check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 28

AUREN  K'ADDARA
               ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

28 «*****» dad yadawo gida  ya sanarwa mom yanda sukayi dasu umma, 
Mom tace alhaji aida bakace musu hakaba.
To bilkisu ya kike so nace musu lokaci yayi dazan daina barin su yaya suna danne hak'in iyalina, dan bazai yuwwuba ace ni bani da 'yanci iyalinama basuda shi,
  "Mom tace to shikenan ALLAH ya zab'a abinda yafi alkairi"
    "Dad yace amin"
"Mom tace to masu kai amaryafa sun shirya dannaga abokan angon harsun iso, dad yace nagansu awaje harma mun gaisa, ai kawai abasu amarya sutafi, tunda bakunce can zasu kwana da k'awayentaba??
    "Mom tace eh"
"To sai ku had'asu da manya uku suje su kwana can"
To shikenan alhaji mom tafad'a tana nufar hanya.

Ankai amarya d'akin mijinta kowa yaga gidan saiya rud'e da kyansa. To shima dai ango anan ya kwana ab'angarensa, washe gari akayi walima 'yan yola suka wuce gida, suka bar amarya na kwasar kuka, danma su kairat da kausar suna gidan tare da ita har dare, saida suka gyara mata ko ina sannan, mom ta aiko musu direba da abinci mai kyau da dad'i, yatafi da 'yan biyu gida, suka bar Munneerah na ta kuka.

Dady yana gidan har wajan k'arfe tara yana sak'a da warwara akan amaryar tasa, ak'arahe ya mik'e yay wanka yashirya cikin fararen kayan barci gajeren wando da riga mara nauyi, ya bud'e jikinsa da turare mai k'amahi, sannan ya kwashi wayoyinsa da jakkar aikinsa ya nufi d'akin amaryar tasa.

Itako Munneerah tunda su 'yan biyu auka tafi tayi zaman awa d'aya tana kuka, dataga ba mai lallashin ta, tamik'e tai shirin barci takulle d'akin  ta kwanta, wai dan kar dady yashigo.

Ya iso ya tab'a kofar arufe yay d'an tsaki wai wannan yarinyar shi take rufema k'ofa dan ta rainasa, da har yayi niyyar komawa b'angaren sa ya kwanta abinsa, sai yatuna nasihar iyayansa, dan haka yazube kayan dake hannunsa saman kujeran dake kusa da k'ofar bedroom d'inta yafita ya koma b 'angaren sa ya d'akko wani key d'in yadawo.......

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *