check your best novels here

Monday 20 February 2017

NI DA AMINIYATA!!! 26 to 30

[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 26~October~2016



NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM




26

...........Tunda tabar office d'in tazama wata shiru shiru, gaba d'aya abin mamaki yake bata jitake tamkar amafarki, wai itace zata zama matar uncle G!, kai wannan lamari tamkar ba gsk bane, lallai ko bata son uncle G! tofa dolene ta aureshi, kodan ta k'ara nisanta kanta da Abdul, da fareeda, wasu hawaye suka zubo akan kumatunta, wlhy tana son fareeda, amma gashi fareeda tajawo abinda yanisantasu da juna, tana matuk'ar kewarta da son ganinta, takifa kanta saman tebir tana kuka.
   Zaliha ta tab'ata, sopy lfy dai ko? Sopy tad'ago tana kallon zaliha, fuska share share da hawaye, ta ce, "babu komai wlhy zazzab'i nakeji".
   Ayya sannu to kitashi na kaiki hostel mana.
  Sopy ta girgiza kai ki bari mu gama lecture tunda saura d'aya.
  Zaliha ta ce, "to shikenan", amma fa wata magana najiyo yanzu akanki!!.
    Sopy ta ce, "akaina kuma zaliha??, wace irin magana kenan?.
   Zaliha sarkin gulma ta gyara zama, wlhy wasu samari naji suna fad'in way soyayya kukeyi keda uncle G! Wai shiyyasa kikema samari girman kai, dan anga wai yabiki library d'azu.
    Sopy ta k'urama zaliha idanu, kamar zata cinyeta, saida zaliha ta tatab'ata, sannan taja ajiyar zuciya, zaliha ta ce, "mi kuma kike tunani?
   Sopy ta girgiza kai babu komai, amma ni k'arya suke min, dan kawai sunga yashiga library sai suce wajena yaje.
   To aii wai bayan fitowarsa ke kuma kinje office d'insa!.
   Sopy taja tsaki, ta ce, "kai magulmaci madai yaji haushi wlhy, to uncle G! Abokin uncle d'inanane tare sukai karatu a wannan makarantar, wannan itace dangan takar dake tsakaninmu, sai a daina gulmarmu aii, ta maida kanta ta kwanta.
    Zaliha uwar gulma aka jinjina kai, kinsan ba kowane yasan hakaba, dan nima dabaki fad'aba ban saniba, dan wlhy nima nazata soyayya kukeyi, to ammafa kallon dayake miki irin na masoyane, idan fa yana lecture to gaba d'aya hankalinsa yana kanki, to kinga aii masu fad'a basuda laifi.
   Banza sopy tayi mata, dan tasan zaliha magul maciyace tafad'a aji, ita ba k'ok'ariba sai iyayi da gwalli.
   Ganin sopy ta shareta sai tatashi ta fita, wajen samarin ta nufa tazauna, suka shiga tambayarta zaliha tagaya miki, zaliha ta rik'e baki tana fad'in kukam magulmatane wlhy, idan ance maxa sun iya gulma ku musa mana, to ta ce, "wai abokin uncle d'intane.
    Wani acikin samarin ya ce, "kai wlhy ban yardaba, k'arya ta fad'a miki, amma kicigaba da saka mata ido zaki hano gskyr maganar, zaliha tamik'e tana fad'in aiko saina gano bari naje dan za'ayi mana lecture yanzu.
   Samarin suka shek'e da dariya, suna fad'i zaliha dama ke kina fahimtar karatune.
   Zaliha ta hararesu tai gaba, dan tasan magana suka gaya mata.

Koda sopy ta koma d"aki takasa aywatar da komai, tunani ya bai baye kwakwalwarta, ji tai yau son Abdul ya dawo mata sabo azuciya, jitai a yau zata iya auren Abdul suyi kishi da fareeda, ta rintse ido ta bud'e tana fad'in, ya ALLAH idan shaid'an ne yake k'awata mini hakan ALLAH ka dawo dani cikin hayyacina!, ta fashe da kuka tana girgiza kai, wlhy bazan iya zaman kishi NI DA AMINIYATA ba har abada, fareeda na hak'ura na bar miki Abdul har abada wlhy, nabar miki! Na bar miki!!! Ta k'arasa fad'a cikin kuka mai ban tausayi, masu karatu nimadai saida na matse hawaye dan sopy tabani tausayi.
    Ta dad'e tana kuka daga k'arshe ta dangana, tayi shiru, sai shashsheka da takeyi, dahaka wani waha lallen barci ya d'auketa.
   Da safe da ciwon kai mai tsanani ta tashi, dan haka bayan gama sallar asuba saita koma barci.
     Wringing d'in wayartane ya tasheta, sunan uncle kabeer tagani akan wayar, ta tashi da sauri, tana amsa wayar, bansan miya fad'a mataba ta tashi da sauri tahau shirin fita.
   Kai tsaye office d'in uncle G! Tanufa dan tasan uncle kabeer yanacan, ta kwankwasa aka bata izinin shiga, da sallama tashiga, suka amsa mata,  ta rissina tana gaishesu.
    Uncle kabeer ya d'ora da fad'in my daughter ya dai? Naganki kamar kina cikin damuwa?,
   Sopy ta girgiza kai, ta ce, "uncle lafiyata k'alaw kainane kawai keyin ciwo.
   Ayya sorry my daughter, yanuna mata kujera ta zauna, uncle G! Ya ce, "kinsha magani ko?.
   Ta ce, "e nasha shine ma yasakani barci.
Okey ALLAH yabaki lfy.
  "suka amsa da amin."
Uncle G! Yamik'e yana fad'in bari naje nagabatar da lecture.
  Okey lecturer!! Uncle kabeer yafad'a cikin tsokana.
  Uncle G! Yafita yana fad'in kana nan baka canjaba kabeer.

Bayan fitar uncle G!, uncle kabeer yadawo da hankalinsa ga safiyya da kanta yake kasa tana wasa da zoben hannunta yay gyaran murya, sopy ta d'ago tana kallon sa, yay mata murmushi d'iyata yaya dai??.
  Itama ta murmusa ta ce, "bakomai uncle.
   Ya ce, "okey to shikenan, dama wata magana ce takawoni, duk da youseef yasanar dani kun fara maganar jiya ko??.
   "E, uncle! Hakane".
Uncle kabeer ya ce, "to ke yakika gani?? Kin amince??.
   Sopy tay kasa da kai saboda kunya.
   Karki damu d'iyata, karki bari kunya tahanaki fad'ar gskyar ki, inhar baki sonsa ki sanar dani.
   Sopy ta rufe fuska da hannuta ta ce, "ina sonsa uncle!!.
   Uncle kabeer yay dariya, "ALHAMDULILLAH", yafad'a yana gyara zama, lallai ina tayaki murna d'iyata!!, da samun miji nagari mai addini da tarin ilimi, nasan watarana zakiyi alfaharin kasancewar youseef a matsayin mijinki, zakiji dad'in zama dashi domin kuwa mutumin kirkine shi, ALLAH ya kaimu lokacin musha biki.
   Sopy taja hijjab  ta rufe fuska.
  Uncle kabeer yayi dariya, bazakice amin ba sopy.
   Ta ce, "kai uncle wlhy kana bani kunya.
 To bani kunyata uncle kabeer yafad'a.
   Haka sukaita hirarsu, har uncle G! Yadawo, tunda ya shigo bakin sopy ya mutu, ta daina magana takuma sunkuyar da kai k'asa.
    Uncle G! Ya nunawa uncle kabeer sopy da baki, uncle kabeer yay dariya ya ce, babu ruwana nidai, kunfi kusa.
   Sopy ta d'ago karaf ta kama uncle G! Yana mata gwalo.
  Batasan sanda ta harareshiba, ya ce, niko!!. 
 Saida taje bakin k'ofa sannan ta ce, "e, ta fita da gudu.
   Dariya sosai sukeyi, uncle G! Ya ce, "kabeer dama haka safiyya take??.
   Uncle G! Yay dariya ya ce, bazakaji mutuwar sarki abakinaba.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, sopy tana karatu yanda yakamata, takanje gida weekend lokaci2 idan tasamu dama, shak'uwa kuma tana k'ara shiga tsakaninta da uncle G!................




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 27~October~2016




NI DA AMINIYATA!!!



NA  BILKISA IBRAHIM 




27

..........BARI MU WAYWAYI FAREEDA....
   Fareeda kam rayuwa ta canja mata, kwance take tana fidda numfashi da k'ar sakamakon zazzab'in dake jikinta, babu abinda ya haddasa mata zazzab'in sai uban aiki da umman Abdul tasakata, dak'yar tagama aikin tajawo jiki tazo ta kwanta.
   Abdul yashigo ko sallama babu, ko kallo bata isheshiba ya wuce yana canja kaya, fareeda tabishi da kallo tana zubar da hawaye.
   Ya gama yanufi hanyar k'ofa domin fita, ta daure ta ce, "Abdul!!.
   Ya juyo yana kallonta awulak'ance batareda yayi maganaba,
   Cikin kuka ta ce, "dan ALLAH Abdul inaso muyi magana, ka taimaka kazauna.
  Ya gyara tsayuwa kinga malama idan zaki fad'a ki fad'a dan babu wani zama dazanyi, inada gurin zuwa.
   Fareeda ta cije baki, cikin k'arfin hali ta tashi zaune.
  Ta ce, "Abdul dan ALLAH miyasa ka juya mini baya, yakamata ka fahimceni, yanzu ka daina kula dani, kana ganin wahalhalu dana ke ciki agidannan ga gallazawar mahai fiyarka amma baka tab'a nuna rashin jin dad'in kaba, dan ALLAH karka barni Abdul, yanzune nafi buk'atar zama dakai Abdul, karka manta saboda kai nabar iyayena, nabar 'yan uwana, nabar aminiyata mai sona dason ganin farincikina, amma danmi zaka barni bayan yanzu kai kad'ai gareni, saikuma wannan cikin dakake gani bai dace yazoba ayanzun.
   Abdul yaja tsaki, yanuna ta da d'anyatsa yana fad'in, wlhy idan kina tare da wannan shegen cikin bazaki tab'a samunaba, zaki cigaba da rasa abubuwa arayuwarki kuwa, kamar yanda wad'ancan mutanan suka barki to nima haka zan barki, amma har yanzu kinada sauran dama, inhar kika yarda aka zubar da wannan cikin tofa zan dawo miki a matsayin Abdul d'inki nada, inko har kika cigaba da bijirewa buk'ata ta tofa zaki shiga k'angin rayuwa wanda yafi na yanzu, kuma bazaki raini d'an dake cikinkiba agidannan, dan nafad'a miki ban shirya haihuwaba yanzu, ban shirya zama uba ba yanzu, amma kikayi sakakin d'aukar ciki saikace wata akuya, acikin wata biyu da zuwanki, ke wlhy yanzuma dan abbana ya hanani sakinkine, amma kicigaba da zama akan taurin kanki kigani, idan ban yi waje dakeba, nabaki nanda sati biyu ki yanke wadda zata fisheki, ko ki yarda azubar da ciki, kicigaba da zama dani, ko kik'i yarda nayi waje dake.
   Fareeda ta fasheda kuka ta ce, "haba Abdul kayimin adalci mana cikinnan fa d'an kane, ta hanyar aure muka sameshi, kuma namiji shike bada kwan haihuwa, miyasa bazaka gane ba laifina bane? Kuma wlhy ana mutuwa wajen zubar da ciki ko mutum yarasa mahaifarsa, baka gudun d'aya acikin wad'annan yafaru dani ne??.
   Abdul yaja tsaki, yafice yana fad'in matsalarkice kuma wannan, nidai nafad'a miki buk'a tata, idan kin kiyaye kin tsira, idan kin cigaba da bijirewa zaki koma gidan tsohone.
    Kuka sosai fareeda takeyi dan duk taji kalaman Abdul na k'arshe, ta tura kanta cikin filo tana gunjin kuka, yaune rana ta farko data tab'ajin wani abu mai kama da nadama ya ziyarci zuciyarta, saidai har yanzu tana son Abdul d'inta, tanaji kuma a zuciyarta tafi safiyya sonsa walhy, lallai dolene tabi hanyoyin dazata magance matsalar dake tsakanin ta da Abdul, koda kuwa zubar da cinne, tunda shine tushen faruwar matsalarsu, lallai fareeda bakida hankali.

Agidansu sopy kuwa anata shirin bikin uncle kabeer, sopy duk tazama busy sakamakon duk abinda uncle kabeer zaiyi saida ita, ga makaranta damma cikin weekend za ayi bikin, batada wani lokacin kanta, yauma suna gama lecture uncle kabeer yakirata akan tashirya gashinan zuwa zai d'auketa suje wani waje, gudu2 tayi wanka bata tsaya yin wata kwlliyaba ta zura doguwar riga ta shadda tasaka hijjab sai dai yau iyakarsa guywa tad'ansaka turare ta fito.
    Bata dad'e da fitowaba shikuma ya shigo cikin makarantar, bayan sun gaisa ta ce, "to uncle mutafi ko?.
   Ya ce, "sai mun jira youseef dan hardashi zamuje.
   Sopy tai saurin kallon uncle kabeer, uncle dammi sai da shi zamu?.
   Uncle kabeer ya ce, "dan yanada muhimmanci atafiyar.
   Sopy tayi shiru dan ita kam gsky bata son tafiya tare da shi, inhar yana guri bata sakewa, saboda tsananin kunyarsa datakeji......, muryarsa ce ta katse mata tunaninta, yak'araso yana fad'in sorry na b'ata muku lokaci ko?.
    Uncle kabeer ya ce, "A'a, itama aii yanzu tazo.
   Sopy ta daure ta ce, "ina yini sir! ?.
   Ya ce, "lafya lau maa!.
Uncle kabeer ya tuntsure da dariya ya ce, "one  one, kenan.
   Suka shiga mota suna dariya banda sopy datad'an murmusa kawai, tunda suka shiga mota sopy tayi tsit, sai dai duk d'agowar dazatayi saitaga uncle G! Ita yake kallo ta madubin gaba, ganin yasaka mata ido saita daina d'agowa ma gaba d'aya.
   Kasuwa sukaje, suka lodo kaya, na duk amfanin dazasuyi awajen biki, tundaga kayan abinci da drinks, da duk wani abunda zasu iya bukata, sun siyo dai dai k'arfinsu, suka zubo amota suka kai inda zasu ajiye.
   Uncle kabeer ya ce, "auta saura d'inkinki ko?.
   Sopy ta ce, "uncle aii telan ya ce, "sai gobe idan ALLAH yakaimu.
   Okey to ALLAH yakaimu goben, yanzu bari mu kaiki makaranta ko?.
   Ta ce, "dan ALLAH uncle ka kaini gida gobe sai nadawo.
   Uncke G! ya harareta, saboda son yawo ko?? To makaranta zamu maida ke, dan goben da safe nine zan fara yi muku lecture, kuma harda test mai zafi, kinsan kuwa idan bak'ya nan hukuncin ki yafi nakowa.
   Uncle kabeer ya juyo yana kallonta, to kinji fa, kinyarda na kaiki gidan??.
   Sopy ta d'ago ta kalli uncle G!, daya tsura mata fararen ida nunsa masu haske, tai saurin maida kanta k'asa kamar xatai kuka.
  Uncle kabeer ya ce, "sopy shagwab'arki tayi yawafa, ko kin manta kin girma, nafa kusa aurar dake.
   Aii kamar jira take saita rushe da kuka.
   Sukuma sai dariya ta kufce musu, suka fita daga motar suna dariya, uncle G! ya ce, "gsky kabeer bakada kirki, ya bud'e baya yashiga inda sopy take zaune, yakai hannu zai kama hannunta saita k'ank'ame jikinta, shima saiya fasa,.
   Cikin taushin murya ya ce, "to kukan ya isa haka, ke dai abu kad'an sai kuka, kabeer ya shagwab'aki dayawa.
   Ta turo baki gaba, ya ce, "hummm, ashe idan baki maida bakin nanba zan tsotseshi yanzunnan.
   da sauri ta rufe fuskarta, ta kama k'ofa zata gudu, amma sai tajita gam arufe.
   Ya murmusa da ina zakije??
Ta ce nidai kutafi na fasa zuwa gidan.
   Uncke G! Ya ce, "aii dama dole ki fasa, tunda na hana, ya mik'a mata wata leda ga wanna kiyi kwalliyar biki ko,.
 Ta ce, "uncle kabeer da babafa duk sunyimini d'inki.
  Ya ce, "to aii nasu daban, nawa daban, su iyayene, nikuma mijine.
  Tai k'asa dakai tana fad'in nagode ALLAH yak'ara bud'i.
   Ya murmusa dan jin dad'in addu'arta gareshi, yad'ora da fad'in, kamar yanda nayi miki alk'awari gobe zan aika a d'akko miki Aysha.
   Da sauri ta ce, "dan ALLAH dagaske sir!.
   Uncle G! Ya harareta oh, bazaki daina cemin sir! D'innan ba ko?.
   Ta ce, "to aii dai sunankane ko.
 Ya ce, "humyim, zanyi maganin bakinki, nan bada dad'ewaba.
  "Shiru tayi masa."
Yayinda uncle kabeer yashigo motar yana fad'in kunga kumuje nifa inada aikin yi, dannaga ku soyayyace agabanku.
   Sopy ta ce, "kai uncle nidai dan ALLAH kabari.
   Uncle G! Ya koma gaba yana fad'in kaidai anyi uban banza, nikam ban more sirikiba.
   Uncle kabeer yay dariya yace, "habawa kaidai kabini ahankali idan ba hakaba na hanaka d'iyar.
   Taf, dakasha matsa kuwa, kaga aii kabayar da wuriko?? uncle G! Yafad'a yana tada motar...................




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 28~October~2016



NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM




28

...........biki dai ya kankama, komai yana tafiya yanda akeso, Aysha k'anwar uncle G! Tazo, sopy tayi farincikin ganinta, itamadai Ayshar! sopy! ta burgeta, tana ganin kuma ida yayansu ya aureta bazasu samu matsalaba, dan suma talakawa ne kamarsu, kuma gidan mutunci.
   Duk inda sopy tashiga Aysha na biye da ita, wannan yasa tasamu sauk'in wasu ayyukan, uncle G! Kam bata ganinsa domin suma suna can suna hidimominsu.
  
Yau aka d'aura auren KABEER MUKTHAR da ASIYA ALIYU d'aurin auren yasamu halartar mutane masu yawa, musamman abokan aikinsa da kuma wad'anda sukayi karatu tare, ga mutanen baba suma, to saimuce ALLAH yasanya alkairi uncle kabeer ALLAH yabada zuri'a d'ayyiba, nanda wata tara mu dawo suna.
    Da daddare aka kai amarya d'akin mijinta, su sopy sun isa gidan tun kafin zuwan amarya, amarya da danginta suka iso, anyi musu tarba ta mutunci, bayan an kammala abubuwan al'ada, motoci suka kwashi mutane domin maidasu gidajensu, amma sopy da Aysha sunanan, uncle kabeer ya ce, "su tsaya su gyarama amrya inda aka b'ata, dan k'awayenta sun tafi dan gudun karsu rasa motar dazata maidasu gida, bayan tafiyar kowa suka k'uk'e suka gyara gidan suka bajeshi da k'amshi, wajan k'arfe tara abokan ango suka rako angon k'amshi.
   Sudai su safiyya k'ofar gida suka koma domin jiran su, basufi minti talatinba suka fito, motar uncle G! Suka shiga ya maidasu gida, a k'ofar gidansu sopy uncle G! ya ce, "Aysha tashiga gida, Sopy ta ce, "to nima aii gidan zanje.
  Ya ce, "A'a zamuyi magana ne.
Dole tayi shiru.
   Bayan fitar Aysha, uncle G! Ya kalli sopy, ita kuma tayi k'asa da kai, ya d'an murmusa yana fad'in Safiyya! sarkin kunya.
  Yanda yakira sunan nata saida tsigar jikinta ya tashi, tabbas babu wanda ya iya fad'ar sunanta kamar uncle G!, yakan fad'i sunan dawani irin yanayi mai saka mamallakiyar sunan cikin wani irin yanayi.
   Yay gyaran murya, tareda k'ara ambatar Safiyya!!
  Itama cikin sanyin muryarta mai zak'i ta ce, "Na'am.
  Yad'an gyara zamansa, ina ganin gobe idan ALLAH ya kaimu zan maida Aysha gida, daga nan kuma zan taho da magabatana domin kawo kud'in aurnmu!!.
  Sopy tayi shiru tana tunani, yad'an buga yatsunsa biyu sukai k'ara, ta juyo tana kallonsa, yay murmushi tunanin mikikeyi ne?.
 Ta ce, "bakomai, amma dan ALLAH kabar Aysha tad'an k'ara kwana biyu.
  Ya ce, "bazai yuwuba Safiyya saboda Aysha tana makaranta kuma kinga gobe litinin, tamayi asarar karatun goben kenan.
  Sopy ta ce, "hakane, amma dan ALLAH idan anyi musu hutu zaka kawota.
  Karki damu, zatazo insha ALLAHU sannan ma kina gidanki!.
   Tasa hannu tarufe fuska.
Humm sarkin kunya kenan, nikam kar kunyarnan ta cutar dani a abayan aure.
  Bata ce, "komaiba tabud'e motar ta fita.
 Yay murmushi to saida safe tunda babu sallama.

Washe gari uncle G! Yazo d'aukar Aysha, da kuka suka rabu da sopy, inna tanata lallashin Aysha, haba Aysha kukan ya isa haka mana, insha ALLAHU kwanannan ma zata dawo wajenku kinji, kiyi hak'uri kibar kuka ya isa haka.
  Da haka dai sopy tarako Aysha wajen uncle G! Dake k'ofar gida, yabisu da kallon mamakin dan ganin idanunsu duk hawaye, ya jinjina kai yana fad'in sannunku da kuka, saikace wad'anda zasu mutu.
   Sopy ta gaidashi ya amsa yana kumshe dariya.
   Ahaka dai sukai sallama, uncle G! Yaja mota suka tafi, tunda suka tafi Aysha take kuka, saida uncle G! Yadaka mata tsawa sannan tayi shiru.
  Cikin fad'a ya ce, "kinbi kin dameni da kuka, saikace har abada bazaku sake had'uwa ba? Inhar bakimin shiruba to wlhy zan tsaya na zaneki anan.
  Tasan halinsa sarai dan haka tayi shiru, ta ce, "yaya dan ALLAH kayi hak'uri wlhy aunty safiyya tanada kirki, duk wanda ya zauna da'ita dole yayi bak'in cikin rabuwa da'ita, dan ALLAH yaya kuyi aure da wuri dan tadawo gidanmu gaba d'aya.
   Uncle G! Yay murmushi oh Aysha kinda abin dariya wlhy, to wai mi auntyn nan taki tayi miki hakane kiketa yabonta??
   ALLAH yaya sunada yawa, yanzu haka bakaga tsarabar datayo minba, ta gwaggo da ban ta baba daban hardasu aunty hafsat ma duk tayi musu suma.
   Uncle G! Ya jinjina kai lalai aunty tana jidaku, kenan ni kad'aine batayima tsarabarba??. Aysha tayi dariya to yaya ai kai kuna tare kulum shiyyasa.
   A'a bawani muna tare ita dai ta wareni kawai.
   Haka sukaita hira har zuwa gida.

Itamadai sopy tunda suka tafi taiyi shiru dan tana k'aunar Aysha, yarinyar tanada shiga rai ga wayo da son aiki, zuwan su aunty NAFISA ne yasaka tad'an ware, suka shiga aikin gyaran gida, da kaiwa mak'ota kwanikansu da sauran abinda aka aro domin yin amfani, dayake duk danginsu anan cikin kano suke, sai yazama babu kowa a gidan sai isu isu, inna dakanta ta shirya karin kumallo sopy taje takaiwa su uncle kabeer.....................





Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 29~October~2016




NI DA AMINIYATA!!!




NA BILKISA IBRAHIM




30

........Akwana atashi babu wuya gurun "UBANGIJI", biki dai ya kankama, dukkan gidajen biyu sunata shiri, hakama uncle G! Yayi wuyar gani, ita kanta sopy baganinsa takeyiba, sai idan yaje musu lecture, ko kuma idan ya kirata a waya su gaisa.
  Yau da yamma Sopy tashigo anguwarsu, tana shigowa layinsu tayi kicib'is da Abdul, suduka gabansu ya fad'i, yabita da kallon k'urullah, itako ta tamke fuska kamar bata tab'a dariyaba, ta ratseshi zata wuce, da sauri yasha gabanta, takauce zuwa gefensa nanma ya tareta.
  Ta ce, "malam bani hanya nawuce.
   Ya ce, "haba gimbiyata ninefa Abdul d'inki mai sonki da k'aunarki, wlhy ina kewar rashin ganinki, dan ALLAH ki tsaya muyi magana.
   Ta balla masa harara tareda jan wani mugun tsaki ta ce, "kaga malam tunkafin na shuka maka rashin mutunci kabani hanya na wuce, wlhy Abdul natsaneka.
   Ya rinyse ido ya bud'e dan tabbas kalmar tata ta daki zuciyarsa, ya marairaice murya yana fad'in, Sopy nasan baki tsaneniba haryanzu kina sona, kina cikin b'acin ran abinda yafaru abayane, dan ALLAH kibani dama namiki bayani yanda zaki fahimceni, kece kad'ai nakeso kuma ashirye nake dana aureki ahalin yanzu.
   Sopy ta tuntsure da dariya, sannan ta tamke fuska tamkar ba ita tayi dariyarba, ta nunashi da d'anyatsa Abdul wai kaine! kake tunanin zama mijina!, tad'an murmusa, Abdul har abada bazan zama shashashar macen dazanyi miji irinkaba, ka d'auka SAFIYYA IBRAHIM KABEER ta sub'uce maka har gaba da abada, ta ciro kati daga jakarta ka karanta wannan shi kad'aima ya isa yabaka amsa, inama gayyatarka, dan nasamu miji mai tarin ilimi k'yau, aji mutunci, kai idan ina lissafa maka abinda ya dangan ceshi tofa sai mu kwana anan,kuma katashimin ahanya kafin natara maka mutane wlhy.
  Jiki asanyaye yamatsa mata ta wuce, tunda yafara karanta katin yake fitar da numfashi  mai kama da nishi, yajingina da bango gudun karya fad'i, cikin murya kamar mai kuka ya ce, "fareeda kin cuceni ALLAH ya isa tsakanina dake, kuma wlhy yau saikin gayawa aya zak'inta, yanufi gida kamar mayun wacin zaki.
  Da sauri muka bishi dan muganewa idanmu abinda zai faru.
      To bari mugani fareeda kota zubur da cikin??.
   Tunda nagabato b'angarenta nakejin ihun kukanta, wanda inada tabbacin suma mutanen dake gidan sunajinta, amma babu wanda yay yink'urin zuwa yaga abinda yafaru.
   Nak'arasa d'akin da sauri nida  madina, Abdul ne ke lakad'awa fareeda dukan 'yan danbe, duk yaji mata ciwo, amma wannan baisa ya daina d'irkartaba, dak'yar muka iya kwatarta, ya bimu da kallo yana huci kukuma daga ina??.
   Madina ta ce, "tofa, Abdul maida wuk'ar mu bak'in fareeda ne, yaja tsaki tozaku iya tafiya aii ko.
   Na ce, "kayi hak'uri Abdul kabari mu taimakawa fareeda kaga duk ciwone a jikinta, wata uwar harara yasakarmin, to aii ko uwar tace tazo gidannan saita fita, tunda sunce sun sallama mini ita, bareku gayyar sod'i, wlhy tun kafin nabud'e idanuna kubar gidannan idan kuwa bahakaba tokuwa jikinku  zai fad'a muku.
   Aii kafin yagama rufe baki madina uwar 'yan tsoro taja hannuna munyi waje, ta ce, "humm aunty bily naga mutuminnan yafara haukacewa wlhy zai iya dukanmu, kekam gaki lutiya idan yasamu wannan tsokar aii kinga takanki.
   Na balla mata harara ina fad'in ALLAH madi kin rainani, ni son k'ibar nan tawa nakeyi idan baki saniba.
  Amma gsky Abdul bashida mutunci irin wannan duka dayake mata kamar wata karuwarsa, kuma muta nen gidan sunaji amma sunk'i cetonta.
   Madina tayi dariya aii ni dad'i nakeji wlhy ALLAH yasa yay mata abinda yafi hakama, aii maganin maci amana kenan, kad'amma tagani.

To yaudai lefe ya iso na sopy, mota guda muta nen GURUM sukayo domin kawo lefen Safiyya.
   Akwati uku da karami na sama, babu laifi uncle G! yataka rawar gani, dan lefennan saidai mak'iyi amma yayi atalauce ba a sarauceba, anyi musu tarba ta mutunci, irin wadda suka tabbatar da sunzo gidan karamci, sun kuma tabbatar d'ansu yasamu d'iyar gidan tarbiyya,agidansu fareeda aka amshi lefen dan babanta ne zai d'aurama Sopy aure, aka had'a musu shatara ta arzik'i sukatafi, suna yabon wad'annan muta nen kirki.

Sopy tagama shirinta tsaf, tafito tana fad'in inna nashirya bari natafi kafin su cinyeni da masifarsu, bakamar aunty Nafisa sai bala'i takemin ina b'ata musu lokaci.
  Inna ta ce, "to adawo lfy, kuma aii sunfiki gsky tun yaushe suke jiranki amma kina d'aki kina lank'andi, aii mijinki yaga takansa, mutum yay ta abu kamar kwai yafashe masa aciki.
   To yi hak'uri inna bari natafi ina k'ara b'ata lokaci.
  To ki gaishesu, kicema yayar taku gobenfa sutaho da wuri dan ayi aikin cin-cin d'innan agama da wuri.
  To inna zan fad'a mata, tatafi tana dariyar inna, tunda bikinnan yamatso kullum tana kan aikin abubuwa bata ko hutawa .


30

..............Da sallamarta tashiga gidan, suduka suka hauta da jaraba, aunty hauwa'u ta ce, " 'yarrainin wayo, kin zauna kinata yan kwana mu, saikace mu zai amfana, gwarama ki nutsu dan wannan mijin naki d'an kwalisa gara kije masa zam zam d'inki, ki rik'e abinki tunkafin wata takwace miki, irin wad'anna rubibinsu akeyi.
   Sopy ta tab'e baki, nidai baruwana, dan tun wurima idan wannan zancen zakumin na koma, aunty asiya matar uncle kabeer ta tuntsure da dariya, barsu d'iyata wad'annan yayun banzane zoki zauna, aunty nafisa ta ce, "karma tazauna aii ita zai amfana bamuba, hakadai sukaita tsokanar sopy tana musu shagwab'a.
   Gyarata suke kamar babu gobe, tundaga jikinta harzuwa inda ba'a fad'a;sunsha gyara, zata zauna agidan auty Nafisa dan suci gaba da gyarata, tunda bawasu k'awaye garetaba wad'anda zasu takura mata.
  Bata zuwa ko'ina daga d'aki sai tsakar gida, kunji 'yar gatan auntys d'inta, wayartama ankarb'a ankashe, hankalin uncle G! Duk yatashi yanaso yaganta kodan su tattauna amma hakan tak'i samuwa.
   Ya kira uncle kabeer ya tambaya?.
   Uncle kabeer ya ce, "lafiyarta k'alau wlhy, nima haka nemanta nake amma tak'i yarda naganta, way tana wani gida b'oyo.
  Tofa, uncle G! Yafad'a, to watake b'oyemawa??.
   Uncle kabeer ya ce, "agonta mana.
   Uncle G! Yay dariya to shikenan tunda dai lfy ai da sauk'i, amma yakamata kazo gobe mu had'ufa.
   Okey to badamuwa, zuwa k'arfe hud'u zan shigo insha ALLAH.
  TO ALLAH YAKAIMU.

yau k'unshi amma babu amarya, inna sai fad'a takeyi akan b'oye Sopy amma sunk'i fito da'ita saidai subata hak'uri, can gidan aka kai mai k'unshi tamata ta'iya sosai wlhy karkuga yanda Sopy tayi k'yau kamar ba'itaba, jikinnan yasha gyara, Nadiya kad'ai tasan inda take, dan ita take kula da abinda yashafi k'awayensu na makaranta da wanda sukayi secondary tare.
   Sai a daren d'aurin aure aka dawo da sopy gidansu, inna ta rud'e daganin k'yawun da sopy tayi, sai latsa jikinta take tana fad'in kaga yara da dabara mikukaima auta na ne tayi haka?.
  Su aunty asiya sai dariya suke ma inna.
  Inna ta ce, "A lallai dole nabaku tukuyci dan gyaran dakukaima autata yayi.

MASU IYA MAGANA SUKANCE RANA BATA K'ARYA SADAI UWAR D'IYA TAJI KUNYA, to haka kuwa wannan ranar take ga uncle G! da Sopy.
   Ayau dai and'ara auren Youseef Hussein Ahmad da Safiyya Ibrahim kabeer, karkuso kuga wankan shaddar da ango yayi, yayi kyau matuk'a, da yawan d'alibansa da malamai 'yan uwansa sun halarci d'aurin auren, mutanen GURUM kuwa aii ba'a magana, matasan garinsu d'ai d'aine basu zoba, sai washe baki yake dan farin ciki wasuma bai sansuba, lallai naga taron gagarimin d'aurin aure, abin sai wanda yagani.
     Dak'yar na iya nemo muku amarya sopy, itamadai taci gayu cikin wata atamfa mai k'yau, idan natsaya bayyana muku kwalliyarta sai nacika littafin, amma dai tabbas ta had'u tamkar zata gasar sarauniyar k'yau, tana zaune itada k'awaenta agidan su fareeda, dukkanin 'yan professional writer da Zumunta sunje, sunkumayi rawar gani wajen mik'awa Sopy gudummawa, canna hango Hauwa lele kusada amarya, to sopy saimuce ALLAH yasanya alkairi.
    Wajen k'arfe hud'u aka shirya amarya domin kaita garinsu uncle G!, dan sai ankaita can sun gama bikinsu, daga baya sai angonta yadawo da ita gidansu dake nan kano.
    Sopy sai kuka take, dan iyayene suka zagayeta ana mata fad'a da nasiha, irin wadda akema amare, "sai dai wasu amaren basa d'aukar irin wannan fad'an saboda kunnen k'ashinsu", to ita dai sopy da alama komai yana zama a kwakwalwarta.
    Da haka dai aka d'ungunma da amarya zuwa GURUM dake acikin k'aramar hukumar Tsanyawa, tareda gayyar 'yan uwa da abokan arzik'i, a k'awayenta Nadiya ce kawai taje, muma dai munbi ayari nida gayyar 'yan group d'ina dan kar abamu labari...................





Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 29~October~2016


NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM



29

........Gwaggo ta tari autarta da murna, dan kwana biyunnan tayi kewarta, Aysha ta ce,"gwaggo wlhy nayi kewarki kwana biyu, sai dai naji dad'in zuwa kano.
   Gwaggo ta ce, "kai auta fad'i gaskiya dai, kinga yanda kikai haske da k'iba a kwana biyunnan kuwa, mikike cine haka? .
   Aysha tayi dariya, aii wlhy gwaggo bazasu lissafuba, kai matar da yaya zai aura tanada kirki gwaggo gata mai k'yau.......tayi shiru domin shigowar uncle G!.
   Ya ce, "to uwar surutu ince har kin fara zubama gwaggo shi.
  Gwaggo ta ce, "to badoleba tayi kewanane aii.
  Uncle G! Yazauna a kan tabarmar dake shimfid'e ad'akin yashiga mik'a gaisuwa ga gwaggo.
   Gwaggo ta amsa cikin fara'a, ta ce, "ya aikin? Da abokan zama?.
   Wlhy lfy law gwaggo sunata gaisheku, da kuma godiya.
  Kai haba saikace wani abu, mu abinda kabiru yay mana aii bazamu iya biyansaba.
   Uncle G! Yay murmushi, ya ce, "gwaggo ina baba yake?.
    Baban ku yana wajen zana idar malam haruna mai gari.
   ALLAH sarki, gwaggo malam haruna yarasu?.
  Wlhy kuwa d'annan yanzu badad'ewa aka fad'i mutuwarsa, inagama ba'a binnesaba.
   To ALLAH yagafarta masa da dukkan musulmai baki d'aya, amma mutuminnan yasha wahalar jinya, ALLAH dai yasa kaffarane.
   To amin gwaggo tafad'a tana mik'ewa, bari nakawo muku ruwa, munata surutu ko ruwa ba'a bakuba.
   Uncle G! Ya ce, "bakomai gwaggo da kin barima Aysha saita d'ebo aii, gwaggo ta ce, bari nad'ebo tunda natashi, saima ahad'o da abinci, saidai kuma ban bayar ansiyo maka awarar taka ta famaba, wannan tararrabin rasuwar ya mantar dani,, Aysha taso ki siyo masa, ALLAH yasama bata k'areba kinsan Awarar uwaliya kamar nama take agarinnan.
  Aysha ta ce, "to gwaggo kawo kud'in??, ki d'akko a k'ark'ashin filo, akwai d'ari biyu.
  Uncle G! Ya ce, "karb'i barmata kud'inta, ya mik'a mata dubu d'aya, ta ce, "yaya daka bari na d'auki d'ari biyun dan wlhy sai kaga anata neman canji ak'isamu.
 Ya ce, "to, kuma kiyi sauri, dan karki zauna neman zance.
  Aysha tafita tana turo baki.
Gwaggo tashigo da ruwa a kofin silba, ta koma ta d'akko samira ta ajiye gaban uncle G!, ya ce, "yawwa gwggonmu sannunki da aiki.
   Ta zauna tana fad'in aii kune da sannu, kuda kuka sha hanya, ya d'auki ruwan yasha, yana murmushi, suka cigaba da hira kafin Aysha tadawo.
  Badad'ewa Aysha tadawo, sukaci suka k'oshi yafita danyin sallah da ta'aziyyar rasuwar da'akayi.
     Baba yashigo, Aysha taje ta taroshi cikin farin ciki, A'a Ayshatu! saukar yaushe??, aysha tayi dariya baba tun d'azu mukazo harda yayama.
  Ya ce, "madallah ina yusufan yake?, baba yanzu yafita sallah baku had'uba?, A'a bamu had'uba, k'ila masallaci juma'a yaje sallar dan sune naji sun tada sallah yanzu.
  Saida yay gasuwar yadawo, ya tsugunna ya gaida baba, baba ya amsa cikin fara'a, yusufa! ya jama'ar birni?, dasu kabiru ango??.
  Wlhy lfy law baba, yanata godiyar d'awainiya.
   Kai haba in banda abin kabiru miye na godiya, abun nawa yake, tunda ALLAH bai nufa zamu d'aurin aurenba.
   Aii bakomai baba hakanma angode ALLAH yasaka da alkairi, Aysha aii ta wakilceku.
  Sun dad'e suna hira, anan nema uncle G! Yasanar da baba maganar tura manya gidansu safiyya, ckin jin kunya yake maganar.
  Baba yayi dariya aii ko yusufa nayi farinciki da wannan magana, wlhy dama zamannan naka ya isheni haka, mutane sai surutu sukeyi wai dan kayi boko kak'i yin aure, sun manta aure lokacine.
  Uncle G! Yay k'asa da kai yana fad'in gsky ne baba, amma kuyi hak'uri.
   A'a aii bakomai yusufa tunda gashi lokaci yazo, aii mu sadai muce ALLAH ya kaimu lokaci, yasa kuma ayi da ranmu.
   Akan leb'ensa ya ce, "amin.
Bayan sun gama tattaunawa yafita domin ganawa da matasan k'ungiyarsa kamar yanda yasaba, domin suma tuni sun hallara gurin dasuke had'uwa tunda sunsan da zuwansa.

Da dadadare aunty hafsat suka zo itada libabatu dan tuni Aysha taje gidajensu takai musu labarin matar da yaya zai aura, harda tsarabarsu, sannan ma shi bai dawoba yana waje.
   Basu dad'e da zuwaba ya shigo shima, ya ce, "A'a 'yan uwa kune da daddarennan??
   "Sukace mune!!.
  Yaja kujera 'yar tsugunno yazauna, suka gaisa, sukai masa godiyar tsaraba, ya ce, "wace tsaraba kuma aii ni! banyima kowa tsaraba ba.
   Aunty hafsat ta ce, "e, auta tace k'anwar muce tabamu ALLAH dai yasaka da alkairi yakuma kawo mana ita lfy.
  Uncke G! Ya ce, "to amin, yakuke da yaranku da mazajen!! ku?
  Suka ce, "duk muna nan lfy.
 Ya ce, "aii haka akeso.
Baba yashigo yana fad'in tofa yau gidan biki akene?
  Sukayi dariya, kowa ta gaidashi, sannan sukace munzo sannu da zuwane.
  Baba yazauna yana fad'in ince ko har Aysha taje muku?.
  Sukace aii baba tun d'azu ma kuwa.
  Ya ce, "auta kenan sarkin hidima, nan dai sukayita hira, harma baba yay musu bayanin maganar auren yayansu.
  Sunyi murna kwarai da gsk.

Washe gari uncle G! Yataho damasu kawo kud'in aure, anyi musu tarba ta mutunci, daganan komai ya gudana, atake kuma baba ya saka ranar aure nanda wata hud'u, iyayen uncle G! Sunji dad'i domin kuwa babu wani jan rai, bayan sun kammala uncle G! Yakaisu tasha suka hau mota domin komawa gida.

Haka rayuwa tacigaba da gudu da sauri, sopy tana karatu, kuma sukan yi hira jefi jefi da uncle G!, Dan bai cika takurata ba, saboda Baya son tasamu matsla a karatunta, yakan taimaka mata akan abinda yashige mata duhu, dukda har yanzu tananan cikin jin kunyarsa bata cika sakin jikintaba idan yana guru, zuwa wannan lokacin kuma labari yabaza makaranta cewa uncle G! Zai auri safiyya.
   Wasu har zuwa suke takanas domin ganin mai sa'ar data samu zuciyar tsadajjen namiji mai aji da ilimi irin uncle G!, dayawa sukanyi mamakin ganinta, dan azatonsu farace k'al kuma mai shegen k'yau, wasu sukance dama masu k'yau basu cika zab'ar mace mai k'yauba, wasukuma sukanga safiyyan tadace da uncle G! D'in, domin itama tanada k'yau, sai dai k'yawunta mai b'oyuwane, irin wanda saika cika kallonta ko kana tareda ita kullum kake gani, to koma dai miye 'yammata saiku saurara domin kuwa safiyya itace tauraruwar uncle G!, dan shiyyasan sirrikan daya gano agareta.
  Magulmata dai anata aikin gulma, yayinda wasu 'yammatan suke jin haushinta dan sunnunama uncle G! D'in so amma yay burus dasu, itakam ko kallo basu ishetaba dan bata shiga sabgar kowa, garama Nadiya sukan d'anyi hira amma itama bakomai tasani dangane da sopy ba.
  Dan sopy ta daina k'awa bare AMINIYA, anriga anmata tabo azuciya akan AMINTAKA............




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *