check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA page 49

AUREN  K'ADDARA
               ko  BIYAYYA

Na billkisa ibrahim 


49 «*****» ya tsura mata fararen idanunsa masu yalwar gashi, sai asannan ya lura ma ba riga a jikinta, jiyay yana neman zaucewa, dama haka Munneerah take, ya rintse ido ya bud'e, lallai d'an hakkin da ka raina shike tsonema ido, dan shikam yau Munneerah ta tsone masa nasa idon.
    "Yamik'e  kamar wanda kwai ya fashema aciki, gaba d'aya jikinsa yayi masa nauyi, k'irar Munneerah ta birkita masa kwanya, yaje wajen dirowarta ya d'akko mata riga, yazo yasaka mata.
      "Palo ya fito yaci abinci, ya kwashe kayan zuwa kichin, 6angarensa ya koma ya kashe komai ya kulle wajan yadawo, wajen Munneerah cikin shigar kayan barci, yazauna yana binciken nasa nafama, duk da yau bayama fahimtar karatun nasa, dan sai Munneerah kemasa gizo a ido.
  Ya dai rufe duk book's d'in, ya tashi ya hau gadon, kusa da ita yakwanta, yay musu addu'a, jikinsa ya jawota ya rungume, yaja nunfashi da k'arfi  tare da fad'in ya salam.
    "Yauce rana ta farko daya fara rungume Munneerah, yakan dai zauna kusa da ita, ya kuma matseta kam ajikinsa har saida tad'an motsa, ya sassauta mata, yace kaji wani lafiyayyan jiki, lallai mata suna suka tara, hakadai yay ta tunane tunanen sa, harsai gabannin asuba barci ya kwasheshi, hakanne yaja masa makara da asuba, sai agida yay sallah.

 Ya dawo kan gadon ya kwanta, wajan k'arfe 7:24 am, Munneerah ta farka, jintatai ajikin mutum, tai saurin bud'e idanu, ta saukesu akan dady dake barci fuskarsa tamkar yana murmushi, ta dad'e tana kallonsa, har saida ya motsa ta runtse idonta da sauri, saida taji bai bud'e idoba sannan ta bud'e nata, tai k'ok'arin zame jikinta, ya bud'e ido yana kallonta, tasa hannu ta rufe fuska, wai ita kunya, dady yay Murmushi.
     "Ai idan kin bar jikina dole na tashi, ya fad'a yana zame hannunta daga kan fuskarta, ta rintse ido kam, yay dariya yau kuma kunyar yaya akeji??
   " tad'aga kai tana murmushi"
"Ya mik'e zaune yana kallon agohon d'akin, to ai nima lokacin tashina yayi, bari naje na shirya zuwa office, ya kamo hannunta ya summba ta, da sauri tacusa kanta k'ark'ashin pilo.
Ya fita yana dariya.
   "Yay turus danganin ikileema da husna tsaye kowacce rik'e da k'ugu.........


billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *