check your best novels here

Monday 20 February 2017

AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA? page 63 to end

AUREN K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

63 «*****» cikin fushi yanufi d'akin Munneerah, dak'afa yadoki k'ofar ta bud'e, dasauri Munneerah tad'ago tana kallonsa, jikinta yakama rawa dan tsoro, dan taga dady tamkar mayunwacin xaki, yana xuwa yasauke mata k'yak'yk'yawan mari.
Tadafe kunci tana hawaye.
   " yace ubanwaye yace kikaimin yaro wajan wad'ancan dabbobin ??.
 Tace kayi hak'uri bansan haka xata faruba wlh.
Yakuma nufota yana fad'in oh hakama zaki cemin.
   "Da gudu tanufi bedroom d'inta tarufe harda saka key.
 Ya dunk'ule hannu ya naushi iska, wlh dakin tsaya saina koya miki hankali, yaxo yad'auki Muttallaf daketa kuka, yafice dashi da alama dai Asibiti yanufa dashi.

Su husna kuwa dasuka sha duka, kowacce tasami hanyar fita xuwa gidansu, jiki duk jini suka tari mai mota yakaisu gidan umma, komai motar basu biyaba kud'in saba  suka tafi, yanatayi musu magana sukai banxa dashi, shikam yay musu ALLAH ya isa yatafi.
  Iyayensu maza suna gidan umman ana k'ulla zuwa wajan wani boka dan kashe Alh.EL MANSUR, su ikilima suka shiga suna kwala ihun kuka dakiran sun shiga uku, kowacce jikin baban ta tafad'a tana kuka.
  Suko sun rud'e suna kiran lfy? dan ganin jikin 'ya'yansu duk jini, cikin kuka suka sanarma iyayen nasu abida yafaru.
   " umma tamik'e tana fad'in tafd'ijan wallahi baxai yuwwuba, shi har ya isa yadakeku akan wannan janaren yaron, to aiko ubansa mansur bai isaba bare shi, bari kuga naje gidan naji ubanda ya d'aure masa kugun dukarmin jikoki.
 Abban husna yace umma kiyi xamanki bama saikinjeba muma xamu wajan mansur d'in dakanmu yanxunnan, koma asibiti baxamu kaisuba sai munje wajan ubannasa tukunna.
    "Umma tace ai itama da ita xa'a"

Mom da y'an biyu suna xaune afalo suna hira, kairat tanama kausar kitso, saidai kawai sukaga mutane kansu ko sallama babu, mom tamik'e da sauri tana kallon jikin su ikileema, dan tasan d'antane yay wannan aika aikar, sun kai hakurinsa karshe.
   Umma tadaka mata tsawa to kilaki kin tsaya kina k'are mana kallo saikace wasu bak'inki, ina mansur ??
 Dad dake k'ok'arin sakkowa daga samansa yace ganinan, axuciyarsa yace dama nasan hakan xai faru, dan dady yakirashi tawaya yasanar masa komai.
 Tun kafin ya k'are sakkowa umma tak'arasa gareshi tana zaginsa.
Dad yace kiyi hak'uri umma suma da abinda sukaimasa dan nasan babana mai hak'urine acikin magidanta.....
Cikin tsananin bala'i abban ikileema yace oh hakama kace ko mansur, d'anka yadakar mana yara sannan kakareshi saboda kaidama tarbiyya taimaka k'aranci.

Kausar tace wallahi mu dad d'immu yanada tarbiyya saidai idan kune waccan munafukar tsohuwar bata bama tarbiyyaba....
Marin daya sauka afuskarta yahana k'arasawa, mom tace kausar dama bakida kunya suba iyayenki bane.
Kausar tanufi d'akinsu tana fad'in mom niba iyayena bane, dan baxan ta6a son wanda baya k'aunarkuba wallahi.
itama kairat tace axxalimai kawai haka zaku k'are kundaiji kunya wallahi, kuma haka xaku k'are.

Aiko jin haka yasa su umma k'ara yayyafa ruwan bala'i da zage zage, suka gaji dan kansu dan bawanda yakuma tankasu suka tafi kaisu husana Asibiti ...


billy
{Mrs Abdus'salam}
AUREN  K'ADDARA
              ko  BIYAYYA

Na billkisa ibrahim

65 «******»  yau akayi addu'ar arba in ta umma, su abban ikileema suna Asibiti har yanzu.

Mom da dad suka tsare su dady suna musu fad'a dan ganin kwakwata basa shiri, anmusu nasiha sosai wadda taratsasu.
 Suka tafi gida da d'ansu Muttallaf da tuni ya warke sarai.

Su husna dai an tuba dan sunsan yanxu basuda kowa sai dady, dan haka suke dana sanin abinda suka shuka abaya dan gashinan suna girba d'aya bayan d'aya .

Da daddare Munneerah tad'au wankanta itada yaronta sunata tashin k'amshi mai dad'i, suka nufi b'angaren dady.
Yana kwance akana gadonsa shima cikin shirin barci.
Munneerah tashigo da sallama ciki ciki ya amsa ya karb'i yaronsa yana tawani cin magani, yayta tarairayar d'ansa haryay barci, shima ya kwanta yaja musu bargo.
Munneerah dake xaune tana kallonsu itama tamik'e ta tashige bargon takwanta abayan dady, wasanni tashiga yimasa, masu rud'a jiki.
Shikuma yay fuska abinsa yak'i ko motsi.
Itako tacigaba, can mutiminku yaji yana neman zautuwa aisai yajuyo yafara maida raddi, dan dama akame yake sosai, nan dai suka mantar dajuna fishin, suka bama soyayya hakkinta batare da kwangeba.
   ""Saida komai yalafa sannan suka rink'ama juna dariya, da tsokana, tare sukai wanka, suka dawo makwancinsu dady yahad'asu yarungume yanamai alfahari dasu 

TONIMA INA MAI ALFAHARI DA MASOYANA

IRINSU
ZUMUNTA GROUP 
HOUSE OF NOVELS  GROUP
LABARUN LITTATAFAI GROUP
ABBA GANA 
H BOOK 
HAUSAWA GROUP 
Da dakkan sauran group's daban saniba, ma abota KARATU BOOK D'INA NAGODE! NAGODE!! NAGODE!!! 

ALLAH YABAR ZUMINCI YABARMU TARE.



Dan ALLAH duk wanda yaga kuskure  a book d'ina ko gyara yasanarmin


ALHAMDULILLH. ALLAH KAYAFE MINI KUSKUREN DANAYI ACIKIN WANNAN BOOK, ABINDA NAFAD'A DAI DAI HAR YA AMFANI MUTANE ALLAH KABANI LADA  Amen

I LOVE U ! LOVE U !! LOVE U MY FAN's

AUREN  K'ADDARA
             ko  BIYAYYA

Na billkisa ibrahim 

64«******» dady yakai Muttallaf asibiti aka dubashi, harda targad'e sukai masa, aka gyara masa, Muttallaf yana kuka shima yanayi , har aka gama gyarawa, yad'akko shi suka taho gidan su mom, tafiyarsu umma badad'ewa shikuma yaxo.
    ""Mom takarb'i Muttallaf dasauri daga hannun dady, mom tafara kuka, ohni.bilkisu yanxunan wannan d'an yaron akaima wannan xalincin dan rashin imani??
Dad yakarb'esa shima ida nunsa taf da hawaye, suma su kairat kuka sukeyi, mom tace yanxu ina Munneerah take??
   "Dady yace tana gida itama dukanta nayi"
 To babana in banda abinka itakuma miye laifinta aciki ?
 Dad aitafi kowama laifi wayace tad'aukesa takai musu, ai wallahi ban ma gama mata ba, saina sake xaneta.
  A'a babana kul d'inka kasake tab'ata kaji nagaya maka, yanxuma kad'aki yaronta kakaimata dan hankalinta ya kwanta.
A'a mom abarsa anan saiya warke.
Mom tahararesa idan anbarsa anan kanada abincin bashi ?? 
Kad'aukesa ka kai mata shi nima ina nan xuwa gidan.
Badan yasoba yad'auki Muttallaf ya kaishi wajan Munneerah, saidai yanzu baya shiga harkarta kwatakwata, xaizo dai yad'auki d'ansa yay masa wasa idan dare yayi yasashi agabansa sukwanta dasafe yaymasa wanka ya shiryashi, ko abincin ta yadainaci.
Wannan abu bak'arami dafa xuciyar Munneerah yakeyiba, kullum saita bashi hak'uri amma yak'i saurarenta.


Bari nalek'a su ikileema.
Nashiga gidan umma dan su husna suna gidan naga sun warke sarai saidai tabbunan raunikan.
Yau suka shirya xuwa Nijar wajan wani la'anannen boka.
   "Sun isa Nijar ankuma kaisu har gidan bokan, sun sanar dashi dukkan abinda suke buk'ata, akan akashe dad da mom da dady da Muttallaf, suna son sugaji dukiyarsa, bokan yace musu sun nema sunkuma samu, yahad'a musu asirirrika masu yawa suka taho washe gari.

Sun iso cikin katsina, acikin jibiya motarsu tai had'ari, atake anan umma ta amsa kiran ALLAH, ta mutu, shikam abban ikileema k'afafunsa biyu duksun cire, abban husna kam shima sai abinda ALLAH yay dan baya ganima ga hannu yacire, hancinsa ya gutire da kunne d'aya.

Dad suna kallon labaran yamma suka ga wannan had'ari, kuka dad yakeyi sosai shida mom, suka shirya tafiya jibiya dan ankaisu babban asibitin jibiya.

Shikuwa dady yagani amma tsakima yaja yace kad'anma suka gani.
Su dad sunje suka taho dasu da gawar umma, washe gari akaimata suttura akakaita gidanta nagaski ajecan kuma ataras, su abban ikilema kuma aka kaisu Asibiti, su ikileema sai kuka sukeyi, dad shiyya d'auki nauyin komai na Asibitin.
Su abban husna saikuka sukeyi suna fad'in tsiyatakun dasuka shiryama dad abaya, da wanda yanxun yazama sanadin tsugunnawar su, saidai dad yasa ayi musu allurar barci idan surutun nasu yay yawa......

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *