check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 40

AUREN  K'ADDARA
               ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim

39«*****» tana bud'ewa suka afko harda k'ok'arin tureta, ta bisu da kallo cikin mamaki, umma ta daka mata tsawa to mara kunya kinyi tsaye kina kallon mutane ko baki sammu bane??
Cikin ladabi Munneerah ta durk'usa tace ina kwana??
Banza umma tai mata, takuma maimai tawa,
Umma ta harareta to sarkin iyayi, tunda kinyi na farko, aiya isa zakibi kidamemu,husna tace, inafa zatai shiru ana neman gindin zama, aiko indai ananne bazata samuba har ta mutu, cewar ikileema.

Umma tace to bara kiji bawai narasa mai gaisheni bane, nazo namiki kashedine ga jikokinanan karnaji karna gani, kinsan dai sunyi k'anwa dake tawajan uku, to wallahi nasake naji wani abu ya b'ullo saikin gawa aya zak'inta, nasan hajiya salaha uwarki sarai, to nasan dai halinta babu wanda 'yay'anta suka bari, makirci,kissa, iyayi,dahad'a kiahiyoyi da miji, to wallahi anan kikai mana irin wannan halin acikin kwana kad'an zaki kama hanyar gidan ubanki, idan kunne yaji jiki  ya tsira, ta fice.
Ikileema ta dinguri Munneerah, shegiya faratun banza sai munyi maganinki agidannan, 
husna tace saita barsa da k'afarta tsinanniya gadon tsiya, suka tafa suka fice.

Munneerah ta durkushe agurin tana kuka, nashiga uku ni Munneerah wannan wane irin bala'ine haka, tadad'e tana kuka daga k'arshe ta share hawayenta, tatashi tashiga kichin domin yin girkin rana.

Bayan tagama ta nufo d'akinta, ta d'auki waya tanason kiran anty Ni'ima dan tasanar da ita damuwarta.

Ta zaro idanu waje , dan ganin dady yakirata har sau 8, na shiga uku tafad'a tana juya wayar, har sau takwas yaya ya kirani ban ganiba, yau naga ta kaina..........

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *