check your best novels here

Tuesday 21 February 2017

NAWAFF!!! 7 to 12

[04/12/2016 12:54] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆NAWAFF
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM




Page 10

......Yau takama d'aurin aure amma yasmeen batada niyyar zuwa, umma tayi mata maga ta ce, "bazata jeba sai anjima.
      Shima dai Nawaff ya halarci taron d'aurin auren daganan yakama gabansa, dan shi mutumne dabaya son yawan hayaniya, gashi da mutane sun ganshi bazasu bari ya huta ba.

3:30pm
   Yasmeen kwance a falo tana kallon film, umma tafito daga d'akin abba, ta zauna kusada yasmeen.
    Yasmeen ta d'ago tana kallonta, umma ta ce, "mamana yau bazaki wajen bikin asma'u d'in ba??, yasmeen ta ce, "gsky umma bazan jeba bana jin dad'i, amma idan naga zuwa anjima naji sauk'i sai naje.
   To shikenan ALLAH ya sauwak'e.
    Amin yasmeen tafad'a tana kallon tv, lfyr yasmeen k'alau, batason zuwa wajenne su had'u da Nawaff, tana tsoron karya aikata mugun nufinsa akanta, jadabaya ga rago kuwa aiba tsoron fad'a bane, inji masu iya magana.

Badan ALLAH Nawaff yay shirin zuwa wajen walimar ba, yajene kawai domin yasmeen, amma saidai kash ita batajeba, tunda yaje yake baza idanu, amma komai kama da ita bai ganiba.
   Duk abinda yake mus'ad yana kallonsa, dukda yasan Nawaff bazai aikata abinda yafad'a akan yasmeen ba, amma yayi matuk'ar farin ciki da bata zo wajenba.
   Bayan antashi daga walimar su Nawaff sukai saurin guduwa, saboda mutane, amota mas'ud ya ce, "bro's waimi kake nema d'azu kaketa lek'e2.
    Nawaff yad'an ja hancinsa tareda kwantawa sosai ajikin kujera yana kallon titi, daga bisani yadawo da kallonsa wajen mas'ud dake tuk'i, ya ce, mara kunyar yarinyar nan nake nema, amma ban gantaba, inaga tsoro yahanata zuwa.
   Mas'ud yay murmushi, hankalinsa na bisa titi, ya ce, "aii masu iya magana suna cewa hanyar lafiya abita da shekara, nikaina naji dad'i dabata zoba.
    Nawaff ya harari mas'ud, kai malam mikake nufine?? wai ko dai son k'abar nan kakeyi??.
   Mas'ud yay dariya yana fad'in A'a alhaji maida wuk'ar niba sonta nakeyiba, kada kishi yasa ka b'arar dani.
    Banza Nawaff yay masa, dan yasan halin Mas'ud sarai yanzu saiyayita jan wannan maganar har momcy taji.
    Dahaka suka k'arasa gida, kai tsaye b'an garen momcy suka nufa, afalo suka iskesu itada papa da Abdallah.
    Nawaff yazauna kusada k'afar papa yana kwasar gaisuwa, shima mas'ud ya gaisheshi, suka gaida momcy, Abdallah ya gaishesu.
    Papa ya ce, " 'yan samari daga ina haka??.
   Nawaff yad'an sosa sumarsa ya ce, "papa daga wajen bikin Safwan muke.
   Papa ya ce, "masha ALLAH, ALLAH yasanya alkairi, kuma aii yakamata kufito da matan auren ko??,  da sauri Nawaff yad'ago yana fad'in papa aurefa kace??.
   Papa ya ce, "o, ashe kajini modeebbo!!.
   Nawaff ya ce, "papa 27year's fa.
   Momcy ta ce, "toshi wannan dakukaje bikin ba abokinku bane, amma gashi yayi, kudai nakula daga kai har Mas'ud bakwa sonyin aure, ko sokuke saikun tsufa??.
   Barsu ummul'khairi, aimun yanke magana da Alhaji, nanda k'arshen shekara idan har basu kawo matan aureba, tomu zamu nema musu.
   Nawaff ya ce, "papa saikace mata.
   Papa yakama kunnensa, yana fad'in toku zauna kukagani, sadaka zamu badaku.
   Abdallah ya tunysure da dariya.
   Nawaff ya harareshi yana mazurai, kai wa kakema dariya??, mas'ud ya ce, "bro's barshi zaizo ya samemune.
   Momcy tayi dariya A'a karku huce akan d'ana, tunda bashi ya ce, "ayi sadaka dakuba.
   Papa ya ce, "barshi ai shima hardashi.
   Abdallah ya zaro idanu, papa nikuma asuwa wai kare da gudun layya, 'yan 27year's basuyiba, bare ni d'an 20years papa kwanan fa nashiga jami'a.
    Nawaff ya daka masa tsawa, kai dallah kaima mutane shiru, kabi ka ishi mutane da shegen surutu.
   Abdallah ya zunb'uro baki gaba yana gunguni, amma Nawaff bayajinsa, Dan yasan idan yajisa, hummm. 
    Saida sukaci abinci sanan suka tafi b'an garen Nawaff.
  Mas'ud ya ce, "kai malam kahuta wlhy karigaya ka kama matarka ahannu, babu rabon ayi sadaka dakai.
   Nawaff ya ce, "agidan ubanwa nasamu matar, ALLAH mas'ud kaifa d'an iskane.
   Mas'ud ya tun tsure da dariya, kazauna kallon ruwa wlhy kwad'o yamaka k'afa, kanaji kana gani za'ayi sadaka dakai.
   Nawaff yaja tsaki tareda kwanciya saman kujera, ya lumshe idanu.
   Duk surutun da mas'ud yakeyi yana jinsa amma yay kunnen uwar shegu dashi................





Bilyn Abdul
    Mrs Abdus'salam
        LUV U OLL MY FAN's 
[05/12/2016 00:40] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆☆
NAWAFF  
☆☆☆☆☆☆☆☆





NA BILKISA IBRAHIM





Page 7

......WAYE NAWAFF SA'EED MODEEBBO???.
      ALHAJI sa'eed umar modeebbo shine mahaifinsa, babban alak'aline mai gsky da rik'on amana, bashida tsoro Ko kad'an, yakan yanke maka hukunci dai2 da abinda ka aikata, duk kud'inka ko mulkinka bazaisa ka kub'uta ahannunsa ba, sai dai gskyr ka ta kub"utar dakai.
    Kaifi d'ayane shi, idan ya ce, e,  "baya cewa A'a.
    Alhaji sa'eed bafulatanine irin na daji, dan k'yak'yk'yawane abin so dagani, d'an asalin garin safana ne dake k'aramar hukumar caranchi,  safanar ma acikin wani k'yauye suke cikin rugar jauro, amma yanzu yana zaune a kano.
    Matarsa d'aya hajiya ummul'khairi, balarabiya ce cikakkiya, k'yak'yk'yawar mace, mai hak'uri da ilimin addini, ga son mutane.
    A Egypt ya aurota lokacin yana d'alibin ilimi a jami'ar AL'AZHAR, soyayya sukayi har ALLAH ya mallaka masa ita amatsayin mata.
    Momcy  Nawaff tafara haifa daga shi ta dad'e bata sakeba, sai bayan shekara bakwai ta haifi Abdallah, sai auta Anwar, 
     Nawaff k'yak'yawane  fari amma ba tas ba, ya biyo momcy sosai, dan shikad'aine yake tsananin kama da ita, kana ganinsa kasan itace ta haifesa, sai dai ita tafishi fari.
    Momcy tanada hak'uri batada hayaniya ko kad'an, amma Nawaff yanada zafi, indai wajen haline  papa yabiyo Alhaji sa'eed kenan, Nawaff baya son raini ga son girman tsiya da miskilanci, gakuma ilimi, dan yanada sani wajen addini sosai, shima yanada son mutane.
    Nawaff yana son k'annensa sosai, duk abinda sukeso yana musu, shiyyasa suma suke sonsa da girmamasa.
    Nawaff tun yana primary yakeson kwallo har yashiga secondary, lokancin dayake a secondary sukanje gasar kwallo zuwa wasu makarantun, cikin ikon ALLAH sai sun ciyo kuma Nawaff ne mai zira musu kwallon.
    Bayan ya kammala secondary saboda k'aunarsa da kwallo papa, wato mahaifinsa ya nemi shawarar momcy domin kai Nawaff wata makaranta da ake kira School Academic domin k'ara samun ilimi a fannin kwallon k'afa.
    Fatan alkairi momcy tayi masa tareda addu'ar samun nasara arayuwa.
   Babu dad'ewa aka kaisa wannan makaranta ta (School Academic dake jihar kwara) iyaye da 'yan uwa suka bishi da addu'ar samun nasara, aiko ansami nasarar, dan addu'ar iyaye babbar katanga ce.
     In tak'aicemuku dai, Nawaff bai rufa shekara biyu ba yasamu nasarar shiga jerin wad'anda (NAJERIA's Foodboll Asocion NFF)  suka gayyata zuwa abuja dan yin screening nazuwa kwallon kasa da kasa, na 'yan kasa da shekara 17, (under 17 play engle of Najeria ).
    Awannan screening ansha gwagwar maya, har ALLAH yabawa Nawaff nasarar fitowa d'aya daga cikin wad'anda aka zab'a, harda muk'amin capten na k'ungiyar kwallon kafar Najeria wato ta (under 17).
    Shigarsa (under 17) ta bashi damar wawuro nasarori da dama, dan sun ciyo kofin duniya na wannan lokaci, yasamu damar zurama Najeriya kwallo 9, wannan yasa yazama (here Gold scores )na wannan gasa,   har aka bashi k'yautar, ( Golden but) 
    wannan nasace tajawo hankalin manyan club club na duniya kansa.
    Samun wannan nasara yasaka family nasa cikin farinciki, yayinda shugaban k'asa na wannan lokacin ya shirya musu liyafar cin abinci tareda shi, da k'yautittikan ban girma.
    Bayan dawowarsa daga kwallon k'asa da k'asa wani (club na F,C 20)dake k'asar HOLLAND   yasami damar d'aukarsa.
      ya rattab'a hannu da k'ungiyar na tsawon shekara 5, shigarsa wannan club ya k'ara fito da kwazonsa, yasamu nasarrar buga musu kwallaye masu yawan gsk.
   Awannan lokacin duniyar masana kwallon k'afa suka saka idanu k'ur akan Nawaff, manyan club club suka fara jawarcinsa.
    Daga k'arshe wani club mai fad'a aji yasamu nasarar sayen NAWAFF.
    To ayanzu haka dai girma da cigaba yazo masa, yasamu nasarar tsintar kansa a cikin club d'in (Barcelona F,C )dake k'asar Spain, wannanne ya tabbatar dashi zama babban d'an kwallon k"afa, wanda duniya tasani take kuma alfahari dashi, musamman ma k'asarsa NAJERIA.
    yanzu haka yazo hutun k'arshen shekarane da sukan samu, kwanansa d'aya dazuwa suka had'u da Yasmeen, har ya takaleta.
   Wannan shine tarihin NAWAFF SA'EED MODEEBBO atak'aice....................





©2016


Bilyn Abdul
    Mrs Abdus'salam
         LUV U OLL MY FAN's
[05/12/2016 14:06] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆
NAWAFF 
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM




Page 8 & 9

.....Mas'ud d'an abokin papa ne Alhaji khasim, tare sukayi karatu da papa a Egypt shima masanine ab'angaren ilimin addini danshi har isalamiyya gareshi.
     NAWAFF da MAS'UD tare suka tashi tun suna k'anana, bayan sun gama secondary ne kowa yakama inda yafi wayau, Nawaff yatafi makarsantar koyon kwallo, Mas'ud yatafi kasar INDIA domin k'aro ilimi a fannin Likitanci.
    Yanzu haka shi cikakken Likitane, a babban asibitin Aminu kano, Nawaff bashida wani aboki wanda ya wuce mas'ud, haka shima Mas'ud.
    Sun shak'u da juna matuk"a suna kuma k'aunar juna, saidai halinsu ya babbanta, domin mas'ud mutumne mai sanyi da hak'uri, amma Nawaff yanada fad'a, kuma baya son hayaniya.
   Basa shaye2 bare neman mata, hasalima shi Nawaff baya dariya gaban mata, dan ya ce, "yawan yima mace dariya yakan sa ta rainaka.
    Hummm kunji son girma, naga yannda za'ayi yayi aure tunda baya son mata su rainashi.


A'ban garen yasmeen kuwa tunda suka shiga gida take kuka, umma bata tanbayeta abinda yafaruba, saidai tanata lallashinta, yaseer yashigo hannunsa rik'e da leda, yazauna kusada umma yana turo baki.
    Umma ta ce, "kaikuma lafiya??, ya nuna mata yasmeen data d'ora kanta saman cinyar umma, waishi adole kishi, ya ce, "ALLAH umma wanima saiya d'auka itace auta!.
    Umma tayi masa da'kuwa tana fad'in kaci gidanku bakaga halin datake ciki bane.
    Yaseer yad'an le'ka fuskar yasmeen saiyaga hawaye, yad'an zaroidanu yana fad'i sister miya faru dake??, tad'ago tana kallonsa saikuma ta fashe da kuka, da sauri yadawo kusada ita yana share mata hawaye, ya ce, "haba auntyna yakamata ki daina saka damuwa azuciyarki haka nan, ki manta da komai na rayuwa, idan kuma wannan d'an iskanne yake saka ki kuka kiyi ha'kuri ALLAH zai mana maganinsa, kuma insha ALLAHU abinda yake burin bazai ta'ba kasan cewaba, kullum muna miki addu'oin samun nasara a rayuwa, yafad'a shima yana hawaye.
    Da sauri yasmeen tatashi ta rungimeshi suka cigaba da kuka, sun bama umma tausayi, dan haka itama ta share nata hawayen, saida sukayi kuka mai isarsu, daga baya sukayi shiru.
  
WAI WACECE YASMEEN????.
    FATIMA shine cikakken sunanata, malam Yakubu shine mahaifinta, su 'yan asalin kasar Nijar ne, awani gari kwangwalan, kwangwalan yana nan kusada jihar katsina, dan za'a iya cewa a boda suke.
   Kharima itace mahaifiyarsu wato umma, malam yakubu makiyayi ne a garin kwangwalan mutumne mai tsananin hak'uri, 'yan uwansa basa sonsa, kasancewarsu 'yan ubane, shi kad'ai mahaifiyarsa ta hafa a gidansu.
    Yaransa biyu Fatima sunan mamansa aka saka mata, shiyyasa suke kiranta da yasmeen, saikuma ABUBAKAR shima dai sunan baban umma ne, shiyyasa suke kiransa da yaseer.
    Yasmeen da yaseer k'yawawane, dan sunada kala irinta asalin buzaye.
    Yasmeen tun tana yarinya takeda farin jini, kowa sonta yake, dan haka dangin babanta suka tsaneta laifin babanta ya shafeta.
    Lokacin da yasmeen takai shekara 12 sai dangi suka matsa akan ayi mata aure, zuwa sannan yasmeen tanada wanda takeso wani sule, tana sonsa sosai shima haka, dan haka lokacin da'akace za'ayimata aure saitayi murna.
    Amma saidai kash, dangin mahaifinta sunce sun za'ba mata miji, d'an wan babanta wato Tanimu, yasmeen sam bata son Tanimu dan d'an iskane kowa yasani kuma, amma babu yanda zatayi.
    Aka saka biki wata hud'u, amma amarya bata so, dahaka biki yarage saura sati d'aya.
    Ana saura kwana hud'u d'aurin aure Tanimu yazo gun yasmeen, abin yabata mamaki dan bai ta'ba zuwa wajentaba tunda aka saka musu rana.
   Da'kyar umma ta lalla'bata ta fita, ko sallama bata yimasaba bare gaisuwa, yasaki baki yana zuba mata surutan banza, wai idan sunyi aure randa aka kaita zaiyi kaza zaiyi kaza.
    Yasmeen taji yana d'akko mata zancen daya fi karfin tunaninta, dan haka takama hanyar gida zata tafi, da sauri Tanimu ya dam'ko yasmeen, ya matse abango.
    Yasmeen tafara ihu dan ganin abubuwan daya ke mata, kafin mutane su kawo mata d'auki ya turmushe ta ak'asa, lokacin da mutane suka zo yana saman yasmeen amma baiyi mata komai ba, sai rigarta daya yaga, nanfa mutane suka shiga jibgarsa dan dama haushinsa akeji.
    Kafin safiya labari ya baje garin kwangwalan wai Tanimu yayima yasmeen fad'e a daren jiya.
    Duk gari ya d'auka cewa an lalata yasmeen, dan hakama fita ta gagareta, dan babu wanda zai yarda da ba haka bane, aranar kuma dangin mahaifinta sukace sun warware maganar auren, wai yasmeen 'yar iskace tana neman maza.
    Abu kullum k'ara gaba yake, harta kai umma da baba basuda ikon fita sai ayita zind'ensu, harda yaseer dabai san komai ba, idan yafita sai ayita tsan gwamarsa, itako yasmeen ma aibatada ikon fita ko k'ofar gida.
    Ahaka aka kulla wata 7 amma komai bai canja ba, kuma babu mai zuwa wajen yasmeen, sule ma iyayensa sun hanashi.
   Bak'in ciki da damuwa suka ishi baba, dama akwai wani Alhaji dayake zuwa sayen dabbobi a wajensa, shi d'an Najeria ne a jihar kano.
   Baba baiyi k'asa aguywa ba wajan sanarma Alhaji halin dasuke ciki,, Alhaji buba ya tausaya musu sosai, dan haka ya ce, "su baba su shirya yatafi dasu Najeria.
   Babu musu suka yarda, batareda kowa yasaniba suka baro kwangwalan, koda Alhaji buba yakawo su gidansa sai hajiya jummai ta nuna musu tsangwama, ta ce, "saidai baba yarink'a musu gadi dama mai gadinsu yagudu saboda wahala.
    Baba bai musaba yakar'bi tayinta, baba yana gadi umma tana taya hajiyar wasu 'yan ayyukan gida.
    Alhaji buba yanada wani yaro mara jin magana, sunansa Fasal, shikad'ai ya haifa dan haka ake nuna masa gata na tsiya, tunda faisal ya 'kayalla idanu yaga Yasmeen ya kafa mata k'ahon zuk'a.
    Yasmeen bata manta da abinda yafaruba a garinsu dan haka take baya2 da faisal, duk abinda yake faruwa hajiya jummai tana kula, tasan kuma halin d'anta yanzu saiya 'bata yarinyar mutane, dan haka ta tsawatar masa.
    Alhaji buba yasaka su yasmeen makaranta , ahankali k'yawun yasmeen yafara fitowa, zawa sannan faisal yakai 'kololuwar sha'awar yasmeen, awata ranar lahadine, yad'auki hanyar cimma burinsa, yasaka yasmeen ta gyara masa d'aki, daga haka ya rutseta a d'aki, ihu takwala wanda yasa hajiya jummai isowa da gudu d'akin faisal, saita tarar yana shirin aikata ta'asa, ta daka masa tsawa sanna ta 'ban'bare yasmeen dak'yar.
    Babu wani mataki da 'aka d'auka, dan ko fad'a basuyima faisal ba, dan haka hankalin umma da baba yatashi, suka fara tsanar zaman gidan, dan indai aka cigaba da tafiya haka wataran faisal saiya lalata musu yarinya.
    Da alhaji buba yaga hankalinsu yatashi saiya ce, "yana nemawa faisal auren yasmeen idan yadawo daga karatu america za'ayi biki, inko har basu aminceba to zasu barmasa gida, indan suka amince to zai siya musu gidan dazasu zauna ya nemawa baba aikinyi yabar gadi, zaikuma d'auki nauyin karatun yasmeen da faisal harzuwa inda suke buk'ata.
    Da farko basu aminceba dan sunsan faisal bashida tarbiya, amma dasukaga babu sarki sai ALLAH saisuka amince.
    Aka saka rana da komai, faisal yatafi america karo karatu, badan yasoba, dan yaso saiya mallaki yasmeen kafin yatafi, bawani so yake mataba sha'awarta kawai yakeyi, daya sami biyan buk'ata zai watsar da banxa.
    Bayan komai ya kankama alhaji buba yacika al'kawarin duk daya d'auka yasiyama baba gida madaidaici, yakuma d'auki nauyin karatun su yasmeen, yanzu haka yasmeen tana karatu a (FCE KANO ) yaseer yana shekararsa ta k'arshe a secondary, idan yasmeen zata makaranta ko anguwa kaita akeyi, dan an d'akko mata direba na musamman wato balarabe, duk motar dayaso yake d'aukowa a gidan su faisal yakai yasmeen makaran ta daduk inda take buk'ata.
    Sutura kuwa mai tsadar gsk su alhaji suke sayama yasmeen, haka kayan kwalliya, hajiya jummai tana k'ok'ari wajen sayama yasmeen, waya mai tsada yasmeen take ri'kewa, wata sa'in agidan take weekend, sunayin waya da faisal, saidai hirar tasa duk takan kasance batsa, abun yana damun yasmeen amma babu yanda zatayi.
    Yanzu haka saura wata 5 faisal ya kammala karatunsa, yana dawowa kuma za'asha biki, saidai yasmeen da iyayenta duk basa son wannan aure, kullum addu'arsu ALLAH yakawo sanadin da auren zai rushe, wannan shine tarihin yasmeen....................






©2016

Bilyn Abdul
    Mrs Abdus'salam
        LUV U OLL MY FAN's
[08/12/2016 15:20] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆
NAWAFF
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM




Page 11

....koda daddare yasmeen k'in zuwa kai amarya tayi, ta langyare akan batada lafiya, ta kashe wayarta kuma dan kar akirata.
    Haka rayuwa tacigaba da gudu da sauri, Nawaf yagama hutunsa ya tattara ya tafi kasar Spain domin cigaba da biga kwallo.
    Har ya taho bai k'ara had'uwa da yaesmeen ba, hasalima yamanta da ita, yacigaba da harkokinsa kamar yanda yasaba.
   Itakam yasmeen bata manta dashiba, ko makaranta zata takan fita cikin d'ar2, kullum addu'ar ta kada ALLAH ya had'ata da Nawaff ko da amafarki.
   Dahaka dai aka shere wata uku bataji d'uriyarsa ba, ahan kali tafara sakin jikinta.

Yau agajiye tadawo daga school ta shigo falon tana jan k'afa kamar kazarda kwai ya fashewa aciki, yaseer ne kawai afalon yana cin abinci, idanunsa nakan TV ko k'yaftawa bayayi.
   Yasmeen tadaki kujerar dayake zaune dan taga alama baisan tashigoba, yajuyo da sauri yana kallonta.
   Yasmeen ta harareshi kaidai ALLAH ya shiryaka, shikenan indai kana kallon kwallo sai a rasa hankalinka gaba d'aya.
     Yaseer yay dariya, sorry my aunty ALLAH bansan kin shigoba, kinsan yau mutumina yake buga kwallo bana son komai ya katseni wlhy.
    Yasmeen ta tab'e baki, waye kuma mutuminka??, ata k'aice ya ce, "modeebbo mana, gaban yasmeen yafad'i ras danjin sunan wanda yazame mata baraxana arayuwarta ta yanzu, ta ce, "waye kuma modeebbo??.
    Idonsa na kan tv ya ce, "kalli tv zan nuna miki shi, shine number 10.
    Yasmeen taja flet d'in abincin dayakeci gabanta, ta hauci, saidai itama hankalinta yana kan tv d'in, wani uban ihu yaseer yatashi ya kwala tareda fad'in goooooooooooooo!!!!!!!!!.
   Yasmeen tai saurin rufe kunnenta danjin zai fashe saboda k'arar da yaseer ya kwala, cikin kara ta ce, "dalla malam karka fasamini dodon kunne.
    Ya zauna yana dariya tareda ,yana fad'in sai modeebbo, kana wuta my gay.
    Sai asannan idanun yasmeen suka kai kan Nawaff tamik'e da sauri tana fad'in yaseer kana nufin wannan gay d'in, ta nuna Nawaf da aka nuno ya durkusa akasa yad'aga hannunsa samma  yawani wage baki da alama shima ihun yakeyi dan murna, wasu 'yan kwallo sukazo suka rungumeshi suna ihu.
    Yaseer ya ce, "shine sistona, tauraro kenan mai haskawa a duniyar kwallo, yanzu su duniya take yayi dason gani, hala kin sanshine kika mik'e zumbur.
    Yasmeen taja ajiyar zuciya ta ce, "natab'a ganinsa dai, da sauri yaseer ya ce, "dan ALLAH dgsk kikeyi??.
    Yasmeen ta tab'e baki, ta ce, "kaji yaro natab'a yimaka k'aryane??, awajen bikin Asma'u natab'a ganinsa, dama d'an kwallone??.
    Yaseer yagyara zama Taf sisto idan kinji ana fad'in mai laya kiyayi mai zamani to modeebbo kenan!!, ai duk ranar dana had'u da bawan ALLAH nan to sainayi sadaka.
    Yasmeen ta tunysure da dariya, amma kaidai d'an wahalane wlhy, tafad'a tana mik'ewa.
    Yaseer ya ce, "kedai tafi dan bazaki tab'a ganewaba.

Nawaff zaune ad'akinsa akasar Spain, yana zaune bisa kujera mai zaman mutum d'aya, hannunsa rik'e da remote, yana neman tasha, wayarsa dake gefensa tayi wringing yakai hannu yad'auka.
   Saida yad'an murmusa sannan ya ce, "Hello my gay ykk?
    Daga can mas'ud ya ce, "ina lafiya my bro's, naga wasa d'azu yayi k'yau, ammafa kayi k'ok'ari, acinkin minti biyu na farko fa ka jefa mana kwallo a raga, ina alfahari dakai my bro's.
    Nawaf yay sassanyan murmushi tamkar yana gaban mas'ud, ya ce, "nagode d'an uwana, kana k'ara mini karfin gwuywa a rayuwa.
    Karka damu bro's, dama Anwar ne ya ce, "nakira masa kai, tun d'azu yake nemanka bai samuba, yanaso yayi maka murnar nasarar dakuka samu.
   Nawaf ya ce, "ayya my little bro's banishi.
   Anwar yakarb'a wayan cikin 'yar muryarsa ya ce, "yaya  congratulation!!,
   Tnx my boy, ykk??.
  Ina lafiya yaya, momcy ma ta kalli wasanka na d'azu.
   Woow nice, kace ina gaisheta kajiko??.
   To yaya bye.
Okey bye autan momcy.
    Mas'ud yakarb'i wayan suka cigaba da tattaunawa, mas'ud ya ce, "to shikenan bari nabarka haka, amma gsky kayi k'ok'ari nanda 2month d'in kazo, indai kanada dama, ko kwana uku kayi ma ya isa.
   Okey I will try, my bro's
 Okey ALLAH yakaimu lokacin.
  Sukayi sallama kowa ya kashe wayar.
       Nawaf ya kwantar da kansa ajikin kujerar tareda lumshe idanu..................






bilyn Abdul
     Mrs Abdus'salam
         LUV U OLL MY FAN's
[08/12/2016 19:16] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆
NAWAFF
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM




Page 12

....Zan iya cemuku biki yanata matsowa, dan shirye2 akeyi na garari agidan Alhaji buba, gidansu faisal kenan, shirin biki suke na d'an gata, dukda shi yana America abinsa, amma duk shirin da'akeyi da saninisa.
    Yau tunda safe hajiya jumai tasa balarabe yakawo mata yasmeen gida.
   Tunda balarabe yazo da sak'on kiran yasmeen ta had'e girar sama da k'asa, harga ALLAH bata son zuwa.
   Umma ta ce, "wai yasmeen banaji balarabe ya ce, "hajiya na nemankiba??.
   Yasmeen ta matso hawayen datake matsewa tun d'azu, ta shagwab'e murya umma dan ALLAH kibarsu nikam babu inda zanje.
   Dak'uwa umma tayimata, kinci gidanku, hajiya ba mamarki bace ba, za kitashi kije kosaina Ci k'aniyarki, ko kin manta nanda wata d'aya kin zama surukarta.
   Yasmeen tafashe dakuka, umma yanzu nan har fata kikemini nazama matar d'anta??.
    Umma tayi murmushi mai ciwo, wanda ya nuna ainahin damuwarta, ta kamo hannun yasmeen tayi, ta zaunar da'ita gefenta tana shere mata hawaye, kinga mamana bar kuka, ba fata nake miki ba, amma yakama ta kisa a zuciyarki hajiya uwace awajenki, kuma bamusan abinda ALLAH ya shiryaba nan gaba, karki manta da irin hidima da d'awainiyar dasuke damu, komi muka zama a Najeria sune sila.
   Umma aii badan ALLAH sukayi manaba, sunyine domin d'an iskan d'ansu.
   Umma ta harareta banace karna sake jiba wai.
   Jiki asanyaye yasmeen ta tashi, to umma na daina.
   Bawata kwalliya tayiba kaya kawai ta canja ta k'ara turare ta fito.
    Umma ta ce, "adawo lafiya d'iyar kwarai.
   Amin kawai yasmeen ta ce, "dan idan tayi magana mai tsawo kuka zai iya zuwa mata, tasan umma ma tana cikin damuwa, tana dannewane kawai saboda ita.
   A k'ofar gida suka had'u da yaseer yadawo daga islamiyya, ya ce, "sisto sai ina haka??, ta ce, "anguwa zanje.
   Shiyyasa bakije islamiyyaba??, malam Dawud yanata nemanki!!.
    Yasmeen ta zaro idanu da gsk kakeyi yaseer??, ALLAH karkiji wasa, dan aunty Amina ta ce, "ya karb'i hadda yau.
    Yasmeen ta ce, "naga banu, bari nadawo naje wajen Aminar.
   To saikin dawo, yaseer yafad'a yana nufar gida.

Tunda suka tafi take sharar kwalla, balarabe yana kallonta, harga ALLAH yana tausayama yarinyarnan, duk da bata tab'a fad'a masa damuwarta ba, amma ya fahimci bata son maigidansa, inama yanada hanyar taimaka mata wajen rushewar wannan auren K'ADDARA ko BIYAYYAR (book d'ina danafi k'yauna ), amma zai gwada sa'arsa yagani.
    Dahaka suka isa gidan, mai gadi ya bud'e musu get, balarabe yasamu guri yay parking.
    Da sand'a yasmeen tashiga falon tamkar wata muna fuka, tai turus dan ganin samari guda uku zaune suna kallo, ta gaishesu sannan ta shige bedroom d'in Hajiya jummai dan babu inda bata shiga a gidan.
    Tunda ta tafi suka bita da kallo tamkar goyon mayu, saida tashige suka kalli juna, d'aya ya ce, "kai gays badai wannan beautyn  ce sakarannan zai auraba.
   D'aya ya ce, "mudai tsaya mugani.
   Suna nan zaune yasmeen ta fito itada hajiya jummai, suka zauna, sai asannan yasmeen talura da kwallo suke kallo,  tashiga baza idanu dan son ganin mugun nan ko yananan.
   Cikin sa'a kuwa aka hasko fuskarsa, yana tsaye zai buga kallon jikinsa sanye da jan JC sunyimasa k'yau, a bayan rigar anrubuta Modeebbo, kasa ansak 10, ya take kwallo da  k'afarsa, da'alamadai penerrity zai buga, dan naga kowa tsaye yana kallonsa, yasaki wani murmushi maikama dana mugunta, sanna ya harba kwallon, cikin sa'a tashige cikin ragar, gurin ya kaure da ihu, yayinda sauran 'yan kwallon suka d'agashi sama suna ihu, sumadai samarin saida suka furta gooooooo.
    D'aya acikin samarin ya ce, "kai gay d'innan lucky nefa wlhy, kaga yacimana kwallon nan.
   Hajiya ta ce, "umm kullum kudai bakuda aiki sai kallon kwallo da wak'a, ni bari na shige ciki, ga yasmeen d'innan.
    Yasmeen ga abokan mijinki nan, tare suke karatu a america su sun kammalane shiyyasa, sunzo ku gaisane.
    Yasmeen ta ce, "to momy.
 Hajiya jimmai ta shige, sai asannan yasmeen tad'an kallesu, saitaga ai ita suke kallo suma tai k'asa da kai tana fad'in sannunku  da zuwa.
    Suka amsa da yauwa 'yammatanmu ykk?, ya Najeria??.
   Cikin jin kunya ta ce, "lfy lao kuma ykk, ya turai??.
   Suka amsa da lfy lao, d'aya ya ce, "sunan izziddin, wannan kuma hisham, wannan kuma hashim, mu abokan angonkine kodayake baki tanbayemu ya yakeba??.
    Yasmeen tayi murmushi mai ciwo ta ce, "karku damu ai nasan yana lfy, d'ayan data kula yafi kowa surutu iziddin kenan, ya ce, "duk da haka yakamata a tanmbayemu.
   Cikin kosawa ta ce, "to ya yake??.
   Sukace yana lfy ya ce, "agaidaki dak'au.
  Ta ce, "ina amsawa ngd.
  Nan dai sukayita zuba mata surutu, harda wanda bata tambayesuba, tanaso tatafi dan tagaji, amma bataso suga kamar ta wulak'antasu.
   Saida suka gaji dan kansu, konace saida suka gama kallon kwallon sannan sukai musu sallama suka tafi.
    Bayan tafiyarsu yasmeen ta ce, "mom nima bari nawuce magriba tayi.
   Hajiya ta ce, "aii nazata anan zaki kwana.
  Yasmeen tad'an sosa gefen wuyanta tana fad'in A'a mom, zanje gida nayi karatu dan gobe inada test a school.
   Okey to ALLAH ya taimaka d'iyata.
  Amin yasmeen tafad'a.
 Babudai wata matsala ko??, hajiya ta tambaya?, yasmeen ta d'aga kai alamr babu, to shikenan ina balaraben yazo ya kwashe miki kayannan dasuka kawo miki.
  Lah mom to kema d'iba mana.
  A'a d'iyata ke suka kawo mawa, dan haka jeki da abinki.
    Har wajen mota hajiya jummai tarakata, dan har zuciyarta tana k'aunar yasmeen, tamafi d'annata sonta.

Ana sallar magriba yasmeen tashiga gida, balarabe ya tayata d'aukar kayan suka shiga, sallah tafara k'ok'arinyi dan kar lokacinta ya shige.

Abangaren samarin nan kuwa tunda suka fita suke santin k'yawu irin na yasmeen, ixiddin ya ce, "hisham gafa hanya mai sauk'i ta d'aukar fansa, dan maida murtani ga abokin dambe ba laifi bane.
    Hashim ya ce, "gsk yarka iziddin, hisham yakamata ka rama abinda faisal yayi maka, dan wannan itace dama ta k'arshe dazaka iya samu, karka bari ta k'ub'uce maka.
   Kuma tabbas idan muka aikata, munyi jihadi, dan na lura yarinyar kamilace, bata dace da d'an iska irin faisal ba.
    Hisham ya dafa kafad'un abokan nasa, ya ce, "karku damu abokaina, kudai kusaka idanu kusha kallo, amma tabbas gsky kuka fad'a yasmeen kamilallaiyar mace ce, inhar ta airi faisal d'an giya manemin mata tofa tabbas ta cutu.
   Dan haka ku biyoni domin kallon wasan, kud'auka nine zanyi wining, faisal zai samu game over, yafad'a yana wata dariyar mugunta.
     Na ce, "tofa ana wata ga wata, to bamusan waye keda nasaraba saimunyi bulayiiiiiiiii........................






©2016

Bilyn Abdul
    Mrs Abdus'salam
        LUV U OLL MY FAN's
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *