check your best novels here

Wednesday 1 March 2017

NAWAFF!!! 27 to 30

[26/02 13:31] ‪+234 814 643 8985‬: ☆☆☆☆☆☆☆
 NAWAFF 
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM



Page27 & 28

......Washe gari akayi walima, dakuma wa'azi wanda manyan malamai suka gabatar.
   Masha ALLAH wanda akayi dansu sun 'karu sosai, daga 'karshe aka rufe taro da addu'a.
   Kowaya kama gabansa, musamman ma abokan Nawaf dasukazo daga 'kasashe daban2, karfe 2:30pm na rana jirginsu ya ďaga, cikin 'yan katsinama wasu sun tafi mazansu da matansu, sai 'yan kaďan aka bari.
   'Yan saudia ne dai sai gobe wasu zasu tafi.

8:30pm
   Da daddare aka shirya yasmeen tsaf, dan za'a maida ita 6angaren Nawaf, wata 'kanwar papa tashigo tana faďin amarya tashi akaiki ďakin ki ko??.
   Yasmeen ta marairaice fuska kamar zatayi kuka, ta ce, "inna dan ALLAH abarni anan, yafi daďi ga abokan hira.
   Murmushi tayi, ta ce, " 'yanan idan anbarki anan ďakinki kumafa, da angoki, mukuma dakike gani nanda jibi bazakiga kowaba fa?, dan haka tashi muje kinji 'yar albarka.
   Badan yasmeen tasoba ta tashi suka rakata, wooow!! Lallai an gyara 6angaren Nawaf sosai an sake masa fenti, sannan komai na 6angaren an sake, tundaga kujeru labulaye tv kayan gado, komai ansake, dama papa cayayi karsu abba suyi komai, amma duk dahaka saida umma tasayi kayan kichin masu yawa, aka kawo, gakuma wanda momcy tasaya, kichin ďin kam aii ya 'kayatu da 'kyau.
   Tana kuka suka tafi suka barta bayan an kaita bedroom ďin Nawaf, wanda shi kaďaine a6angaren nasu.
   Falo ne babba sai bedroom, kichin da sito, dakuma wani 'karamin ďaki agefe wanda Nawaf yacika da kayan motsa jiki, sai kuma wani ďan fili awaje wanda aka 'kawata da kujeru masu 'kyau domin hutawa, komai yayi awajen kuma komai naciki 6angare lemon green ne.
    Yasmeen tana zaune a tsakkiyar gado inda su inna suka barta, kuka taketa yi, na ce, "dama aike gwanace wajen iya kuka.
   Har 'karfe goma Nawaf bai shigoba ta mi'ke ta cire kayanta ta canja da marasa nauyi, gadon ta haye batareda wani tunaniba ta kwanta abinta, dan danan barci yay awon gaba da ita.
   Nawaf kam yana ďakin daya koma harma ya kwanta, momcy tazo kawoma papa lifton sai taga wuta a kunne, ta ce, "oh ni modebbo akunne yabar wutar ďakinnan, tura 'kofar tayi tashiga da nufin kashe wutar, turus tayi dan ganin Nawaf bisa gado yayi ďai2 yana barci.
   Kai ta girgiza ta 'karasa gaban gado tafara kiran modebbo! Modebbo!!.
   Nawaf ya buďe idanu ahankali yana kallon momcy.
  Ta ce, "mikakeyi anan???.
     Ya ce, "momcy kamar ya??.
   Hararar sa tayi, ta ce, "shine kabaro matarka ita kaďai kazo nan ka kwanta, maza katashi kafin raina ya 6aci kawuce ďakin matarka.
   Baki ya buďe zaiyi magana........da sauri momcy ta ďaga masa hannu kaga bana son jin komai, katashi kawai ka tafi.
   Bayanda zaiyi dole ya mi'ke wayoyinsa kawai ya ďauka, dan tunda rana momcy tasa Anwar yamaida masa kayansa 6angarensa, yafice yana turo baki gaba.
   Momcy ta bishi da kallo tana girgiza kai.
    Nawaf yashigo ya rufe ko'ina mai makon yatafi ďaki saiya kwanta saman kujera doguwa.
   Can dare Nawaf yakasa barci dan bai saba kwanciya ahakaba, sai tsaki yakeyi yana juyi, ga kujerar ledace.
   Ya sakko 'kasa saman kafet ya kwanta aii saiyaji tamkar ana tsira masa allurai, yatashi zaune ya rabga uban tagumi kamar wanda uwarsa ta mutu, ga barci yana cin idanunsa.
  Tashi yay yanufi ďakin, ahankali ya tura 'kofar, amamakinsa saiya jita abuďe, baiyi zaton hakaba.
   Yasmeen tana kwance ďai2 dan barci ya saceta, ga gajiyar biki, yanda ta kwanta saida ya ta6a zuciyar Nawaf.
   Ya kauda kai daga kallonta tareda fitar da huci mai zafi daga bakinsa, asanyaye ya zauna saman kujerar dake ďaki, yakai minti biyar ahaka, sannan ya tashi yanufi bayi, shawa🚿 yasakarma kansa, na ce, "ai dama ka saba.
   Yadaďe ruwa yana ji'kashi, wanda 'karar ruwan tasa yasmeen farkawa atsorace, tana nan zaune yafito jikinsa ďaure da farin tawul, hannunsa ri'ke da 'karami yana tsane sumar kansa.
   Kallo ďaya tai masa ta kauda kai, shima haka, durowar gefen gadon ya buďe yaďakko wasu magunguna ya watsa abaki ya kora ruwa, gefen gadon ya zauna yana faďin ya salam!!.
   Ahankali yasmeen ta sauka daga gadon ta koma saman kujera ta kwanta.
   Yakai minti5 azaune kafin yatashi yahau shirin barci.
   Yabi yasmeen dake kwance saman kujera da kallo, ahankali yafurta kin taimaki kanki yarinya, gadonsa ya haye yay kwanciyarsa harda jan bargo.
   Yasmeen tana kallonsa taďan ta6e baki, itama ta maida kanta ta kwanta, babu daďewa barci yay gaba da ita.
    
WASHE GARI
    da safe yasmeen ta tashi ta gyara ďakin tsaf ta wake bayi sannan tayi wanka, dan Nawaf tundaga sallar asuba bai dawo ďakin ba, yana ďakin motsa jiki.
   Gayu ta ďauka cikin atamfa siket da riga tayi 'kyau sosai, bawata kwalliya tayiba fauda kawai tashafa.
   Ta le'ko falo azatonta Nawaf yana nan, saitaga babu kowa ta fito ta lalle'ka ko ina, komai ya burge ta, tagama zagayawa tazo tashare falon duk da bawani datti yayiba, amma taďan 'kara gyarawa.
    Har waje ta fito ta gyara tsaf, alokacin Nawaf yafito daga ďakin motsa jiki yashiga bedroom, wanka kawai yashiga yadaďe sosai kafin yafito, bayan fitowarsa ya shirya.
    Yasmeen tana zaune afalo tayi shiru tana tunani.
   'Karar takunsa yasata juyyo da sauri, Nawaf tagani cikin shadda orange color, ďinkin zamani yayi masa 'kau sosai, amma fuskarsa babu walwala.
   Ta ďauke kanta daga kallonsa, dan ganin gurinta ya nufo.
  Cikin takun 'kasaita ya 'karaso gareta dan iña ganin yau sarautarce ta motsa, ya ce, "k ki tashi muje mu gaida mutane.
   Banza tayi masa.
  Hannu yasa ya fincikota "k 'karamar mara kunya har kin isa ina miki magana kimin banza.
   Ta ce, "anyi maka ka ďauki mataki mana, ta murguďa masa baki.
   Shi dariyama tabashi, amma saiya gimtse, ya ce, "zanyi maganinki ki bani lokaci.
   Tayi wata dariyar rainin hankali, aii ba saina baka lokaciba yanxu yadace kaďauki mataki.
   Ya zaro wayarsa dake wringing momcy ce, cikin girmamawa ya ce, "momcy ina kwana??.
   Daga can ta ce, "lafiya lao abbuna kun tashi lafiya.
   Ya ce, "lafiya lao my momcy,  ta ce, "ina ďiyar tawa bata mugaisa.
   Ya ce, "momcy ai yanzu zamuzo gaisheku ma.
  A'a modebbo karka wahalarmin da ďiya kabarta ta huta.
   Haba  dai momcy yazamu zauna bamu gaida su hajjaba, bawani wahalar da ita daza ayi.
   To shikenan bata mu gaisa.
 To, juyowa yayi domin yabata wayar, saiyaga bata nan, bin bayanta yayi zuwa bedroom, batareda yayi mata maganaba ya manna mata wayar kawai a kunne.
   Tabuďe baki zatayi magana saitaji maganar momcy tana faďin ďiyata kin tashi lafiya??.
    Cikin girmamawa ta zamo daga kujera ta ce, "momy ina kwana??, lafiya lao ďiyata ya ba'kunta.
   Ta ce, "lafiya lao.
  Masha ALLAH momcy ta faďa, ta ďora dafa ďin babu wata matsala dai ko??.
   Eh babu komai momy.
 To shikenan gasu talatu nan zasuzo suďan gyara miki inda aka 6ata kinji.
   Lah momy ai bama sai sunzoba nariga na gyara.
  Kai ďiyata damme??, daga yau karki 'kara wahalar da kanki akan aiki, akwai masu yi kinji.
   Ta ce, "to momy ngd ALLAH ya'kara girma.
   Momcy ta ce, "amin ALLAH yay muku albarka.
  Ta ce, "amin.
                Nawaf yaji daďin yanda yasmeen ta girmama mahaifiyarsa, amma sai ya kanne dan yasan matar tasa 'yar haya'kice.
    jallabiya ya ďakko ya cilla mata, gashi nan kisaka mu tafi.
   Kai taďago daniyar yimasa rashin kunya, amma saitaga ya tsare gida kamar bai ta6a dariyaba, bata ta6a jin shakkar yimasa rashin kunyaba irin yau, ďauka tayi tana zum6ura baki tanufi bayi ta canja, tayi mata matu'kar 'kyau dan rigar ta haďu, shi kansa saida ya yaba amma bai nuna mataba, ya ce, "muje, yafaďa yana nuna hanya.
   Batayi musuba suka tafi, 6angaren papa suka fara zuwa yayi farincikin ganinsu, yasmeen ta zube tana kwasar gaisuwa wajen surikin nata, shima Nawaf yakai tashi gaisuwar, papa yay musu nasiha mai shiga jiki.
   Daga nan wajen momcy sukaje suka gaisheta, itamadai nasihar tayi musu.
   Sai 6angaren dasu hajja suke, cikin farinciki hajja ta rungume yasmeen itako sai kunya takeji.
   Nawaf kuwa tsakkiyar kakanninsa yaje ya zauna yana gaishesu cikin harshen larabci, suka shiga tambayarsa ya amarya.
   Ya ce, "gata nan lafiya lau.
  Taďan yi 'ko'kari wajen gaishesu da larabci, saboda islamiyya datake zuwa, daga nan sai Nawaf yakoma yimusu tafinta, idan sunyi magana da larabci ya fassara mata, idan tayi da hausa ya fassara musu, Nawaf sai dariya yake mata wai bata iyalarabci ba.
   Momcy ta ce, "rabu dashi yasmeen kema zaki iya indai larabcine.
   Yasmeen ta ce, "momy sainama fishi iyawa insha ALLAHU.
   Nawaf ya harareta wazakifi iyawar??, 
   Ta ce, "kaimana.
 Haka dai sukaita hirarasu, saida hajja ta ce, "su tashi suje 6angarensu.
    Tun ahanya aka fara faďa, na ce, "kai ALLAH ya shirya waďannan gays ďin.
   Talatu da ladidi suka shigo da kayan break suka jere a dinning, sanan suka tafi.
   Nawaf yatashi yanufi dinning batareda yabi takan yasmeen ba, abincinsa yaci ya 'koshi kunsandai 'yan kwallo sun iya ci.
    Yasmeen tana zaune a falo ko kallo bai ishetaba, saida yagama yafita sanan taje taci nata, ta gyara wajen.
   Falo tadawo ta ďauki wayarta tahau chatting dan tarage kaďaici, dama kallo bai cika damun yasmeen ba.

``````````````````````````````````
    Sai bayan sallar la'asar Nawaf yashigo gidan lokacin tasake wanka cikin sket da riga na shadda tayi 'kyau, tana bedroom bayan ta idar da sallar la'asar,   zaune ta ke kawai tunani fal zuciyarta.
   'Karar buďe 'kofa yasata juyowa da sauri tana kallonsa, kallo ďaya yay mata ya ďauke kai, itama kanta ta maida gefe, tana ganin yafara cire kaya tatashi ta fice, yarakata da harara.
   Tana nan zaune afalo saiga 'yammatan danginsa na saudia, suka zauna ana hira harda ummu habeba, yau tasaki jiki anayin hirar da'ita.
   Suna nan zaune Nawaf yafito sanye da 'kananun kaya sai zabga 'kamshi yakeki, kan hannun kujerar da yasmeen take zaune ya zauna, suka shiga gaidashi, daga nan aka ďora da hira, ummu habeba sai kallonsa takeyi, ita dai tana 'kaunar Nawaf, amma gashi ya zagaye yayi aurensa ya barta, kwata2 ta kula ma shi nunawa yake baisan tana sonshiba.
     Sai gab da magriba suka tafi 6angaren momcy.
   Shikuma Nawaf yatafi sallahr magriba masallaci.

____________________________
    Yau jirgin muta nen sudia ya ďaga, hajja kawai aka bari zatayi ďan kwana biyu sanan ta tafi, da'kyar tayarda ta zauna.
   Yau gidan shiru babu kowa saisu kaďai.
   Nawaf yadawo daga motsa jiki ya zube afalo saman doguwar kujera yana faďin wash ALLAH na nagaji yawa yau.
   Yasmeen tafito hannunta ďauke da kofin kunun gyaďa dan tana sonsa sosai, tundaga lokacin da Nawaf ya ce, "bayasan 'yan aiki awajensu  idan bazatayiba tabarshi.
   Momcy ta ce, "bata yardaba yasmeen ďin nawa take daza a sakar mata aiki, dayaga momcy ta dage saiya ce, "to saidai ita ta rin'ka musu girki, dan bazaici girkin 'yan aikiba.
    Momcy ta ce, "wanan mai sau'kine, yasmeen kiringa yimuku girki tunda ku biyune kafin yatafi, dan tuni mijinki baya cin abincin 'yan aiki.
   Yasmeen ta ce, "to momy hakanma yayi, nima nafiso nayi da kaina.
     Yabita da kallo danganin shigar dake jikinta, wandone iya guywa da 'karamar riga mara nauyi, rigar ta fallasa asirin jikinta sosai, kanta yasha gyara sai wal'kiya yakeyi.
    Tasan babu wanda zai shigo musu shiyyasa tayi wannan shigar, dan Tun agida yasmeen tanaso shigar 'kananun kaya damma wataran umma tana hanata ne.
   Ta wuce kamar bata ganshiba.
   Ya ce, "k zonan!, banza taiyi masa tunda ba "k aka raďa mataba agidansu, bedroom tashige abinta.
    Nawaf ya haďiye wani mugun yawu jikake 'kuttttt, gaba ďaya ta rikita masa lissafi ya rintse ido ya furzar da huci mai zafi, ya ce, "wai sai yaushe za'a kai 'karshene??, wata zuciyar sa ta ce, "randa ka shirya kwatar ha'k'kinka dan kasan indai dan itace ayita zama ahaka.
    Yay wani murmushin mugunta, afili ya ce, "aii ko ankusa zuwa 'karshen, ya mi'ke yanufi bedroom domin yin wanka.
   Koda ya shiga ďakin baibi takantaba yashige wanka abinsa, ita kuma tadawo falo tana faďin ďan rainin wayo ai wlhy yanzu na daina zama kana raina mini hankali, idan zaka shekara kiran "k! Bazan amsaba tunda bashi iyayena suka raďa mini ba.
    Tana nan zaune yafito shima cikin 'kananun kaya, kusada ita ya zauna, bata ko kalli inda yakeba taci gaba da shan kununta.
   Gashin kanta yaja aiko ta kwala 'kara, yasa ďayan hannunsa ya rufe mata baki, tasaki kofin hannunta saboda zafi, ya ce, "k wacce irin mara kunyace ne?, kinaji ina kiranki ďazu kikai mini banza, ni tsarankine??.
   Cikin kuka ta ce, "kai kasani nidai kasakeni mugu kawai.
   Birkiceta yayi ya haye saman cikinta, tafara mutsu2n kwacewa.
   Amma takasa saboda yafi 'karfinta, ALLAH Yabata sa'a ta gallah masa cizo.
   Da sauri yasaketa danjin wani azababben zafi, mari ya kaimata ta kauce da gudu ta shige bedroom ta rufe, ya take mata baya........... 









© 2016


Bilyn Abdul
    Mrs Abdus'salam
        luv u oll my fan's
[26/02 13:31] ‪+234 814 643 8985‬: ☆☆☆☆☆☆☆☆
 NAWAFF  
☆☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM




Page29 & 30

.....kafin ya 'karasa ta kulle 'kofar yashiga bugawa da 'karfi amma yasmeen tai masa banza, saida yaga batada niyyar buďewa sannan ya ha'kura, falo yadawo ya zauna zuciyarsa cike da haushi, daga baya yatashi ya fice.
   Yasmeen taďan le'ko ta wata 'yar 'kofa ganin baya nan yasa ta buďe 'kofar ahankali tafito.
   Hijjab tasaka tanufi 6angaren momcy, tanata addu'a a zuciyarta ALLAH yasa bacan Nawaf yajeba.
   Da sallama tashiga falon, hajja da Anwar ne kawai zaune, tasaki ajiyar zuciya, gurinsu ta 'karasa hajja tanata mata murmushi, ta tsugunna har 'kasa ta gaisheta, Anwar ya ce, "aunty mu dama yanzu zanje 6angarenki hira.
   Kai Anwar banyardaba kullum haka kake faďa amma komai kama dakai ban ganiba.
  Anwar yay dariya, A'a aunty kinafa ganin mai kama dani baga yaya nan ba, dariya sosai sukeyi harda hajja, momcy tashigo itama tana waya, bayan ta kammala ta ce, "A'a ďiyata kece kika zomana, cikin jin kunya yasmeen ta gaisheda momcy.
   Momcy ta amsa cikin fara'a, tana mai 'kara jin 'kaunar yasmeen har cikin zuciyarta, itako saiwani sissinne kai take dan kunya, hajja sai tsokanarta takeyi, Abdallah yashigo shima aka fara hirar dashi.
   Anwar yabata wayarsa tana kallon hotunan biki wanda yaďauka, tayi mamakin irin 'kyawun datayi, gashi  wasu wuraren tana murmushi, wanda batasan lokacin datayiba, wani hoto yaďauki hankalinta awajen dinner, tatuna faďa sukeyi da Nawaf awanan lokacin shine ya harareta ta rama, amma idan kagani saika ďauka kallon soyayya sukema juna, Anwar ya ce, "kai aunty nakula pic ďinnan yayi miki 'kyau sosai, nima duk nafi sonsa wlhy.
   Abdallah yataso domin yagani shima, bayan kujerar yakoma yana kallo ta bayansu.
   Nawaf yashigo da sallama saida gaban yasmeen yafaďi, amamakinta saitaji ya ce, "dama kinanan inata nemanki, wani iri yasmeen taji aranta gashi yawani tsareta da mayun idanunsa masu hasken tsiya, ta daure ta ce, "yi ha'kuri bansan zaka dawoba yanzu, jinai 'kaiďaici zai dameni shiyyasa nataho nan.
  Okey to nima bari nazauna ayi hirar dani, ya zauna kusada hajja, hajja ta ce, "o, sai yanzu ka tuna dani.
  Nawaf yay dariya to dama na'isa na manta dake!.
  Momcy ta ce, "aii daga yanzu indai yafita kiringa tahowa nan saboda kaďaici babu daďi.
  Yasmeen ta ce, "to momy.
   Nawaf yafaki idonsu ya harareta, ita kuma ta murguďa masa baki, ya nuna kansa wai shi!, ta kaďa kai alamar eh., le6enasa na 'kasa ya cije, itakuma ta maida kanta ga kallon pictures.
   Haushi kamar ya kashe Nawaf, amma babu damar ďaukar mataki, dole yasaki jiki suna hira da hajja da momcy, dansu hankalinsu yana kan waya.
   Saida aka kira sallar azhur suka tashi, masallaci suka tafi shidasu Abdallah, yasmeen kuma tanufi 6angarensu.
   Wanka tafara shiga sanan tayi sallah, agurguje ta shirya tafito da nufin tasake guduwa 6angarensu momcy, sai sukayi kici6is da Nawaf a'kofa, kallon kallo aka tsaya yi, kowa ya ďaure fuska.
    Tsaki Nawaf yayi tareda jan hannunta zuwa cikin falon, cikin tsiwa ta ce, "malam kasakeni, banza yay mata yacigaba da janta, saman kujera mai zaman mutum ďaya ya hankaďata, damma kujerar da laushi shiyyasa bataji zafi ba, yaďora 'kafarsa ďaya saman kujerar ya tsareta da idanu.
   Ta kauda kai daga kallonsa, dan ita idanunsa tsoro suke bata, haskensu yayi yawa, sunkai minti2 ahaka, sanan ya ce, "wai ke na tambayeki ni sa'ankine??, banza tamasa kamar batajiba, yacigaba da faďin ďazu harda wani faďin aibansan zaka dawoba ne shiyyasa nafito, dan kaďaici yaymin yawa, yafaďa yana kwaikwayon muryarta.
          abin yabama yasmeen dariya amma saita gimtse, ta ce,  "oho dai naga kaine kafara, kaga kenan a wajenka na koya, agabansu hajja kayita wani kakkafi waikai mai gida, sai andawo nan kafara mazurai, ta 'kare maganar da murguďa baki .
     Nawaf ya ce, "niko?"
    Cikin tsiwa ta ce, "eh kaiďin saime".                              
yasaka yatsansa ďaya ya ďago ha6arta, ta rintse ida nunta, yaja tsaki yana faďin ke nifa nafiki miskilanci!.
   Sai asanan ta buďe idanu, dukda zuciyarta tana dukan uku2 saboda tsoro wannan bai hanata sake murguďa masa bakiba.
   Ya ce, "ni dai ko??.
    ta ce, eh, ni kadameni da tambaya? ?".
  Kafin ta rufe baki yasa yatsunsa biyu  ya kama la66anta ya matse da 'karfin tsiya, yasmeen tashiga tsungunin hannunsa tana hawaye, amma mugun ya'ki yasaki, gashi sai murzasu yatsun nasa yakeyi dan mugunta akan bakinta, saida yayi mai isarsa sanan yasaki, zuwa sanan la66an yasmeen sun kunbura, sunzama 'katun2n, yasaki yana dariyar mugunta.
   Yasmeen sai hawaye suke zirara a fuskarta, tana shafa la66anta, har yanzu 'kafarsa tana saman kujerar, ya ce, "yammata za'a sake mini rashin kunyarne??, hararar sa tayi ga hawaye fal fuska.
   Nawaf ya tuntsure da dariya, yasmeen tai sagade tana kallonsa, batayi zaton yana dariya hakaba, saida yayi mai isarsa sanan ya sauke 'kafarsa yanufi bedroom yana cigaba da dariyar.
   Yasmeen ta kifa kanta saman hannun kujera tana kuka, ahaka barci yay gaba da ita.
   Saida yay wanka ya shirya tsaf yafito cikin manyan kaya, wani farin yadine shara2 yay masa 'kyau sosai harda ďora ba'kar hula wanda gays ďin yanzu suke yayi, ya kai kallonsa ga yasmeen dake barci a takure saman kujera, murmushi yasaki yana faďin yarinya tayi barcin wuya.
    Har yakai 'kofa kuma yadawo, ďaukarta yayi tsak yakaita bedroom, a saman gado ya kwantar da'ita, yana kallon la66anta dasuka kummbura yana murmushi, ahankali yajuya ya fice.
     Saida yashiga 6angaren momcy yafito sanan yashiga mota yafice, yana bani mamaki yanda yakeson mota mai ba'kin gilas, kobayaso idan yafita agansane oho??.
   A'kofar gidan su mas'ud yatsaya, ya ďauki wayarsa yakirashi, malam kafito muwuce ko??, kai haba dan baka da kirki saikace bazaka zo ka gaida Ameena ba??.
   Kai mutumina ALLAH inajin kunyar zuwa haka.
   Tsaki mas'ud yayi aikai kajika, dan ALLAH kashigo ku gaisa saimu wuce, yakashe wayar.
   Dole Nawaf yafito yashiga gidan, da sallama yashiga falon, suka amasa.
   Mas'ud yashiga tsokanarsa kaga angon yasmeen, wanan irin 'kyau haka malam, lallai amarcin ya kar6eka.
   Nawaf ya zauna yana hararar sa, mas'ud kaifa ďan iskane wlhy, nazata idan kayi aure zaka canja, amma kananan yanda kake, saima 'karawa dakayi.
   Kafin mas'ud yay magana Ameena tashigo hannunta ďauke da tire.
   Nawaf ya ce, "amarsu ta ango!, sai dai baki more angoba, dariya tayi tana zuba masa lemo, bayan tagama ta gaisheshi ya amasa, ta ce, "ina 'kawata??.
   Tana gida nabarota lfy, ta ce, "na gaidaki!.
    Ameena ta ce, "ina amasawa.
   Kaďan yasha lemon ya mi'ke kai malam tashi mije yamma tanayi.
   Mas'ud ya mi'ke yana faďin gsky ne, saida ya sumbaci goshin ameena sanan ya fito, Nawaf yana kallonsu shiyyasa yayo gaba, dan yasan mas'ud ba kunyarsa zaijiba.
    Amota mas'ud ya ce, "mutumina aure da daďi wlhy, yanasaka nishaďi da farinciki, musaman idan kasamu matar data iya tattalinka.
   Nawaf ya ta6e baki, kai Alhaji kai yayima daďi, nidai bandani!, dan ni takurani akayi, dana 6ararraje nikaďai aďakina amma yanzufa??, ankawo mini wanan mara kunyar duk ta takurani.
   Dariya mas'ud yayi, haba malam faďi gsky dai, kowa yaganka yasan ka 'kara 'kyau, zaka wani dozani, 'kilama mun samu baby.
   Nawaf ya ce, "kai mutumina ammafa ka iya tsiya ka ce, "har resold yafito??.
   Kai ďan rainin hankali ka gama wani kauce2n ka kafaďi gsky, aii dakai nake!!.
   Tofa, Nawaf yafaďa yana 'kara dafe sitiyari, to indai nine wlhy kama fidda rai, bawai tonon asiriba, ko makwancima ni bamu ta6a haďawaba wlhy.
   Idanu mas'ud yazaro, kai amma dai kai garane wlhy.
    Oho kama faďamin abinda yafi gara mana, kai kanka kasan ba son yarinyar nan nakeba, kai nama ta 'kaice maka zance, kullum saimunyi faďa.
    Dariya sosai mas'ud yayi, ya ce, "lallaikam zaku barine, koda yake shima faďan duk acikin soyayyane.
   Tsaki Nawaf yayi daganan yay masa banza.

________________________________     a6angaren yasmeen kuwa sai la'asar ta farka, tayi mamaki data ganta akan gado, itadai tasan ba'a nan ta kwantaba, zata iya cewama tundaga randa aka kawota batasake hawa gadon nanba da niyyar kwanciya, saidai kawai ta gyara masa.
   Bayan tagama mamkinta ta sakko, wajen madubi taje tana kallon fuskarta, la66anta sunyi fushi sosai, ta ce, "ALLAH yasaka mini mugu kawai, tunda nake arayuwata banta6a ganin mugun mutum irin Nawaf ba, ruwa zafi taje ta ďebo a kichin, awani ďan bokiti, tazo tazauna gaban mudubi, tasaka wani hankacif ďinsa ta gasa bakinta,, dukda zafin datakeji haka tadaure tana hawaye ta gasa, saida taji ruwan ya huce sanan ta ha'kura, tashiga wanka.
   Tafito tayi sallar la'asar, ta shirya tsaf cikin doguwar jalla biya ba'ka, mai duwatsu.
   Falo tafito taci abincin, da momcy ta aiko musu, dama har yanzu bata fara abincin ranaba, saidai na safe, da daddarema ba girki sukeyiba, dan kowane daren duniya kayan fruit ne abincin Nawaf, sukaďai yakesha sai shayi na 'ka'ida, wanda saiyasha sau goma arana batareda ya isheshiba.
    Ta kammala cin abincinta tadawo falo, yasmeen bata cika damuwa da kalloba, idan itace sai ayi sati ba'a kalli tv ba, dan haka tai kwanciyarta saman kujera tana game a waya.
   Yaseer ya kirata awaya, taďaga cikin fara'a tana faďin ďan 'kanina nayi missing ďinka wlhy.
    Ya ce, "nima haka sisto na, ykk?, ya gida?.
   Ta ce, "komai lafiya Alhmdllh, ka'ki kazo ko??.
   Karki damu zanzo, school ce ke hanani wani motsi wlhy, amma zuwa weekend zaki ganni.
   To ALLAH ya kaimu lfy, yasu ummana da abba??, suma duk suna lafiya wlhy, aii yanzu su yaya Nawaf suka tafi, tun ďazu suke anan.
    Yasmeen taishiru azuciyarta ta ce, "mugu, wato bayan yagama mini mugunta ashe gidanmu yaje, taďan murmusa koba komai taji ďaďi...........yaseer ya ce, "hello sisto kina jina kuwa??.
    Saida tayi ajiyar zuciya sanan ta ce, "ina jinka, ka ce, "tunďazu yake anan??, eh, shida yaya mas'ud sukazo, bakiga alherin daya kawo manaba wlhy, ki 'kara yimana godiya, gsky aunty kin more miji..
   Hummm to uban 'yan surutu anji, yaseer yay dariya, kai sistona daga faďar gsky, ina aunty amina??, tana gidanta itama nima bamu haďuba.
    Kai aunty gida biyune fa tsakaninku.
   To yaseer basai anbar mutum zuwaba?, ya ce, "hakane kuma.
   Sun daďe suna hira, ta ce, "ka gaishemin da umma, itama zan kirata mu gaisa insha ALLAH, dan jiya mun gaisa da abba.
   To shikenan zataji insha ALLAHU, saina zo.
   Okey to saikazo.
  Shiru tayi tana tunanin mijin nata, tana mamkinsa, agaban mutane yakan nuna yana sonta, amma idan su kaďaine sai muguntar tsiya.
   Anwar yashigo da gudu yana faďin aunty kina ina??, yasmeen ta tsshi zaune, ganinan Anwar, ya mi'ka mata kofi, yayinda Abdallah ma yashigo da gudu, yatsaya yana hakki yana hararar Anwar.
   Yasmeen tayi dariya tana tambayarsu miya faru, Anwar ya tuntsure da dariya, yaya ne ya haďa askirim na ďebo miki, shine yabiyoni zai kwace.
   Yasmeen ta ce, "kai Abdallah ALLAH yashiryaka wlhy, nixaka yima rowa.
   Ya 'karaso yana faďin ALLAH aunty dama nayi niyyar kawo miki, banfa gama haďawaba ya ďebo, kuma dafarko bake yay niyyar kawomawa ba, kansa ya ďebar mawa.
    Anwar yay dariya kaidai yaya faďi gsky.
   Dagudu Abdallah yabiyoshi suka fara zagaye falon, yasmeen tana tun tsura musu dariya.
   Nawaf yashigo da sallama, bashiri suka nutsu, kowa yana hakki, yasmeen ce kawai taketa dariyarta.
   Nawaf yatsaya yana kallonsu kawai, yayin da yakejin kamar kar yasmeen ta daina dariyar dan tayi 'kyau da dariyar.
    Su Anwar suka ra6a ta bayansa suka fice, sum2 kafin akai musu masga.
    Bayan fitarsu Nawaf yay tsaki yashige bedroom, babu daďewa yafito sanye da jallabiya, ko kallon yasmeen baiyiba ya fice.
   Tabishi da kallo tana ta6e baki.
     Koda yadawo sallah wajen papa yawuce dan amsa kiransa, ya rissina ya gaisheshi.
   Papa ya amsa yana faďin zauna sosai mana.
    Nawaf ya zauna.
  Papa ya ce, "dama inaso na sanar makane ka shirya kaida matarka kuje safana, ku gaishe da jama'a damusu godiyar hidima.
   Da sauri Nawaf ya ce, "papa safana fa ka ce??.
   Eh, safana na ce, yakamata ka kaita tasan tushenka, tasan kaiba ďankowa bane, talakane kamarta, baka fita da komaiba, wannan 'katon gidan datake gani da taimakon ALLAH aka ginashi, shima saida aka đauki shekaru ba'a gamaba, dan har aka haifeka ban gama ginin nan ba, kuma haka mahaifiyarka ta zauna dani, duk da ita tafito daga wata 'kasa, kuma gidan arzi'ki.
   Nawaf ya ce, "to shikenan papa zamuje, amma aranar zamu dawo??, kai papa ya girgiza, ya ce, "A'a, kwana uku zakuyi ku zaga dangi ko'ina, kushiga ko'ina da ina.
    Nawaf ya ce, to shikenan zamuje nextweek, dan inaso 'karshen watanan na koma Spain!!.
   To ALLAH yakaimu lafiya, saikayi 'ko'karin shrya muku tafiyar, ALLAH yay muku albarka, yabaku zuria ta gari.
   A la66ansa ya ce, "amin.
   Sunďan daďe suna hira, saida papa ya ce, "yatashi ya je wajen matarsa, anbarta ita kaďai.
   Akunyace Nawaf yami'ke yafice.
   Papa yabishi da kallo yana murmushi.
  Saida yaje wajen hajja yay mata saidai safe sanan yatafi 6angarensu.

Afalo ya iske yasmeen tana kallon hausa film, ya ďauki remote ya canja, wai shi bazai kalli wannan shashancinba, yasmeen ta turo baki gaba, a zuciyarta ta ce, "bagara hausa film ba wataran suna faďakarwa, akan 'yan kwallo da rashin aikinyi yay musu yawa...........Nawaf ya katse mata tunani da faďin "k ina shayina??.
    Banza tayi masa, tayi kamar batajishiba, ya mi'ke, da sauri ta tashi tsaye itama, tanufi kichin da gudu.
   Dariya ta su6cewa Nawaf, ya tuntsure da dariya, cikin dariya ya ce, "kai matsoracima baiji daďin kansaba wlhy.
   Babu daďewa ta dire masa shayi agaban sa, tana wani zuzzun6ura baki gaba, ta ajiye zata wuce, ya ce, "k dawo nan, ta tsaya cak ita bata tafiba, kuma bata dawoba.
   Cikin faďa ya ce, "wai badake nakeba??, saida ta murgiďa baki sanan ta juyyo, tazo ta tsaya akansa, ya watsa mata harara, wlhy yarinya kishiga hankalinki dani, inba hakaba kin rin'ka shan wahala kenan.
   Ta yatsine fuska sanan ta ce, "wlhy saidai musha wahala, kabar ganin ďazu ka kumbura mini le6e na 'kyaleka, zan ramane.
    Ya tashi zaune daga kwanciyar dayayi, yasa hannu ya fisgota ta faďo jikinsa, runtse idanu tayi kam, tana rawar jiki, ya matseta kam ajikinsa, bata ankaraba taji bakinsa cikin nata, wata mahaukaciyar sumba yake mata, ga le6enta bai gama warkewaba, dan har yanzu yana mata zafi, amma dan muginta irinta Nawaf sai yahaďe bakinta da nasa sai murza yakeyi.
    Itako hawaye kaiwai take zubowa, tana tsunguninsa da hannunta ďaya, amma ko'a jikinsa, dan ya'ki sakinta.
   Saida yaga taji jiki sannan yasaketa, tana hawaye, tama kasa tashi daga jikinsa.
   Ya lumshe idanunsa dasukai jajir, yamaida kansa jikin kujera yana fitarda numfashi.
   Ahankali ta tashi daga jikinsa ta shige bedroom, saman gado tafaďa tana kuka, saida tayi mai isarta sanan ta shiga bayi taiyi wanka, tafito tayi shafa'i da wutiri, tana nan zaune yashigo ďakin tai 'kasa da kai kamar bata ganshiba.
   Shima bai kalletaba yashiga cire kayan jikinsa, tashi tayi ta haye kujera takwanta.
   Yashiga wanka shima, yafito yagama komai na al'adar rayuwarsa, shafa'i da wutiri, karatun alkir'ani, sanan yaje kichin dakansa yasake dafa wani shayin dan wancan ya huce.
   Falo yay zamansa saida dare yayi sosai yashigo, sanan yasmeen ta daďe dayin barci akan kujera.
   Kallo ďaya yay mata ya ďauke kai, ya hau gado yakwanta.
  Na ce, "mu kwana lafiya, nima wajen nawa handsome ďin nataho.
________________________________  WASHE GARI.
    lokacin dana iso 'yan aiki harsun gama gyarama yasmeen 6angarenta, tagama haďa break a falo na tarar da Nawaf yana break na ce, "tofa yau ba'a ra'ayin dinning ďin??.
  Yasmeen ta fito daga ďaki, hannunta ďauke da littatafai, ko kallon inda Nawaf ya ke batayiba, ta zauna saman kujera tana karatun ta, yaďago yana kallonta, wani abu yana ta6a zuciyarsa, amma yanaji har aransa bazaiyi fatan yafitowarsa filiba.
    Yasmeen taji ajikinta ana kallonta, ta ďago tana kallon inda Nawaf yake, ta murguďa masa baki.
   Ya 'kara ďaure fuska, "k dawa kike??, ta ce, "da wanda ya tsargu mana.
   Ya ce, "toni na ysargu.
   Ta ce, "matsalarkace.
   Ya ce, "kema yanzu zata zama taki!".
    Aii tana ganin ya mi'ke ta tashi ta fallah da gudu zuwa waje, dama shiyyasa ta zauna kusada 'kofa.
    Nawaf yay kwafa zaki dawo ki sameni aii, matsoraciyar banza kawai.....................





Assalamu alikum
Masoya littafin NAWAFF kwana biyu kunji Shiru hakan tafarune sakamakon rashin lafiya danayi, amma yanzu komai normal, ngd da 'kyaunarku gareni, luv u oll




©2016


bilyn Abdul
   Mrs Abdus'salam
       luv u oll my fan's
Share:

1 comment:

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *