check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 50

AUREN  K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

50 «******» ku kuma lafiya??
    "Husna tace lafiyarce takawo haka, tafad'a tana murgud'a baki
     "Yaratse ta gefensu zai wuce ikileema tai saurin shan gabansa, ya tsaya yana kallonta,itama kallonsa takeyi cikin tsakkiyar ido, ya sake canja hanya husna ta tareshi ta can, kai wai lafiya kuwa??
    "Ikileema tace kace haka kuwa, amma cakai kowacce acikin mu ta rink'a zuwa d'akinka ko???
       "Eh hakana ce, yanzu miyya faru???
  Husna tace abinda yafaru shine munga kafito daga nan 6angaren, da alama ma nan ka kwana??
"Can na kwana sai mi,kuma yafaru?
         Kace haka kuwa, mudai inhar aka cigaba da cin amanarmu ALLAH ya isa wallahi.
Suka bar gurin da sauri, dady yabisu da idanu, yana mamkin rashin tarbiyya irin na yarannan, amma zai gyara musu zama kwanannan.

 Ya wuce yay shirin zuwa office, sanda yadawo 6angaren Munneerah harta gama had'a break , ta shiga wanka, ya zauna yay break d'insa, yana cikin cin abincin Munneerah ta fito cikin bak'ar soguwar riga da ratsin blue, ta d'aura blue d'in d'an kwali.
    "Ta zaro ido waje, yaya dakanka? mai makon kajirani nazo na zuba maka??
          "Yay murmushi, saikace wani aiki?
Wallahi aikine yaya kamarka kana zuba abinci da kanka, aiba girmanka bane.
     "Ya jawota jikinsa ya zaunar da ita kan cinyarsa, to minene girmana my beauty!!! ???
 Ta sinne kanta cikin k'irjinsa tana shak'ar k'amshin turarensa mai dad'i, yay kissing d'in kunnanata, kibar jin kunyata my beauty, nifa mijinkine, kuma ai mata batajin kunyar mijinta.
  Takuma cusa kanta a k'irjinsa tana dariya, kinga tashi kici abinci, kisha maganinki, dukda nasan mak'iyinkine magani.
 Ta tashi zaune ta yinkura zata tashi, yarik'eta da sauri ina zaki kuma??
  "Ai ni zan baki da kaina 'yan mata"
 Yaya please zanci da kaina, ALLAH kunyarka nakeji.
aiko ki ajiye wannan kunyar yau da hannuna zan baki abinci, dole ta hak'ura yabata da kansa tana zaune asaman cinyarsa, da kyar ya barta, amma da yadage saita cinye filet guda na abinci, yabata maganin tasha tana yatsina baki, saida yayta lallashinta sannan tasha.

Tarakashi har mota kamar yanda tasaba, suka rabu cikin tsantsar farinciki, da kewar juna.
     "Ta juyo tanata murmushi, ganin su husna ak'ofar 6angarenta sai jikinta yay sanyi dan tasan ba alkairine ya kaisuba.

Aiko,tanazuwa suka hau zaginta,
Ikileema tace shegiya karuwa dangin tsiya, yanda uwarki ta mallake ubanki, taraba shi da kishiyarta, haka kikeso ki mallake mana miji, kirabamu dashi.
 Husna ta cafe haba ALLAH yakiyaye muzauna wanan 'yar yariyar ta mallake mana miji wallahi.
Husna takawo mata duka, aida Munneerah da gudu ta fad'a palonta tarufe k'ofa tunkan su shigo, tana fad'in bazan zauna ku dakeni abanzaba wlh.......


billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *