check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA page 9

AUREN K'ADDARA
               Ko BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

9 «*****»da safe haka ya tashi duk ransa ab'ace wata k'arin tsanarsu yakeji aransa,dan yasan itama husnar duk tafiyar d'ayace,tunda bata da k'awar data wuce ikileema,bayan yayi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya yayi kyau, ya tara matan nasa yagaya musu doko kinsa,cikin isa  yay musu sallama"
" suka amsa "
"Yay musu kallon second biyar, yak'ara tsare gida ina san sanar daku hanyar dazamu iya zama lafiya daku in kunso,
Na farko bana son k'azanta,
Na biyu   bana son yawo,
Na uku    bana son hayaniya,
Na hud'u bana son taron k'awaye acikin gidana, bana cin abincin 'yan aiki, ban yarda 'yan aiki sushigar mini d'akiba da nufin gyara, wannan kad'an daga cikin doko kina ida kun kiyaye kun tsira in kuma kun k'iji ba kwak'i ganiba, ya mik'e ya kwashi wayoyin sa da makullin mota yay waje"
Husna tamik'e kai dai kasani miskilin banza, mutum kullum ba dariya sai kace wanda uwarsa ta mutu.
Ikileema kam kwanciya tayi bisa kujera tana fad'in saika nemi mai bin dokarka dan wallahi ba 'yan aiki aka kawo makaba masifaffe.
    "
Itama dai husnar yanda yazata haka ya tarar fanko ce, haha suka cigaba da zama,ikileema da husna kullum fad'a kamar  karnuka,arana saisuyi dambe sau uku,ga cin mutun cin iyayensu kamar ba 'yan uwan junaba,
Shikam baya kulasu dan bayason hayaniya,
             »«°°°°°°°°°°»«°°°°°°°°°°°°°»«
   Jin anturo kofa ya bud'e idanunsa farare tas masu yalwar gashi ya kalli k'ofar,
Husnace yaja doguwar ajiyar zuciya,
"Tace my one ga abinci canfa yana jiranka.
Yace kun gama damben ne? Ta yatsine fuska ai ita taja, kasan ta da rainin hankali.
Yata shi zaune kudai kuka sani,niba wannan na tan bayekiba,
Tad'an tab'e baki, nidai ga abinci can nace,
  "Na koshi aikinsan bana cin girkin 'yan aiki, ta waro ido waje kar dai gayannan ya k'i cin abincinnan,in baiciba ai ta banu yanda mamy ta gargad'eta akan tatabbatar yaci dan ba k'aramin kudi ta kasheba wajan amso maganin da aka dafa abincin dashi ba,
Tuna nin mikikeyi inata magana,
Tai saurin dai daita natsuwarta, aiba 'yan aiki suka girkaba nina girka dakaina,
Cikin fasifa yace to nace na k'oshi ko dolene saina ci,dalla fi cemin ad'aki ina buk'atar hutu,ya koma ya kwanta.....

billy
{Mrs abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *