check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA page 3

AUREN KADDARA
                  Ko BIYAYYA 
09093044460
Na bilkisa ibrahim

3 «*****»  TUSHEN LABARI alhaji el~mansur adam sa'id sunan mahaifin abdul'aziz (dady)  su uku mahaifinsu ya haifa  alhaji adam sa'id yola, matan alhaji adam biyu halima wadda suke kira umma itace uwar gida tana da yara biyu ashiru, da salisu, 
Sai amarya maryam dasuke kira gwaggo tanada da guda daya mansur, alh adam dan kasuwa ne babba a yola domin in har za a lissafa manyan 'yan kasuwa na yola zai iya zuwa na goma. Gidan alh. adam anayin zama bana jin dadiba domin uwargidansa haj.halima  macace mafada ciya sosai, amaryarsa kam tada matukar hakuri haj.maryam,dan haka yaronta mansur yakasance mai hakuri gashi kuma karami acikinsu 
Yaran haj.halima  sun gado halinta kaf suna bin hudubar ta daki~daki sun raina gwaggo danma suna tsoron babnsu 
     Amma gwaggo da danta suna shan wahalarsu agidan, har amakaranta kullum wahalar da mansur sukeyi bashida ikon shiga cikinsu yayi wasa saisun dokesa koda gwaggo tagani bata magana saidai taja shi daki ta rarrashesa
Wannan yasa yatashi atsan gwame acikinsu  ahaka akaita tafiya harsuka girma su la kammala karatunsu  ashiru, da salisu, suka aure bayan kamar shekara uku shima mansur yay aure ya auri diyar kanwar gwaggo sunanta bilkisu, salisu, da ashiru, suka sami aiki dan sunce basa son kasuwa.
Mansur kam yana kasuwa wajan babansu, ana haka ciwon ajali yakama alh.adamu allah ya dauke abinsa  ba a rufa shekara ba gwaggoma ta rasu,bayan rasuwar gwaggo mansur da matarsa suka kara shiga halin takura awajen 'yan uwansa da mahaifiyar su  sun kwace gadonsa da sunan za a hada ajuya.
           Ana haka billkisu tasami ciki mai wahalar wa ko dayau she tana cikin jinya  idan mansur yatan bayesu kudin dazai kaita asibiti saisuce basudashi, wannan halin yasashi fara neman aiki amma aikin yaki samuwa
Ga bilkisu da ciki ga mansur ba aikiyi, ga matansu  salisu sun takurama ta da aiki duk da wahalar
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *