check your best novels here

Monday 20 March 2017

SABON AL'AMAREE 57/60

[18/03 12:19] bilyn Abdul: [17/03 21:36] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》









NA BILKEESA IBRAHEEM. 
      {♡bilyn Abdul♡}






HIQAYA ONLINE WRITER'S
https://mrsbilkisa.blogspot.com 



57

........Koda suka isa gida sai kowa yanufi ďakinsa, ko sallama basuyima aunty bily ba dake zaune afalon, tabisu da kallo cikin matu'kar mamaki, lalai akwai wani abu a'kasa kenan?, tomike faruwa??, tasan kotaje wajen ya Mahmud bazai sauraretaba tunda ransa a 6ace yake, tadafa kujera ta tashi da 'kyar saboda cikinta yafara tsufa, kofar Nurr tanufa amma koda ta ta6a saita jita gam akulle, tayi tunanin kwankwasawa saikuma ta sake tunani, falon takoma ta zauna cikin jimami da damuwa fes afuskarta.
      Itakam Nurr tana can hankalinta gaba ďaya yana kan buk ďin da dady yabata, ta haye gadonta tazauna tana buďewa.
  Da wani hoto ta fara karo, ta tsurama hoton idanu tabbas suna tsananin kama da matar dake jikin hoton, dabadan itace azaunaba, tasan kuma bata ďauki hotonba datuni tace itace, saidai matar jikin hoton babbace, ta karanta rubutun kasan hoton.
   "Asma'u Mutallaf sardauna".
 Shine taga an rubuta, gabanta yashiga harbawa da sauri da sauri, wato mahaifiyarta ce kenan, wasu siraran hawaye suka fara zirara akumatunta, takai bakinta ajikin hoton ta manna masa kiss tareda rungume book ďin a 'kirjinta, takai minti goma ahaka idanunta arintse amma hawaye nafita daga cikinsu, ta cire littafin daga 'kirjinta tacigaba da dubawa, a gaba kuma hoton wani namijine, hakan na nufin mahaifinta, jitayi batayi wani murna da ganinsaba, amma itama batasan dalilin hakanba, bata wani daďe tana kallonsaba tawuce.
    
                  ashafi na biyu tafara karo da cikakken bayani akan abinda ke cikin littafin.
      Sunana Asma'u Mutallaf sardauna,, ni ďiyace ta goma sha...... agidanmu, hakan yana nufin ni autace awajen iyayena, inada yayye maza da mata masu tarin yawa, wanda mahaifammu suka haifa.
     Muntaso a gidanmu cikin gata da ilimin addini dana boko, dukda iyayenmu masu haline(masu kuďi) matuka hakan bai saka mun lalaceba.
    Musbahu ya kasance ďa ga abokin mahaifina na kut da kut, yakasance maraya saboda rashin mahaifiyarsa data rasu bayan haihuwarsa, wannan yasa mahaifinsa ya ďakkoshi yadan'kama mahaifiyarmu akan ta raineshi.
   Ba'a ta6a banbanta Musbahu damuba, tundaga suttura ci sha, ilimi daduk wani abu da ďa yake samu acikin gidansu, idanma baka saniba saika ďauka shima agidanmu aka haifeshi.
    auren zuminci akeyi agidanmu tunkafin tasowarmu, dan haka muma akai mana, an haďani aure da Musbahu domin shima tamkar ďangidanmu muka ďaukeshi, banyi ba'kincikiba kasancewar dama can muna soyayya nidashi.
   Lokacin da akai aurenmu Musbahu yanuna min soyaya kamar gaske, har ALLAH ya azurtamu da samun ciki saidai kash cikina bai rufa wata uku ba yazube, mun ďauki hakan amatsayin kaddara wadda har Musbahu yanuna damuwarsa fiye dani, in ta'kaicemuku na samu ciki yakai sau 6 amma baya kaiwa labari saiya zube, ban ta6a yunkurin zuwa asibitiba kasancewar mijina likitane, dan haka idan yadubani saiyace babu wata matsala lokacin haihuwarne dai baiyiba.
    Ban ta6a kawo komai arainaba, hakama ban ta6a zargin kowaba, ahaka muka kai shekara biyar da aure nida musbahu.
      Rana tsaka yazomin dabatu akan komawa kano gidan mahaifinsa, hankalina yatashi harma naje gida na sanarda mahaifana, lallashina suka shigayi damin nasiha, sun nuna min abinda zaiyi shine daidai saboda kowa da gidansu yake ado, nayi ba'kincikin haka amma babu yanda zanyi dan kowa bai goyamin bayaba.
    Damuwar dana shiga yasa Ya Abdul'malik yabani mahmud akan natafi dashi wajena sun bani, hakan yayimin daďi dan kaf family ďinmu banida 'kawar data wuce majaifiyar Mahmud, ina kaunarta matuka itama tana kaunata, sanda aka bamu mahmud bai wuce shekara 6 ba aduniya.
    Haka muka tarkata mukatafi kano ina kukan rabuwa da dangina, dan kusan nice aka ware acikinsu, amma dayake inason ya Musbahu sai bakincikina ya ragu.
    Humm komawata kano tasani damuwa matuka domin kuwa tarbiyyar gidansu Musbahu bata minba, shikansa mahaifinsu yanda yake mu'amalla dasu babu tsari, nayi mamaki matuka yanda ada danake kallonsa daga nesa nake masa kallon mutumin kirki, kenan yanayin fuska biyu agaban mahaifinmu, tokomadai miye gamu a family ďin ya Musbahu.
    Munada babbancin tarbiyya gsky shiyyasa nashiga damuwa matuka zamana a cikinsu, rayuwa ake gudan tamkar ta yahudawa babu tsari bare birgewa, wanan yasa na tsame kaina acikinsu banida abokin hira sai mahmud, idan yatafi makaranta kuwa ina ďaki kulle amma wanan bai hana kannen musbahu biyoni suna bugamin kofaba saboda 'yan akuyanci.
   Abin yafara damuna sainayima ya Musbahu magana, amma abin mamaki bai nunamin wata damuwarsaba, saima cemin yayi k nanfa bakamar rayuwar gidanku bace ta takura, munan kanmu awaye yake, bamu ďauki a'kida mai zafi munsa aranmuba, dan haka idan zakiyi yanda kowa keyi kiyi, idan kuma bakida ra'ayi ki kama kanki, dan bazan ďauki salon kawo zugar 'yan uwanaba.
   Tab lallai wanan abu yasakani acikin maye da ruďani, amma saina danne kodan Mahmud dayake shiga damuwa idan na shiga, ko yaya yaga fuskata ta canja shima saiya fara kuka, dan haka nafara ke6e damuwata dan karya gani, ana haka nasamu ciki amma shima saiya zube, nanma ban kawo komaiba.
    Ahaka muka cigaba da tafiya, har wataran naga abin yafara sakani cikin ruďu akan addinina dan haka nasake yoma Musbahu magana,, humm awanan rana naci duka bana wasaba tamkar kurar wasa, bayan yagama dukana kuma yabar gidan, nikuka Mahmud kuka, dan kuwa yaron yanada hankali sosai dukda 'karancin shekarunsa, ahaka muka kwashe tsawon shekara goma a kano, ina cin ba'kar azaba agurin musbahu, amma nakasa faďama kowa saboda ina tunanin kona faďa baba bazai yardaba, ita kanta mahaifiyar Mahmud nakasa faďa mata, kowa yakawomini ziyara yaga yanda narame nayi baki idan yatanbayeni sainace babu komai.
   Babu wanda yata6a kawo musbahu zaimin haka danhakama basu kawo komai aransu gameda halin danake ciki.
    Wata safiya muka tashi da ba"kin cikin kama mahaifin musbahu da akayi a airport ďin kasar amurika (America) da hodar ibilis, ya ilahi hankalin duk wani masoyinsa ya tashi, wasu suce basu yarda zai iyaba sharri aka yimasa wasu kuma dama sun san yanayin harkar ta karkashin kasa.
   Mahaifina yana ďaya daga cikin waďanda basu yardaba, dan haka yashiga cuku2n fito dashi saboda kasancewarsa baban ďan kasuwa kuma sananne.
    Bamusan miya faruba saidai ganin musbahu akayi da sojoji sunje har gida sun kama baba, tashin hankali wanda ba'asa masa rana kenan, tun anan yayenmu suka fara tambayar ba'asi amma sai akace baza'a bama baba ikon yin magana ananba dan haka su biyosu.
    Koda akaje inda akakai baba sai suka sanar dasu ana tuhumarsa da saida miyagun kwayoyi kuma shinema yasakama mahaifin musbahu dan akamashi shikuma yayi basaja.
    Tabďijan inji mata, tunda musbahu yafara maganar yayena suke kallonsa dan basu ta6a tunanin fitowar wanan magana daga bakinsaba, nanfa suka tasammasa da faďin yafaďi gsky fa, humm musbahu ya kekashe kasa yace gskyar kenan.
    Bayan kwana biyu da faruwar haka aka tafi da babanmu kasar amuruka akan tuhumarsa da saida hodar ibilis, wai duk kuďinsama tana yasamesu, munyi bakinciki matuka danhaka musbahu yana dawowa nace yasakeni.
    Naci duka ranar saboda firicin danayi, aiko yaďaukemu cikin dare yakai wani gida nida Mahmud, bamusan inaneba bare mu kubtar da kanmu, awani ďaki akakaimu mu biyu, daganan bamusan halin da'ake cikiba gameda kes ďin su baba.
    Kulum ta ALLAH sai anzo ammana duka nida Mahmud, kuma abincima kaďan ake bamu, sauďaya arana, hakama ruwa, duk sanda musbahu kuma yaso zaisa aďaukeni akai wani ďaki danya kusanceni, wanan abu namin bakin ciki matuka, domin kuwa ko sallah bama samunyi tunda ni banida tsarki dan koya gama abinda zaiyi dani baya bani damar tsarkake jikina, ahaka nafara laulayin ciki.
    Humm musbahu yazo yabani magani da karfin tsiya nasha cikina yazube, a wannan lokacin nagane cewa dama shike zubarmin daciki, baima 6oyeminba yasanar dani haka, dan yace baya bukatar haihuwa ayanzu, nayi kuka sosai nida Mahmud, mahmud har zazza6i yayi saboda kuka, da'kyar naroki mai kula damu ya taimaka min da ruwa na gyara jikina dayake akwai bayi ađakin...............



              58

........duk wanan abun dayake faruwa anacan ana nemanmu agida, dan Musbahu ya ce, "baisan inda mukeba shima ya wayi garine kawai bai gammuba.
    Tashin hankali biyu yataso family ďinmu gaba, gana rashin baba gana 6atanmu.
   Ana haka aka yankema su baba hukunci ďaurin rai da rai, duk wani masoyinmu yashiga tashin hankali, anata kuma zagin mahaifin musbahu dan ansan shiyayi wanan zargen har aka saka mafita, saikuma hatsabibin ďansa dayaketa rantsuwa akan saboda koken da baba yake siyarwa yasa yabaro gidanmu.
    Anzo bincike har gida kuma sun samu hodar ibilis agidanmu, wanan duk yana cikin kullin musbahu saboda yasan sirrin gidanmu gaba ďaya, danhaka yayi yanda yayi yakawo koken cikin gidanmu, baikuma 6oye manaba yafaďa mana duk kullin dayakeyi akan mahaifina.
    Saidai kawai na rungume Mahmud musha kuka, ahaka nakara samun ciki amma awanan lokacin bai saniba, ALLAH ya makantar da jinsa da ganinsa akan cikin dake jikina, ALLAH sarki Mahmud haka yayta ďawainiya dani idan nayi amai, abincin da'ake bamu baya isarmu amma haka mahmud zaiki ci yabarmin naci, asana  mahmud yana shekara 18 danya gama secondary ďinsa, danaga Mahmud yafara fita hayyacinsa saboda yunwa saina daina yarda naci saidai muci tare, ganin haka yasa Mahmud yafara rokon mai kula damu akan ya ringa karamana abinci saboda baya isarmu gashi kuma bamuda ishashshar lafiya.
     Mai kula damu bai kiba saidai yace akwai sharaďi indai zai dinga bamu abinci fiye da yanda aka umarcesa tofa zai dinga yima Mahmud bulala ashirin kullum, da sauri mahmud ya amince amma ni nace ban yardaba.
    Bansan mahmud ya lla6a ya sake rokon mutuminba.
   Haka yakara mana abinci, amma kullum saiya yima mahmud bulala ashirin, jikin mahmud duk yafashe cikin sati ďaya danba dukan wasa yake masaba, hankalina yatashi matuka amma banida damar hanawa.
    A family namu kuwa andage da addu'oi aduk masallatai dake cikin kaduna harma da wajen kaduna dan baba mutumne na mutane.
    ALLAH gafurun rahimun sai gsky ta bayyana aka gane baba baya ta amulli da saida miyagun kwayoyi, aka sakkoshi, aka sake kama mahaifin musbahu, tofa awanan rana Musbahu yay niyyar kashemu saboda abin yay masa ciwo matuka.
     Bai 6oye manaba ya zayyane niyyarsa akanmu, amma wai ba rana ďaya zai kashemuba, dan haka muza6i wanda za'a fara kashewa, da sauri Mahmud ya ce, "afara takansa dan bazai iya ganin an kasheni agabansaba, nima kuma nace saidai afara ta kaina.
    Washe gari aka kulla igiya da shirin ratayemu, angama shirin komai dan har an ďora mahmud akan tebir inata kuka saboda tashin hankali, kamar daga sama aka bugo kofar ta buďe saiga sojoji da ya usman da Abdul'malik, atake anan aka damke su musbahu, mukuma aka kwashemu sai asibiti.
    An bamu taimakon gaggawa dan muna cikin halin ha'ula'i kam awanan lokacin, in ta'kaicemuku dai munsami taimakon gaggawa ga dangi.
   Cikin amincin ALLAH muka warke cikin wata biyu, lafiyalau mukadawo kamar yanda muke saidai rama, itama ahankali muka fara kiba.
    Dayawa dangi sunce azubar da cikin jikina amma mahmud yayta kuka shifa yanason abinda zan haifa, nima da nayarda azubar amma saboda tashin hankali da Mahmud yashiga yasa nace nima inaso abarmini.
    Haka nayita rainon ciki kusan tareda mahmud dan baya matsawa konan dacan, koda yaushe yana tareda ni har ALLAH yasa na haihu mace.
    Mahmud yayi farinciki dan har yafini farinciki nida na haifi 'yar, ina tausayin ďiyata dan ina tsoron kar abinda mahaifinta yay min yashafeta itama mijin dazata aura yaymata haka, dan ance duk abinda kayi kaima sai anmaka.
     Hakadai nayita rainon yarinya dataci suna nan mahaifiyarmu wato Maryam, amma muna kiranta da Nurr, babu wani taron suna da'akayi dan nace banaso, babu lalashi daba'a minba amma nace banaso, ahaka Nurr tacika shekara ďaya, sanan Mahmud yafara karatunsa a jami'a, amma dukda haka saida yayima Nurr bikin cika shekara ďaya, awannan ranane nayi al'kawarin mallaka masa Nurr har abada indai har yana sonta amatsayin mata, nayi hakane saboda Mahmud kawai nake ganin zai iya ri'ke Nurr tsakani da ALLAH, batareda ya kyaretaba bare cutarwa.
   Mahmud yayi matu'kar farinciki kuwa  hakama baba da ya Abdul'malik.
     Bayan kwana uku dafaruwar haka natashi da ciwo wanda yakasance mini ciwon ajali.........

BAYAN RASUWAR ASMA'U.
    Rainon Nurr yakoma hannun mama mahaifiyar Mahmud, alokacin tana goyon Saiff dan haka suka tashi tamkar tagwaye, ita kuma mami tana goyon madeena (deena) kenan, mama ta ďauki son duniya taďora akan Nurr fiyema da 'ya'yan da ta haifa.
    Babu mai ta6a Nurr ta yarda, Nurr ta tashi cikin gata batareda tasan wani abu shi maraiciba, harta shiga shekara ta takwas, alokacinne kuma Alh mutallaf yashiga ciwo, ganin kamar bazai tashiba yasa aka ďaura auren Mahmud da Nurr domin cikama Momy Asma'u burinta, bayan ďaura aure da kwana goma yace ga garinkunan.
    Sardauna family sunshiga ruďu da rashin mahaifinsu, hakama al'umma sunyi kukan rashinsa, dan mutumne mai taimakon al'umma, duk hanyar dazaibi dan nemawa matasa aiki yasani.
    Indai aka tauye maka hakkinka kaje gareshi tofa saiya kwato maka hakkinka koda shi zai cutu, Alh mutallaf yakasance babbar katanga ga 'yan arewa, amma yau ALLAH ya ďaukeshi.
    Bayan lafawar rasuwarsa Nurr tacigaba da zama wajen mama batareda tasan ala'kar dake tsakaninta da ya Mahmud ba, har kawo randa za'a akita gidan miji.
    Wanda zuwa sanan mahaifinta yarasu kuma an aiko har family ďin amma babu wanda ya damu da rasuwarsa.

Nurr tunda tafara karanta littafin take shashshekar kuka da tsinuwa akan azzazlumin mahaifinta mugu da kakanta, kuka take tamkar ranta zai fita, tabuďe wata takarda dake kunshe acikin ambulan, ga abinda ke ciki.

Assalamu alaiki ďiyata.
    ALLAH ya kaddara bazan rayu dakeba, amma inamai nasiha gareki idan har kin girma kin mallaki hankalinki har kika tsinci kanki agidan yayanki Mahmud.
   Kiyi masa biyayya, idan kika sa6ama mahmud kodana minti ďaya ban yafemikiba saidai akan kuskure.
    Kiyi masa biyya dan mutumne mai muhimmanci arayuwarki.
    Karki rabu dashi.
  Idan kikayi haka bazan yafe mikiba.
   Ban yafeba! 
      Ban yafeba.!!
          Ban yafeba.!!!

Kuka Nurr ta fashe dashi, tamike da sauri tafice kamar wadda hauka ya saukar mawa.................








Luv u oll my fan's
©2017
[19/03 10:34] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》
🔚
      🔚
            🔚





NA BILKEESA IBRAHEEM
    {♡Bilyn Abdul♡}





HIQAYA ONLINE WRITER'S 
https://mrsbilkisa.blogspot.com 
Wannan page ďin nakine amarya teema, ALLAH yasanya alkairi yabaku zaman lafiya keda angonki, ALLAH yasa baďi mudawo suna. 
     Kuyi hakuri darashin jina kwana biyu wlhy nayi busy ne,  ina muku fatan alkairi arayuwarku




59 & 60

........Dagudu tafice daga ďakin, aunty bily dake zaune afalo tun ďazu takasa tashi tabi Nurr da kallon mamaki, saman ya Mahmud tahaye tana rubzar kuka, yana falo kwance akan doguwar kujera idanunsa alumshe, da'alam yana duniyar tunani, yatashi zaune da sauri danjin shigowar Nurr tana kuka, jikinsa tafaďa yay mata 'kyakykyawan ru'ko, sai kawai jiyayi hawaye sun fara zirara daga idanunsa shima, Nurr ta tuna masa abinda ya wuce shekar 34 dasuka wuce, shima kuka yashiga rerawa tamkar wani mace, shida Nurr ďin aka rasa wanda zai lallashi wani, saidai aikin shafa kanta yakeyi ahankali, itakuma tana 'kara lafewa ajikinsa tamkar wata mage.
   Sunkai tsawon minti 30 ahaka suna abu ďaya daga baya ya Mahmud ya lallashi kansa, ahankali yaďago fuskar Nurr daga jikinsa yana mata murmushi, itama batadan sanda ta maida masa murtanin murmushinba, yasake rungumeta tsam ajikinsa, yana kara faďaďa murmushinsa wanda shima baisan dalilin yinsaba.
    Ahankali yaji dashashshiyar muryar Nurr tana furta I luv u my yaya.
    Yasake ďago kanta da sauri Nurrina da gsk kina sona???, taďaga masa kai tana rufe fuska alamar kunya.
   Yaci gaba da faďin maryam kin amince zaki cigaba da zama dani???, zaki sake haifamin abinda ke cikinki da 'kannensa??, bazaki rabudaniba har abada??, duk cikin rikicewar murna yake jero mata waďannan tanbayoyin??.
     Taďago matsakaitan idanunta dasuka jajur tana kallonsa, ahankali ta ce, "yaya na amince da dukkanin bu'katarka, zan zauna dakai, zan haifa maka yaran dakakeso insha ALLAHU, wlhy yayana inasonka ina 'kaunarka, bakuma zan daina sonka ba har 'karshen numfashina, tayi saurin sakkowa 'kasa ta durkusa agabansa, yaya dan ALLAH ka gafarceni akan abinda namaka abaya......takasa karasa abinda takeson faďa saboda kuka daya sarke muryarta.
   Shima sakkowa yayi kasa yay saurin rungumeta ajikinsa, nayafe miki Haskena dama ni ban ta6a fushi dakeba, akullum ina miki uzuri, kuma ina 'kaunarki bazan daina 'kaunarkiba har abada Haskeena, ya ALLAH na gode maka daka kawoni randa Nurrina ta amince da 'kaunar danake mata, ta fahimceni harta ďaukeni amatsayin miji kuma uban 'ya'yanta, matseta sosai yasakeyi tamkar zai maidata cikinsa, bayan wasu 'yan muntina yaďago fuskarta suna kallon juna sai murmushi sukeyi, Nurr takama hannunsa ta rumtse anata, taďan langa6e kai gefe tana kallonsa, yauce rana ta farko data tsaya tayi masa kallon tsaf, tabbas ya mahmud yanada 'kyau dukda kasancewarsa ba'ki sosai, abin alfaharin kowace macece inhar tasameshi amatsayin miji, yanada kwalitis masu yawa wanda sukaďai dasuka kasance matansa suka sani, saima yayi dariya fararen hakoransa sun bayyana da wushiryarsa matsakaiciya datakan kara masa armashi wajen kyawu, uwa uba kwarjini da ALLAH yayi masa na musamman.
   Ya bushe mata idanu takawo numfashi da da sauri, saikuma suka tuntsure da dariya, yaďan lumshe idanunsa tareda sumbatar hannunta, nayi miki 'kyaune??, yatambaya yanaďan zaro idanu kaďan, ta sakar masa murmushi har kumatunta suka lotsa, ahankali ta furta sosaima.
    Yajawota jikinsa yana 'yar dariya, cikin kunnenta ya ce, "kiyita kallona haskeena babu mai hanaki, niďin nakine, ina fata zaki shaidama su dady haka asafiyar gobe idan ALLAH yakaimu.
   Ta ce, "insha ALLAHU mijina, ayanzu bana shakka ko shayin faďar ina 'kaunarka agaban kowa, komin tarin ko dandazon jama'ar kuwa, ta raunana miryarta ya mahmud kai mutumin kirkine adalin namiji mai kuma matukar muhimmanci arayuwata, kataka matukar rawar gani acikin rayuwata tun ina ciki, ayayin dakuke fuskantar zalunci daga azzalumi musbah........da sauri ya Mahmud yarufe bakinta, Nurrina ki daina faďa har yanzu yanan amatsayin mahaifinki bakida kamarsa........ta zame hannunsa daga kan bakinta, ta ce, "niba 'yarsa bace domin kuwa baima san dazamana aduniyaba, ALLAH ya isa tsakanina dashi......haďe bakinsa da nata yayi, yashiga mantar da'ita 
duk wata damuwarta, tabbas yau ya Mahmud yashaida Nurr tana 'kaunarsa, dan tabada muhimmiyar gudummawa afagen soyayyar tasu mai daďďen tarihi, ta nuna masa itamafa ta kware afagen karatun nasa, takuma haddace duk abinda ya koyar da'ita harma tana 'ko'karin zarcesa, yaukam sababbin ango da amarya suka koma fil masu tsananin so da 'kaunar junansu, yaukam dabance acikin aurensu dan har sun sakata cikin tarihin rayuwar auren nasu.
   (Nima nayi matu'kar farinciki masu karatu, dama kullum burina naga Nurr ta 'kaunaci ya Mahmud, tokuwa saigashi ranar tazo).
     Washe gari har 'karfe takwas suna manne da juna, dan ya Mahmud ya hanata wani kwakwkwaran motsi, datace ihin!!, zaice miye damuwarki??, jikinta kam sai ciwo yake saboda murzar datasha ahanunsa, kwankwasa kofar da'akene yasa suka tashi, ya Mahmud ne yatashi yaje ya buďe saiyaga aunty bily, rungumeta yayi tareda mannawa cikinta kisses guda uku, ya ce, "kuna lafiya my bily??, ta ce, "dadai sauki kam, da sauri ya ce, "miye matsalarki??.
   Ta taka ahankali zuwa cikin falon shikuma yana tsaye yana binta da kallo, ta juyo suna fuskantar juna, yaya damuwata itace taku amma kun lilli6eni bakwason sanar dani, bansan miyasaba??, kokuwa ban cancanci na sani bane oho??.
     Yazo da sauri yasake rungumeta bama 6oye miki komai dan baki cancantaba, saidai dan kare lafiyarki bilyna, bawani abu bane dama kanwarkice tasamu ciki, saitace saita zubar, shine nakai kararta wajensu dady, kinji abinda yafaru, amma yanzu komai normal ta hakura.
   Nurr dake la6e tana jinsu tasaki ajiyar zuciya taji daďin abinda ya Mahmud yay mata, taji daďi daya rufe sirrinta dana mahaifanta.
   Fitowa tayi itama takama hannun aunty bily tana bata ha'kuri, akan damuwar dasuka sakata aciki, aunty bily ta ce, "karku damu yawuce babu komai, nayi muku uzuri, rungumeta sukayi suna sake bata hakuri, wlhy yawuce kunji, daga nan nasiha tashiga yima Nurr mai shiga jiki da ratsa zuciya, sanan suka sakko falon 'kasa domin yin breakfast, da aunty bily ta 'ko'krta wajen haďa musu.
     Bayan sun kammala sukayi shirin komawa gidan dady, sukacema aunty bily zasuje gidan dady dan yace su koma yau da safe.
   Aunty bily ta ce, "babu damuwa sai sun dawo.
     
GIDAN DADY.
       cikin 'yan mintuna suka isa gidan dady saboda babu nisa tsakaninsu, dady yana gida bai fitaba yana jiransu, tunda suka shigo yake binsu da kallon mamaki dan ganin fukokinsu cike da annuri, yabasu izinin zama bayan sun gaidashi, zamansu babu daďewa mama da mami suka shigo, Nurr da ya mahmud suka gaida iyayen nasu dan basuje ďakin kowaba, shiru ya gifta naďan wani lokaci, dady yay gyaran murya batareda 6ata lokaciba inason kusanar dani saka makon maganar jiya da'aka fara, Nurr da ya mahmud suka haďa ido tareda sakarma juna murmushi, dady dasu mami suka kalli juna suma.
    Dady ya ce, "ina saurarenku, ya mahmud yay 'kasa dakai yana murmushi, dady komai ya wuce mun daidaita kammu, babu sauran wata matsala yanzu.
   Dady ya jinjina kai inason jin hakan daga bakin Nurr ne.
  Nurr ta ce, "duk abinda ya mahmud yafaďa dady hakane, na amince zan zauna dashi har karshen rayuwata kuma cikin so da aminci.
   Dady ya washe baki kai amma naji daďi sosai, haka akeson mutum yakasance ALLAH yay muku albarka kunji, amin suka faďa suna kara yin kasa da kai saboda kunya.
  Nurr tafara shashshekar kuka dady dama haka azzalumi musbahu yay muku da momyna ALLAH ya isa ban yafe masaba, dady miyasa kuka 6oyemin, naso ace kunsanar dani tun ina karama nayita tsinemasa har karshen rayuwata...mama tajawota jikinta tana lallashi, saida ta tsagaita da kukan sanan suka shiga yimusu nasiha mai tsuma rai da zuciya, musamman ma Nurr anmata nasiha sosai akan muhimmancin iyaye komi suka maka, sun ďan daďe agidan daga baya dady ya sallamesu.
   Suna mi'kewa danufin tafiya saiga su waleeda, aiko ganin iyayensu suka manne musu, babu lalla6awar daba ayiba amma suka nani'ke akan sai sun bisu, dady ya ce, "shikenan kutafi dasu daga yau kuma yaye ya'kare, aii sunyima 'kokari, dama mamansu bilkeesu tanata mana zarya, wai anzo gaishemu nasan kuma dan 'ya'yanta take zuwa.
    Dariya suka saka gaba ďaya mami ta ce, "dama kawaici kawai ake mana, amma an kagara sukoma, to aii yau anbasu saisu gaida gida suda 'ya'yansu mama tafaďa tana ďan murmushi, daga yau kuma karna sake ganin kafafunku, dady da mami suka tuntsure da dariya.
   Ya mahmud dama haka yakeso, sukayi musu sallama suka taho.
   Ahanya Nurr ta ce, "Kai yaya ALLAH baka 'kyautaba, ya kalleta saboda mi kikace haka??, saboda amso su waleed daga gidan dady, yayi dariya haba 'yammata ainayi hakurima, wata biyu fa, kema dakiketa wani noke2 nasan kinyi missing nasu, nida bily munata kewarsu wlhy, aiko idan nice wlhy ko yini bazan sake ďaukarsuba, yayi dariya kawai batareda yayi maganaba, dahaka suka 'karasa gida, aunty bily tayi farincikin dawo war su waleeda, har ďan faty tahaďa na murnar dawowar yaranta  aunty bilynmu nakine ooh.
     
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, Nurr da ya mahmud anata shan soyayya kamar su cinye juna, dama gashi yanzu mijin ahanunta yake, saboda aunty bily ciki ya tsufa, soyayya suke zabgawa kamar babu gobe, abin sai wanda yagani (na ce, "ALLAH ya cida 'yan baya haka irinsu Ayeesh da ikilee).
     Cikin amincin ALLAH aunty bily ta haihu, ta sambaďo ďanta namiji kyakykyawa sankon kowa kin wanda yarasa, kai zokaga murna gun Nurr da uban gayya ya mahmud, hakama dangi sunyi murna dan aunty bily tasha fama na asarar babys datayi tayi abaya, to gashi ALLAH yabata itama, dama ance mahakurci shine mawadaci.
    Komai Nurr tanayi, Duk abinda yadace tayima mai jego tanayi, tana bata kulawa yanda ya kamata, agefe kuma tana bawa ya mahmud tasa kulawar ta musamman, saikuma 'yan yaranta datakema aunty bily kara akansu.
    Bayan zagayowar sati yaro yaci suna habib sunan dadyn aunty bily, suna cemasa Arfat, to saimuce ALLAH yaraya Arfat gambon 'yan biyu waleed da waleeda.
      Bayan suna aunty bily da sati biyu deenama ta sauka ta haifi mace, masha ALLAH itama tasamu Aysha ALLAH yaraya Aysha humaira. Ameen.
    Sun cigaba da zuwa makaranta yayinda Nurr taketa rainon cikinta dayayimata ďas yasakata fari da jiki, dan har wani 'yan mazaunai ta ajiye na musamman, waďanda suke burkita kwanyar gwaskan nata ya mahmud.
   Ya Mahmud yana nunama matansa da 'ya'yansa soyayya ta musamman, yana 'kokarin nuna adalci atsakaninsu, koda yaushe yana manne da 'yayansa da matansa ababen tushen farincikinsa.

To ALLAH dai yasauki Nurr lafiya, ansamu mace AMEENATU, bayyana muku yanda shagalin suna yakasance 6ata lokacine, amma komai yabada ma'ana.
   Bayan kawana biyu Khairat da rabi'a suma suka haihu, zoga murna wajen ya mustapha da ya mubarak suma sunzama baba ooh.
    
BAYAN WANI LOKACI.
      ya mahmud yau yana gida kasancewar weekend ne, Nurr da aunty bily duk suna falonsa harma da yaran, zuwa yanzu meenal da Arfat babu inda basa zuwa ga surutu kamau akkuna, sunata wasansu iyayen nazaune suma suna hirarsu.
     Ya mahmud sai binsu da kallo yakeyi, wani daďi yakeji idan yakalli yaran, yanzufa nan duk mallakinsane shi kaďai yađan lumshe idanu yana sakin murmushi, Meenal da Arfat sukazo suka faďa jikinsa suna kiran Abba abba!!!, yakama hannunsu yana murmushi yaran abba ya akayine???.
   Abba ka kaimu gidan dady yau ko gidan uncle dady, ya mahmud yay dariya, wato yarannan kun maidama fahad suna uncle dady ko??,  waleed da waleeda dasuka girma sosai suma suka 'karaso suna faďen dady muma zamuje gidan dadyn.
   Ya mahmud yace watodai yau kowa yawo yakeji, suka haďa baki suna faďin ehh Abba ehh abba suna faďi suna tsallen murna.
   Ya maida kallonsa gasu aunty bily dasuke kallonsu suna dariya, ya ce, "to inaga harsu momy suma su shiya kawai mufita yawon buďa ido da shan askirim, yeeeee yaran suka ďau ihun murna danjin za'a shan askirim.
    Nurr ta ce, "kai abba ammafa mun gode dama zaman gidan duk ya ishemu, yaďaga musu gira tareda kanne ido ďaya, sukace yarankadai masu wayon tsiya suna kallonaka, dariya kawai yayi yamike..
   Dandanan suka gama shirinsu suka fice, ya mahmud da aunty bily suna gaba, Nurr tana baya tareda yara, data ďago saisu haďa ido da ya mahmud ta madubi yana kallonta, saidai su sakarma juna murmushi kawai, haka yayta yawo dasu wajajen sha'katawa da wasan yara na musamman, sai dare suka dawo gidan cikin farinciki da 'kaunar juna....

     Tonima inamai farincikin kammala wanan ďan littafi nawa masoyana.
      Ina godiya ga 'UBANGIJINA daya bani dama da basirar rubuta wanan littafi nawa daya kasance sadaukarwa ga masoyana, Abinda nafaďa dai2 ALLAH kabani lada, wanda nayi kuskure ALLAH ka yafemini.
     
     SADAUKARWA GA MASOYANA.
       karku manata masoyana wanan littafi sadaukarwane agareku, dan haka banida damar ware sunan wani, saidai ina alfahiri daku gaba ďaya, duk inda masoyina yake bana mantawa dashi ina alfahari daku da wanda nasani da wanda ban saniba, ina godiya ga group group da admin's nasu, ALLAH yabar 'kauna, nagode da ďumbin soyayyar dakuka nuna mini, nima ina 'kaunarku bakuma zan manta dakuba, muassaman ma 'yan group ďina ina alfahari daku, luv u oll my FAN'S.

    KUNA RAINA 'KAWAYEN KWARAi.
ummi sani tyw
Hadiza ďayyabu fama.
Fateema ďayyabu fama.
Sadiya sulaiman tyw
Zakiyya liti tyw
Ameera musawa.
Sadiya Abdulahi tyw
Bahijja musa tyw
Hauwa muh'md Nsrw
Umayya yuseef R/gado
Fa'iza zakari tyw
Nafisa ibrahim Gidan mutum 1
Bariya salisu yashe
Hadiza umar fama.
Zainab adam tyw
Ikileema muh'md kano
Zahariyya idiris R/gado.
Hadiza yakubu tyw
Rabi'a lawan tyw
Ru'kayya muh'md tyw
Nafisa kabir tuge
Shamsiyya kabir tuge
Halima lawan fama
Jamila Abdullahi bichi
Aysha safiyanu kabagiwa
Naja'atu Rabi'u R/gado
Zuwaira Abdullahi kabagiwa
Fateema musawa
Bilkisu musawa (nana)
Aysha musawa
Sa'adatu musawa
Amina Rabi'u na iya bichi
Zainab adam bichi
Sha'atu Nuhu bichi
Hauwa'u giďe Dutsamma
Maryam Tasu'u tyw (ALLAH yajikanki ya gafarta miki, yaraya abinda kika bari.
      Ina mi'ko gaisuwa gadukkan 'yan 2010 Graduation (Zolo) na D/zabuwa, ALLAH yajikan waďanda suka rasu, waďanda suka haihu kuma ALLAH yaraya mana yaranmu, waďanda basuyi aureba ALLAH yabasu miji nagari.
     Sako daga
   (Bil~Gur)'yar tsanyawa

   To masoyana saikunjini asabon buk ďina maisun BAN SAKETABA.
    shima zaizo muku danasa sabon salon, faďakarwa, nishaďantarwa, ilimantarwa, kardai nacikaku saikun gansa.
   Saidai kuyi hakuri dan zaiyi jinkiri wajen zuwa gareku, saka makon shirin bikin 'kanwata damukeyi, amma bayan biki zakugansa, banaso nafara kuma na tsaya.
   Kardai ku manta da sunan.
 BAN SAKETABA!
         BAN SAKETABA!!
                 BAN SAKETABA!!!
SAIKUNJINI!!!!!!

    TAku bilkeesa ibrahim (bilyn Abdul).
    Writer ďin
RASHIN SANI
AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA
'KANWAR UWACE ko KISHIYAR UWA.
NI DA AMINIYATA
NAWAFF
KUKAN KURCIYA....
SABON AL'AMAREE.
     

Taku bilyn Abdul

bye bye.

LUV U OLL MY FAN'S
©2017
Share:

SABON AL'AMAREE 54

《《SABON AL'AMAREE》》







NA BILKEESA IBRAHEEM
    {♡bilyn Abdul♡}




🏻HIQAYA ONLINE WRITER'S🏻
https://mrsbilkisa.blogspot.com 




5⃣4⃣.

........Cikin lokaci 'kankani gidan yacika da dangi, tuni su deena sun iso harda amarya khairat, su aunty suhaila aunty khadija duk suna gidan, an haďu anata barkwanci, jarirai kowa yagani saiya yaba, har zuwa dare mutane suna tururuwar zuwa ganin baby's.
     Sai bayan isha'i suka lafa, suma deena suka tafigida, yanzuma mamace tadawo tayima Nurr wanka dan tunda safe takoma gida, suma jarirai akayi musu, sanan mama tatafi gida bayan ta shirya yaran.
     Gidan shiru saisu kaďai, ya mahmud ma baya nan, aunty bily tana zaune aďakin Nurr ri'ke da jarirai, Nurr kuma tana kwance, aunty bily sai yabama yaran take dafaďin kyawun da ALLAH yabasu, Nurr dai bata tankaba saima ta6e baki datakeyi.
   Aunty bily taďago tana kallon Nurr autar mama wai bakijinane??, humm ina jinki aunty bily banida abin faďane kawai, dariya aunty bily tayi kai kodai kina kishine? yarana sun fiki kyau.
    Hhhhh aunty kenan, aiko makaho yashafa yasan nagaba yayi gaba, wlhy babu abinda yaranki zasu nuna mini.......kafin aunty bily tayi magana ya Mahmud yashigo, ohh ashe kuna nan inacan ina nemanki.
   Yaya ai yanzu babu inda zaka ringa samunmu sai gaban sanyin idaniyar mu, ya zauna yana dariya kumafa hakane my bily, Nurr tazame ta kwanta batareda ta tanka musu ba.
   Yauwa yaya dama gardama akeyi dan ALLAH da yarannan da autar mama wayafi 'kyau??, ya mahmud yakali Nurr yana dariya, ya nuna yaransa da hannu.....Nurr ta ta6e baki to aidama kai koba'a faďaba bakinku ďaya da aunty bily.
   Ya mahmud ya tuntsure da dariya, to bily kinji kin yarda kuwa??, inafa batun yarda itama tasan yarana sunfita 'kyau garama ta hakur kawai, ya mahmud yaďanja hancin ďaya acikinsu wow!!! Dan ALLAH my bily kalli hanci har baka masha ALLAH, Nurr ta ce, "kwadaiji dashi, haka sukaita tsokanarta ita kuma tana kare kanta.
    Washegari mama ta turo mai kula dasu saboda dare, tunda babu dama ya mahmud yaringa kwana dasu tana jego, yanzu kuma lokacin aunty bily ne (to kema ALLAH yabaki naki awanan lokacin auntynmu).

Haka suka cigaba da zaman bakwai, kullum dangi suna tururuwar ganin baby, gidan kullum wuni yake da mutane ana hidima, dahaka suna yazo.
    Yau daren suna daga gidan dady har gidan ya Mahmud suna cikin hidima, dady yayima yara huďuba da kansa, har gida yazo ya gansu yay musu huďuba, shima yayi farinciki da samun jikoki daga yaron kirki ya mahmud, kuma babban ďansa abin alfaharinsa.
    To yaudai suna amasallaci aka raďawa yara sunan dady da momy mamar Nurr, wato Asma'u da Abdul'malik kenan, za'a ringa kiransu waleeda da waleed, to saimuce ALLAH yaraya.
    Da yamma kuma akayi taron suna mai 'kayatarwa da burgewa shagali ake tamkar babu gobe, abin sai wanda yagani, naga masu karatu dayawa awajen taron sunan nan, lallai kunyima ya mahmud da Nurr halacci.
   Masha ALLAH taron suna ya kayatar yanda yakamata, sai makiyi zai kushe, kawo muku yanda shagalin sunan ya kasance 6ata lokacine amma nabama kowa dama ta kiyasta azuciyarta da irin farin cikin daya dace.
    amaryar jego Nurr sai shiga ďunkuna take tana fita itada aunty bily, duk sun 'kyayatar da kwalliyarsu masha ALLAH.
    to hakama angon jego ya Mahmud baki yakasa rufuwa sai tallar makilin yake😁dan farin ciki, jiyake kamar yau an masa rahama, ya haďa kayatacciyar walima shida abokansa da sauran 'yan family ďin, iya maza dai akayi walimar cin abincin dayima jarirai addu'oin fatan Alkairi.
   Iyayen yara su ya Fahad sun taka rawar gani suma saidai muce ALLAH yabar zuminci da 'kaunar juna, ameen.
    To zuwa 'karfe tara na dare kowa yakama gabansa akabar mai jego da aunty bily matar kwarai, saikuma ya mahmud angon jego da 'yan yaransu waleed da waleeda.
   'Yan aiki suka ďan rage abinda ba'a rasaba saboda gidan duk ya hargitse da tarkace.
   Yau Nurr duk agajiye take, hakadai tadage ta gaggasa jikinta dan tursasawar inna magajiya, tsohuwar dake zaune dasu, suma yaran akai musu wankan sanan akayi musu shirin barci.
   Aunty bily na kwantar dasu aďan gadonsu ya mahmud yashigo da sallama, sukai masa sannu ya amsa yana tambayarsu ya gajiyar suna??.
   Aunty bily ta ce, "Alhmdllh, amma Nurr tayi gum da bakinta, ya tsugunna ya sumbaci kumatun yaransa, yana faďin 'yan albarka yagajiyarku??.
   Aunty bily tayi dariya, yanzu gajiyarsu zatabi gado aii, shima dariyar yayi, ya ce, "hakane kam my bily, gashima harsunyi barcinsu hankali kwance, amma mu aii saimunyi jiyyar jikinmu.
   Aunty bily tayi dariya ta ce, "aii saima bawa yakwanta zaiji ajikinsa, Nurr dai tana jinsu tayi shiru, ya Mahmud yami'ke zuwa inda Nurr take tana cin abinci, zama yayi kusada ita, to 'yammata wanan wani salon rowane kuma??.
   Nurr taďan kalleshi batareda tayi maganaba, yaja hancinta kokin zama kurmane??, humm da bakina raďam.
   Maganarce ba'a ra'ayin yi damune??, no kawaidai bajin yin surutu saboda ciwon da kaina keyi, o, sorry hayaniya ce kawai, amma kinsha magani??, a'a tafaďa ata'kaice, okey kigama cin abincin kisha magani insha ALLAH zai daina, yagajiyar taro??, ni bana tareda gajiya, dan taron banawabane, saidai katanbayi aunty bily, itace uwar taro, o, hakanefa na manta sorry ashefa ke 'yar karoro ce.
    Aunty bily dake jinsu ta tuntsure da dariya, ALLAH idan kuna wani abu saikace yara......ya Mahmud ya katseta da faďin to kinsan halin gwamnati dai saida lallashi, Nurr ta kalleshi okey nice gwamnatin kenan??, yayi dariya a'a karkimin sharri nidai ban ambaci sunaba ko my bily??, Nurr ta ce, "aii basai ka ambaci sunaba kowa yay zagi akasuwa yasan da wanda yake........dariya sosai ya mahmud da bily sukeyi.
    Nurr dai tayi musu shiru danta sha'ka, itafa bakomai ya mahmud yakeyi ya burgetaba, abu kaďan zaiyi yabata haushi, tana ďan raga masane saboda kwarjini dayake mata kawai, dakuma darajar shi yayan tane.
    Haka sukaita hira har karfe goma, sanan aunty bily da ya mahmud suka mata saida safe suka fice, suna fita ta kwanta sai barci, ko sanda inna magajiya tashigo tayi barci.
    Aďakin ya Mahmud kuwa ya rungume bilynsa tareda bata 'kyawawan sumba, my bily kema lokaci yayi da za'a buďe mahaifarki ki haifomin yara kema, yau Dr yay mini wannan albishir ďin.
   Ta rungumeshi jiki a sanyaye yayana inajin tsoro wlhy, idan dantanine abarni kawai yaran da Nurr zata haifa mana sun ishemu wlhy, kara rungumeta yayi shima, no my bily kema ina bu'katar kihaifa mini naki 'ya'yan, duk saiki haďa sunzama naki, inason naga natara yara dayawa, dan inaso naga babban family kamar yanda Alhaji mutallaf ya haďamu gamunan cuke kamar karmu 'kare.
    Ta shafa kirjinsa karka damu yayana ALLAH yacika maka burinka.
    " amin my bily".

Kwana biyu da faruwar haka aka kwancema aunty bily mahaifarta.
    Nurr tayi murna sosai da hakan, hakama su mama da 'yan gidansu aunty bily.

Haka sukaci gaba da rainon 'yan2 iyalan baba, koda yaushe suna hannun aunty bily, shan nono kawai yake haďa Nurr dasu, saikuwa barci, itama har cikin ranta tanason yaranta, tana yima aunty bily kawaicine kawai da alkunya, Alhmdllh yara sunyi 6u6ul dasu masha ALLAH kamar abani aro, lol.

AKWAN ATASHI.
    Babu wuya gurin "UBANGIJI", su waleeda sun shiga wata na biyar, Alhmdllh harsun fara koyan zama, ya mahmud yayi farinciki sosai, ya ďaukesu ďai2 yana ďagawa sama sukuma suna 6angale masa baki, harsun fara gane dadynsu, aunty bily tayi dariya, yaya yaran nanfa sun fara ganeka wlhy.
   Ya zauna kusada ita ri'ke da waleeda ai saima nan gaba, da nakula 'kyuya sukaso fara yimin basafa yarda dakowa agidannan saike, mamarsuma idan ta ďaukesu sai kuka, saidai idan Nona zasusha, aunty bily tayi dariyar jin daďi, tabbas tanason yaran har cikin zuciyarta, tanaji tamkar itace ta haifesu, tana fata bazata ta6a ban bantasu da 'ya'yan dazata haifaba har abada, waleed yakama zaninta yami'ke, kai yaya kalla kagani, waleed badai tafiyaba kuma??.
    Dariya sosai ya mahmud yake mata, to momy idan banda abinki mutum yata6a fara tafiya wata biyar??, zumuďinku yayi yawafa??, dariya tayi to kanadai ganin yanda yakama xanina yami'ke??, eh yanaso ki ďaukeshine kawai.
    Duk wanan hidimar da akeyi Nurr tana zaune afalon, ita saima kallonsu takeyi kawai, yanda suka zauna suna koďa yara 'kanana haka?, ta ďauke kallonta daga kansu dan ganin sun haďa ido da ya mahmud, murmushi kawai yayi, Nurr ďinsa tana burgeshi akoda yaushe gsky.
    Haka sukaita abinsu batareda ta saka musu bakiba.

Yau tunda aunty bily ta tashi takejin jikinta babu kwari, yanzuma tana kwance kan gado ta kwantar da waleeda da waleed agenta sunata barcinsu, jitai amai yana taso mata, tun tana iya rikewa harta tashi zuwa bayi da sauri, acan tashiga shekashi babu arziki.
   Kamar daga sama saiga Nurr tashigo, dasauri tadoshi bayin danjin kakarin aman aunty bily, ri'keta tayi tana mata sannu, saida tagama tas sanan ta taimaka mata ta gyara jikinta, takamota suka fito, saman gado ta kwanta; Nurr kuma ta ďauki wayar aunty bily domin kiran ya mahmud.
    Bugu ďaya ya ďauka yana faďin assalamu alaiki my bily, Nurr ta ce, "ba ita bace, da sauri ya ce, "Nurrina yaya dai??, wlhy aunty bily ce taketa amai shine nace katuro mana doctor plzzz.
   Da sauri ya ce, "tofa ganinan zuwa gidan.
  To saikazo tafaďa tana kashe wayar, bayin takoma tagyara inda aunty bily tayi amai..................✍🏻







Luv u oll my fan's
©2017
Share:

SABON AL'AMAREE 55/56

[15/03 16:36] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》








NA BILKEESA IBRAHEEM 
    {♡Bilyn Abdul♡}





HIQAYA ONLINE WRITER'S
https://mrsbilkisa.blogspot.com





55

..........Babu daďewa saiga ya mahmud da Dr Asheer, da sauri ya Mahmud ya'karaso gaban gado dan ganin waleed na niyyar faďowa, ya tareshi yana faďin wanan wane irin gangacine zaku ajiye min yaro kan gado, idan yafaďo yaji ciwofa??, jin masifa sama2 ya sa Nurr fitowa daga bayi, dan aunty bily barci ya ďauketa.
    Nurr ta ce, "baccifa yakeyi saidai idan yanzu yafarka".
      daga yau idan kunsan ba'a cikin ďaki kukeba ku daina kwantar dasu su kaďai, tunda zasu iya tashi harma suyi kokarin sakkowa, yanzu daban zoba saiya faďo awajenan ya fasa kai.
    To kayi ha'kuri baza'a sakeba insha ALLAH, yanzu ina doctor ďin??, yana falo bari nace yashigo tunda barci takeyi, Shiru tayi masa, yana fita ta ce, "masifaffe tunda bamuda aikinyi saimu zauna gadin 'ya'yanka.........sallamarsu tasata yin shiru, waleed yana hannun Dr, Nurr ta gaisheshi, ya amasa da tambayar yamai jiki??, da sau'ki tafaďa tana saka hijjab ďin aunty bily dan kayan jikinta 'kananane.
    Ya Mahmud ya zauna yatada aunty bily, ya ďagota zuwa jikinsa sannu bily kinji, ya jikin??, tayi ďan murmushi da sauki yaya, to ga Dr nan zai dubaki dan yasan maganin dazai baki, ta jinjina kai tana gyara zama, Dr Asheer yami'kama ya Mahmud waleed datun ďazu yake zille2n son zuwa wajensa saboda 'kiywa, yana kar6arsa ya kankame aunty bily dake kusada ya Mahmud, ta shafa kansa, ya Mahmud yaďageshi sama yana faďin Waleeden abba yau mom babu lafiya barta ta huta.
     Gwajin farko ya nuna aunty bily tanada shigar ciki na wata biyu, wayyo murna, Nurr kamar itace akace tanada cikin, to balle uban gayya ya Mahmud, aunty bily kam zuciyarta cike da fargaba, tana tsoron abinda yafaru baya karya sake faruwa a yanzu, amma tana addu'ar kar hakan ta faru.
   Dr Ashir yasaka mata 'karin ruwa sanan yatafi.
     ganin tayi barci ya mahmud ya ce, "Nurrina bari naje office tunda tasamu barci, akwai ba'ki damuke jiran zuwansu.
    To ALLAH ya kiyaye hanya, cikin jin daďi ya ce, "amin haskena, yana mamakin canjawar wasu dayawan haleyen Nurr, shin dama idan mutum ya haihu saiya 'kara hankali??, to shidai koma ba haka bane yaga fa'idar haihuwar Nurr, dan haihuwa ta canjata 60% daga shirme koyace kuruciyarta.
     Ya sumbaci kumatunta dana waleed dake wasa a 'kasa, yana kaiwa kofa waleed yasaka kuka, ya Mahmud yadawo yana dariya tokai Alhajina office fa zan koma yaza'ayi kenan??.
    Kayi tafiyarka kawai idan yagaji aii zaiyi shiru, yaďan harareta kina nufin natafi nabar yarona yana kuka, har kukan yaja masa zazza6i, ganin kallon dayake mata ta ce, "ALLAH yabaka ha'kuri, shiru yay mata yamaida kallonsa ga waleed daya wani kankamesa sosai dan kar atafi abarsa, yayma yaron kiss a kai, su waleedi manya, wato kai nan duk wayone karna tafi nabarka ko??, shine kayi mini wanan ri'kon haka??, kamar waleed yasan abinda Abban nasa yake faďa saiya ďago yana 'yar dariya, shima ya Mahmud dariyar yayi.
   Komawa yayi kusada Nurr ya zauna, ko kallonsu batayi ba, ya ďora mata waleed akan cinyarta, Haskena dan ALLAH kimasa wayo nagudu mana, itama ďaukar waleed ďin tayi tamaida masa akan cinya, toni miye nawa, can ta matse muku, ka ďaukeshi kutafi kawai, dan karkabarsa yay kuka har ciwon kai ya kamashi.
   Ya Mahmud yay murmushi to yi hakuri ALLAH inada ba'ki a office kar Fahad yayta jirana, Nurr tayi murmushi a'a kutafi tare mana, ya rungumota ajikinsa itada waleed cikin kunnanta yagaya mata wata magana, da sauri ta ce, "banyarda ba, sai anjima katafi kawai na yarda, Mi'kewa ya mahmud yayi yatashi tsaye yana shafa kan waleed, ya'karasa inda aunty bily da waleeda suke barci ya sumbaci kumatunsu sanan yafaki idon waleedi yafita da gudu, tuni Nurr ta tuntsire da dariya, waleed kuma yafara kuka daya waiga yaga abbansa bayanan.
    Wasa tafara masa saikuma yafara dariya, dahakadai ta hanasa kukan.
      Alhmdllh aunty bily tasamu sau'ki dama ita cikinta bai cika bata wahala ba sosai, saidai kasala da abunda ba'a rasaba, tom yanzu dai dukkan aikin gidan yadawo kan Nurr, komai itace dan ta saukema aunty bily komai, mijinma kusan yanzu ahannunta yake, shiyyasa yake shanawa yanda yakeso, to itama dai takan bada haďin kai dan gwaskan nata gwanine a6angaren sosayyay, ana cikin haka yakawo mata albishir ďin samun makaranta itada deena, sun samu Admission a (B.U.K).
   Wow!!! Zokaga murna wajen Nurr, dan danan takira deena ta guntsa mata suka kaure da murna acikin waya, ya mahmud yana zaune yana kallon ikon ALLAH, ya rikota zuwa jikinsa to Nurrina miye tukuycina??.
    Tasakar masa murmushin da har kumatunta ya lotsa, yaya mikakeso amtsayin tukyci??, ya tsirama kwayar idanunta ido, sunkai minti kamar biyar ahaka suna kallon juna ido cikin ido, yauce rana ta farko da Nurr ta ta6a tsayawa suka kalli juna ido cikin ido itada ya mahmud, wasu abubuwa taga suna fitowa daga idanunsa zuwa nata, yakama hannunta ya rumtse anasa, tasaki wata sassanyar ajiyar zuciya, ahankali ya Mahmud ya ce, "i luv u so very much my Nurri, ina sonki dayawa harma nakan kasa control ďin kaina asonki, Haskena yaushene zaki soni??, yaushene zaki kar6eni amatsayin mijinki???.......cikin raunin murya yake maganar.
     Yabama Nurr tausayi kwarai da gsk, dazata iya yimasa 'karya to da saitace tana sonsa, amma bazata iyaba dan bata iya karyaba bare yaudara, dan haka taja numfashi, azatonsa itama zatace tana sonsane, amma saiyaji ta ce, "yaya mubar zancenan kawai plzzz.
   Idanu ya kafeta dasu cikin damuwa, ahankali ya zare hannunsa daga nata, yazame yakwanta sosai asaman gadon, waleeda yajawo yarungume ajikinsa yana shafa kanta ahankali, yarinyar gaba ďaya takoma kamanin Nurr, yaďan tsura mata idanu dan yana 'kyaunar yaransa sosai, harma baisan adadain yawan kaunar dayake musuba, ya lumshe idanunsa sosai.
    Nurr ma idanu ta tsura musu dagashi har ďiyar tasa, tabass abubuwa dayawa suna tsunkulinta azuciya gameda ya Mahmud amma itafa har yanzu basanshi takeyiba, takuma rasa hanyar dazatabi domin su rabu, tashi tayi tashiga bayi tayo wanka domin yin shirin barci, hartagama shirinta ya Mahmud yana nan kwance a inda ta barsa.
    Ta hawo gadon ta kwanta itama, yana jinta amma ya shareta, jitayi kuma babu daďi, domin yasabar mata duk dare ajikinsa take barci, amma yau yayi canjinta da Waleeda, kuma waleeda wajen aunty bily suke kwana, yanzuma daga can ya ďakkota dan tuni waleed yayi barci acan.
    Haka tayita juye2 dan barci ya'ki ďaukarta kwata2, shima yakasa barcin saboda damuwa, yayi shirune kawai dan bayaso tagane idonsa biyu, duk juye2n datakeyi akan kunnrnsa takeyinsu yana jinta sarai yakuma san abinda ya hanata barcin, shima kuma shine ya hanashi barcin amma zai daure kodan yafara maganin Nurr ďin.
   Yaudai haka akayi wannan kwanciyar kowa zuciyarsa babu daďi, itama aunty bily tayi mamakin rashin dawo da wakeeda ďakinta, amma bata kawo komai a rantaba ta rungume waleed sukayi barcinsu mai daďi.
      Da safe Nurr ta tashi dawani ciwonkai saboda rashin isashshen barci, gakuma tun shekaranjiya batajin daďin jikinta dama.
   Da yake yau weekend babu inda ya mahmud yake zuwa, haka ta daure tashiga kichin shikuma yakoma barci, dan yana bu'katar barcin shima tunda baiyi isashsheba adaren jiya.
      Tagama haďa break da taimakon 'yan aiki, suka gyara gidan tsaf, tacika ko ina da kamshi, suna cikin gyaran waleed yafito dan yanzu sun fara tafiya, ta ďaukeshi tana murmushi damasa kiss akumatu, yaron mom tashi kayi kabar mom ďin??, bari to namaka wanka kafin waleeda ta tashi, tasan yanzu idan taje ďakinta dashi saiya tada su yaya da waleeda, dan haka sai kawai tanufi saman ya mahmud, acan tayi masa wankan ta gyara shi tsaf, saita dawo ďakin aunty bily danta saka masa kaya, dan kayansu suna ďakin aunty bily, sun tararma aunty bilyn ta tashi, Nurr ta ce, "aunty kintashi??.
   Wlhy yanzu na tashi nafara jajen waleed ma kuka shigo, Nurr ta mi'ka mata waleed tana faďin fita yayi bayan yatashi, gashinanma namasa wanka, to mungode Ummi.
     Nurr tafito tana dariya, zuwa tayi ta iske ya mahmud yayima waleeda wanka itama, yanata 'ko'karin saka mata fanfas ta'ki tsayawa, sun bata dariya dan haka taďan murmusa, ta karasa inda suke yaya Ina kwana??, lafiya yafaďa ata'kaice, ta daure ta ce, "kakawota nasaka mata to, ďaukar waleeda yayi yana faďin barshi bari na kaiwa My bily ta saka mata.
     Jiki a sanyaye tabishi da kallo, bataso taga ana fushi da ita ko yaya ne wlhy, jiki babu kwari tagyara ďakinta tayi wanka itama, a dinning ta iskesu har sun fara break basu jirataba, ta zauna tana satar kallon fuskar ya mahmud.
     Fuskarshi aďan hađe take, kuma babu walwala atare dashi, to amma sanda take tahowa aitaji suna dariya shida aunty bily  saida tazo ya canja fuska, abincinta tahaďa tanaci badan daďiba, sukuma sunaci suna bama yaran, aunty bily taďan so fahimtar wani abu atsakaninsu to amma tunda basu gaya mataba itama bazata tambayaba.
    Gaba ďaya yau haka ya mahmud ya wuni yana fushi da Nurr, to itamabata cika walwalaba saboda ciwon kan dake damunta tun dare.

Rayuwa tana tafiya yanda yakamata, Nurr sun fara zuwa makaranta itada deena, aunty bily tana rainon cikinta cikin addu'a da fatan ALLAH yasa ta sauka lafiya, yanzu haka cikinta yakai wata na biyar zuwa shidda, Nurr ta yaye su Waleed jiya dan haka mama tazo ta ďaukesu yau da safe ta tafi dasu wajenta itace zata yayesu, sai sukaji gidan shiru babu daďi saboda babu iyayen 'kiriniya, zuwa yanzu ya mahmud yadaina fushi da Nurr amma ba sosai yake shiga harkartaba, kwata2 batajin daďin hakan dayake mata, tarasa yanda zatayi tashawo kansa sukoma kamar da.
   Ita kuma batason gayama aunty bily matsalarta domin wannan sirrintane tsakaninta da mijinta.
    Deenama tana yawan tambayarta saboda rashin walwala datake gani atare da ita, amma Nurr ďin tadage akan babu komai, 'kila wannan yayen ne datayi.
    Deena ta ce, "babu wani yaye, abinda yaran ma bawata shakuwa kukayiba, yanda suka shaku da aunty bily ma aibasu shaku dakeba, kina ganin jiya damukaje gidan kodamuwa basuyiba dazamu taho, amma mama ta ce, "da aunty billy tazo saida wayo tabar gidan, hakama ya mahmud idan yazo gaidasu da dabara yake fita.
    Nurr tayi murmushi to aii sune iyayensu ni miye nawa aciki,, deena ta ce, "aii shiyyasa nace miki bahakan bane yake damunki akwaidai abinda ke damunki bakison faďane kawai.
    Nurr ta ce, "kinga uwar biyu abar maganar wataran zan faďa miki amma bawata damuwa bace, yanzudai mutafi gida tunda bamuda wasu lectures a gaba,  wlhy nagaji.....
   To shikenan, amma kema kina hanyar zama wata uwar biyun kwanan nan, Nurr ta ce, "tab rufani ki sayani, nikam yanzu aii bana fatan ciki, kudai kuyita ja, nasan kila kusan tare zaki haihu da aunty bily.
    Gsky kam inaga kusan tare zamu haihu, mota suka shiga direba yajasu sai gida..............








Luv u oll my fan's
©2017
[15/03 18:49] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》









NA BILKEESA IBRAHEEM 
     {♡Bilyn Abdul♡}







HIQAYA ONLINE WRITER'S
https://mrsbilkisa.blogspot.com 



56

..........'Yan kwana kinnan Nurr batajin daďin jikinta, tana daurewane kawai saboda bazai yuwu ita kwance aunty bily kwanceba, damma su waleed suna wajen mama ayuka sun mata sau'ki, tana yawan yin ciwon kai, ga aikin gida ga makaranta, lamarin sai addu'a.
    Haka tadawo daga school yau agajiye, tazube saman kujera tana fidda numfashi, aunty bily tayi dariya 'yan makaranta sannunku.
   Yauwa auntyna ykk?, yazama da tashi?, tasake yin murmushi, gamunan munayi, kasa tashi tayi sai marka ta kwalama kira takawo mata ruwa, harda abinci, Nurr ta kalleta cikin mamaki marka waya girka abinci kuma??.
   Hajiyace tayi".
  Cikin mamaki Nurr take kallon aunty bily, kai aunty dan ALLAH kibar wahalar da kanki da babynmu, ALLAH banason naga kina aikinnan, shiyyasa naketa hanzarin dawowa gida.
   To autar mama aii yakamata naďan ringa motsa jikina ko??, zaman isata yakeyi, gashi mama taki dawo mana dasu waleedi gidan shiru babu daďi, sai idan su Abdul sun dawo makaranta sun shigo.
     Ayya my aunty wlhy nima idan natafi makaranta kina raina nasan kaďaici yana miki yawa, idan yaya ya dawo kice yadawo miki dasu mana,, aikuwa za'akai ga hakan Nurr baridai yadawo.
   Nurr tanacin abinci suna 'yar hirarsu, har tagama tashiga ďaki ta watsa ruwa, sanan tadawo.
   Aunty bily anya kuwa yau yaya zai dawo daga abujar nan??, naga har biyar ta gotafa??, wlhy nima abinda nake tunani kenan Nurr, nakira wayarsa kuma yaki ya ďaga, inaga suna mitinne.
   Nurr ta ce, "to ALLAH yasa lafiya dai, amin ya rabbi........maganar Nurr ta kakare saboda turo kofar ya mahmud, gaba ďaya suka maida kansu inda yake yatsaya bakin kofa yana kallonsu ďaya bayan ďaya fuskarsa cike da murmushi, aunty bily tace oyoyo Abban 2, yay sama da kai, babu wani oyoyo, dan ba'a tareniba hakan ya nuna ba'a murna da dawowata kenan??.
    Dariya aunty bily tayi, nidai amin afuwa tashi wahala yakemin, to 'yar uwar ďayarfa??, Nurr kenan yake nufi, Nurr tai kasa da kai tana murmushi, aunty bily ta ce, "auta atashi to.
     Kai aunty dan ALLAH kibarsa nifa bazan iyaba, ya ce, "lallai ashe yau zan kwana nan kenan, Nurr taďan zaro ido kai haba??, oh kin ďauka wasanake yi kenan??, to zauna kigani, Nurr tami'ke tsaye A'a aiba ayi hakaba dadai badaga tafiya kakeba dasai abarka ka kwana, takarasa tana kar6ar jakar hannunsa, haďata yayi itada jakar yarungume tareda bata sumba akumatu, itadai kunyar aunty bily takeji shiyyasa taketa zille2.
    Yasaketa ya'karaso ga aunty b, itama zama yay ya rungume ta yana shafa cikinta, my baby kana lafiya??, ta sumbaci kumatunsa yana lafiya my handsome saidai yana kewar yayyensa da Abbansa.
    to gani nadawo, suma yayunsa yau zasu dawo gareshi, lah yaya da gsk??, insha ALLAHU yafaďa yana shafa kumatunta, amma yaya shine ba'a faďa manaba mushirya tarbarsu, yami'ke yana dariya oh kumfi ďokin dawowar yaranku akan Abbansu ko??, haba mu mun isa, munyi missing nasune dai.
   Samansa ya haye yana faďin nima nayi missing nasu, acan yatarar da Nurr tagama haďa masa ruwan wanka, yariko hannunta suka koma ciki dan tana niyyar fitane, 'yammata aibakida damar fita.
    Yaya zan kawo maka ruwan shanefa, no karki damu yanzu nasha ruwa amota, wanka nake bu'kata amin dai dan nagaji wlhy.
      Tab yaya kaima kasan babu 'yar haka tsakanina dakai, ALLAH bazan iyaba, ya rungumeta sosai ajikinsa, yakamata mubar wannan 'yar kunyar, dan yanzu babu maganar kunya a tsakaninmu, karki manta harfa kin haifa mini yara, ta rintse idonta dan ita bawai wankanne bazata iya yimasaba, kawaidai bata sonsane, ya sumbaci ďan bakinta, ki za6a wanka ko wani abu daban, dolene amin ďaya aciki, da sauri tabuďe ido tana kallonsa, miye ďayan??, da hannu ya nuna mata gado, ta waro idanu, shima saiya waro nasa, sai suka tuntaure da dariya, da wayau yasata tamasa wankan, yana fitowa yashirya cikin doguwar riga yafice masallaci domin yin sallar magriba.
   Itama sakkowa tayi tashirya abinci a dinning sanan tatafi ďaki, tana zaune kwatsam wani tunani yazo zuciyarta, shine rashin ganin al'adarta, idan bata manta lissafinba yau wata kwanansa goma sha uku da tsayawa, kuma tanayin al'adarta a farkon watane, dan danan tsoro ya kamata hankalinta yatashi sosai, tafara safa da marwa aďakinta, bataso abinda take tunani yazama gsky wato ciki, ta maimaita sunan ciki!!!! Kuma??, kai dasake wai abama mai kaza kai.
    Ya mahmud yashigo ďakinta dan yunwa yakeji, ganinta a birkice yasakashi tsayawa kallonta, itama da sauri taďago tana kallonsa, Nurri lafiya kuwa??, ta ďan dafe kai inafa lafiya yaya, dan ALLAH idan bazaka damuba inason magana da doctor Asheer.
    Ya sauke numfashi tareda 'karasawa inda take, miyasa kikeson yin magana dashi??, taďan tsaya daga yawon datakeyi, ta cije ďan yatsanta, ina cikin damuwane yaya bana fatan abinda nake zargi yakasance akan yawan ciwon danakeyi 'yan kwanakinnan.
     Ta 'kara sakashi aduhu, dan haka ya ce, "kinga nutsu kimin bayani yanda zan fahimta, yaru'ko hannunta suka zauna.
    Ina saurarenki,,".
    wato dama ina tunanine akan al'adata sainaga har na shige lokacin danakeyi da kwana goma sha uku, shine hankalina yatashi.
   To kinga kwantar da hankalinki bari na kira doctor muji mizaice, waya ya ďauka yakira Dr Asheer, bayan sun gaisa ya ce, "doctor dan ALLAH inason na tambayekane??, okey Sardauna ina saurarenka.
   Wato matanane lokacin al'adanta yashige saita tada hankalinta da tunanin kowani ciwone??, kuma a 'yan kwanakinnan takanji canji ajikinta, komiye dalilin hakan??.
   'Yar dariya Dr Yayi, Sardauna to anawa tunani matarka tanada ciki kenan inhar hasashena yayi dai2, da sauri ya ce, wow!! Dr da gsk??, insha ALLAHU hakane Sardauna, babu wani ciwo dake damunta saina laulayi, amma kaima yakamata ka shaida hakan, dan zakaji ta canja maka, lallaikam doctor ammafa ngd da wanan albishir saika jini da safe dan kawo maka goro.
    Nurr tanajinsu dan haka tuni tayi mutuwar zaune, sai hawaye daketa zirara a idanunta.
   Ya Mahmud yayma Doctor sallama ya kashe wayar,, cikin farin ciki yajuyo ga Nurr, amma saiyayi turus dan ganin tana kuka, Nurr kibar kuka babu cutar datake damunki, sai abin farinciki daya samemu.
   Da sauri ta ce, "kokuma bin ba'kin ciki ko??, yaya dankaga nasaki jiki na haifi su waleeda shiyyasa kake tunanin zan cigaba da haihuwa dakai??, kayi kuskure daka cigaba da wannan tunanin,, ka ďauka baka samu wanan cikinba dan zubar dashi zanyi.
    Tami'ke da sauri domin barin wajen, damke hannunta yayi da 'karfi, yay matu'kar canja fuska cikin matu'kar 6acin rai ya nunata da ďayan hannunsa "k walhy kishiga hankalinki, koda wasa kikayi kuskuren zubar min da ciki saikin fiskanci fushina, ''k wai wacce irin mutumce ne!!!??, wlhy Nurr wanan shine zai zama mafi girman kuskure dazakiyi arayuwarki, bazan hanakiba ga fili gamai doki, kije kizuba mara mutunci kawai!!!!, afusace ya mi'ke yabar ďakin.
    Zubewa Nurr tayi akasa tana kuku kamar ranta zai fita, ya Mahmud kuwa koda yafita saiya nufi gidan daddy, baishiga ďakin kowaba yawuce saman dady, dady suna tareda mama danyau aikintane, yashigo falon kamar mai shirin yaki sai huci yake da hura hanci, mama da dady suka bishi da kallo, da sauri waleeda dake zaune kan cinyar dady tazo ta tareshi, yarike hannunta kawai yau babu zancen ďagasu sama kamar yanda ya saba, dady ya ce, "mahmud lafiya kuwa??.
   Dady da sau'ki dai kawai, yafaďa yana zama..   .
     to mikuma yafaru??, kaidawa??,.
    Nida Nurr ne.
Nurr kuma??, miya haďaku, zayyanema su daddy komai yayi batareda yarage komaiba har kiran doctor, da i'kirarin Nurr na zubar da ciki, suma hankalinsu yatashi kwarai da gsk, dady ya ďauki waya yakira Nurr.
   Tana zaune inda ya Mahmud yabarta tana rabzar kuka, sai wayarta tafara wringing da kamar bazata ďagaba saikuma taga sunan daddy, tabbas tasan ya Mahmud yaje gida, tabďi tafaďa tana gyara zama, to aii ita a wanan karon tayi shirin komima zai faru ya faru, dan haka zata gayama su dady gskyar abinda ke ranta gameda zama da Ya Mahmud, wayar ta katse aka sake kira, ta ďaga batareda wani shayiba.
     Nurr kizo gida yanzu inason ganinki, bai jira amsartaba ya kashe, itama mi'kewa tayi ta zira hijjab tafice, ko aunty b batayima sallamaba.
    Afalon dady ta iskesu dan haka tarissina ta gaishesu, waleeda tana jikin ya Mahmud amma koda taga mamanta bata tasoba.
    Dady ya ce, "yanzu yayanku yazo mini da wata magana shin gsky ne??, babu ko tsoro atare da ita ta ce, "eh gsky ne, ta ďora da faďin dady kuyi ha'kuri idan ranku ya 6aci.
    Dady ya girgiza kai a'a mu ranmu bai 6aciba, yanzuma banida ikon hanaki abinda kikayi ra'ayi, saidai kafin ki zubar da cikin inason nabaki wani abu ki karanta, daga nan saiki yanke hukuncin dakiga ya dace dake.
   Idan zaki iya cigaba da zama da mahmud bazan hanakiba, hakanma mu zaiyi mana daďi.
   Idan bakida ra'ayin cigaba da zama dashi bazamu tauyekiba, zamubi hanyar daya dace ya sakeki ki auri wanda kikeso,ALLAH yaraya abinda kuka haifa.
   dady yami'ke yashiga ďakinsa.
      Nurr kanta na 'kasa ta kasa kallon mama, shikam ya mahmud aii yashiga ruďani da bayanin dady, har ga ALLAH baiga guguwar dazata taso akan rabashi da Nurr ba komai ruguntsumin dake cikinta kuwa......dawowar dady ta katse masa tunaninsa, ya mi'kawa Nurr book gashi kuje gida ki karanta, ina jiranku gobe idan ALKAH ya kaimu da safe.
      Kutashi ku tafi, mi'kewa sukayi ya mahmud yami'kama mama waleeda datayi barci suka fice sai gida..................

tofa masu karatu, kunji kuma wani SABON AL'AMAREE.
    Koya zata kasance???, kubiyo mata agidan Abdul kawai










Luv u oll my fan's.
©2017
Share:

Tuesday 14 March 2017

SABON AL'AMAREE 50/53

[12/03 16:29] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE 》》







NA BILKEESA IBRAHEEM 
    {♡bilyn Abdul♡}











50

...........Murmushi ya Mahmud yasaki wanda har ya bayyana matsakaiciyar wushiryarsa dake tsakanin fararen ha'koransa, Nurrina kenan ke kina tunanin wani abune yake damunki??.
   ALLAH yaya serious nake maka maganar nan, karka ďauka wasa nakeyi, ta ďaga rigarta kallifa kagani dan ALLAH.
   Takardar hannunsa ya ajiye ya fuskanceta sosai, yana cigaba dayin murmushinsa, ya ďora hannunsa kan cikin nata kai Nurrina kumafa da gsk kikeyi cikinki ya'kara girma wlhy, ta langa6e kai gefe to kagani shiyyasa nace bari nasanar maka kakaini asibiti adubani, wlhy inajin tsoro.
    Jawota yayi jikinsa yana shafa cikin kinga ki kwantar da hankalinki inagafa yawan kwaďayin dakikeyine yasa kika fara tunbi, kai yaya tunbi kuma?, nikam wlhy banason tunbi, dan haka zan fara training kwannan kuwa, A'a basaikinyi training ba kibari zan sanar da Dr Asheer saiya baki magani, amma koba nanan karkiyi wani training shima matsalane ga mace, ta ce, "to shikenan kafa amsomin dan ALLAH, Karki damu zan kar6o miki.
   Ya faďa mata hakane dan kar wataran tadage da yin training wajen tsalle2 taimasa aika2.
   Ta yunkura zata tashi daga jikinsa, A'a ina kuma zuwa??, zan kwantane yaya kacigaba da aikinka kaima, wlhy nagaji sosai gashi gobe idan ALLAH yakaimu aunty bily ta ce, "zamuyi tashin wuri.
   Gsky ne, dan zanzo da abokaina suci abincin sallah, ta kwanta tana dariya ainima gidan dady zanje ko gidan deena na wuni, ya ce, "kilaba.
   Yaya kamar ya 'kila? bazaka barni najebane??, zan barki amma sai jibi idan ALLAH ya kaimu, kinga nace abokaina zasuzo gobe baikamata ba kuma ace wata acikinku ba tanan, to shikenan yaya ALLAH yakaimu jibin.
    Amin Nurrina yafaďa cikin matu'kar jin daďi, lallai Nurrinsa tafara hankali, da dane aikoda bala'i saitaje, babu daďewa barci ya kwasheta, shikuma yaciga dayin aikinsa.

YAU TAKE SALLAH
          YAU take sallah dukkan al'umar musulmai sun tashi cikin matu'kar farinciki, kowane 'kofar gida ka gifta 'kamshin suya kakeji da jar miya, maza da 'yammata da yara sunata shirin zuwa idi, kai harma dawasu matan auren, abin gwanin sha'awa da birgewa.
    Tunda asuba aunty bily ta tashi take aiki itada ya Mahmud dake tayata wasu abubuwan saikuma masu aiki, Nurr dai bayan tayi sallah barci ya Mahmud yasata takoma dan tana bu'katar abarta taringa isashshen barci.
    Wajen karfe bakwai itama ta tashi saitaje ta canji ya Mahmud akichin ďin shikuma yadawo falo yazauna.
   Zuwa 'karfe tara sun kammala komai daya dace, suka shiga kujiba2r gyara gidan, alokacin kuma ya mahmud yanacan yana ďaukar gayu aďakinsa, suna gama gyaran falo suka koma ďakunansu nanma suka gyara tsaf.
      Ya mahmud yasakko cikin wata ďanyar Sky blue ďin shadda, yau harda malun2, wow!!!! Nafaďa a zuciyata guy ďinfa yagama hađuwa tamkar angon dazaiyi auren fari, sai baza kamshin turarensa yake, kafarsa sanye da dark blue ďin takalmi sau ciki sai 'kyalli yake da ďaukar idanu, asama ma ya murza hula 'kube dark blue sai mai'ko takeyi, ďakin aunty bily yafara shiga yana ďaura ba'kin agogo a hannunsa.
    Tsayawa tayi cak tana kallon ikon ALLAH daya girma ya ďaukaka, ko 'kyafta idanu batayi, tunanima takeyi anya wannan mijintane kodai canjashi akayi, a slowly ya 'karaso inda take ya hure mata idanu takawo numfashi da 'karfi.
    Cikin kunnenta ya ce, "yammatana mikike kallo haka, tayi murmushinta mai 'kayatarwa, mijinane yatafi da dukkani hankalina, my handsome irin wanana ďaukar wanka haka saikace mai shirin sabon aure??, yayi 'yar dariya to kika sani ko yau nasamo ta uku??, humm aiko ina addu'a ALLAH ya makantar da kowace mace daga kallonka.
    Yaďan zaro idanu my bily wanan wace irin addu'ace kuma??, yazakimin bu'kulun samun sabuwar amarya??.
   Ta ta6e baki, ai inda akan amaryarnane zan 'karama wata addu'ar yanzu,, a'a yi ha'kuri karki zamin narasa amarya aranar sallah, ai kama ďauka karasa, kai namune mukaďai dagani sai Nurr ďin mama.
   Murmuahi yasakeyi tareda manna mata kiss akumatu, ALLAH yabarmin ke my bily, kemafa kin iya kishi?, amma miyasa bakiyi da Nurr??,  aini ban ďauki Nurr kishiyaba she is my blood sister!!.
    Ya kuma manna mata kisses a kumatu ina al'fahari dake my bily, ke macece tamkar da dubu ALLAH yay miki albarka.
   Ameen yayana ngd tafaďa tana manna masa kiss itama, ta ce, "sai masallaci??, ya ďaga mata kai yana murmushi.
   To adawo lafiya ALLAH yatsare mana kai, yadawo mana dakai lafiya.
  Ameen bilyna ngd da addu'arki, bari nawuce karna makara ko, ya kalli agogonsa, to bey bey.
      Shima hannu ya ďaga mata yafito, ďakin  Nurr ya shiga. 
   Gaban madubi ya isketa zaune tana tsara kwalliya, lallai yau ranar farincikice irin wanan kwalli haka, Nurr tajuyo tana kallonsa, itamadai yayi mata 'kyau lallai kwalliyar tasa tabada ma'ana, jitayi kamar tace karya fita wasu matan su gansa (na ce, tofa Nurr kina kishi kar irinsu Deexerh gwauraye su 'kyasa miki shine??).
    Cikin takun gayu ya 'karaso inda take, tabayan kujerar yaran'kwafo ya ďora kansa a gefen kafaďarta suna kallon juna ta madubi, Nurr ta lumshe idanu tana murmushi, shima murmusawar yayi, Nurrina miyasaki murmushi haka??, takuma murmusawa har kumatunta suka lotsa, babu komai yaya happy sallah!!.
     D/same 2u my luv!!, yafaďa yana sumbatar kumatunta, kinyi kyau Nurrina, kaima kayi 'kyau aii yaya.
   Wani daďi yaji ya tsargashi azuciya, da gsk??, ta jinjina kai ALLAH kuwa yaya, ya lumshe idanunsa l luv u Nurrina naji daďin yabawarki, kema inason kafin nadawo na tarar kinďau wanka na fitar hankali, dan dana dawo zan bada barka da sallah.
    To ALLAH ya kiyaye hanya, ameen Nurrina, amma baza abani wata tsaraba ta barka da sallah??.
    Taďan kalleshi cikin rashin fahimta, to ni yaya minike dashi dazan baka??, keko kikeda abin bani Nana maryam, ya mi'ko mata kumatunsa a bani sumba ďaya mai 'kyau.
    Hannu tasa ta rufe fuska ALLAH kuwa yaya inajin kunya, babu wata kunya nidai sai anmini, yafaďa maganar cikin shagwa6a.
   Ta ce, "kai yaya saikace yaro??.
   Ni yarone mana idan ina gaban Nurrina dan haka idan bakiminba bazanje masallacinba.......A'a ba ayi hakaba to rufe idonka, gam ya rufe idonsa kuwa ta manna masa kiss a kumatu.
    Wow!!!! Yafaďa tareda sauke wani nannauyan Numfashi, l luv u my Nurri!!!!.
   Hannu tasa tarufe fuska, ya ce, "natafi idan nadawo ma gauraya.
    Yana fita wani haushi ya turni'ke Nurr, komiyasama tayi masa kiss ďinnan??, tasa tawul tana faman goge bakinta(na ce, "humm wai daga baya kenan inji 'keya).
      Da har ta fasa kwalliyar saikuma ta ce, "aibama danshi zanyiba, zanyine dan ina murna yau sallah, saita cigaba da tsara kwalliyarta, ta shirya cikin wata haďaďďiyar atamfa orange color ta naďa ďaurin ďankwali na ďaukar hankali, kai masu karatu Nuriin ya mahmud tafitofa, dama 'kyawun karamin ciki yana ďawainiya da ita, ďan cikinta yaďan fito kađan saiyayi mata 'kyau kuwa, ta saka sarka da zobuna abin hannu dadai duk abinda yadace, ďakin aunty bily tashiga, wow!!! Nurr kinyi 'kyau wlhy, kai auntyna kema kin haďu kinma fini yin kyau.
    Aunty bily tayi dariya kin rama kenan, itama dariyar tayi, ta ce, "aunty bily ALLAH turaren ya Mahmud nakeson satowa, ina kuma tsoron karna shiga ďakinsa yadawo ya ritsani.
   Dariya aunty bily tayi, ai bazaice komaiba kije kawai ki sawo, kina ganin babu matsala aunty ???, insha ALLAH aunty bily tafaďa.
   Nurr ta ce, "to ina zuwa, samansa ta haye ta feso turare bana wasaba, ashe wajen kala huďu yake haďawa shiyyasa takan kasa banbance turaren nasa, akan madubinsa ta tarar dasu reras dan haka taďauki kowanne tafesa, dama ta feso wasu ađakinta, tuni jikinta ya kwaure da 'kamshi harma yana hawa kai, amma ita ko ajikinta haka takeso.
    Tana sakkowa su ya Mahmud suna shigowa falon shida gayyar abokansa harsu wajen bakwai, idanu yakafama Nurr tamkar yau yafara ganinta gashi duk tacika falon da fitinannan 'kamshi, sumadai abokan nasa idonsu na kan Nurr, ahankali ya 'karasa tareda kama hannunta ya kareta sosai dankar abokan nasa suganta, ( nace ya mahmud kishi kenan?? ) saida yakaita ďaki sanan ya rungumeta Nurrina irin wanan 'kyau haka kamar zaki za6en sarauniyar 'kyau??, batace komaiba saima ta6e baki datayi, yay kissing ďin fuskarta, kinga ďauki gyale kisaka sanan kifito ku gaisa, bai jira amsartaba yafice abinsa.
     Jitayi kamar karda tafita,, amma abokansa sun riga sun ganta kuma harda yayyenta aciki bai dace ace taki fitaba, gyale taďauka kalar kayan tafito, itama sanan aunty bily tafito suna gaisawa, Nurr ma takarasa tana gaishesu, ya mahmud yakasa ďauke ido daga kan matan nasa, kowacce tabada ma'ana acikin kwalliyar sallar.
   Aunty bily takama hannun Nurr suka tafi kichin, abinci suka fara shiryawa a dinning ya mahmud yataso yana faďin aikamata yayi ashiryashi afalo ko? inaga zaifi musake sosai.
   Okey babu damuwa, afalon sukacigaba da shirya komai ya Mahmud yana tayasu dawasu abubuwan, abincine kala2 na gargajiya dana zamani, ga soye2 na nama da abinda yadanganci filawa, sai lemuka kala2 suma duk namu nagida, falon ya kaure da wani shahararren kamshi na musamman.
    Sukansu abokan na ya Mahmud sun 'kagara sufara ďibar gara dan duk kamshi yacika musu hanci tuni.
   Har sun tsugunna zasu fara Sarving nasu ya Mahmud ya ce, "ku kyalesu su zuba dakansu, karku wahalar da kanku.
    Hafiz ya ce, "kai Sardauna mufa bakinkane??, aina sani idan kunji haushi kuyi aure mana, dariya sosai sukeyi tareda faďin abinma 'yar gorice Alhaji??, to gara aimuku gorin ko kwayi zuciya kuyi kuma, kudaina bin gidan mutane cin tuwon sallah.
    A'a kaima yaushe kafita acikinmu?, kwanannane fa, amma karka damu zamu rama muma muna hanya insha ALLAHU.
   to ALLAH ya yarda ya mahmud yafaďa yana cire babbar rigarsa.
    Sosai sukaci abincin sunata zuba santi, komai saida sukaci tareda yabawa matan na ya mahmud masu kwazo da iya girki.
    Sun dađe agidan daga baya sukai musu alkairi suka fita harda ya Mahmud ďin, amma ya canja kayansa zuwa wata ďanyar farar shaddar itama mai mai'ko.......................










Luv u oll my fun's 
©2017
[14/03 11:14] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》








NA BILKEESA IBRAHEEM 
    {♡Bilyn Abdul♡}




HIQAYA ONLINE WRITER's
         




51

........Haka bikin sallah yacigaba da gudana, su Nurr buri yacika ansha yawo gidan dangi harda inda ba'a aiketaba duk saida taje, gidan dadyne karshe sukaje suka wuni itada aunty bily, har dare, saida magriba suka dawo gida.
    Rayuwa tanata tafiya yanda ALLAH ya tsara, yau akayi sunan ďangidan deena wato Ibrahim khalil, to ALLAH yaraya babana daduk kan sauran 'ya'yan musulmai, taron suna ya 'kayatar yanda yakamata su Nurr sune amarori kirjin biki, komai saidasu, taron sunan ya 'kyatar yanda yakamata, dangi sun nuna bajinta, dahaka taro yatashi lafiya kowa ya kama gabansa.

Yau Nurr agajiye take saboda shagali dasukasha, akan gado tazube tana maida numfashi na gajiya, ahankali ya mahmud yaturo 'kofar yashigo da sallama, tana daga kwance ta amsa masa, akusada ita yazauna yana faďin 'yan suna kamarku daban.
    Nurr tayi 'yar dariya tana tashi zaune, lallaikam munsha  shagalin suna  yau, wlhy bakaji 'kafafunaba yaya kamar su cire, tofa miye dalili??, wlhy zirga2 ce kawai yaya, kafafuwan yakamo ya ďora saman cinyarsa yanaďan matsa mata ahankali, Nurrina harmafa sun ďanyi fushi.
   To yazanyi babynane yajamin haka, daga yaukuma sai wani, wannan kam ya wuce, hakane daga nan kuma saike, humm kaji yaya dawata magana nikuma miya haďani da suna??, murmushi yayi yana kallon fuskarta kika sani kokema kin samu cikin??.
     idanu tazaro waje a'a yaya daina yimini wannan fatan inani ina ciki yanzu, nifa burina nakoma makaranta kawai.
   Ya tuntsire da dariya, nikuma kinga burina naga 'ya'yana aduniya, kuma kece zaki haifamin da bily.
   Toni yaya ainayi 'karama dayawa garama aunty bily ita babbace, sai dai nace ALLAH yasa ta haifa maka to, ya langa6e kai gefe "k baki fatan ki haifamin sai bily kawai??, taďan kwa6e fuska dan bata fata ta haihu dashi itakam, so take idan yasaketa taje ta auri wanda take so ta haifi yaranta acan (na ce, "huumm hajiya Nurr kenan, ashe bazaki farka a wanan mafarkinba kenan??).
    Yaďan matsa kafar takawo numfashi, tunanin mikike kuma Nurrina??, ta ta6e baki babu komai.
    Shiru yayi yayi niyyar gaya matane tanada ciki, to amma yaga yakamata ya ďan tsahirta sai nan gaba, ya ce, "kinga mubar wanan show ďin, yanzu dai tashi muje na gasa miki jiki da ruwan zafi saikiji daďin jikinki.
    Ta ce, "kai yaya kullum saikaita maidani 'karamar yarinya.
   Ooh namantafa ashe k babbace, to amma yanzu kika gaya min k yarinyace ba yanzu zaki haihuba.
    Shiru tayi dan ganin ya harbo jirginta, ta zame 'kafarta daga cinyarsa yaya bari nayi wankan dan nafara jin barci, to jekiyi yafaďa yana kwanciya akan gadon, harta shige bayi yana binta da kallo, komai na Nurrinsa mai 'kyaune, yana son yarinyarnan sosai amma yana damuwa sosai idan yatuna ita bata sonshi, ya lumshe idanu tareda fitar da huci mai zafi daga bakinsa, ALLAH yakaimu ranar da Nana maryam zata soni koda rabin son danake matane ( na ce, "ameen ya Mahmud).
      Babu daďewa tafito tayi shirin barci suka kwanta, dukda ita ba'a son ranta yake kwana aďakin nataba, amma babu yanda zatayi tunda yayantane har yanzu yanada daraja irinta babban wa agareta, kai tsaye bazata iya yimasa rashin kunya ba ko wani abu mara 'kyau, saboda tarin kwarjini da ALLAH yabashi.
   Sau'kin tama yanzu ba kullum yakan cika matsa mataba, wani lokacin ma acikin kwana biyu dayakeyi a ďakinta saiya bar ďakin nata bai mata komaiba, kokuma ya kusanceta sau ďaya acikin kwana biyun.
   A hakama abun na bata haushi amma yazatayi, tana gudun tsinuwar mala'ikune akanta, agefe kuma ya Mahmud yakan mantar da ita soyayya ko kiyayya ayayin dayake nuna mata zallar soyayyarsa mai aminci da nagarta, sai bayan wucewar komai sanan takan tuna da bata sonshi.
     Taďan tsurama fuskarsa idanu, babu laifi ya Mahmud 'kyakykyawane dukda kasancewarsa ba'ki sosai, gashi nutsatstsen mutum mai ilimi da iya zama da mutane, yanada faďa da saurin fushi, ga son addini da dangi, koya ďan uwansa yake zakaga yana kaffa2 dashi, ya iya soyaya mai tafiya da kwanyar mace, tuni zaitafi da imaninki ya mantar dake damuwar ki, abinda ke haďata dashi masifa ya Mahmud ďan hayaniyane dukda shi baya son haya niyar........ahankali ya buďe idanunsa shima yana kallonta, Don yanaji ajikinsa shi take kallo, tai saurin rufe nata idon, dan azatonta barci yake, yayi murmusgi mai sauti, ki buďe idonki Nurrina ki kalli mijinki babu mai hanaki, ni nakine babu shamaki Haskena!!, itadai takasa ko motsi saifaman rintse ido take tana murmushi, kunya takeji ya kamata tana kallonsa, ya sumbaci idanunta shima yana murmushi ya ce, "Nurri sarkin kunya, inason mace mai kunya, rungumeta yayi tsam ajikinsa yana gaya mata kalamai masu daďi da kwantar da zuciyar mai sauraro, (tabbas wataran ya Mahmud zai canja Nurr kodan iya salon soyayyarsa ga 'ya mace).

  Yauda gobe sai ALLAH, har gashi cikin Nurr yashiga wata biyar, ayanzune kuma yakamata tafara zuwa awo, amma ya Mahmud yana fargabar yanda zai kaita aii mata awo dan yasan tabbas zata gane, gashi ďazu Dr Asheer yakirashi yasanar masa ranar monday yakaita asibitin domin awo.....
      Aunty bily ta 'katse masa tunani da ta6ashi abaya, ya ďago idanunsa dasukayi ďanja yana kallonta, tazauna kusadashi sosai yayana miye damuwarka??, yaja numfashi wlhy bily Nurr ce damuwata, Nurr kuma yaya??, miya faru da ita??, a'a babu abinda yafaru da ita akan maganar awone danake gaya miki Dr ya ce, "a kaita ranar monday.
    Yaya ai inaga wanan ba wani abun damuwa bane, bata ba6ace maka tanason shan maganin rage tunbiba??, ya ce, "eh hakane, to kawai kace tashirya kuje za'a duba aga mike damunta inaga hakan zai fiddaka daga ruďani.
    Rungume ta yayi yana bata kisses ako ina najikinta, ina sonki dayawa bily, akwaiki da hikima da dogon tunani wlhy, kema ALLAH yakaimu randa zaki haifamin yara daga wanan cikin, to amin yayana, amma wanda za'a haifama yanzu nawane, dan duk nafiku sonshi, yakuma matseta ajikinsa hakane bilyna, kowama yasan nakine, ko an haifama mallakinkine, haka sukaitayima juna kalamai masu daďi da kwantar da hankali, (nace masoya juna kenan).
    Yau deena tana gidan tazo musu yini, suna ďaki itada Nurr, khalil kuma yanacan aunty bily ta goyashi, Nurr ta ce, "deena gsky inada damuwa.
    Cikin kulwa deena take kallonta 'yar uwa miye damuwarki??, ko yayane??.
   Nurr ta gyara zama, to kusan hakane, deena kalli cikina mana tafaďa tana ďaga riga, deena ta kalli cikin to miya samu cikin naki??, bakiga ya 'kara girmaba, deena tayi murmushi nagani to miye??.
    Yazaki cemin miye?, baki tunanin wata cutarce ta shigeni, yau tsawon wata biyar banida cikakkiyar lafiya, daga inji nan yana ciwo yau sai inji nan yakamu gobe, narasa wannan dalili, saikuma abin mamaki saina farga cikina yana 'kara girma, wanan yasa na sanar da ya mahmud dan ya kaini asibiti adubani amma saiyace tumbine, to alokacin bai kai haka girmaba shiyyasa na yarda dashi, to amma saiya cigaba da girma kuma kullum jikina sake salon ciwo da canji yakeyi, deena miye yake shirin faruwa dani hakane??, ta kare maganar da zubo da hawaye.
    Hannu deena tasa ta share mata hawayen, saida taga ta nutsu sanan ta ce, "Nurr in tambayeki mana?.
   Nurr ta ce, "to ina saurarenki.
  Watanki nawa bakiyi al'adaba??, gaban Nurr yafaďi, itafa bata ta6a yin wanan tunaninba, ta ce, "deena nakai wajen wata biyar fa, deena ta jinjina kai, to amma miyasa baki ta6a tunanin miya hana al'adarki zuwaba??, wlhy deena nima ban saniba, kinsanni da 'kyankyamin jini musamman ma na al'ada, shiyyasa alokacin danaga banayi sainayi matu'kar farinciki, dan ina ganin yanzu nahuta ne kawai.
    Murmushi deena tayi, to Nurr a ilimin da ALLAH yabaki miyake kawo ďaukewar al'ada ga mace matashiya mai kuruciya???.
   Cikin sanyin murya Nurr ta ce, "cikine ko rashin lafiya.
   Masha ALLAHU deena tafaďa, Nurr ina mamaki yanda ciki yana jikinki kika kasa fahimtar hakan, nasan har yanzu kina ďaukar kanki yarinya 'karama, amma atunanina ko yarinyar kauye 'yar shekara goma sha uku akaima aure idan tasamu ciki takan sani, bareke haihuwar birni, kinsamu ilimin boko dana addini iya bakin gwargwado, shekarunki akalla yanzu sunkai sha bakwai zuwa sha takwas, kinada wayewa iya gwargwado, amma har ki gagara gane cewa akwai ciki atareda ke??.
   Wai kekam wace irin kuruciya ce dakene??,.
   Nurr dai tuni ta daskare agurin kamar wadda kankara ta kafe, takasa ďaga koda yatsan hannunta saboda ta'ajibi, to wai ita miyasama bata ta6a irin wanan tunaninbane??, miyasa hankalinta bai ta6a kaiwa wajen bane, tashiga tuno kalaman ya mahmud na lokuta mabanbanta, lallai buri yayi kama da mutum, wanan shine 6oye2 da ake mata agaban Dr kenan??, wasu hawaye suka ziraro akumatunta.
    Deena ta girgiza kai, Nurr atunanina farinciki zakiyi ba kukaba domin abinda yasameki abin farincikine??.
    Bana farin ciki deena dan bana fatan haibuwa da yaya mahmud.
   Cikin mamaki deena take kallonta, kamarya bakison haihuwa dashi??.
   Saboda bana sonsa.
 Lallai Nurr aiiko idan da wanda ya cancanta kiso bai wuce ya mahmud ba, ya mahmud gwarzone acikin maza, babu abinda ALLAH bai bashiba, ilimi tarbiyya son ibada, gashi 'kyakykyawa son kowa kin wanda yarasa, to miye abin'ki gameda ya Mahmud??, aii duk macen data sameshi amatsayin miji tagama nasara, dan namijine tamkar da dubu, acikin maza dubu sai andage ake samun irin ya Mahmud goma, Nurr kidawo cikin hankalinki ki saita tunaninki sosai.
   Karki bari idanunki su rufe har shaiďan yasamu damar kissifa miki wani abu daban da tarbiyyarki, ya Mahmud fa ďan uwankine najini to miye aibunsa??.
     Itadai Nurr batace komaiba sai faman kuka datakeyi, tun deena tana lallashi har abin yafara bata matu'kar haushi, dan ita bataga dalilin yin kuka a wanan maganarba, kinga nikam zan kama gabana indai kukan zakiyi, dan bazan ta6a goya miki bayaba gsky dan haka kinga tafiyata, duk abinda kikaga yadace da rayuwarki kiyi.......shigowar ya Mahmud ce takatsema deena maganarta..................










Luv u oll mu fan's
©2017
[14/03 11:15] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》






NA BILKEESA IBRAHEEM 
   {♡Bilyn Abdul♡}


HIQAYA ONLINE WRITER's
       





52

........Gabaďaya suka ďago suna kallonsa, shima cikin mamaki yake kallon Nurr dake kuka, domin lafiya lau yafita yabarta har yana tsokanarta tana dariya, ya maida kallonsa ga deena dake tsaye fuskarta atamke.
    Deena lafiya dai kuwa??.
Lafiya lau yaya.
  To miyasa Nurr kuka??.
           Tambaya ta tayi nabata amasa, dan kawai nace tanada ciki shine ta zauna tana kuka, cikin 6acin rai deena take maganar.
    Gaban ya Mahmud yafaďi, azuciyarsa ya ce, "deena kin 6aromin aiki, kin ruguza komai, amma afili saiyaja ajiyar zuciya, ya jungina da bango tareda tura hannunsa cikin aljihu, kafafunsa aharďe, idanu kawai ya tsuma Nurr dan baisan mizai cemataba..  
    su duka sunyi shiru sai shashshekar kukan Nurr kawai, ahaka aunty bily tashigo ta samesu, takawo khalil daya farka yana kuka, ďaya bayan ďaya tabi fuskarsu dakallo, ganin kowa fuskarsa da damuwa gakuma Nurr tana kuka sai gabanta yafaďi, ta ce, "yaya lafiya kuwa??.
    Baice komaiba illa tsira mata idanu dayayi, tasan idan ransa ya6aci baya iya magana.
   Ta maida kallonta ga deena, deena mike faruwa??, deena ta gayawa aunty bily abinda yafaru amma banda Nurr batason ya Mahmud, ajiyar zuciya aunty bily ta sauke, ta mi'kama deena khalil kar6eshi kibashi yasha nono, deena ta kar6i khaleel ta zauna.
    Ita kuma aunty bily ta zauna kusada Nurr, fuskarta taďago ta share mata hawayen fuskarta, cikin sigar lallashi take magana, haba Nurr bai kamata dan ance kinda ciki kiyi kukaba, aii abin farincikine wanan bana kukaba, duk macen datayi aure burinta ta samu 'ya'ya domin wanan shine ribar auren.
   Nurr ki tuna akwai ďunbin mutane aduniya dasuke fafutuka da dukiyarsu da jikinsu domin neman haihuwa, wasu a kullum sai sun zubar da hawaye akan damuwar rashin 'ya'ya, miyasa keda ALLAH yabamawa bazaki gode masaba harki nuna ďunbin farin cikinki, azatona kece wadda zata fara taya yaya murnar samun wanan cikin dake jikinki, Nurr kituna sau takwas muna asarar baby nida ya Mahmud, tare akayi bikinmu da ya Fahad amma yazu yaransa biyu tare zaku haifi na uku da ikileema, amma yaya baida ko ďaya, sai yanzu za'a haifa masa ďan fari, kalli kiga deena harta haihu itama, inaga ko waďannan kananun misalan sun isa a tausayama ya Mahmud.
    Cikin jikinki farincikine ga mutane masu yawa, amma dammi zakiyi ba'kin ciki ke kaďai??, plzzz Nurr kibar kuka ki rungumi alkairi da 'kyautar da ALLAH yabaki, ki gode masa kiyi farinciki kuma domin shima babbar godiyane, idan kikayi hakan muma zamuyi farinciki sosai.
     Nurr taja ajiyar zuciya, ALLAH aunty inajin tsoro haihuwa akwai wahala naji anacewa.
    humm Nurr kenan babu wata wahala acikin haihuwa, kuma da ana gudun haihuwa da iyayenmu sunji tsoron haihuwarmu, na haihu naji kuma ni nafaďa miki haihuwa babu wahala, deenace mai wanan maganar.
   Ya Mahmud yana tsaye yana jinsu amma baice musu kalaba.
   Shikenan na ha'kura kuma na kar6i kyautar ALLAH da hannu biyu, nakuma gode masa.
   Ajiyar zuciya ya Mahmud yasaki, zuciyarsa fal farin ciki, baita6a zaton abin zaizo da sauki hakaba, bayi tunani zatayi saurin kar6ar cikin hakaba, Alhmdllh yafaďa ahankali, aunty bilyma cikin farin ciki ta rungumeta, itama deena sai murmushi take danjin daďin 'yar uwarta ta fahimcesu.
   Ahankali ya Mahmud ya'karaso ya tsugunna agabanta yana mai kallon 'kyakykyawar fuskarta, hannunsa ya ďora saman cikinta yana sakin murmushi, babyna ALLAH yakawominkai duniya lafiya, ALLAH yasa kazama mabuďin 'ya'ya masu tarin yawa danake mafarki da fatar samu arayuwata, Nana maryam ngd miki sosai ALLAH yayi miki albarka kinji.
    su aunty bily sukace amin. tashi yayi yazauna kusada ita suka sakata tsakkiya shida aunty bily, sai kalamai masu daďi suke mata da kwantar da hankali.
   Anan deena tawuni sukasha shafta da kara kwantarma da Nurr hankali.

Da daddare tana zaune saman kujerar dake ďakinta ta rabga tagumi saiga ya Mahmud, kwata2 batasan yashigo ďakinba, ya 'karasa kusada ita yazauna, tagumin yacire shima fuskarsa na nuna alamun damuwa, haba Nurrina ki daure ki cirema kanki tunaninnan kinsan ba'a son mai ciki da yawan tunani yana bata matsala sosai plzz ki rage.
    Jikinsa tafaďa ta fashe da kuka, ya rungumeta tsam yana lallashi da bata ha'kurin 6oye matan dasukayi, sunyi hakane badan komaiba saidan ta kwantar da hankalinta, amma tayi musu afuwa.
   Cigaba yayi da lallashinta, ta ce, "amma yaya nidai wlhy inason karatuna, kenan bazan cigaba da karatuba??, haba Nurrina ki ďauka kun koma makaranta keda Deena, haihuwa bata hana karatu saidai maiyi bai shiryaba, namiki al'kawarin kina haihuwa insha ALLAH zaku koma makaranta keda deena.
    Cikin farin ciki ta ce, "da gsk yaya??, murmushi yay mata ya ce, "da gsk Haskena, ta 'kara kankameshi tana murna, yaji daďi sosai shima saiyayi mata 'kya'kykyawar runguma yana tayata murnar, ya ce, "kinga karki matsemin yaro wajen murna, ta ďago tana murmushi yaya ina farin cikine shiyyasa, fuskarta yakama ya haďe bakinta da nasa yana bata sumba mai 'kyau, (tofa abin mamaki) saiga Nurr tana maida murtani, shi kansa ya Mahmud yarikice da faren ciki, wannan yasa ta 'kara masa 'kaimi akan abinda yake har suka kaiga Nasara ( na ce, "humm 'yammata kodai kodai????).
    Yaudai cikin farin ciki sukayi barci, washe gari ya ajiye aikinsa yakaita awo, saida aka gama komai ya maidota gida sanan yatafi office.

Alhmdullah bikin su ya mustapha yatashi, ALLAH kuma yacikama khairat burinta zata auri ya Mustapha, ya mubarak kuma zai auri Rabi'a itama 'yar family ďince, dama sun daďe suna soyayya, to saimuce ALLAH yasanya alkairi.

Zuwa yansu cikin Nurr yashiga wata na takwas, gakuma binkin su ya Mubarak yazo, dan har anfara shagali, Nurr tana samun kulawa wajen ya mahmud da aunty bily, dai dai da wanka oga ya Mahmud ne keyi mata, aunty bilyma bata barinta aikin komai, daga barci sai kallo, saikuma ya mahmud idan yadawo yakama hannunta suyta zagaya gida saboda likita ya ce, "taďan ringa motsa jikinta.
   Babu laifi yanzu ta kwantar da hankalinta, amma har yanzu tana 'ikirarin bata son ya Mahmud, dukda dai bata faďa agabansa saboda tsoron abinda yay mata akwanakin baya saka makon furta bata sonsa datayi.
   Yanzudai cikinne yake bata haushi musamman yanda duk 'kananun kayanta sukaiyi mata kaďan, batada damar saka 'kananun kaya, Saima dogayen riguna nashan iska da ya mahmud yasayo mata, saikuma waďanda aka ďan ďinko mata, lamarin nabata haushi musamman idan zasu anguwa, saidai tasa doguwar riga.
   To yanzu ga biki yazo ankontama sai dogayen riguna akayi mata, dakuma zani da fly.
    Dahakadai aka shiga hidimar biki, yau lunching amma ya Mahmud ya hanata zuwa, tana zaune abakin gadon mama duk haushi ya isheta, mama tashigo, a'a autata lafiya naga ranki a6ace??.
    Ta turo baki gaba, ba yaya bane ya hanani zuwa lunching, ALLAH mama inason zuwa kuma,, mama tazauna kusada ita tana lallashinta, kinga kiyi zamanki ki huta, aii sauki ya nema miki, yanzu kinyi nauyi bako ina yadace kijeba kiyi zamanki kinji, kingama abinda nayi miki yanzu dan nasan kinaso, ta mika mata filet ďin alalan daketa kamshin kifi.
   Cikin farin ciki ta amsa tana murna, tafara ci kenan saiga aunty khadija da ya mahmud.
   Aunty khadija ta ce, "da 'kyau autar mama kina nan ansaki ďaki kinacin abin daďi, babu ruwanki da wata hayaniya, ya mahmud kana ganifa??.
    Ya mahmud ya ce, "aii kedai khadija bari kawai, mu munacan muna shan rana ita tana nan aďaki da kayan daďi mama najidakefa auta, mama dake zaune tayi murmushi to 'yan sa ido ku saurara mata, auta aii yanzu abin tausayice ga kowa, burina kawai naga ta sauka lafiya, Nurr ta ce, "mama sunafa yin kishine aii tuni na ganosu, ya Fahad ne kawai da ďan uwa Saiff basa kishi dani aďakinnan.
   Dariya su ya mahmud suka saka, harda mama datayi murmushi, ya mahmud ya ce, "wato kishi muke dake??.
   , tace emana.
tafaďa tana saka laumar alalarta.
     Aunty khadija ta ce, "tofa kai yaya an harbo jirginmufa, yayi murmushi ya ce, "saimuyi taka tsantsan, suna haďa ido da Nurr ya kanne mata ido ďaya tareda ďaga mata gira.
    Murmushi kawai tayi ta maida kanta 'kasa dan ganin mama tana kallonsu.
                        Da hakadai aka cigaba da hidimar biki, da 'kyar yabarta taje dinar  danma yaga darene kuma tare sukaje, washe gari aka ďaura aure, da daddare aka kai amare ďakunansu.
    To su khairat ALLAH ya sanya alkairi da zaman lafiya, tareda zuri'a ďayyiba.
    Muma ranar bikin Reefat yahya zamu cashe, dan saimun kwashi shoki nida Manshat lol.
    Ameen ya rabbi.....................







Luv u oll my fun's 
©2017
[14/03 13:08] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》










NA BILKEESA IBRAHEEM 
    {♡Bilyn Abdul♡}






HIQAYA ONLINE WRITER'S




53

...........Haka Nurr tacigaba da rainon ciki, yayinda ya Mahmud da aunty bily suke bata gudummawa agefe.
     Alhmdllh ciki yashiga watan haihuwa, yanzu Nurr ďin tasake zama 'yar shagwa6a sosai, ga saurin fushi, to dama idan ciki ya tsufa sai ahankali, kusan kullum sai mama ko mami sunzo dubata, idan mama tazo taringa shagwa6a kenan, tace wanan tace wancan, (to kowa yasamu dama ya dama).
   Ya mahmud ko ďakin aunty bily yake to idan dare yay nisa saiya dawo ďakin Nurr ya ida kwana daboda gudun kar haihuwa tazo kwatsan babu kowa akusa, to yanzuma da ake saran yau gobe ko jibi sai kawai aunty bily ta ce, "ta yafe yaringa kwana ďakin Nurr ďin har ALLAH ya sauke ta lafiya, yaji daďi sosai har yasaka mata albarka.
   Nurr dake zaune tana jinsu saitaji ta 'kara kaunar aunty bily, tana addu'ar ALLAH yabata ikon 'kyautata mata kamar yanda itama take mata batareda 'kyashiba, har zuciyarta tana 'kyaunar aunty bily da halayenta, har wataran tana sha'awar koyan halin hakuri da kawaici irin na aunty bily, taja ajiyar zuciya danjin anta6ata.
   Aunty bily tayimata murmushi Nurr ďin mama arage dogon tunani kinji??, murmushi Nurr tayi tareda jin jina kai, ya mahmud yabi matan nasa da kallo cikin sha'awa da kara kaunarsu.
   wasu na gudun haďa mata biyu amma shi yaga fa'idar haďa mata biyu, har yakanji yafi kowa sa'a arayuwa, yana fatan ALLAH yabashi ikon cigaba dayin adalci arayuwarsu baki ďaya, ALLAH yacigaba da haďe masa kansu har 'karshen numfashinsu.


                   .☆♡☆.
Yaudai kam tun rana Nurr batajin daďin jikinta, dauriya kawai take, aunty bily taso taďan fahimci hakan, amma da Nurr tafarga aunty bily tana kallonta saitayi murmushi ta basar kawai.
    Aunty bily ta ce, "Nurr kamar bakida lafiya??, Nurr tayi murmushin ya'ke aunty mikika ganine??, lafiyata kalau kawaidai kinsan yauda gobe, gakuma cikinnan ya isheni.
   'Yar dariya aunty bily tayi karki damu muma mun 'kagara ki juyo mana babyn mu, murmushi kawai Nurr tayi dan tanama aunty bily kawaici, suna nan suna 'yar hira lokaci2 Nurr takan ďan cije le6enta, amma bata bari aunty bily tagani.
   Ya mahmud yaturo 'kofar yashigo da sallama, suka amsa su duka, cikin fara'a aunty bily ta tarbeshi, ya mi'ka mata jakkar aikinsa, tareda sumbatar kumatunta, ya ce, "ya gidan?.
   Ga shinan lfy my handsome, masha ALLAH yafaďa yana lumshe idanu, aunty bily tawuce ďakinsa domin kai masa jakkar, yatako ahankali inda Nurr ke zaune, tunda tai masa kallo ďaya bayan shigowarsa ta ďauke kai, tanadai jin maganarsu da aunty bily, durkusawa yayi akasa tareda sumbatar cikinta, ta rintse idanunta saboda haushi, my baby ina fata kana cikin 'koshin lafiya??, Nurr dai tana jinsa amma bata tanka masaba, ya ďago yana kallonta Nurrina ko sannu da zuwa babu??, taďan ta6e baki toni sannun mi zan maka bayan ďankane agabanka.
    Da sauri ya 'mi'ke yakoma kan hannun kujera yana murmushi, ni na isa my Nurri, ya sumbaci kumatunta ina fata kina lafiya??, 'yar harara tayi masa, sai yanzu kayi tunanin ina lafiya??, o, sorry gimbiya amin afuwa, batace komaiba.
    Aunty bily ta sakko ta kawo masa ruwa yasha sanan yay hamdala, yamike daga kusada Nurr kunga bari naje na watsa ruwa ko?, to yaya! aunty bily tafaďa, samansa ya nufa, yay taku ďaya zuwa biyu saiya juyo, Nurr yakama tana kallonsa, da sauri ta kauda kai daga kallonsa, yay ďan murmushi sanan yacigaba da tafiya.
    Har zuwa dare Nurr tana jinta ba daidaiba, ga wani abu yana ta zuba daga jikinta, tsoro yafara kamata, kodai tafaďawa aunty bily ne??, kai bari dai ta'kara daurewa kilama irin ciwon datakejine kullum, tana zaune tanata sake2 saitaji cikinta yajuya kamar an birkita abunda ke cikinta, ya salam tafaďa murya aďashe, tareda kan kame filon kujera, zuwa wani ďan lokaci saiya lafa.
   Ya mahmud yashigo sanye da kayan barci, yaďan bita da kallo dan ganin kamar tana cikin wani hali, Nurri na lafiya kuwa??, ta huro hanci dan har yanzu yana ďan murďa mata kaďan2, kafin tabashi amsa an sake wuntsilawa, ta ce, "inna lillah wa inna ilairraji'u"". 
    Da sauri ya Mahmud yari'keta dan tana shirin faďowa 'kasane, tofa daga nan tafara murkusu2 ajikinsa da kiran yaya ka taimakeni zan mutu, tuni ya ruďe ya sa6eta gaba ďaya yafice, afalo yashiga kwalama aunty bily kira, atsorace tafito itama tana tambayar lafiya kuwa??, ďakko makullin mota bilkeesu Nurr babu lafiya.......ai kafin ya 'karasa faďa takai karshen benen sa, babu daďewa tafito ta shiga ďakinta zumbulelen hijjab tasako akan kayan barcin jikinta, a harabar gidan ta iske su ya mahmud yana ri'ke da Nurr daketa kiran sunan ALLAH, babu 6ata lokaci ya mahmud yashiga baya aunty bily taja motar suka fice daga gidan aguje.
    Asibitin Dr Asheer suka nufa, aiko cikin gaggawa aka amshesu, aka kai Nurr ďakin haihuwa, ya mahmud ma ya danna kai, Dr Asheer ya ce, "Sardauna kayi ha'kuri kajiramu a waje.
   Sorry Dr bazan iyaba wlhy, ka barni kawai, babu yanda Dr ya iya dole yabar ya mahmud, yaje ya rungume Nurr daketa faman kuka da ambatar duk addu'ar datazo bakinta, shima cigaba da taimaka mata da add'ar yayi idanunsa sunyi jajur saboda tashin hankali, gani yake kamar Nurrinsa zata mutune.
    Haka Nurr taci gaba da Na'kuda abin tausayi, cikin amincin "UBANGIJI" ta sallu6o 'katuwar 'yarta mace, mai kama da ita sak, abin sai wanda yagani masha ALLAH, tuni murna ta lilli6e ya Mahmud, acikin jinin yasunkuci 'yarsa yarungume, Dr Asheer ya ce, "wow!! Sardauna, ka 6ata jikinka aii, karka damu doctor ina cikin farin ciki yau, da'kyar ya lalla6ashi ya kar6i baby ana gyarata, dama tuni an ďauke Nurr, fitowa yayi danya kawoma aunty bily albishir sai yatarar dasu mama ma sunzo, cikin zumuďi suke tambayarsa lafiya?? dan ganin jini ajikinsa.
    Ya washe baki yana faďin Alhmdllh ta haihu, gaba ďaya suka kaure da faďin alhmdllh!!!, saikuma ga dector yafito dawani sabon albishir Nurr tasake haihuwar Namiji, wayyo daďi aii sai Murna ta 'kara karfi, cikin minti talatin aka gama gyara mai jego da jarirai, Allurar barci akayima Nurr danta samu hutu, aka kaita ďakin hutu.
   Yaran kuma akace su shigo su gansu, masha ALLAH kowa ke faďa dan yaran masha ALLAHU sunyi ruwa biyune, sun ďebo mamarsu da babansu.
   Cikin kankanin lokaci labari yacika family ďin cewa Nurr ta haihu, ALLAH sarki kowa murna yake dafaďin ALLAH yajikan mahaifiyarta inama tanan, wanan abin farinciki ya faru??.
      Humm ya Mahmud kam ai yafi kowa murna da farinciki awanan rana, jiyake kamar yafi kowa sa'a awajen ALLAH, Nurr dai tanata barci batasan halin da'ake cikiba, sai washe gari tafarka da safe.
     aunty bilky tana zaune itada mama, yaran suna hannunsu, annaďesu cikin pink ďin kayan sanyi sai tashin 'kamshi suke, ya mahmud ya'karasa kusada ita da sauri yana faďin Nurri kin tashi, kai kawai ta ďaga masa batareda tayi maganaba.
   Masha ALLAH yafaďa yana murmushi, zaki iya tashine ???, nanma kai ta jinjina masa, su mama suka shiga yimata sannu bayan ta tashi zaune, bari nakira Dr ya mahmud yafaďa yana fita, babu daďewa suka dawo shida likita, cikin farin ciki likita ya ce, "kai masha ALLAH ai komai Normal inagama zaku iya tafiya da ita gida acigaba dabata kulawa, Amma gobe idan ALLAH ya kaimu akawo yaran dansu amshi allura.
   Babu damuwa Dr mungode sosai, sukayi musbaha da ya Mahmud, Sardauna ina maka murna sosai ALLAH yaraya mana manyan gobe.
   Amin doctor nima ngd sosai ALLAH yabar zuminci, amin doctor Ashir yafaďa shida su mama.
   Nanfa suka shiga shirin tafiya gida, kai tsaye gidan ya Mahmud aka wuce da ita, saidai tuni fuskar Nurr ta canja launi dan ita a tunaninta gidan dady za'a tafi da ita, amma saitaga sa6anin haka, mama tana lura da ita dan haka tayi murmushi kawai, dan tasan halin autar tata da son gida.
    Suna zuwa ruwan wanka aka ďora mama dakanta tayima Nurr wanka, tanata zille2 da faďin zafi, mama ta ce, "haka zaki daure dan idan ba ayimiki wanan wankanba aisai asamu matsala, ana gamawa mama tabarota danta karasa kimtsa jikinta, jariraima an sallesu tareda saka musu kayan sanyi farare masu taushi da laushi, Nurr ma tafito ta shirya cikin sabuwar atamfa siket da riga.
   Aunty bily takawo mata shayi mai kauri da dađi, saikuma farfesun namankai, da gasassar kaza datasha kayan haďi, dakuma dankali soyayye.
    Humm saidaifa nakula mutuniyarku har yanzu banga ta kula jariranba, kokuwa har yanzu tana cikin magagin haihuwar ne??, to baradai muga ikon ALLAH.
    saida mama ta tsareta sanan taci abincin sosai amma da sai wani tsantseni takeyi, bayan tacika tunbinta mama ta ce, "suma yara sai abasu nasu abincin, Nurr tarage fara'a wayyo mama nikam gsky.........mama ta katseta dafaďin ban gane ke gsky ba??, maza ďaukarsu kibasu abincinsu banason shashancin, mama ta ďora mata baby'girl ďin akan cinya, oya fiddo kibasu.
    Babu yanda Nurr zatayi dole tayi yanda mama takeso, saidai tana kamawa tai saurin cirewa wai zafi, mama ta ce, "eh ahakan zaki basu, zafi kam aii dolene tunda yaune na farko.
    Ta 'kara daurewa tasaka mata, data kama saita janye tana faďin wash ALLAH mama zafi wlhy......ahaka ya mahmud yashigo ya samesu, zama yayi yana kallonsu kawai cike da sha'awa, mama dataga Nurr tana 6ata mata lokaci dan sai wani no'ke2 take.
   Sai kaiwai ta dam'ki nonon tasakama yarinyar, caraf kuwa takama tafara sha, Nurr tashiga yarfa hannu da faďin wayyo mama dan ALLAH abarshi haka plzzz. 
    Ina mama ta'ki saurarenta, itako baby babu ruwanta tunbinta take cikawa, tuni dariya ta zoma ya Mahmud dan ganin yanda Nurr take yarfe hannu, yasa hannu yatoshe bakin dan kar dariyar tafito, amma ina tuni Nurr ta gansa, ta fashe da kuka bayan mama tacire yarinyar ta ďakko baby'boy ďin, mama kinga yaya ko yana min dariya, cikin hawaye tafaďa.
    Mama ta harari Ya Mahmud kaikuma sannunka, to miye na dariyar anan, yacire hannun yanaďan haďe fuska shi adole zai kame kansa, mama nifa ba dariya nake mataba kawaidai ta tsargune, mama ta girgiza kai tareda sakama yaron nono abaki, ya mahmud yafaki idon mama yay mata Nurr gwalo......mama wlhy yanamin gwalo.
    Kai tashi kafita daga ďakinnan, mama yafaďa cikin faďa.
   Ya mahmud yami'ke yana kunshe dariya, saida yazo bakin kofar fita sanan yay mata gwalo yafice.
     (kai ALLAH ya shirya masu karatu)..................






Luv u oll my fun's 
©2017
[14/03 15:38] bilyn Abdul:
Share:

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *