check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA page 2

AUREN KADDARA
                   Ko  BIYAYYA
🏼na bilkisa ibrahim

2 «*****» suka bishi da kallo hawayen da mom ke makalewa suka zubo,  dad  ya kalleta haba bilkisu ai dama tunda naga kinyi shuru nasan kuka kikeyi, adda'a yaronnan yake bukata agaremu ba kukaba yasa hannu yana share mata hawayen fuskarta.
Tace hakane alhaji, amma al'amarin yaronnan yana damuna matuka.         
 Hakane amma muci gaba da yimasa addu'a  "ALLAH"ya kawo masa mafita.
To amin alhaji. 

Shikuwa abdul'aziz wato dady bayan fitarsa daga gidan iyayensa  mota yashiga ya nufi gidansa zuciyarsa ba dadi jiyake tamkar kar yakoma gidan  yana isa kofar gidan yay hon mai gadi ya bude masa get yaturo hancin motarsa zuwa ciki ko gaisuwar mai gadin bai amsaba, bayan yayi parking a ma'ajiyar motocin yanufi cikin gidan wanda yake da tazara da harabar ajiye motocin
Tunda ya gabato gidan yake jin hayaniya yay tsaki tare da fadin karnukan  banza,  yaturo kofar falon yashigo, ilai kuwa matan nasane sukecin uban danbe da zagin fallasa tamkar ba 'yan uwan junaba
Kallo daya yay musu ya dauke kansa, dakinsa yanufa da sauri ikileema ta sha gabansa tana fadin malam jimana.. yabita da kallon mamaki, tare dafadi bani hanya nawuce. Tarike kugu da hannu daya tace ba inda zakaje  saika gayama waccan jakar cewa ita ba komai bace agurinka tafada tana nuna husna da dayan hannunta,  husna tazo ta damki wuyan rigar ikileema tace kece jaka banza karamar 'yar iska aike yakamata ya fadama wannan kalmar baniba shashasha kawai, aifa kan kace me danbe yasake har kumewa har suna kokarin fada masa  
 tsawa yadaka musu waiku wadanne irin shaidanu ne ko so kuke ku maida mini gida gidan gala ne , dan danan suka nutsu ya watsa musu harara wallahi kunji na rantse duk wadda na sake jin muryar ta acikin ku kunsan "ALLAH" saita kama hanyar gidansu da saka mako mai kyau dan nagaji da iskan cinku, inkuma kun cika cikakkun 'yan club ku cigaba. Ni nan dakuke gani nafiku iya iskanci. Yashige dakinsa tare da banko kofa da karfin gaske,  sukansu sun razana
Kowa tai tsaki tanufi dakinta, dan suna masifar son dady da tsoronsa.
    "Shikuwa gadonsa yafada yana fadin na shiga uku ni  abdul'aziz wannan wace irin rayuwace ta dabbobi ya "ALLAH" kakawo mini dauki a lamurana....



billy
{Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *