check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page42

AUREN  K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim

42 «*****» ya lumshe idanusa masu yalwar gashi, itako Munneerah sai kallonsa takeyi, maganar umma ta d'azu takuma fad'omata' 

"to wallahi anan kikai mana irin wannan halin acikin kwana kad'an zaki kama hanyar gin ubanki"

Ta gitgiza kai kamar tana gabanta, wlh bazan iya rabuwa dashiba zuciyata takamu da son yaya Abdul'aziz, wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, tai sauri sherewa.
 ta daidaita muryar ta, yaya please dan ALLAH kayi hak'uri kaje kaga hakkinsune tunda suna gidan !!

Banza yay mata, bata gajiba tak'ara maimai tawa, cikin raunin murya.
    "Zumbur ya mik'e yay matuk'ar k'ara d'are fuska, ya nunata 🏻 kinsan ALLAH kika k'ara yimini magana saina kashe fuskarki da mari,ya koma yakwanta abinsa ya lumshe idanu.
Ta dad'e zaune tana kallonsa, daga k'arshe itama ta kwanta can k'arshen gado kamar yanda takeyi.

#""#""#""#""#""#""#
Su ikileema kam tunda  dady yay musu abunnan, sai sukai zuciya, suka nufi b'angaren husna.

" husna tace kenifa bazan juri wulak'anciba, umma xan kira na fad'a mata,
    "Ikilima ta warce wayar, ALLAH husna baki da hankali, ke har yanzu baki shiga karatun tanatsuba, kinsan dai halin wannan jarababbar tsohuwar sarai, wallahi saidai ta sake b'ata komai ingaya miki, kinsandai taurin kai irin na mijinmu da miskilancin tsiya, idan kuma sokikeyi igiyar aurenki ta tsinke to, nidai wallahi inan, samun miji irin dady sai an tona, haka kawai bazanyi saki na dafeba, duk abinda zaiyi zan jure, to ashema idan muka tafi mun nuna ma waccan shegiyar faratun ta ci galaba akanmu, ta mik'a mata wayar, karb'a kikira ta nidai karkice dani, tafad'a tana ficewa ad'akin.

Husna tabita da kallo, kumafa hakane 'yar uwa nagode dakika tunatar dani, dan nasan wallahi nafiki son dady.........


billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *