar tayarda akaimata kwalliyar nanma.
 "Dady ya daure yace anty batasha maganiba ne??
 "Tak'i sha kasan Munneerah Allura da magani🕳duk mak'iyantane"
   Cikin tsokana jafar yace oga aje ayi lallashi, kuma shi kad'ai akace karka zarce, dariya sukasa,dady ya hararesa zan kamaka wlh zakasan dawanda kakeyi
Anty lubna taja hannunsa kaga k'yalesa in kun had'u kwayi.......

billy
{Mrs Abdus'salam}

.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *