check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA page 11

AUREN K'ADDARA
                  ko BIYAYYA

Na billkisa ibrahim 

11 «*****» su mom sun yanke shawarar zuwa yola amma nikaina bansan abinda zasuje yiba,
Kamar kullum yakanzo yagaida iyayensa, yashigo falon mom ce kawai sai kausar tana karatu,guri ya nema yazauna,ya gaida mom d'insa kausar ta gaidashi,yace ina kairat?
"kausar tace tana d'aki tana barci yaya"
  "Yar gata barci yanzu da yamma'
 "Mom tace jibi zamuje yola in sha ALLAH"
Zamu dawo ranar  lahadi.
To mom ALLAH ya kaimu,ke nanma sai ansaka ranar auren su safwan,tunda on Saturday ne?
Ai dama shiyasa zamukai Sunday,
  To ALLAH ya kaiku lafiya kudawo lafiya, nima naso zuwa to munada wani taro na likitoci ranar Saturday,
To ALLAH ya taimaka aigara ka tsaya wajan aikin, tunda bikin ma kusa za asaka,
Dan ina ganinma harda  Munneera za ahad'a,
"Munneera kuma mom wannan 'yar yarinyar za aima aure ince bana ta gama secondary d'inta??
 Mom tai dariya to ai ta isa auren ko, koda yake ku yaran yanzu kunfison auren manya sa'anninku, amma ai auren yarinya yafi komai dad'i, duk training d'in dakai mata dashi zata tashi,
 "To amma mom aizaka sha shirme, dan auren 'yar  seventeen year ai aikine, ya tab'e baki koda yake mijin yaga zai iyane,
Mom tace kace bazaka iya auren 'yar shekara 17 ba kenan,
        "Tab haba mom aini ko 'yar shekara 25 ma bazan auraba, inji da wad'ancan biyun dasuke neman sakamini hypotension, yanzu haka barosu nayi suna 'yar zage zage daciwa iyayensu mutinci,to yanzu mom na auro ta uku ai sai wataran an kashe wata,
 Mom tace to ALLAH ya shiryasu ya kuma kiyaye faruwar haka,
           "Ameen mom"
"Ni bari nawuce gida ina da aikin dare yau,
  To ALLAH ya tsare babana,
Ya kalli kausar da barci ya kwashe, oh kema kinyi barcin,
Mom tace aiyanzu zasu tashi tunda magriba ta kusa........

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *