check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 35

AUREN  K'ADDARA
               ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

35 «*****» Munneerah tana zaune apalo tana kallo bayan tagama sallar isha'i, lokaci lokaci takan d'an cije leb'enta da alama akwai wani guri dayake mata ciwo, ta zame ta kwanta saman doguwar kujerar datake zaune.

Dady ya turo k'ofar ya shigo da sallama, ta amsa cikin dauriya, da cije baki,
  " Yad'an kalleta lafiya kuwa??
Ta daure tace bako mai, yanemi guri ya zauna kujerar dake gefenta, 
 Ta tashi zaune tana fad'in yaya abincifa??
      "Yad'an tsura mata idanu dan son gano matsalarta, amma saita kauda kai tana laluben wayarta,
Ta kuma maimaita tan bayar sa cin abinci?
"Ya girgiza kai saidai zuwa anjima, bani dai lipton na sha"
      "Ta mik'e tana fad'in to"
Bayan kamar minti biyar ta dawo hannunta d'auke da tire k'arami, ta d'oro butar shayi da kofi sai k'aramin cokali, ta ajiye saman tebirin dake gefen kujerar daya ke zaune, ta zuba tasaka shuga ta motsa, sannan ta bashi, ya karb'a yana binta da kallo harta koma saman kujerar ta kwanta, 
      "Gaskiya yana buk'atar abokiyar jalittarsa, sai dai yana ganin Munneerah tayi k'ank'anta, babu abinda zata iyayimasa, ab'angaren auratayya, kai idanma ya b'ullo mata da wannan maganar saita rainasa, girma mawar data ke masa ta daina, to inma banda abinsa mai zai samu wajan wannan 'yar shilar yarin yar, wadda ahaihuwar kaji ya haifeta, a gabansufa aka haifeta susuka rainet.....
  Wayarsa ta katse masa tunani, ya d'auka yana dariya, ango kasha k'amshi, kaima kazama sojan sama ko ka kashe arna dubu??
Daga can b'an garen jafar yay dariya nida kai a tantance sojan sama, d'an rainin hankali, kai mai mata uku ma ba ace dakai sojan samaba har zakace da wani.
  "Dady yay dariya kaini nida gwauro babu maraba ai"
    "Kai haba inji jafar, kodaya ke ance mini matanka sunyi yaji, to aikai gaba ta kaika malam saika kwashi amarci abinka"
   "Kai daina fad'a dan ALLAH ina abin yake bare romonsa ai da sauran lokaci,
 Dariya sosai jafar yakeyi haba d'an uwa kardai nanda wata tara ace muzo suna
 Kai d'an iska sai anjima kaji, ya yanke wayar yana dariya.

Da sauri ya mik'e ya nufi Munneerah dake kuka rik'e da ciki, yay saurin tarbo ta tafad'o jikinsa, cikin rikicewa yace Munneerah mike damunki??
 cikin kuka ta nuna masa k'asan cikin ta,
    "Mararki ke ciwo tad'aga masa kai tana murku susu ajikinsa, ya kalli agogo 8:55 pm, ta k'ank'a mesa cikin zafin ciwo yaya zan mutu wayyo yayan ka taimakeni,
     Cikin sark'ewar murya yace bazaki mutuba Munneerah......


billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *