check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA page 8

AUREN 'KADDARA
                ko BIYAYYA


Na bilkisa ibrahim

8 «*****» husna ta watsama ikileema harara, banza mayyar maza saiki kwana, ta tashi tafice dan dama husna akwai zuciya.
Alwala yayo ya fito,ya kalli ikileema data cika tai fam saboda maganar da husna ta fadama ta tayi mata zafi, yace ke tashi kiyo alwala, yanda taga ya hade rai  saita mike tayo alwalar ta fito, taje dakinta ta dakko zani da hijjabi,
Sunyi nafila raka'a biyu yay musu addu'oi, sannan ya hau yimata tanba yoyi akan addini?? amma ba wadda ta amsa, tundasu ba islamiyya suke zuwaba,ransa yay zafi yaja tsaki kaini dai wallahi ban moreba, to tayaya  za'ayi wannan tabama yaranka tarbiyya?? Azuciyarsa yake wannan maganar,ya tashi ya canja kayansa zuwa na barci yasaka turaren barci, gado ya haye abinsa,itama tamatso kusa da shi dan ganin yanda yakoma karshen gado, amamakinsa saiyaji tana shafashi, ransa ya kara baci, akasar hausa ansan mace da kunya musaman adarenta na farko,amma yazaiyi tunda matarsace, yakuma tuna nasihar iyayensa ta dazu da rana.dole ya daure ya karbi tayinta yabata hakkinta, bayan nutsuwa tazo musu,sai wani farin ciki ya lullube ikileema tuda take hudda da maza bata taba samun gwarzon namiji wanda ya iya soyayya irin dady ba,gaskiya yau tasami natauwa sosai,dukda ta lura dady farin shigane, tana ganin ma yaune rana ta farko da fara sanin mace arayuwarsa, dan ta kula bama wani iya harkar yayiba sosai,amma dai yayi kokari.
Shikam wani irin bakinciki ne yacika zuciyarsa,dukda bai taba kusantar maceba,shi likitane na mata kuma yanada ilimin addini musamman na "fikihu", yayi karatu mai zurfi  akansu,yasan dukkanin suffofin mace budurwa,yasan na wadda tasan namiji,ya fitar da huci mai zafi,"ALLAH"kai shaidane ban taba zinaba,amma ka jarabceni da auren mazinaciya,YA " ALLAH" ina neman afuwarka da gafararka tasanadin hakurin zaman dazanyi da ita,"ALLAH" kafini sanin dalilin yin hakan.ya mike yashiga bayi yay wanka,sanda ya fito har tayi barci, wata muguwar harara ya zabga mata, yaja guntu tsaki, ya dauki filo ya dawo kan kujerar dake dakin ya kwanta,zuciyarsa cike da tsanarta......


billy
{Mrs abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *