check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 36

AUREN  K'ADDARA
             ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

36. «*****» duk ya rud'e gashi likita amma ya kasa yimata komai, k'arshe dai ya rarumo waya ya kira wani abokinsa Dr Anuwar, bayan sun gaisa yace my friend ! Please in ban takuraka ba dan ALLAH kazo gidana yanzu??
    "Cikin sauri Dr Anuwar yace inazuwa"
  Cikin minti 15 ya iso gidan kai tsaye ya shigo dan yasan gidan, har sannan Munneerah  kuka takeyi tana fad'in yaya ya taimaketa.
 Dr Anwar ya shigo, ko gai suwa basuyiba ya fara tanbayarsa  mike damunta ??
   "Dady yace mararta ke ciwo""
Allura Dr Anuwar yay mata, cikin minti 3 sai komai ya lafa, barci ya d'auketa ajikinsa, yay ajiyar zuciya my friend nagode fa"
   "Dr Anuwar yay dariya karka damu my friend, dama haka tana faruwa akanmu likitoci sai kaga wani naka bai da lafiya amma saboda tsabar rikita mukasa bashi kulawa,
  Sai mun nemi taimakon wani.
 Wallahi kuwa hakane kagama inada allurar amma tsabar rikicewa tasa na rud'e"
 Dr Anuwar ya mik'e yana dariya aidama hakane,bara na wuce saimun had'u gobe a asibiti, to my friend na gode, ya fad'a yana kwantar da Munneerah akan carpet, Dr Anuwar yace kaga yi zamanka wallahi na gode ALLAH ya k'ara lafiya, sukai hannu ya tafi.

Dady yadawo yana kallon Munneerah da take barci, karki damu matata in sha ALLAH sai kin rabu da ciwonnan tunda kina tare da gwarzon namiji, ya d'auketa gabad'a ya kai ta d'aki ya kwantar, sannan ya dawo yana nazari akan ciwon nata abincikensa abu ukune ke kawoma mace ciwon mara yayin al'adah, amma zaidai sake bincike akai.......


Washe gari abban ikilima ya isa gidan umma suka had'u da abban husna bayan sun gaida tsohuwarsu suka gaya mata buk'atarsu ta maida yaransu d'akin mijinsu, abban husna ya d'ora da fad'in umma kinsan taurin kai irin na yaronnan Abdul'aziz, ga shegen miskilanci kamar d'an sarauta, to kawai tinda yaran sun buk'aci komawa d'akinsu  a maidasu, duk abinda za'ayi saimuyi suna cikin gidan, kina ganin Mansur tundaga ranar dayazo yabada hakuri sukoma muka k'i baisake yin maganar amaida yarannanba, amma umma yakikagani.

Taja nummfashi to shikenan kuma kun kawo shawara sai su shirya gobe na maidasu d'akinsu in ALLAH ya kaimu
    "To shikenan umma ALLAH ya kaimu kowa ya mik'e yanufi gidansa dankai albishir.......


billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *