check your best novels here

Monday 20 February 2017

NI DA AMINIYATA!!! 42 to 46

[06/11/2016 16:03] bilyn Abdul: 6~November~2016



NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM



42

.............Uncle G yadawo daga masallacin, ganin sopy bata a palon sai yayi tunanin tana d'akinta, yanufi d'akin amma bata nan, fareeda ce kawai take barci, sai yaje kichin, nanma bata nan, dan haka yanufi d'akinsa, tana zaune a bakin gado ta rabga uban tagumi, uncle G yay wata sassanyar ajiyar zuciya tareda girgiza kai.
   Kusada ita ya zauna, amma duk bata sani ba, ya jawota zuwa jikinsa, tai firgigit alamar dawowa.
  Ya ce, "haba Safiyya wane irin tunanine haka??, ta fara mutsu2n kwace jikinta tana wani zumb'uro baki.
   Ya kuma rungumeta tsam ajikonsa ya ce, "kinga yi hak'uri muyi magana ta fahimta.
   Cikin shagwab'a ta ce, "ni dai ka k'yaleni, ba fareeda ta finiba!!.
   Ya sumbaci bakinta ya ce, "ni na isa, aii youseef! sai Safiyya!, aurenmufa yafi auren zobe yanzu dai tashi muyi magana.
   Ta tatashi tana wani zuzzun b'uro baki yanaso yayi dariya, amma yana tsoron karya sake tunzurata, dukda haka saida yad'an dara.
   Ta ce, "O, dariyama kake min!.
 Ya ce, "A'a, aii ke d'ince duk kin wani burkice min!.
   Shiru tai masa, dan shima haushi yake bata.
   Jawota yayi suka hau kan gadon sosai suna fuskantar juna, ta rintse ido kam, dan ganin yanda ya k'ura mata idanu, yay 'yar dariya tareda had'e bakinsa da nata, soyayya mai tsafta yashiga nuna mata, yayinda lamura suka fara nisa sai tsoro yashigeta, ta tuna wahalar datasha kwana uku dasuka wuce, tafara mutsu2n kwace jikinta, amma ina tariga tazo hannu, dole ta hak'ura yaci gaba da sarrafata yanda yaso, har yakai ga zuwa inda yake kwad'ayi.
    Dukda yau batasha wahala kamar ranarba, amma tad'anji jiki, bayan komai yanatsa saiya shiga tsokanarta wai matsoraciya, tasa hannu ta rufe fuska.
   Yaudai tare sukai wanka, sopy tanata wani nok'e2 dan kunya, shiko gogan naku ko ajikinsa, d'akinta taje ta canja kaya, dan har yanzu fareeda barci takeyi.
    A palo ta iske uncle G!, ya ce, "Sopyna yunwa nakejifa.
   Ta ce, "yunwa kuma?.
    Ya ce, "wlhy kuwa, bakin kwashe abincinba.
  Tad'an zaro ido tana fad'in yaushe naje cikinka na kwashe maka abinci?.
   Ya ce, "zona gaya miki.
  Sopy tayi dariya ta ce, "nak'i wayon".
   "Shima dariya yayi."
 Kichin taje ta had'o musu abinci mai d'an sauk'i, ya ce, "to bak'uwarmufa??.
   Saida tad'an rage fara'a sannan ta ce, "to, aii barci takeyi.
   Uncle G! ya ce, "saiki kai mata ki ajiye, idan tatashi zuwa anjima basai taciba, to, kawai ta ce, "masa".
   Bayan sun gama suka zauna kallon labarai, sai zuwa goma ya ce, "tashi muje mu kwanta kinga gobe idan ALLAH ya kaimu zan fara zuwa aiki, ta ce, "haka ne."

♡~♡~♡~♡~♡~♡~♡~♡
    Saida suka kwanta ta ce, "uncle!!.
    Ya ce, "Na'am,
Wai dan ALLAH a ina ka ga fareeda ne?.
   Saida ya rungumeta ajikinsa sannan ya ce, "kin daina fushin da nine?, ta ce, "nidama ba fushi nakeyi da kaiba aii, kawai dai rainane ya b'aci, amma kayi hak'uri bazan sakeba.
   Yay mirmushi tareda sake rungumeta sosai yana shafa bayanta, ya ce, "na hakuta sopyna, amma kinsan ban tab'a ganin fareeda ba, nadai santa a labarine kawai.
  Ta ce, "hakane".
 ya gyara kwanciyarsa zuwa rigingine, ya ce, "bayan fita ta daga gida, asibiti na nufa, dan dubo yayan faruk da baida lafiya, nafito kenan tsautsayi yasa na bige fareeda da mota akan titi, wannan yasa na d'auketa muka koma cikin asibiti, aka karb'eta da gaggawa dan a sume take, amma ""ALLAH gafurun rahimun"" sai ta farfad'o da wuri, kuma babu inda taji wani mummunan ciyo saidai d'an guggurjewa, dan haka aka sallamemu, to sainace tafad'amin gidansu na kaita, saita shiga kuka ta ce, "batada gurin zuwa, to nikuma saita bani tausayi shine nace tabani labarinta, amma saita kasa tanata kuka, nikuma ganin haka yasa nataho da'ita gida dan ta huta, sannan idan inada halin taimaka mata saina taimaka mata, kinji yanda akai muka had'u.
   Sopy taja ajiyar zuciya ta ce, "tomiyasa baka d'aga wayataba?.
  Saida ya kalleta sannan ya ce, "na barta a motane, shiyyasa banga kirankiba.
   Ta ce, "to, yanzu yakake gani zamuyi da fareeda?, dan gsky bazan iya zama da itaba.
   Ya d'an murmusa tareda jawota jikinsa ya ce, "haba sopyna nasanki mai tausayice, kiyi hak'uri mu zauna tare harta warke, sannan saimu san abinyi, ko muje mubama baba hak'uri amaida ita gidan mijinta, nasan har yanzu kina k'yaunar fareeda, ki yafe mata sopyna ALLAH yana tareda masu hak'uri.
   Ta ce, "uncle amma kasan fareeda ta cutar dani ko?, ya ce, "nasan haka sopyna amma ki daure ki yafe mata, aii wani hanin ga ALLAH baiwane.
   Ta rungumeshi itama tana 'yar dariya ta ce, "gashima ALLAH yay min canji da samun gwarzon namiji mai ilimi da k'yau, ga nasaba.
   Uncle G yad'ago fuskarta yana murmushi, ya ce, "sopyna nagode, amma taya nazama gwarzo? Tunda ban tab'a yin wani abu dazai nuna ni gwarzo bane.
   Tayi murmushi tareda b'oye fuskarta a k'irjinsa ta ce, "kaima kasan kai gwarzone.
  Cikin kunnenta ya ce, a wajen....... ya'arasa a hankali batareda najiba, ta kuma cusa kanta a kirjinsa tana fad'in nidai babu ruwana ga bily nan tana kallonmu.
  Ya ce, "aii yanzu zan koreta, dan sa idonta yayi yawa.
   nima sainayo waje tun kafin a koroni, nad'an lek'a fareeda naga har sannan barci takeyi, dan haka nima nataho wajen my sweet d'ina...............

Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[06/11/2016 18:03] bilyn Abdul: 7~November~2016



NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM




43

............Washe gari dak'yar sopy ta iya b'an b'are jikinta daga na uncle G!, dan tunda sukayi sallahr asuba suka koma suka kwanta, takula zaifara wani takale2, gashi yau zai koma aiki, tasamu dai dak'yar yabarta tashiga kichin ta had'a musu break, tana cikin gyaran falo fareeda ta fito, Sopy tayi burus da ita taci gaba da aikinta.
   Fareeda ta daure ta ce, "mizan tayaki dashi sopy?.
   Batareda ta kalletaba ta ce, "kibarshi kawai nama kusa gamawa.
    Fareeda ta dage saita taya sopy aiki, Sopy ta ce, "kije ki kwanta kinsanfa bakida lafiya, fareeda tad'anyi murmushi mai ciwo ta ce, "Sopy kenan!!; karki damu da lafiyata dan nikaina batada amfani agareni, dan haka ki kawo natayaki kedai.
   Sai asannan sopy ta kalli fareeda dake hawaye, saikuma jikin sopy yay sanyi, ta tabbata har yanzu tana k'yaunar fareeda, kawai b'acin raine yahana son tasiri dakuma danneshi datakeyi.
    Fareeda ta surkushe agaban sopy tana zubar da hawaye, ta ce, "dan ALLAH Sopy ki yafe min, wlhy nayi nadamar abinda na aikata, rud'in shaid'anne kawai ya kaini ga aikata kuskure mafi girma ga Aminiyata 'yar uwata, dakuma iyayena, kuyimin kowanne irin hukunci, indai zaku huce, ki daina fushi dani plz, ta rushe da kuka mai ban tausayi.
    Sopy ta kauda kai itama tana hawaye, sunkai tsawon minti uku kowa yana kuka, sannan sopy ta d'ago fareeda ta rungumeta suka cigaba da kuka ahaka, uncle G yana tsaye yana kallonsu cikin tausayi, lallai yasan gurinnan ana k'aunar juna, shaid'anne kawai yashiga tsakanin aminan juna, har yay tasirin b'ata tsakaninsu, ganin kukan nasu bamai k'arewa bane yasa shi yin tafi, da sauri suka juyo suna kallonsa, yay murmushi mai k'ayatarwa, tareda fad'in lallai yau ranace mai tarin farinciki da tarihi, na godema ALLAH dayasa muku hak'iri azukatanku.
   Su duka murmushi suke, farida tai surin dafe kujera danjin jiri yana d'ibarta, da sauri sopy ta ruk'ota tana tambayar lfy??.
   Fareeda ta ce, "kainane, uncle G ! Ya ce, "ki kaita d'aki ta kwanta, to sopy tafad'a tana rik'eda fareeda, uncle G! yabisu da kallo yana murmushi.
  D'aki yakoma ya kwanta dan dasauran safiya, sopy kuma taci gaba da aikinta, bayan tagama tanufi d'aki danyin wanka, amma saita tarar fareeda ta gyara d'akin tsaf, sopy ta ce, "kai fareeda keda nace kizo ki kwanta ashe kina nan kina aiki.
   Fareeda tad'anyi murmushi kawai, wanka sopy tashiga ta tsantsara kwalliya cikin siket da riga na material tayi k'yau sosai, ta ce, "fareeda kema yakamata kiyi wankan dan kiji k'arfin jikinki, saiki fito muyi break, fareeda ta ce, "to.
    D'akin uncle G! tanufa, yana kwance d'ai d'ai yana barcinsa, sopy ta kalleshi tana murmushi, lallaima mutuminnan kamanta yau zakaje aiki ko?, saman gadon ta hau, tad'an jamasa hanci, ya d'an motsa, tashiga shafa kumatunsa da saje yakwanta luf luf na bak'in gashi, ahankali ya bud'e idanunsa, ta nuna masa agogonsa data d'aukko a durowar gefen gado, ya ware ido sosai dan  ganin lokaci, ya mik'e yana fad'in sopyna nakusa makara fa.
    Sopy tayi dariya tana fad'in ato hutun nan yasa kafara mantawa da makaranta, ya juyo yana kallonta, ya matso daf da ita murya kasa2 ya ce, "ba hutune yasani mantawa da makatantaba aii.
   Sopy ta lumshe ido ta bud'e ta ce, "to, miye?, yad'an rungumota gefen jikinsa ya ce, "sopyna ce ta shayar dani zuma mai d'an d'ano, harna manta da kowa da komai.
    Safiyya ta kwace jikinta tana dariya, ta ce, "uncle nidai babu ruwana ga ruwan wankanka can a bayi, bayi yanufa yana murmushi, saida yaje bakin k'ofar yajuyo yana kallonta.
   Ta ce, "miya faru kuma??, ya d'an marairaice fuska ya ce, "baza'a taimaka amin wankanba.
   Sopy ta zaro ido waje tana fad'in rufani kasayani, yanufota yana fad'in to bari na rufaki na sayaki, da gudu tafita tana dariya, shima bayin yashiga yana dariya.


A gurguje yayi break dan yakusa makara, har wajen mota sopy ta rakoshi, ya kalli motar da mamaki dan ganin an gogeta tsaf, ya ce, "Sopyna sannu da k'ok'ari, amma yaushe kikayi aikin nan??.
   Tayi murmushi ta ce, "da safen nan uncle, ya jawota jikinsa ya rungume tsam tareda sumbatar kumatunta, ya ce, "lallai nayi dace da samun mace tagari k'yak'yk'yawa mai hankali, ALLAH yay miki albarka sopyna, yabamu 'ya'ya nagari masu irin halayen nan naki.
   Tayi murmushi tareda fad'in aikafini halaye masu k'yau, nafison 'ya'yanmu subiyoka tafad'a tana rufe fuska dan kunya
    Uncle G! Yay murmushi ya ce, "sarkin kunya, ni bari nawuce dan karna makara dayawa.
   Ta ce, "to ALLAH ya tsare ya kiyayeminkai!!, ka gaida min da mutane.
    Ya ce, "amin, tareda mata hararar wasa ya ce, "ninema d'an aikenki??.
   Ta ce, "A'a nina isa na aiki my sir d'ina, kuma sarkina.
   Yay dariya, idan nadawo zaki gayamin waye sir d'in aii.
   Sopy tashige gida tana dariya, shima yaja motar yatafi yana dariya, da k'ara jin yarinyar a zuciyarsa..................





Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[07/11/2016 19:45] bilyn Abdul: 7~November~2016




NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM



44

............fareeda dake lab'e tana kallonsu sopy takoma da sauri tazauna danganin sopy tanufo palon tana dariya.
   Sopy tashigo da sallama, fareeda taisaurin kauda komai azuciyarta ta amsa cikin fara'a, sopy ta ce, "tashi muyi break ko 'yar uwa, fareeda ta ce, "to, suna break suna hira sama2, dan yanzu babu wani sabo tsakaninsu, kunsan idan karabu dazama da mutum hakan yana faruwa, bare idan sab'ani yashiga tsakaninku.
    Bayan sun gama break sopy tanufi d'akin uncle G! domin gyarawa, fareeda! ta k'urama hoton uncle G! dake palon idanu, wani kuma shida Sopy! suna murmushi, a zuciyarta ta ce, "sopy kedai kullum mai sa'a ce, inama ace............. ..., nad'an zaro ido ina fad'in fareeda!! inama ace mi?????????????????.

Amakaranta kuwa tunda uncle G! yay fakin d'alibai sukayo caa akansa, ya fito daga motar fuskarsa cike da fara'a, sukansu d'aliban fara'ar tasa tabasu mamaki, nan dai suka shiga gaisheshi da k'ara tayasa murnar aurensa.
    Shima gidiya yayita musu da halartar d'aurin aurensa dasukayi, dakuma tanbayarsu karatunsu.
    Sukace komai nomal amma sunyi missing nasa sosai, shima ya ce, "yayi missing nasu.
  Wata ta ce, "uncle G! ina amarya safiyya!!?, saida yad'an murmusa sannan ya ce, "tana gida nabarota, wata ta ce, "bazata dawo school baneba??, ya ce, "zata dawo amma saita k'ara hutawa, gaba d'aya gurin suka sa dariya, shima yayi gaba yana dariyar.
   A office ma bata sake zaniba, dan d'alibaine sukaita yimasa cincirindon taya murna harda malamai 'yan uwansa, wasuma gulma takawosu acikin d'aliban.
   Dak'yar ya samu kansa zuwa sha biyu yashiga lecture, saidai gaba d'aya kewar sopy saita isheshi, ya kalli gurin zamanta yaga kamar zaiganta yanzu, sukansu wasu d'aliban sun harbo jirginsa, dan duk sanda ya kalli gurin daya fara ganinta saiya yi murmushi, dahaka dai yagama musu lecture d'in yafito, suka shiga gulmarsa akan kallon gurin zaman sopy dayayi tayi.
    Daga nan wani ajin yaje yagabatar da lecture, sai karfe biyar na yamma yanufo gida, cikin zumud'in son ganin sopy.

Lokacin daya iso sopy tagama gyara gidan, tayi wanka tad'au kwalliya ta d'aukar hankali, ita kanta fareeda tana mamakin yanda sopy ta ke kwalliya yanzu, suna falo suna hira taji hon d'in motarsa, da sauri tatashi taje tabud'e masa get.
   Tun yana mota yake sakar mata murmushi itama tana maida masa murtani, yay fakin takaraso bayan ta rufe get d'in, dakanta ta bud'e masa mota, maimakon yafito saiya jawota cikin motar ta zauna kan cinyarsa.
    Ya kura mata manyan idanunsa masu haske yana wani murmushi mai k'ayatarwa, ta hure masa idanu tana murmushin itama, suka tuntsure da dariya, ta ce, my uncle kadawo lfy, saida ya sumbaci kuma tunta sannan ya ce, "lfy lau nadawo, saidai zuciyata tana nan gangar jikinace a makaranta.
   Sopy tay wani far da idan ta ce, "da gsk uncle d'ina. Ya lumshe idanu cikin wani yanayi, domin farin nata yatafi da imaninsa, ya bud"e ahankali yana kallonta, sai dai yanzu idonsa yayi d'anja ya ce, "my sopy ina k'yaunarki dayawa, nakan rasa inda zansa sonki, ashe dama haka ma'abota soyayya sukeji??.
   Sopy ta shafa k'irjinsa tana fad'in nima ina sonka my uncle d'ina har nakan rasa yanda zan musalta son naka.
   Ya rungumeta tsam ajikinsa yana wani fidda numfashi dak'yar, sunkai tsawon minti biyar ahaka, sopy ta daure ta ce, "uncle mushiga ciki ko?.
    Ya d'agota yana murmushi, ahankali yace kinsan ALLAH nama manta a inda muke, sopy ta tashi daga jikinsa tana 'yar dariya, ta zagayo tad'ayan gefen ta d'auki jakarsa ta aiki, shikuma ya bud'e baya ya d'auki wata leda suka jera zuwa cikin gida.
    Fareeda tana zaune suka shigo, tai masa sannu dazuwa sannan ta gaisheshi, ya amsa cikin fara'a, ya kalli sopy yana murmushi ya ce, "ashe ma mara lafiyamu ta warke?, sopy tayi murmushi batareda tace komaiba.
    Taja hannunsa tana fad'in sir muje kayi wanka kazo kaci abinci.
   Uncle G! ya harareta ya ce, "waye sir d'in?, sopy tayi 'yar tafiya zuwa k'ofarsa sanna ta juyo ta ce, uncle G!! mana.
  Da sauri yanufota, itakuma tashige cikin d'aki tana dariya.
     Fareeda tabisu da kallo tana ayyana abubuwa dayawa azuciyarsa, ahan kali ta ce, "dama ace................saikuma tayi shiru, nakuma zaro ido waje, wai ita wannan mitakeson fad'ane?????.
    Ad'aki kuwa uncle G sunata zagaya d'aki da sopy yana son kamota, amma tak'i yarda, can yasa k'afa ya tad'ota suka fad'a kan gado suna dariya, yaymata rumfa da faffad'an k'irjinsa ya ce, "waye sir d'in??.
   cikin dariya ta ce, "sorry bafa dakai nakeyiba.
   ya ce, "dawa kikeyi?, ta ce, "to d'agani zan fad'a.
   ya ce, fad'i ahaka mana.
Ta ce, "wlhy kacika nauyi zaka fasa min ciki.
Aiko yau sai dai cikin naki ya fashe dan bazan d'agakiba saikin fad'a.
   Sopy ta ce, "wayyo ALLAH na inna kizo ki taimakeni, uncle G! Ya tuntsure da dariya, aii yau saidai ki kira duk wanda zakai kira amma babu alfarma.
    Ta ce, "ALLAH kanada nauyi fa, ya ce, "kedai kika sani, batai auneba taji yana shafata, zaitai magana ya had'e bakinsa da nata, saida ya cakud'ata yanda yakeso sannan yabarta.
   Ta mik'e tana kallon kayanta dasuka cuccurkud'e, ta shagwab'e fuska tana f'ad'in duk kayimin wani iri da kaya, d'aukarta yayi cak yay bayi da ita, tanata watsal2 da bashi hak'uri, amma bai sauraretaba, yadireta a bayin yarufe.
   Ganitai ya hau cire kaya, tasa hannu ta rufe idonta, yay dariya yana fad'in k'yadai jidashi, amma yau dole kimin wanka shine hukuncinki.
     Sopy ta durkushe kasa ido arufe dan ganin ya cire kaya gaba d'aya, ruwa ya d'iba yazuba mata ajiki, ta bud'e ido da sauri tana kallonsa, yay mata gwalo, doledai tayi masa wanka, itama yay mata suka fito............................




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[17/11/2016 14:12] bilyn Abdul: 17~November~2016




NI DA AMINIYATA!!!




NA BILKISA IBRAHIM


45

.........Rayuwa mai dad'i akeyi agidan uncle G, yana nuna mata soyayya irin wadda kowace mace take buk'ata a rayuwar aurenta,.
            "dan gsky mazan mu na hausawa basu cika nunawa matansu soyayya ba, sukan fifita neman kud'i akan matansu, wani idan ba yazo biyan buk'atarsa ba, matarsa bazata tab'a rab'ar jikinsa taji dad'iba, inko tad'an rab'u jikinsa saiyace bata da kunya, gsky hakan ba dai dai bane, mu mata 'yan son soyayyane da tattali, muna son anuna kulawa akan mu, yakamata mazan mu su gyara, ba ayita nuna miki soyayya awajeba saikinzo cikin gida kiga sab'anin haka, wannan yanasa mata hange hange, ALLAH yasa mugane amin".
    
   Yauma takama weekend dan haka uncle G! yana gida, su duka suna zaune afalo har fareeda, sopy na zaune saman doguwar kujera, uncle G! yana kwance ya d'ora kansa bisa cinyarta suna kallon wani hausa film, fareeda ma na zaune a kujera mai zaman mutum d'aya, itakam ba kallon ne agabantaba, dan taraba hankalinta gida biyu, rabi a kallon tv, rabi a kallon su sopy.
    Uncle G yad'ago idanu yana kallon sopy dake shafa kansa ahankali tana kallo, yay d'an murmushi tareda saka tafin hannu ya kare idanunta daga kallon tv.
    Cikin shagwab'a ta ce, "kai uncle neman magana ko?, ta cire hannunsa ta rik'e, yay dariya tareda fad'in to aii kece naga gaba d'aya kinbama tv amanar idanuwanki, ni koma kallona ba'ayi.
   Sopy ta tuntsure da dariya ta ce, "o, kishi kake da tvn??
  Ya d'anja hancinta yana fad'in indai akan Sopyna ne tofa komaima zan iya kishi dashi.
   Sopy ta shafa sajen sa daya kwanta luf luf akan kumatunsa, suka zurama juna idanu tamkar zasu cinye kansu.
   Sopy tafara janye nata tana d'an murmushi cikin yanayin kasala, shima saiya lumshe nasa idanun yana murmushi.
    Fareeda dake kallonsu ta runtse idanu hawaye suka zubo, tai saurin sharewa da d'an kwalin kanta, tana mamakin yanda kullum Safiyya take kasan cewa asamanta, tunda take bata tab'a wuce safiyyaba, gashidai tafi sopy k'yau nesa ba kusaba, gata fara dirarriya, amma tun suna yara, sai sopy ta samu abu kafin ita tasamu, kuma kota samu saitaga na sopy yafi nata, da tana ganin idan ta samu Abdul kamar tawuce da sanin sopyn ne, amma sai sopy tazo ta auri wanda yafi Abdul komai na rayuwa, k'yawu, ilimi, kwarjini, aji, iya soyayya, da tarin abubuwa masu yawan gskg, itakam saitaga kamar batada sa'a a rayuwarta, "muguwar zuciyarta mai sakata a hanya mara b'illewa ta ce, "mata karkice haka, yakamata ki gwada sa'arki akan uncle G,nace, "itakuwa wannan tana cikin hankalinta?????.
      Ta kai kallonta garesu, ta kula sunma manta tana cikin falon, dan babu abinda sukeyi sai shan sharafin soyayyar su,   uncle G ya matso da bakinsa kusada na sopy, yana nufin suyi kiss, da idanu ta nuna masa fareeda, ya dafe goshi yana fad'in kes.
   Sopy tayi murnushi, cikin tsokana ta ce, "irinku d'aya aii.
   Yay saurin kallonta, ya ce, "dawa??.
    Tayi dariya mai k'ayatarwa ta ce, "da...........sallamar dasukajine yahanata k'arasawa, suduka suka maido kallonsu ga k'ofar.
    Su Nadiya suka shigo da sallama, su biyarne, uncle G! yatashi zaune yana fad'in lallai yau munada manyan bak'i, sannunku da zuwa.
    Sopy taje ta rungume Nadiya, da sauran yammatan, harda zaliha, suka k'araso cikin falon.
  Kowacce ta rusuna ta gaida uncke G!, ya amsa cikin fara'a, ya ce, "zuwa babu sanarwa?
   Sukayi dariya tareda fad'in aii muna son bama sopy mamakine.
    Ya mik'e yana fad'in ayko kun bata, sannunku da zuwa.
    Sopy ta dire tire agabansu, cike da kayan motsa baki, nan suka zauna anata shan hira, da labarin makaranta, fareeda dai babu abin fad'a sai binsu take da idanu.
   Zaliha! ta ce, "kai Safiyya kinyi k'yau wlhy, kodai mun samu ne??.
   Sopy! tad'an harareta cikin wasa ta ce, "kun samu me???.
   Suka tun tsure da dariya, ayeesh! ta ce, komun samu baby mana, ikilee! tai saurin cewa kema daga gani kinsan mun samu aii.
   Sopy ta ce, "kudai wlhy 'yan iskane, nidai babu ruwana.
   Ridallah! ta dafa kafad'ar sopy tana fad'in, barsu sopy!, suma nanda wani lokaci zaizo kansu aii, indai cikine, Nadiya! ta ce, bar 'yan iska, ALLAH yasa uncle G! yajisu.
   Sopy ta ce, "aii nasanma yana jinsu Nadiya.
   Gaba d'aya suka zaro idanu suna fad'in da gske yana jinmu???.
   Sopy ta tuntsure da dariya tana fad'in matsorata, nandai sukaita hirarsu da dariya, wadda fareeda tazama 'yar kallo, dan duk sun wuce da ajinta.
    Uncle G! yafito cikin k'ananun kaya yanata zabga k'amshi, sopy ta bishi da kallon tuhuma, shima ya fahimci mitake nufi, dan haka ya d'an murmusa, sannan yabi su ayeesh da kallo ya ce, "kuna nan ko har yamma??.
   Suka ce, "da anyi la'asar zamu tafi, ya ce, "okey babu damuwa harna dawo.
  Ya maida kallonsa ga sopy data had'e rai kamar zatayi kuka, ya ce, " 'yammata ya dai??, sopy ta turo baki gaba ta ce, "wai ina zaka???, yay murmushi, wajen budurwata zani hira.
    Da sauri ta kalleshi, idanunta suka ciko da kwalla ta ce, "wlhy to ban yardaba, aii kai kace yau babu inda zaka, tazo ta kwace key d'in motar, takoma saman kujera ta zauna, suko su ikilee sai kunshe dariya sukeyi.
      Ahan kali yatako yazauna kusada ita, ya sak'alo hannunsa ta bayanta ya tallafota zuwa jikinsa, ya ce, "sorry my sopy, wasa nake miki, ALLAH wajen kabeer zanje.
    Ta kalleshi tana hawaye, to kabari anjima saikaje, yasa hannu ya share mata hawayen fuskarta ya ce, "A'a kiyi hak'uri naje yanzu, tunda kunada abokan hira, nima sainaje muyi hira da uncle kabeer, aii bazan dad'eba.
   Ta kuma turo baki, amma aii cakayi sai la'asar zaka dawo, yad'n had'eta da jikinsa yana murmushi, A'a, yanzu nafasa anjima kad'an zan dawo, ta ce, "da anyi azahar, ya ce, "nayarda, ya kama hannunta yana fad'in tashi ki rakani.
     Suna fita ya rungumeta tsam ajikinsa, cikin kunnenta ya ce, "sarkin shagwab'a, kinata zuba shagwab'a agaban su Riddallah ko???.
  Ta b'oye fuskarta a k'irjinsa tana fad'in aikaine kasa nayi, ya sumbaci goshinta toshikenan saina dawo, dan idan nabiye miki bazan fitaba, yashiga mota suna dariya.
   Bayan tafiyarsa ta dawo falon, su zaliha suka shiga tsokanarta, way irin wannan shagwab'a haka, sopy ta ce, " 'yan sa ido, kwa gaji kubarmu, gaba d'aya suka shek'e da dariaya, banda fareeda data maida kanta kan tv.
    Anan suka wuni, sunsha hira sosai, dazasu tafi sopy tabasu kayan kwalliya acikin kayan  lefenta, suka tafi suna godiya, da ajandar zata shigo makaranta ranar litinin....................

Assalamu alaikum, ina godiya ga d'umbin masoya, dasuka turo min sak'on addu'a ga sister na datake asibiti, harma wad'anda basu samu damaba, ngd sosai da addu'arku ALLAH yabar zuminci.



Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[17/11/2016 17:35] bilyn Abdul: 17~November~2016




NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM



46

.........yau har sopy tagama aikin gyaran gidan fareeda bata fitoba, da kuwa kullum tare sukeyi, sopy tagama aikinta tsaf batareda tayi wani tunaniba, ko neman fareedar, bayan ta kammala komai tanufi d'akinta, fareeda na kwance abinta saman gado ta k'udundune da bargo, kallo d'aya sopy tayi mata tashige bayi abinta, dan ita azatonta fareedar barci takeyi.
    Tana shiga fareeda ta mik'e, ahankali tafito tanufi dani d'in da'aka cika da kayan break, saida tabi kowanne ta bud'e taga abinda ke ciki, sannan tanufi kicin tana yatsine fuska.
   Ta fito hannunta d'auke da robar gishiri, da sauri na lab'e dan kar ta ganni, ta bud'e ta barbad'e soyayyen dan kalin dashi, ta kuma bud'e sauran ta zuba har cikin ruwan zafi, da sauri ta maida ta koma d'akin ta kwanta kamar yanda take da.
   Sopy tafito tana 'yar wak'arta ta, ta zauna tayi kwalliya mai tsari, wando da riga tasaka na fakistan, rigar tatsaya mata iya cinya, tayi k'yau sosai.
    Tana shirin fita fareeda ta tashi tana wani mik'a alamar yanzu ta tashi a barci, sopy ta kalleta tana fad'in fareeda ince dai lafiya ko??.
    Fareeda tad'an yatsina fuska ta ce, "mikika ganine sopy??.
   Sopy ta girgiza kai, babu abinda nagani, naga yau kin dad'e baki tashiba ne kawai.
   Fareeda ta zuro k'afafubta k'asa tana fad'in wlhy jiya nadad'ene ina nafikar dare shiyyasa yau namakara, na lurama har kin gama aiki ko??.
  Sopy ta jin jina kai tana murmushi, aii babu damuwa, garama da kika huta, tai waje tana fad'in ki shirya muna jiranki a falo.
   Fareeda ta rakata da harara, tana fad'in 'yar rainin wayo, aii na daina tayaki bautar gidannan, nafiso nima nashigo amatsayin matar gidan, dan bazanta wahalar banzaba.

   Sopy kuwa d'akin uncle G! tanufa, tad'an zauna gefen gadon kusada shi tana shafa fuskarsa, ahankali ya bud'e idanu akanta, suka sakarwa juna murmushi, ya mik'o mata hannunsa wai ta tadashi, takama hannunsa tana fad'in ALLAH yasa na iya tada kai uncle d'ina!, dan kayi nauyi dayawa, yajawota tafad'o jikinsa, yasa hannu biyu yay mata zobe, cikin kunnenta ya ce, "nine mai nauyin ko??.
    Ta d'ago tana kallon fuskarsa sukayi murmushi, ta sumbaci k'irjinsa, yaja wata sassanyar ajiyar zuciya tareda k'ara rungumeta.
    Cikin sanyin murya ta ce, "my youseef tashi kayi wanka ko??, yad'an lumshe idanu, cikin shagwab'a ya ce, "saidai idan zakimin da kanki??, tad'an zaro idanu waje tana fad'in nifa nayi wanka aii saina b'ata jikina.
   Ahankali yatashi da'ita zaune shima yatashi yana mata wani sihirtaccen kallo, cikin sanyin murya ya ce, "kinyi k'yau sopyna.
    Tayi murmushi tareda fad'in nagode hubbina.
   Ya ce, "woow nice name, daga yau haka za'a ringa kirana ko??, tai wani walay da idanu ta ce, "inhar kana buk'ata??.
   Ya mik'e yana fad'in aii namafi kowa buk'ata.
   Takama hannunsa suka nufi bayi, taimasa wanka fas sannan suka fito, ta shiryashi cikin k'ananun kaya, dan yau babu aiki.
    Falo suka fito sunata zabga k'amshi mai dad'i, fareeda na zaune itama taci kwalliya cikin atamfa aiket da riga, sopy tabita da kallon dan ganin kwalliyar datayi.
   Fareeda ta basar daga kallon da sopy take mata, ta d'an zamo daga kujerar ta ce, "yaya youseef ina kwana??.
   Uncle G! ya amsa da lfy lao fareeda, kin kwana lfy??.
   Ta ce, "Alhmdllih.
    Ya ce, "masha ALLAH.
 Dani suka nufa domin yin break, sopy tafara k'ok'arin had'ama uncle G break, saida ta zuba masa komai sannan ta turama fareeda kamar yanda ta saba.
   Uncle G yaja filet gabansa yana fad'in yauwa 'yar albarka, laumar farko dayayi ya kume azaune kamar gunki, dan jin wani aza babben gishi har kwa kwalwarsa, yaja kofin shayun da sauri ya kurb'a domin neman sauk'i, amma saidai kash shima shayin haka yake.
   Fareeda tana kallonsa, amma sopy bata lura da halin dayake cikiba, dan hankalinta yana kan zuba abincinta.
   Uncle G! ya d'ago idonsa dayayi d'anja yana kallon asopy, sopy ta d'ago suka had'a ido saita sakar masa murmushi, amma ganin yanda fuskarsa ta canja sai jikinta yay sanyi ta ce, "hubbina yayadai???.
    Ya daure ya ce, "ci abincin kiji.
  Ta d'iba ta kai baki, dan ita azatonta yayi dad'ine sosai, jin gishiri zauzau yasata d'agowa da sauri tana gallonsa, shima ita yake kallo, fareeda da dad'i ya kashe ta, ta d'iba takai baki, da sauri ta zubo dashi a hannunta ta ce, "Sopy yaya haka??.
     Sopy ta maido da kallonta gareta, zuciyarta sai bugawa take da sauri2, wasu hawaye masu zafi suka zubo afuskarta.
   Amamakin fareeda saitaga uncle G! ya matsa da kujerarsa kusada sopy, ya kamo hannunta ya rumtse anasa, yasa d'ayan hannun yana share mata hawayen, cikin sanyin murya ya ce, "sorry safiyya!, karki damu, aii kowa yana kuskure a rayuwarsa, tunda haka bata tab'a faruwaba dole muyi miki uzuri.
   Sopy ta kwanto da kanta saman cinyarsa tana shashshekar kuka, ta ce, "ngd uncle d'ina daka fahimceni.
   Ahankali yake buga bayanta kamar wata jaririya, ya ce, "to ya isa haka nan, kinsan bana son kukanki.
   Ta d'ago suna kallon juna, sukaima juna murmushi, yasa hannu ya kuma sharemata hawayen, ta ce, "uncle bari naje na sama mana wani abun mai sauk'i.
   Ya jin jina kai yana murmushi.
Fareeda tabisu da kallo cikin matuk'ar bak'in ciki da haushin rashin samun nasara, mik'ewa tayi tabi bayan sopyn zuwa kichin.
    Abu mai sauk'i sukayi, dukda sopy ce rabin girkin, dan fareeda bak'in ciki ya hanata yin wani aikin kirki.
    Yana zaune afalo yana kallo suka fito, ya tashi yana fad'in yauwa sannunku, dani suka zauna suna break d'in, uncle G! sai kod'a abincin yake dan sopy ta saki jikinta, dan har yanzu bata cikin walwala, wai abincin yayi dad'i, harma yafi na kullum.
  Sopy tayi murmushin k'arfin hali, ta ce, "uncle kana dai fad'ane kawai.
  Ya ce, "da gsk nakeyi sopyna, ki kuma tambayi fareeda ma, yafad'a yana kallon fareeda datakeji kamar ta tashi tabar wajen, tai saurin k'irk'iro murmushi, cikin daburcewa ta ce, "ALLAH sopy da dad'i.
   Sopy tayi murmushi ta ce, "to shikenan ngd.

Bayan sun gama, uncle G yafita, sopy kuma tanufi d'akinsa dan ta gyara.
   Fareeda tana zaune abin duniya duk ya isheta, dan taso ace uncle G! ya hau kan sopy da masifa, taja kwafa tana fad'in aii idan kunsan wata bakusan wataba, ta mik'e tanufi d'aki.

Sai dare uncle G! yadawo, sopy taje ta taroshi kamar yanda tasaba, suka shigo falon suna dariya, fareeda dake zaune a falon tana kallo tad'anja k'aramin tsaki, amma basujiba, tayima uncle G! sannu da zuwa, ya amsa tareda tambayarta ya gida, ta ce, "lfy lao.
     Sopy taja hannunsa suka nufi d'akinsa, tadawo ta d'aukar masa ruwa mai sanyi takai masa, ya karb'a yasha yana fad'in sannu 'yar albarka.
   Ta karb'i kofin ta ajiye tana murmushi, ta ce, "sai wanka ko?, ya ce, "e, amma fara bani ledar can dana zo da'ita.
   Ta d'akko masa, ya ce, "bud'e ki gani mana.
  Ta bud'e tana dubawa, manyan hijjabai ne guda goma, sai nik'af guda uku, ta kalleshi tana fad'in uncle wannan fa??.
   Ya ce, "nakine, dan gobe zaki koma makaranta, kuma bana buk'ata kowane wawa ya kalle mini matata, dan tawace ni kad'ai.
   Sopy tayi dariya, hubbina kishinka yayi yawa wlhy.
   Yay murmushi, oho, kodai mizakice kice, nidai bana son arink'a kallon min matata.
   Ta ce, "to ngd sosai mijina, abin k'aunata.
   Yay dariya to saka nagani!!.
Ta saka, har k'asa yakai mata, dan wasuma suna d'an jan k'asa, tasaka nik'af d'in shima, ya kalleta ya tuntsure da dariya, wai kamar ojuju.
   Itama dariyar tayi ta ce, "aii kaine dai ka maidani inma ojujunne.
   Ya shige bayi yana fad'in gara dai haka aii.
    Saida yay wanka ya shirya sannan sukaje falo, sukaci abinci, yau basuyi wata hira mai tsawoba suka tashi, dan sopy tana d'okin komawa makaranta gobe.
    Koda sukaje d'akinma ba barcin sukayiba, saida suka kashe juna da soyayya mai tarin lada
   Fareeda kam ana gado anata juye juye dan babu mahad'i.................






Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *