check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page45

AUREN  K'ADDARA
               ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim

45 «*****» yana zuwa office ya fara duba marasa lafiya, kamar yanda yasaba.
     "Bayan yatashi yanufi gidansu
Ya tura k'ofar palon, yashiga da sallamarsa bakowa palon, sai TV daketa 6a6atu, yanufi d'akin mom, nanma batana sai kawai ya haye saman dad, danyana tunanin tanacan.
     "Ilaikuwa suna tare da dad, dad ya washe baki oyoyo babana kaine agidan yau.
 Yazauna yana fad'in dad nine wlh, ya tsugunna ya gaida su.
      "Mom tace babammu daga ina haka??
Mom daga asibiti nake nace bara na gaidaku.
To sannu ya aikin??                        
"Alhamdulillah mom"

Ya rage fara'a
Dad yace dadyna ya akayi ne??
Sunsan tun yana yaro idan yanason abu saboda miskilanci bazaiyi magana ba saidai fuskarsa ta nuna, dan haka sukan gano damuwarsa da wuri ta wannan hanyar.

Yaja ajiyar zuciya dad yarannan ne suka dawo jiya"
 Dad yace su husna?
     "Ya gyad'a kai batare da yayi maganaba"
To ai.shikenan babana saika had'asu ka rik'e  da adalci kaji, kar kuma nasake naji wata fitina ta taso, kazama namiji a gidanka, miye kazama namiji, karka yarda wata ta cutar dawata acikinsu, su duka 'yan uwankane, bana son tasanadin aurennan zumincinmu yay rawa ko kad'an.
   Dady yace amma dad kasan fitinar yarannan, muna zaune abummu lafiya, yanxu sun dawo zasu 6atama mutane zama.
   Kayi hak'uri nida kaina zan tsawatar musu kasami lokaci koda daddarene ka d'akkosu kuzo kajiko.
      "To dad zanyi k'ok'ari"
Mom.ina 'yan biyu??
   "Suna makaranta dady, yanzu zaka gansu nan tunda sunce darasi d'aya garesu yau.
To ALLAH yadawo dasu lafiya.
           "Amin"

"Ya mik'e to bari nawuce gida"
  To babana kagaishe da iyalinnaka.
     "To zasuji, insu 'yan biyu sun dawo ina gaidasu, tunda sunk'i zuwa, Munneerah tanata so suzo.
       "Mom tace makaranta ke hanasu sakewa wallahi. Tayi hak'uri zasuzo"
      "To sai suzo.

Bayan tafiyarsa dad ya kalli mom, bilkisu kinga babana saiwani kyawu yakeyi, gawani tashen k'iba dayakeyi.
 Mom tai dariya, dad'in mace tagari kenan alhaji, da yana ta wani shi bayaso,
   Dad yay dariya aikinga yanzu kinjishi shiru ko.
  ALLAH ya k'ara basu zaman lafiya dai.
To amin........

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *