check your best novels here

Tuesday 21 February 2017

NAWAFF!!! 1 to 6

[28/11/2016 15:15] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆☆
          NAWAFF   
         ☆☆☆☆☆☆☆☆


NA BILKISA IBRAHIM




DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINK'AI, ya ALLAH kabani ikon fad'ar abinda zai amfani al'ummarka, ka tsare harshena daga fad'ar abinda zai cutar da al'ummarka.
  

Assalamu alaikum, 
gaisuwa da fatan alkairi, inamai farin cikin sake had'uwa daku asabon littafina mai suna NAWAFF, ALLAH yasa ya amfanar damu baki d'aya. Amin




Page 1&2

      Yau antashi da tsananin zafi, saka makon ranar data kwalle, mutane kowa yana neman mafaka, a karkashin rumfa ko bishiya.
    Ga k'arar ababen hawa data cika birnin na kano, dukda katafaren gosulo d'in daya cinkushe titin, dayawa mutanen dake cikin moto cin sun gala baita, da tsananin zafin ranar.
     Amma wannan bai hana 'yan tallah daf dalaba suna yayata tallar ababen sana'ar su, musamman masu tallar ruwa, saboda yanayin zafin mutane suna buk'atar ruwa mai sanyi.
       Nakai dubana bisa wata farar mota mai k'yawun gsk, wadda daka mata kallo d'aya kasan mai ita yagama wada tuwa.
    Wata k'yak'yk'yawar yarinya nagani kwance a bayan motar, farace saidai farinta bamai haskeba sosai, tanada kala irinna 'yan itopia, tanada dogon hanci da manyan idanuwa, kwance take abayan motar tana nazarin littafi.
    Agaba kuma direbane, tad'ago kai tareda fad'in balarabe kaga abinda nake jiye mana ko?, shiyyasa nace kar mu biyo ta nan, gashi har ina neman makara, kuma inada lectures yanzu wlhy.
     Balarabe ya ce, "kiyi hak'uri hajiya, wlhy banyi zaton zamu sami wannan cinkoson ba.
     Ta d'anyi k'aramin tsaki tana fad'i ni wlhy saima karasa abinda yake haddasa irin wannan cinkoson a garin kano?, batareda ta saurari sharhin da balarabe yake mataba ta bud'e motar ta fice.
      Tafito dai2 sanda wata jar mota 'yar k'arama ta tsaya saitin ta, ahankali  aka zage gilashin motar zuwa k'asa, wani had'ad'd'en saurayi ya bayyana, saikuma wani danake tunanin abokinsane.
    K'yak'yk'yawan saurayinnan ne matuk'in motar, kallo d'aya zaka masa ka gano yana cikin farin ciki, dan sai kad'a kai yake da alama wak'a yakeji, kuma wak'ar tana masa dad'i.
     Ya d'akko kwalin hollanddia yana sha ahankali yana cigaba da kad'a kai, harda had'e yatsun hannunsa biyu yana bugawa.
      Karku d'auka wannan k'yak'yk'yawar yarinyar shitake kallo, A'a ko kad'an hankalinta baya kansa.
    Jitai wani abu yadaki k'irjinta, da sauri ta kalli jikinta.
   Hummm kunsan miye kuwa??.
Ba wani abu bane illa kwalin hollanddia da gay d'innan yake sha, takuma bin jikinta da kallo, dan ganin yanda yogot d'in yay mata kaca2 da bak'ar jallabiyar dake jikinta, ta maida kallonta ga motar dan ganin wane wawane yay mata wannan aikin??.
     Saitaga mutum yana kallonta yana tuntsirar dariya harda dukan sitiyari, d'ayan saurayin dake gefensa ya d'ago yana kallonsa, ya ce, "kai malam lafiyarka kuwa?, kanata dariya kai kad'ai kamar wani shafar aljanu.
    Cikin dariya ya nuna masa yasmeen dake tsaye tamkar gunki tana kallon ikon ALLAH, tana mamakin wannan wane irin shashashan mutum ne, yayi mata abu amma yana nunata yana dariya.
     Mas'ud ya ce, "amma kaidai d'an iskane NAWAFF, yazaka b'atama yarinya jiki, kakuma rink'a yimata dariya??.
     Kasan kuwa wacece wannan kalli nomber motar data fito fa.
    NAWAFF ya gallama Mas'ud harara yana fad'in aii bani nace tazo ta tsaya anan ba tana yima muta ne iyayi ko?, dazakace nawani kalli nomber mota, to saimi idan na kalla.

Duk abunda suke fad'i Yasmeen tana jinsu, dan haka sai zuciyarta tak'ara tunzura, cikin fasifa ta k'arasa gurin motarsu.
    Ta ce, "kai wawa wanda baisan darajar mutaneba, shin kobaka ga b'arnar dakayi bane??.
   Cikin fushi NAWAFF ya kalleta ya ce, "waye wawan??.
    Itama cikin tsiwa ta ce, "masa kai mana!!!, ko wawan yayi maka kad'an saina had'a da mahaukaci, dan naga kanada k'aramar kwakwalwa.
    Afusace yabud'e mota yafito, ya wanka mata mari, jikake wani tasss.
    Dayawan hankalin mutane yadawo gurin musamman 'yan tallah.
    Ta dafe kunci tana kallonsa, sai kuma ta d'aga hannu itama zata wanka masa mari.
    Da sauri ya rik'e hannun ya murd'e, ta ce, "kai karamin d'an iska ka sakar mini hannu, hannu yad'aga zai k'ara marinta mas'ud yay saurin shiga tsakkiyarsu, ya ce, "haba NAWAFF yazaka mata laifi sannan ka daketa??.
    Cikin masifa ya ce, "dalla malam nibakaga raahin kunyar datake minbane?, ko kai kurmane?.
   Mutane sai kallonsu sukeyi.
 Mas'ud ya ce, "haba NAWAFF kasan dai fuskarka sananniyace dammi zaka aikata haka?, yanzu sakaji 'yan jarida suna yayataka aduniya kadai sani sarai.
    NAWAFF yaja tsaki, karsu fasa gayawa duniya abinda nayi kajiko, kodan kar afad'ama duniya saina zauna yarinya k'arama tayimin rashin kunya.
    Ya juyo gareta ke kuma ki rubuta ki ajiye saina nuna miki ni nafi mahaukaci hauka.
    Yasmeen taja tsaki ta ce, "wlhy nikuma saina nuna maka nike maganin dukkan wani mahaukaci komai haukansa.
    Aifa yasake harzuk'owa zai mareta, mas'ud dake tsakkiyarsu ya kare, wai ku miye hakane? dan ALLAH, waishin bakwa ganin kallon da'ake mukune??, gashi kun tarema mutane hanya.
    Sai asannan NAWAFF ya lura gabansu babu kowa, duk tarin gosulo d'innan ya b'ace, saidai mutanen dake bayansu, sunata danna musu hon.
   Balarabe da tund'azu yake bama Yasmeen hak'uri, amma tak'i saurarensa, ya ce, "kiyi hak'uri Hajiya kizo mutafi kinga kin makara.
   Harara ta watsa masa sannan taja tsaki, mas'ud ya ce, "plz kiyi hak'uri dan ALLAH kinga a titi muke.
    Juyawa tayi ga motarsu dan ganin kawai kallon da'ake musu, amma tad'auki alk'awarin duk ranar data sake had'uwa da gay d'innan saita nuna masa shi k'aramin d'an iskane wlhy.......................

Tusk'ashi masu karatu, komi zai faru?, shin waye NAWAFF??? Miyasa 'yan jarida zasu iya yayatashi???? Wacece Yasmeen?? Kuma 'yar wacece??, kubiyoni danjin amsoshi tambayoyinku....

    Taku har kullum BILKISA IBRAHIM (Bily)
   ( Mrs Abdus'salam)
Ku kasance dani!!!!!!

     Zaizo gareku nanbada dad'ewaba......luv u oll

©2016
Bilyn Abdul
[30/11/2016 14:43] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆
NAWAFF
☆☆☆☆☆☆☆




NA BILKISA IBRAHIM




page 3


      Ta ce, "da direba maidani gida.
    Cikin tsoro ya ce, "to hajiya makarantar fa??.
   Cikin masifa ta ce, "gida nace ka maidani ba dogon bayani na tambayeka ba, kajiko.
    Ya ce, "yi hak'uri hajiya ALLAH ya huci zuciyarki.
     Bata tanka masaba domin zuciyarta sai tafarfasa take, babu abinda take tunowa sai abinda gay d'innan yay mata.
    Tun kafin yayi fakin tayi waje, da gudu tashiga gida.

   Humm kunsan abinda yaba ni mamaki??, gidan da yarinyar tashiga daka gani gidan talakawane, bazaka tab'a tunanin yarinyar da motar 'yan gidan bane,, tokomadai miye agaba zamu sani.

  Tashige falon tana kuka.
   Wata dattiyuwar mace tana zaune a matsakaicin falon, farace tas maik'yau, suna kama da yarinyar, daka ganta kasan ma haifiyarta ce.
    Tafad'a jikinta tana kuka, cikin hanzari dattijuwar ta rungume d'iyar tata tana fad'in yasmeen injidai lafiya?, bakije makarantar bane??.
    Cikin kuka ta ce, "umma bamun tafiba shine gosulo ya rik'emu.
    Umma ta ce, "to mikikema kuka? Ko gosulo d'in?, ta girgiza kai alamar A'a.
    To minene?, umma ta tambaya.
   Ta share hawaye bawani ne ya mareniba, mari kuma? Miki kai masa?, tana kuka tana bama umma labarin abinda yafaru.
    Umma tashiga lallashinta tana bata hakuri, babanta yashigo da sallama, dan tunda suka shingo yagansu, yatsaya tambayar balarabene abinda yafaru.
    Yashafa kan yesmeen ya ce, "karki damu mamana ALLAH yana tareda masu hak'uri, dan haka kiyi hakuri watarana sai labari.
    Ahankali tad'ago manyan idanunta wad'anda sukayi jajur saboda kuka, ta ce, "karka damu abba kabarni dashi dakaina zan rama, wlhy abba saiya raina kansa, dan na daina zama ana rainamu, dan kawai muna talakawa saikowa ya ce, zai rainamu, abba aii babu maraya sai rago.
   A'a mamana kibarsa kawai kinji, abbanta yafad'a yana shafa kanta.
    Shuru tayi batace komai ba, dan tasan bazata iya hak'ura ba.
   Umma ta ce, "mudai idan tamune ki hak'ura, yasmeen bana son tsiwar nan taki, idan kikayi hak'uri sai ALLAH ya saka miki, ki barmu muji da damuwarmu.
    Shuru tayi batace komai ba, sai hawaye da idanunta ke zubarwa, cikin raunin murya ta ce, "kuyi hak'uri iyayena shima ALLAH zaimana maganin sa, ina ji ajikina bazai tab'a nasara akanmuba insha ALLAH.
     Abba ya share hawaye yana fad'in to ALLAH ya amsa addu'ar ki mamana.
   Sukace amin itada umma.

D'akinta ta shige, iyayenta suka bita da kallon tausayi, umma taja ajiyar zuciya mai k'arfi, ta ce, "lallai yasmeen kina ganin taskun rayuwa iri2, ALLAH dai yakawo mana k'arshen abunnan.
    Abba ya ce, "amin.

Yasmeen tana shiga d'aki wayarta tahau wringing jiki a sanyaye ta d'auka, saidai fuskarta ta nuna alamun tsoro, murya na rawa ta ce, "Assalamu alaika.
    Bansan mi akace a d'ayan b'angaren ba, amma naga idanun yasmeen suna zubar da hawaye, saikuma ta ajiye wayar tafad'a saman gado tana kuka, duk da bansan ainahin damuwar yasmeen ba amma tabani tausayi kwarai da gsk, cikin sanyin jiki nabaro gidan nima.

 Ab'an garen su NAWAFF kuwa, sai mas'ud ne ya tuk'a motar, dan NAWAFF ya kasa saboda b'acin rai, tunda ya zauna akujerar gefen direba ya lumshe idanunsa masu haske, bai sake cewa uffan ba.
    Mas'ud yanufi hanyar gida dasu dan yasan ran 'yan maza ya b'aci, kosunje inda sukayi niyyar zuwa NAWAFF bazaya sakeba, saboda yana cikin b'acin rai.
   K'ofar wani matsaikai cin gida mas'ud yay hon, da sauri mai gadi yabud'e get d'in, mas'ud ya danna hancin motar zuwa ciki.
    Ba laifi gidan yanada d'an k'yau kuma daga ciki babbane, NAWAFF ya fito yanufi cikin gidan, kai tsaye gidan ya shiga, amma babu kowa a falon, fitowa yayi yanufi b'an garensa wanda baikai girman inda yafara shigaba.
   Ya fad'a saman doguwar kujera ya lumshe idanu, mas'ud yashigo ya bishi da kallo kawai.
     NAWAFF ya mik'e yashige bedroom d'insa, bayi yafad'a batareda ya cire kayan jikinsaba ya sakarma kansa shawa, yakai tsawon minti goma ahaka, sannan ya cire kayan jikinsa yay wanka yafito.
    Jalla biya kawai ya zura ya dawo falon, mas'ud na kwance a kan kujera mai zaman mutum biyu, ida nunsa nasaman tv yana kallon.
     NAWAFF yafito yazauna batare da yayima mas'ud maganaba.
    Mas'ud yad'ago yana kallonsa, dan shima yasan bazai tanka masa d'inba, yako bushe da dariya yana kallon NAWAFF.
    Nawaff ya d'ago yana hararar sa, yaja tsaki, tareda d'aga goran ruwa ya kwankwad'a, har sannan mas'ud yana kunshe dariya.
    Cikin masifa Nawaff ya ce, "dallah malam wai miye hakane??, zaka wani tasa mutane gaba kana musu dariya.
    Mas'ud ya ce, "kajimin mutum, ina ruwanka da dariyata, ko kaji na ambaci sunan kane??
   Ammafa wlhy d'an uwa kun dace da yarinyar nan gsky.
   Wata uwar harara ya yasakar masa, batareda ya tanka masaba ya mik'e ya fice.
   Mas'ud yacigaba da dariyarsa, kamar wani mahaukaci................


Ina godiya ga d'umbin masoya, dasuka turomin sakwannin taya murnan kammala book d'in NI DA AMINIYATA ngd ALLAH yabar k'auna   




Kuyi hak'ura daga nan zuwa wani lokaci, zaku cigaba da samun page 1 ne kullum arana, kawai, kafin komai ya daidaita ngd.



bily
Mrs Abdus'salam
LUV U OLL
          ©2016
[30/11/2016 17:36] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆
NAWAFF
☆☆☆☆☆☆☆





NA BILKISA IBRAHIM




Page 4


    Yasmeen tafito sanye cikin jan les, d'ikin riga da siket, ta nad'e kanta da d'auri mai k'yau sai zabga uban k'amshi take, ga farin mayafi da farin takalmi, abin sai wanda yagani.
    Mahaifiyarta ta bita da kallo, ta ce, "kai yasmeen d'in abba kinyi k'yau, kamar kece amaryar.
    Hannu tasaka ta rufe fuska ta ce, "kai umma.
    Umma tayi dariya ta ce, "to nabari, yanzu ke dawa zaki tafi, koda yaseer zakuje.
    Yasmeen ta turo baki gaba, ta ce, "ALLAH umma bazanje dashiba, kina ganin jiya abinda yay min aii.
    Yaseer dake zaune yana cin abinci ya ce, "nima ba zuwa zanyiba, dan haka maida wuk'ar, ni nan dakike gani kallon kwallo zani.
    Yasmeen ta harareshi, aii kallon kwallo kawai ka'iya, mara aikinyi.
   Yaseer ya tab'e baki, ke kuma zuwa biki kawai kika iya, ni wlhy nak'agara abba ya aurar dake abar mini filin ma.
    Yasmeen ta kai masa duka, ya kauce yana dariya, cikin shagwab'a ta ce, "umma kin gansa ko?, umma tayi dariya, ta ce, "nikam babu ruwana, tunda kekika zauna yaseer ya rainaki, wanima saiyace shine yayanki aii.
    Yaseer ya ce, "to umma ba'ita ta tsaya shagwab'a ba, shiyyasa akecewa nine yayanta, yafad'a yana mata 
    Yasmeen tabishi zata daka, suka fara zagaye falon, umma te ce, "kinga mamana k'yaleshi, zokiyi tafiyarki, kinga karkije ki fad'i da wannan takalmin mai tsinin tsiya.
   Yasmeen ta tsaya tana turo baki, yayinda yaseer yake tsaye bakin k'ofa yana dariya, ta harareshi, habawa yaro wlhy zan dawo nasameka, saika gayama aya zak'inta.
    Yaseer ya ce, "saidai mu fad'ama ayar tare, yana gama fad'a ya fice.
    Itama dai sallama tayima umma, ta ce, "zataje su tafi da ameena, umma ta ce, "to hakanma yayi, amma kudawo da wuri.
    Yasmeen ta ce, "to umma za'a kiyaye.

Tana fita gidan su Ameena ta shiga, gsky gidansu ameena yafi nasu yasmeen k'yau sosai, a get suka had'u, ameena ta ce, "yauwa garama haka, dama bana son nashiga mu b'ata lokaci.
    Yasmeen batace komaiba taja hannun ameena suka shiga mota balarabe yaja.
    Wani had'ad'en guri aka kaisu, bazan fad'i gurinba dan karsu teema suce zasu itada deexerh, wajen yayi matuk'ar had'uwa, anshirya komai, yanda yakamata, yasmeen ta ciro waya a jakarta takira wata no.
    Ana d'auka ta ce, "Asmy ALLAH ke 'yar is... ce, kince babu African time amma gashi waje babu kowa.
    Daga can akace sorry my dear gamunan, wlhy laifin Safwan ne shida abokansa, wai sun tsaya jiran babban aboki, kuma har yanzu bai isoba, amma gamu nan zuwa.
    Yasmeen tayi d'an tsaki ta ce, "inji dai ba d'an iskan jiya bane daya shanyamu.
    Amaryar ta ce, "wlhy shine.
Yasmeen taja tsaki, tswww, sai kuma akace dole saidashi za'ayi komai, cikin haushi ta kashe wayar batare da tajira amsar Asmy ba.
     Ameena ta ce, wai mitace miki??, yasmeen ta yatsine fuska, wai d'an iskan jiya suka tsaya jira, saikace wani d'an gwal, kina ganin yanda ya shanyamu jiya, daga k'arshe dan rainin hankali saiya aiko mana direba.......
     Yasmeen bata rufe bakiba motocin su Asmy suka fara shigowa.
   Bayan tsayawar su mutane suka fara fitowa, kowa yana neman wajen zama, saida kowa ya zauna sannan yasmeen ta je tafito da Amarya, ango ma yafito, 'yammatan amarya da abokan ango suka take musu baya har inda aka tanadar musu.
     Sai kujeru biyu a gefe wanda babbar k'awar amarya zata zauna, da babban abokin ango.
    Yasmeen ta zauna kusada asmy amarya suna magana kus2, yayinda aka fara gabatar da abinda yatara mutane.
    Zuwa can mai gabatarwa ya fara wasa babban abokin ango da aka dad'e ana jira, gaba d'aya hankalin mutane yakoma kan had'ad'd'iyar motar data tsaya kalar jaa da ratsin fari, gsky motar ta d'auki hankalin mutane, sai dai banda yasmeen,  da waya ta d'auki hankalin ta. 
   Tunda yafito ake ihun fad'in sai modeebbo! Sai modeebbo!!.  Shikam hannu kawai yake d'aga musu yana murmushi, har wajen zamansa aka rakashi wato kusada ango.
      Bayan anyi shiru, akayima babban abokin ango barka da zuwa, ya k'ara d'agawa mutane hannu yana murmushi.
   Ango ya ce, "mutumina ina ka mak'alene haka, tuni kai ake jira, cikin muryarsa mai dad'i ya ce, "ayimin afuwa my friend wlhy matsaya jiran mas'ud ne, baima dawoba hakanan na hak'ura na taho.
    Ongo yay murmushi ya ce, "anyi maka modeebbo, sukai murmushi tareda yin musabaha.
    Yasmeen koda tagama wayar bata damu kanta da son ganin waye babban abokin angonba, dan haushinsa takeji sabida b'ata musu lokacin dayayi jiya.

   Mai gabatarwa yafara kwala kiran sunan yasmeen Abubakar habeeb, tazo ana gayyatarta.
    Yasmeen ta dad'e zaune bata motsaba saida Asmy ta ce, "plz dear kitashi mana, yasmeen ta ce, "ALLAH kunya nakeji dear.
    Asmy ta harareta lallai dear awajen aurena kike jin kunya.
   Aka cigaba da yayata sunan yasmeen dole ta mik'e tsam tanufi inda aka tanada.
    Ya mik'a mata abin magana, tareda fad'in munaso ki gabatar mana da kanki, dakuma tarihin amarya.
   Jiki a sanyaye ta karb'a, duk ta takura saboda kallon da mutane suke mata, ta d'auki hankalin yawancin gays d'in wajen, ahankali tafara magana, cikin murya mai zak'i, aii wasu saida wutar kansu ta d'auke, harda babban abokin ango (modeebbo) yak'agara yaga fuskar mamallakiyar muryar nan.
    ta fad'i sunanta da alak'arta da amarya, bayan tagama aka shiga yimata tafi.
   mai gabatarwa ya ce, "itace zata gayyato babban abokin ango zuwa wannan waje.
     Batare da musuba takarb'a takardar tafara kiran  NAWAFF SA'ED MODEEBBO. 
    Takira yakai sau biyar amma bai ko motsaba daga inda yake, tajuyo dan ganin wai waye wannan d'an rainin wayon abokin angon.
    Karaf idanunsu suka had'u a k'ar kashin inuwa d'aya, zumbur NAWAFF yamik'e tsaye.
    Yasmeen ta ce, "taf tsuntsu daga sama gasashe, azuciyarta take maganar.
   shima dai NAWAFF raya abinda zai faru yakeyi dan yasan dole sukwashi 'yan kallo, amma yasan maganin ta..........................
    Hahahha yauda budiri tsakanin YASMEEN DA NAWAFF.





Bily
Mrs Abdus'salam
LUV U OLL

             ©2016
[04/12/2016 17:04] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆
NAWAFF 
☆☆☆☆☆☆☆





NA BILKISA IBRAHIM




Assalamu alaikum.
    Alhmdllh 'yan uwana kamar yanda nafad'a muku natsaya da rubutu sabida wani dalili.
    To Alhmdllh yanzu komai ya dai daita, in farincikin kasancewa daku





Page 5


.....Nawaff ya tsuke fuska, itama yasmeen ta tsuke tata fuskar.
    Yak'araso gareta cikin wani taku na isa da tak'ama, wajen yayi tsit ana kallonsu, yayinda masu hotuna suketa haskasu.
    Yak'araso daf da ita, tamkar zai shige jikinta, tayi saurin ja baya, ya had'a yatsunsa biyu yana bugawa, yay k'asa da murya yanda ita kad'ai zata iya jinsa, ya ce, "wlhy kika yimini hauka awajennan saina aikata miki abunda 'yan jaridu da mujallu zasu buga a safiyar gobe juma'a.
     Dukda tsoro mai tsanani yashigi yasmeen wannan bai hana ta hararar saba, ta rik'e k'ugi cikin tsiwa ta ce, "kai baka isa kasa 'yan jarida yad'aniba, kuma ALLAH shizaimin tsari da sharrinka.
    Nawaff modeebbo yad'an d'ago yana kallon yanda hankalin mutane yadawo kansu, saiya saki murmushi na basarwa.
    Gaba d'aya gurin yad'auki sowa da fad'in sun dace da juna.
    Nawaff yaja tsaki tareda fad'in shashashu kawai, ta ina na dace da wannan mai kama da aljanar.
    Yasmeen ce kawai taji furicinsa saikuma mai gabatarwa dayake kusada su tsaye.
     Yasmeen tai murmushin takaici ta ce, "ai basu bane shashashun kaine babban shash............kafin tarufe baki ya damk'o hannunta ya murd'a da k'arfi, wani tsananin zafi yaratsata har kwakwalwa, ALLAH yasota fitilar gurun Blue ce tana kuma kunnawa ta kashe, dan haka ba kowa yaga muguntar da Nawaff yake mataba.
     Zafin ya ratsata sosai, afusace ta watsa masa mari, da sauri yasaketa yana murza kumatu, itama takoma kusada amarya da sauri ta zauna tana haki.
   Nawaff yad'ago da sauri danjin andafa shi, mas'ud yagani tsaye.
   Mas'ud ya ce, "plz my bro's ka share kawai, karka bari wani yagane wani abu dake faruwa.
    Nawaff ya kalli mas'ud da idanunsa dasukayi jaa, ya ce, "wlhy Mas'ud saina yima yarinyarnan abinda zatayi dana sani arayuwarta, kamar yanda ka buk'ata zan barta ammafa had'uwarmu tagaba batada k'yau ko kad'an, kuma ka rubuta ka ajiye.
  Yana gama fad'a yakoma mazauninsa dake kusada ango, mas'ud ne ya wakilcesa, wajan fad'ar duk abinda ake buk'ata.

  Asmy ta ce, "yasmeen wai miye had'inki da modeebbo??,    yasmeen ta share hawayen fuskarta, ta ce, "karki damu zan sanar miki, amma ba yanzuba.
    To shikenan asmy tafad'a, tacigaba da lallashin yasmeen, yasmeen ta ce, "Asmy kiyi hak'uri zan tafi gida, dan kaina yana mini ciwo.
    Asmy ta ce, "babu damuwa dear kije gobe ma had'u, ngd da k'ok'arinki.
    Yasmeen ta mik'e tana neman Ameena, bayan ta ganta suka fice, duk abinda take Nawaff yana kallonta, suna fita yarufa musu baya, shima mas'ud binsu yayi.
       Yasmeen tana k'ok'arin neman balarabe saitaji an fisgota ta baya, tajuyo da sauri, gabanta yafad'i rass dan ganin NAWAFF, 
    Ya had'e fuska kamar bashiba, yasmeen ta ce, "lfy konaci bashinkane??.
    Nawaff ya damk'i gashin yasmeen data d'aure abaya, ya murd'e da karfi, tako kwalla k'ara, saidai babu maijinta saboda hayaniyar wajen tayi yawa, gakuma kid'a yana tashi, gashi a tsakankanin motoci suke.
    Cikin sark'ewar murya ya ce, "nikika mara ko??, to wlhy ki rubuta ki ajiye, wannan marin saiya zama FANSAR BUDURCINKI, NA MELODY , saikinyi dana sanin aikata hakan agareni, ya hankad'ata tadaki motar bayanta.
    mas'ud dake bayansu yabi NAWAFF da kallon mamaki, shin miyake nufi da marin datayi masa saiya zama FANSAR BUDURCINTA!!!!????.
    Da sauri yarufa masa baya, yayinda ameena ta k'araso takama yasmeen dake kwasar kuka, hannunta kawai taja batareda tace mata komaiba,    mota suka shiga bala yajasu suka tafi.
    Ahanyama yasmeen sai kuka take, dan furicin NAWAFF yayi matuk'ar gigitata, 
    ya dawomata da tunanin rayuwarta ta baya, lallai itakam tana cikin tarkunan maza azzalumai, shiyyasa takema maza KALLON KITSE na @UT@R H@JIYA@",, shin wai ita haka rayuwarta zata k'are, kowane NAMIJI burinsa yarabata da Abu mafi muhimmanci ARAYUWAR ta, miyasa haka???, mina musu???, miyasa suke son su rabani da mutuncina???, ta fad'a tana wani irin kuka mai ban tausayi,, Ameena da balarabe duk tausayin yasmeen ya cika musu zuciya, dan afili take maganar batareda ta saniba.
     Ameena ta rungumeta tana lallashi, dahaka suka k'arasa gida..........................





© 2016


Bilyn Abdul
    Mrs Abdus'salam
          LUV U OLL
[04/12/2016 18:54] bilyn Abdul: ☆☆☆☆☆☆☆
NAWAFF
☆☆☆☆☆☆☆





NA BILKISA IBRAHIM




Page 6

........Nawaff kuwa tafiyarsa yayi yabar mas'ud, mas'ud bai damuba dan dama batare suka zoba,  komawa yayi wajen taron dan baikama ta  ace suduka sun tafi ba.

NAWAFF kwance afalonsa dayaji kayan more rayuwa iri2 yana kwance saman doguwar kujera idanunsa lumshe, tamkar maiyin barci, amma idanunsa biyu, yana cikin tsananin b'acin raine kawai, tunani yake mizaima yarinyar nan ya huce haushinsa, dan ya tsaneta, hangota kawai yake lokacin data maresa, yakai hannu yashafa fuskarsa.
    Yay kwafa, wlhy sai yarinyarnan ta raina kanta inhar yana numfashi.
   Kofa aka kwankwasa, ya ce, "kowaye ya shigo.
      Wata 'yar aikin gidansu ce, d'auke da tiren kayan marmari, ta d'ora asaman tebirin dake tsakiyar falon, tad'an jawo tebir d'in gaban kujerar da Nawaff yake kwance.
    Watama tashigo da kuloli, ta d'ora inda 'yar uwarta ta d'ora, sannan suka duk'a suna kai gaisuwa wajen oga Nawaff!!.
    Hannu kawai ya d'aga musu sannan yay musu nuni  dasu tafi.
   Da sauri suka wuce dan sunsan halinsa baya son wargi.

D'aya acikinsu ta ce, "wlhy talatu yaya Nawaff yana burgeni, dama zaice yana sona!,
   Talatu ta rik'e baki, lallai ladidi yau na tabbatar bakida hankali, garama tu wuri ki fidda wannan tunanin a ranki, tun kafin wanima agidannan yajiki, in banda wuce gona da iri, yazaki had'a kanki da wannan had'ad'd'en mutumin, mai ilimi da kud'i, ga k'yau, wanda duniya tasan da zamansa.
    Ladidi tayi dariya kujimin wannan talatun, to kika San abinda ALLAH zaiyi ne??.
   Talatu ta ce, "A'a. 

Tunda suka fita baiko motsaba bare yaga abinda suka kawo masa, wayarsa tashiga k'ara cikin sauti mai dad'i, idonsa arufe ya mik'a hannu ya d'auka, ahankali ya bud'e idanu dan ganin wake kiransa, momcy yaga ansaka.
    Wayar ta k'atse aka sake kira.
  Cikin ladabi ya ce, "momcy barka da dare.
   Daga can ta ce, "barka dai, wai lfy banga kashigoba?, kuma ance mini kadawo.
    Wlhy babu komai momcy ina d'akine, nagajine shiyyasa kika ga ban shigoba, inaso nayi barcine da wuri, dan gobe d'aurin auren SAFWAN, banaso nak'i zuwa gashi kuma na safene.
    Okey to shikenan, dama nazata ko bakada lfy ne??.
   A'a lfyta k'alau momcy na!!.
 To shikenan saida safe.
    ALLAH yakaimu my sweet mom!!!!.
Saida takashe sannan ya kashe.
   Number mas'ud yakira, batareda yayi sallamaba ya ce, "waikai malam kana inane??.
      Gani nanma shigowa gidan mas'ud yafad'a.
     Kashe wayar yayi batareda ya ce, "komaiba.

Mas'ud yaturo k'ofan yashigo da sallama, bai saurari amsaba, dan yasan bazai samuba, saboda mutumin yau cikin fushi yake.
   Kujera yanema ya zauna, tareda fad'in gani neman mi kake mini??.
    Nawaff yatashi zaune, yad'an tsurama mas'ud idanu, bayan kamar minti d'aya ya ce, "bro's plz inaso ka taimaka mini??.
   Mas'ud ya ce, "to wane irin taimako kenan??.
    NAWAFF yad'an cije leb'ensa na kasa, ya ce, "na nemo yarinyar nan, inaso nasan ita wacece?, 'yar kuma wacece?.
   Dan wlhy idan banyimata rashin mutunciba zuciyata zata iya fashewa, ALLAH na tsaneta, kuma saina koya mata hankali, daga kaina bazata sake rashin kunyaba, ko kuskurwn marin wani.
     Mas'ud yay masa kallon tsaf dan ganin yanda  yafita hayyacinsa yau d'aya.
   Yaja numfashi, Nawaff! Yakamata kadawo hayyacinka, karka manta kaifa kafara tsokanar yarinyarnan, kamareta, kayimata dariya.
    To dankuma yau tarama saikaji haushi, yakamata ku tsaida fad'annan haka tunda kowa yayima kowa, sannan ka janye k'udirinka na d'azu, dakace marin data yimaka shine zai zama fansar budurcinta, Nawaff bansanka da irin wannan halinba, kar ka aikata abinda zaizo ya dami kowa, wannan ba hanyar bullewa bace, kai dama soyayya kuka koma dan wlhy kun dace da juna sosai.
    Harara Nawaff ya watsama mas'ud, wadda dama tun d'azu ita yake masa bai ganiba.
    Ya ce, "ALLAH kuwa mas'ud yau dawanine yafad'a mini maganar nan wlhy dasai na bubbugeshi, amma............. yay kwafa kaiwai batareda ya karasaba.
     Mas'ud yay murmushi ya ce, "amma mi....?, ka karasa fad'a mana, to konima zaka bibbigeni ne?, ka huce haushinka!!,.
    Tsaki NAWAFF yayi yatashi zaibar falon, mas'ud ya tuntsure da dariya, tareda fad'in sakai a wahala kenan,, duk wanda dai yaga wannan fad'an naku yasan na masoyane.
     Har Nawaff yakai k'ofa yadawo ya ce, "kai dallah malam sauraramin!, mixanso a jikin wannan faratun yarinyar mai kama da aljana, kai dana so wannan yarinyar gara naso 'yar k'auye wlhy.
   Dariya mas'ud yake tuntsurawa harda hawaye, cikin dariya ya ce, "aii kaima faratunne Nawaff, koka manta?, amma mudai 'yan kallone mijin faratu, mas'ud yafad'a cikin tsokana.
    NAWAFF ya kula mas'ud yana neman maidashi wani sakaraine, dan haka yashige bedroom yay kwanciyarsa.
    Dak'yar mas'ud ya lallab'ashi yafito sukaci abinci.


WAYE NAWAFF SA'EED MODEEBBO???????, kubiyoni danjin wannan amsar.





©2016


Bilyn Abdul
     Mrs Abdus'salam
            LUV U OLL
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *