check your best novels here

Monday 20 February 2017

NI DA AMINIYATA!!! 20 to 25

[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 21~October~2016




NI  DA  AMINIYATA




NA  BILKISA IBRAHIM 



21

...........safiyya ana gida anashan weekend, inna tayi farincikin ganin yanda sopy ta canja, tasaki jikinta sosai sai dai haryanzu tananan arame, dan bata k'ara k'ibaba.
   Yanzu tarage yawan tunani, tafi maida hankali wajen karatunta, babama yaji dad'in ganinta sosai.
    Taje tagaida maman su fareeda, harma tatayata wasu ayyukan, maman fareeda tanata k'ara lallashinta akan abinda yafaru, sopy ta ce, "wlhy mama ni yawuce awajena, dama can ALLAH yarubuta Abdul mijin fareeda ne, dan haka kudaina ganin laifinta, kud'auka wannan yana cikin k'addarar rayuwarmu ne kawai.
    Mama ta ce, "hummm safiyya kenan ke dai mai hak'urice kawai!! Kuma insha ALLAH saikin sami miji nagari wanda yafi Abdullahi k'yawawan halaye, itakam mun barta da wayonta!!.
   A'a mama dan ALLAH karkuce haka wlhy har yanzu ina k'aunar fareeda bana son iyayenmu suyi fushi da ita!!, dan ALLAH kuyafe mata!!.
   Mama ta tsurama sopy idanu, tana matukar k'aunar yarinyar, saboda hak'urinta ga nutsuwa, lallai d'iyarta tayi asara, tunda har tarabuda safiyya bata koyi k'yawawan halaye daga garetaba.
   Nan dai sukaita hirarsu har yamma.
   Tayi k'ok'ari taje gidan aunty Nafisa da auty hauwa'u, har gidan aunty zainab yayar fareeda, nanama hak'uri tayita bata, sopy ta ce, " bakomai yawuce".
   Ranar lahadi uncle kabeer yazo gidan dan shine zai maidata school, ya d'auketa sukaje yayo mata sayya ta kayan provision da Duk abunda zata buk'ata, 'yar gatan uncle kabeer kenan, har d'unkuna yaymata yasaya mata takalma da hijja bai, da yamma tashirya suka tafi, harda kukan rabuwa da inna da baba.
     Amota uncle kabeer! ke tambayarta taje gidan fareeda!? ta ce,:"haba uncle ALLAH ya kiyaeye aii har abada bazanje gidan fareeda ba, saidai idan tazo anguwar magaisa amma bazanje gidantaba!!.
   Uncle kabeer yay murmushi saboda kishi??? Tai saurin fad'in uncle aii ni! Har abada bazanyi kishi da fareeda ba, koda d'imma ina bak'in cikin sub'ucewarta daga garenine, da kuma abunda ta aikata saboda son zuciya, amma ni yanzu haka na yafe mata, sai dai kuma bazamu tab'a komawa kamar daba, dan yanzu banida aminiyar data wuce inna da baba, sai uncle kabeer da my auntys d'ina.
   Uncle kabeer yay dariya to shikenan kema ALLAH yabaki miji nagari.
  Sopy tasa hannu tarufe fuskarta saboda kunya.
  Adai dai wannan lokacinne kuma suka iso cikin makarantar, yasamu guri yay parking, ya zaro waya bari nakira abokina yazo yataremu.
   Sopy ta ce, "waini waye wannan abokin nakane uncle?? Ni tunda nazo school d'innan ban sanshiba.
  Ya ce, "zaki gansa yanzu nan.

Cikin 'yan mintina ya iso, hankalin sopy yana kan waya tana chatin, uncle kabeer yabud'e motar yafito, suka rungume juna shida abokin nasa.
   Kai abokina nazata makarantar nan zata zama gurin zuwanka fiye da haka, amma sainaga sab'anin haka, indai har bawani abu bane yakawoka ba, ba'a ganinka.
   Uncle kabeer yay dariya karka damu indai nine yanzu zaka rink'a ganina sosai tunda my daughter d'ina tana school d'in!!.
   Ya ce, "gsky ne, aii nima yakamata yau nasan wannan d'iyar tamu.
   Uncle kabeer ya ce, "aii gata nan amota ma ita nakawo!! 
   Malamin yay dariya to ta fito, saimu k'arasa office ko?? Murnar ganinka tasa na manta a inda muke tsaye.
   Uncle kabeer ya ce, "sopy tafito ga abokin nasa.
  Da zumud'inta tafito kuwa, tayi turus tana kallon abokin na uncle kabeer,, ba wani bane illa uncle G!, shima kallonta yakeyi cikin wani yanayi mai wutar fassara,, uncle kabeer! Yay dariya to da alama kumma san juna kenan?.
   Uncle G! Yay murmushi, ai d'aliba tace, kaga duk laifinkane kenan???. Uncle kabeer ya ce, "to, kayi hak'uri, ranar dana kawota ina sauri natafi wajen aikine wlhy.
  Sopy ta daure ta ce, "uncle good evening!.
  Ya ce, "ya weekend??
 Ta ce, "ALHAMDULILLAHI.
MASHA ALLAH yafad'a yana kama hannun uncle kabeer!, abokina muje ciki ko.
   Sopy ta ce, "uncle bari nakai kayan d'aki saina dawo muyi sallama, sannan kun gama.
   Okey to shikenan babu damuwa, jeki kai, amma kisamu wasu sutayaki, dan kayan sunyi miki nauyi.
  To uncle!.

Sopy takira zaliha awaya sukazo itada wata k'awar zalihar, suka tayata kwashe kayan, saidai gaba d'aya zuciyaryata cike take da tunanin dama uncle G! Shine abokin uncle kabeer??, k'in fita tayi har saida uncle kabeer ya kirata a waya sannan tafito.
    Bayanda zatayi dole tanufi office d'in dan uncle kabeer ya ce, "tasameshi a can.
 Ahankali ta tura k'ofar office d'in tashiga, office d'in sai tashin k'amshi yakeyi, uncle kabeer ya nuna mata kujerar dake kallonsa tazauna.
   Ya ce, "kindai gama ko?? Ta d'aga kai alamar e, ya ce,"masha ALLAH, yagara zama to sopy! Ga abokina malam youseef tare mukai school d'innan dashi, amma dayake shi abincinsa anan yake, to gashi yana aiki anan, munsha gwagwarmayar rayuwa tare, komai namu tarene a school d'innan, gashinan duk abinda kike buk'ata to kizo wajensa ki karb'a, kokuma idan wani abu yashige miki duhu a b'angaren karatu, to kizo zai warware miki, domin wannan dakike gani kwarone, uncle yafad'a yana kallon uncle G!.
   Uncle G! Yay dariya kaidai masherancine abokina har yanzu kana nan baka canjaba ko?
  Uncle kabeer ya ce, "aii gsky ce, uncle kabeer yacigaba dafad'in abokina ga d'iyata wadda nafiji da ita acikin 'ya'yana, batada damuwa kamar yada nasanar maka, itama tanada kwakwalwar karatu, dan haka ka taimaka mini wajan cika mini kwakwalwarta da karatu.
     Uncle G! yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, yad'an tsurama sopy idanu tai saurin janye idanunta daga kallon datake masa, yay d'an murmushi, babu damuwa abokina nakarb'a, ainima d'iyatace.
   Sopy tana mamakin yanda taga uncle G! yanata fara'a yau, domin yau itace rana tafarko dataga murmushinsa, sannan duk d'agowar datayi saita kamashi yana kallonta.
   Sun d'an dad'e suna hira, kafin uncle kabeer ya tafi,  saida suka rakashi har wajen motarsa bayan ficewarsa daga cikin makarantar uncle G! Ya juyo yana kallon sopy, tai kasa da kai dan tasan batada gsky....................





Bily 
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 22~October~2016



NI DA AMINIYATA!!! 



NA BILKISA IBRAHIM 



22

...............yagara tsayuwar sa,  aii dole kiji kunya, dan kinsan kinyi laifi.
    Sopy tad'an d'ago ta kalleshi, ganin ita yake kallo yasata saurin yin k'asa da kai, ta daure ta ce, "laifin mi nayi??
  Ya jin jina kai, okey tunda baki d'auki abinda kika aikata amatsayin laifiba shikena, ya kalli agogon hannunsa, yanzu inada wani aiki, amma zuwa gobe zan jiraki a office, kinada lecture d'in safene???
   Sopy ta amsa da e, inadashi.
Okey to karfe nawa zaki fito??
Tayi d'an jim alamar tunani, karfe sha biyu.
  Okey bada muwa, jan jiraki k'arfe hud'u, yajuya yana kallon yanda wasu tsurarin d'alibai masu dawowa weekend damasu harkokin gabansu, dayawansu su suke kallo, yad'an girgiza kai, kinga kije d'aki amma karki shanyani, inko bahakaba to zanzo har ajinku gaban kowa muyi magana.
    Ta zaro ido waje.
yay murmushi kina mamakine ?? To indai hakane kik'i zuwa kigani, saidai kawai ki ganni.
  Ina saurarenki, yafad'a yana tafiya.
    Sopy tabishi da kallon mamaki, wai mutum mai aji da nuna isa, mai ilimi wanda 'yammatan!  da samarin! university ke son yay musu magana,  shine yau agabana, yake buk'atar naje wajensa, tad'anyi murmushi mai k'ayatarwa tanufi hostel.
   D'aliban dasuka gansu aka d'auki gulma zuwa hostel, wasu kuma ganinsu harda uncle kabeer saiba su kawo komaiba aransu, to ALLAH yashiryi magulmata dai.

Washe gari sopy tanata harkokinta, dukda gargad'in da uncle G! yay mata baisa tayi yink'urin zuwa office d'insaba.
   Shikam gaba d'aya hakalinsa yana kanta, karfe d'aya da 'yan muntina yashigo musu lecture,  saboda shi tak'i zama gaba, amma wannan bai hana idonsa lalibota ba.
  Zaliha ta ce, "sopy wai kin kula da kallon da uncle G! Yake miki kuwa, wlhy tun d'azu hankalinsa yana kanki.
   Sopy ta harareta, to uwar magul mata, ke bama karatun kike saurareba, wanda yake kallone agabanki, ni kibarni naji karatu, tana d'agowa suka had'a ido kuwa, tai surin kauda kai gefe.
   Yagama lecture nasa yafita.

Har k'arfe hud'u tayi sopy batada niyyar zuwa office d'in uncle G!, tanata harkokinta abinta, suna zaune itada Nadiya, tana koya mata wani aiki.
    Nadiya ta ce, "kai sopy kekam kin more wlhy, ina son mutum mai kwakwalwa arayuwata, wannan yana d'aya daga cikin abinda yasa kike matuk'ar birgeni.
    Sopy tayi murmushi kekam Nadiya kinada yawan tsokana.
   Nadiya ta ce, "wlhy babu wani tsokana gsky ce nake fad'a, kuma kema kin sani, saidai ki godema ALLAH.
   Kafin sopy tayi magana wani saurayi ya k'araso wajen, ya ce, "waye safiyya ibrahim kabeer!!? Sopy ta amsa da nice, ALLAH yasa lafiya?? Saurayin ya ce, "lafiya k'alau, dama uncle G! ne ya ce, "kizo yana office d'insa, sopy tad'anja tsaki sannan ta ce,"to ina zuwa.
   Aii kije kawai danni ba komawa zanyi office d'inba.
  Nadiya ta ce, "kitashi kije bakisan miya faruba, badan tasoba ta mik'e tanufi office d'insa.
    Saurayin ya kalli Nadiya, Nadiya dan ALLAH uncke G! Surayin yarinyar nan ne??
   Nadiya ta girgiza kai, A'a, ba saurayinta bane, amma nima bansan dalilin dayasa yake nemanta ba, amma kai miyasa ka tanbaya?
   Naje wajensane, shine ya ce, "nakira masa safiyya ibrahim, toni abunne yabani mamaki, danshi bai cika kula matan makarantar nan ba.
  To babu abinda yake tsakaninsu, kuma maza dai kunzama magulmata.
  A'a bawani gulma daga tambaya?.
  To miye na tambayar, shin uncle G! Ba mutum bane, koko shi bazai iya yin soyayyaba ne?? Inma hakane wlhy nikam zanyi farinciki.
    Saurayin yay dariya aii munga shi baya kula mata, gashi kuma kun mutu asonsa, kamar makarantar nan babu wani namiji sai uncle G!, bakuda wata hira sai tashi, komai uncle G!, tamkar wanda aka halitta da gold.
   Nadiya ta ce, "yanada kamun kaine, ya iya rik'e mutuncin kansa fiyeda sauran malaman da d'alibai, baya wasa da kowa, gashi kuma mai aji da ilimi.
   Saurayin yay gaba dan jin haushin furicinta.

Safiyya ta nufi office d'in uncle G!, saida taje k'ofar takasa shiga, tadad'e a tsaye, dan takasa kwankwasawa, ganin wasu d'alibai suna kallonta yasa ta daure ta kwankwasa ahankali batayi zaton zaijitaba ma, amma sai taji ya ce, "yes come in.
   Ta d'auki tsawon minti biyu bata shigaba, ganin batada fafita yasa ta tura k'ofar office d'in tashiga, wani k'amshi ne yadaki hancinta, tashak'a tad'an lumshe idanu.
   Cikin muryarsa mai dad'i ya ce, "shigo mana".
   Cikin sanyin jiki ta ida shigowa ta maida k'ofar ta rufe,, ta jingina da k'ofar.
  Yana zaune a kujerarsa, gabansa da tarin takardu, yana dubawa inaga namasu test ne, dan ya kware wajen yima d'alibai test, jin anyi shiru yasashi d'agowa, azatonsa komawa tayi, amma saiya ganta atsaye, tana kallonsa, ya ce bismilla zoki zauna.
  Ganin fuskarsa babu walwala yasa ta k'arasa ta zauna a d'aya daga kujerun dake gaban tebir d'in gabansa, yacigaba da duba takardun gabansa, batareda yakuma bi takan taba, yad'auki tsawon minti bakwai, kafin yad'an d'ago ya kalleta, tana zaune kanta ak'asa tana wasada wani zobe dake yatsanta na biyu, yad'anja numfashi sannan ya maida kansa ga aikinsa.
    Cikin muryarsa mai amo da taushi ya ce, "yauma da bansa a nemomin keba da bazaki zoba ko?? Yacigaba da fad'in babu k'yau sab'a alk'awari dai.
    Sopy ta ce, " azuciyarta aii ni ban maka alk'awarin komaiba,, amma afili saita te ce, "aii dama zanzo.
  Ya ce, "aii koma bakizoba ni zanje nemanki, dan na matsu muyi magana, tad'ago tana kallonsa, yana duba takardunne yana maganar.
    Yad'ago zai mata magana, tayi saurin maida kanta k'asa, ya murmusa, tareda mik'ewa yanufi inda take, d'ayar kujerar dake kallonta ya zauna, k'amshinsa ya yawaita agurin, yay gyaran murya tare da fad'in kinsan abinda yasa nake nemanki??.
   "Ta girgiza kai"
 Yad'ora kafarsa d'aya saman d'aya, ya kwantar da bayansa ajikin kujerar,, saida yay mata kallon mintina uku sannan yaja numfashi, ina son na tambayeki samarinki nawa???.
   Da sauri sopy tad'ago tana kallonsa, amma saiya gimtse fuska dan baya son raini.
  Ta maida kanta k'asa tana cigaba da lankwasa yatsun hannunta suna k'ara.
   Ya ce, "ina sararenki!!.
Sopy ta daure ta ce, "ni fa banida saurayi, cikin shagwab'a tayi maganar.
   Yay murmushi tareda fad'in masha ALLAHU, yakuma ce wa," to yaushe kika shirya yin Saurayin?, nanma saida ta kalleshi sannan ta ce, "banda lokacin aikata hakan.
  Nanma saida ya murmusa, ya ce, "masha ALLAHU, yataso daga kwanciyar dayayi, ya ce, "toni na shirya yin auren safiyya, domin matata tarigaya ta iso, ba wasa nazo dashiba, domin inda buk'atar yin aure yanzu, yaya kenan??.
  Sopy ta ce, "a zuciyarta, to ni ina ruwana da shirya yin aurenka ne??
   Yaci gaba dafad'in nina shirya kefa?? Dan inason muyi aure ba soyayyaba, idan kinje gidana zan nuna miki dukkan soyayyata.
   Sopy ta ce, "ban ganeba??
Ya murmusa zaki gane nan bada dad'ewaba, kije kiyi tunani akaina, kabeer yasanar dani komai daya shafi rayuwarki, dan haka bakida matsalar yimin bayanin kanki, nakuma yimiki alk'awarin mantar dake abinda yafaru dake abaya, sannan daga yau karna sake ganinki da zaliha, dan batada tarbiya, nasan bak'ya kula samarin  makarantar nan, to karki fara domin inada kishi mai tsanani, zan iya komai yayinda naga abinda zai tada min kishina, ya mik'a mata wani littafi mai d'an girma, ga wannan ki karanta lokacin dakika samu dama, zaki samu dukkan abinda ya danganceni acikinsa, dukkan tarihina yana nan.
    Tasa hannu biyu ta karb'a, ya d'akko lemon dake saman tebir d'in ya mik'a mata, sorry ga wannan kisha!.
  Ta girgiza kai A'a nagode.
Ya ce, "kina nufin bazaki shaba, ko kina kyankyamin abin hannuna ne??.
   Tai saurin girgiza kai, ya ce, "to karb'a kisha, ta ce, "aii ina azumine.
Ya ce, "wow nice, azumin me kenan??, ta ce, "na nafila.
   Ya kuma cewa nice, aii haka akeso, to idan kinsha ruwa wace addu'a zakiyi akan aurenmu?.
     Ta k'ara k'asa da kai, batareda tayi maganaba.
    Ya ce, "kunyarki tayi yawa, amma zsn rage miki ita, dan dama haka nakeson matata ta kasance mai tarin kunya da nutsuwa, gashi ALLAH ya kawo min alokacin danake tsananin buk'ar hakan, wannan week d'in zanje gida nasanarda iyayena nasan zasuyi matuk'ar farinciki, dan kullum burinsu kenan, gashi dama sunsan kabeer, dan haka ki zauna da shirin zama matata nanda k'arshen shekara 2016.
   Tayi saurin kallonsa, ya kashe mata ido d'aya, ina fatan kin shirya salo salo na soyayyar dazaki nuna min, danni mutumne mai buk'atar a soshi da nuna min tattali yak'arasa fad'a a hankali.
    Itadai sopy takasa koda k'yak'yk'yawan motsi, dan ita mamaki ma yake bata, ko ina miskilancin da jan ajin nasa?? Dama yana magana haka??.
    Kamar yasan tunanin datakeyi, ya ce, "kina mamakina ko? To daga yau kibari, domin ni mijinkine, ina fatan  kwaykwayon {MANZON ALLAH S A W} ne, domin ya nunama mana yanda zamu so matanmu da kuma yanda zamu zauna dasu, dan haka kinada matuk'ar aiki agabanki,, ki shirya kuma.
    Ya d'auki wayarta dake kan cinyarta, nomber d'insa yasa yakira wayarsa, sai kuma yacigaba da binciken wayar, babu wani abu mara k'yau aciki, saima hotu nanta masu k'yau, yagama gani ya mik'a mata.
     Ta ce, "bari natafi kar mutane su zargi wani abu.
   Ya gyara zama karki damu dasu, danni basu bane agabana, amma duk da haka na fahimceki, nima bana buk'atar kowa yasan wannan maganar sai an gama komai, kinji ko.
   Ta jinjina kai alamar to.
 Ya ce, "to tashi kije dan yamma tayi, sainazo barka da shan ruwa....
Aii kafin yarufe baki tayi waje.
   Ya kwanta ajikin kujerar, ya lumshe idanu yana murmushi, ya ce, "ya ALLAH ka mallaka min wannan baiwa taka mai tarin nutsuwa da addini.
    "muda muke a lab'e, ni da su pii pii mukace amin ya Rabbi.....................




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 23~October ~2016




NI DA  AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM





23

..........kwance take bayan ta gama shanruwa, tayi zugum dan kuwa tana duniyar tunanin abinda yafaru d'azu, tsakaninta da uncle G!, ta tuna yanda yake magana cikin gadara da bada umarni.
    "Toni na shirya yin aure safiyya, domin matata tarigaya ta iso, bawasa nazo dashiba, domin inada buk'atar yin aure yanzu,"
    Tayi murmushi, tareda sake tuno wata maganar tasa.
 "Dan inason muyi aure ba soyayyaba, idan kinje gidana zan nuna miki dukkanin soyayyata".
  Taja numfashi tareda gyara kwanciya, wato shi baya lallashi, kai tsaye yake magana babu wani kwala kwala, to amma shi baisan ba'a umarni a soyayyaba ne?.
  Ta tuna inda yake fad'in, daga yau karna sake ganinki da zaliha dan batada tarbiyya, nasan bakya kula samarin makarantar nan, to karki fara domin inada kishi mai tsanani, zan iya komai yayinda naga abinda zai tada min kishina".
    Ta murmusa, su uncle G! Masu kishi, to ina ruwana da kishinka, ni nan dakake gani maza duk d'aya na d'aukeku, a kan mizani d'aya nasakaku, taja ajiyar zuciya domin jin an kwala kiran sallar isha'i, tamik'e domin gabatar da sallah.
    Saida ta kammala komai na al'adar rayuwarta, sannan tazauna domin duba book d'in da uncle G! Yabata, ga gajiyar azumi, tazauna tana fad'in wash ALLAH!! aii duk gajiyar danayi bazata hanani karanta book d'innan ba, tai saurin kallon wayarta datake wringing sabuwar nomber ce, dan haka ta share, saida aka k'ara kira sannan tad'auka tana mita, tai shiru batareda ta amsa ba, daga camma ank'iyin magana.
   Ta daure ta ce, "kowaye idan bazaiyyi maganaba tofa zan kashe".
   jitai wata sassanyar murya ta ce, "assalamu aliki?.
   Sopy taja ajiyar zuciya domin tagane mai maganar, ta amsa da wa'alaikassalam, ta d'ora da fad'in good evening sir.
   Yay murmushi mai sauti, ya ce, " evening, kinsha ruwa lafiya?
   "Lafi law, sopy tafad'a"
Ya ce, "masha ALLAH", Amma a canja min wannan sir!! D'in.
   Tai d'an murmushi, to aii kai malaminane, in bance maka sir!! Ba mixan ce maka?
  Ya ce, "hummm, ga sunaye nan masu yawa, darling, honey, dear, my love, prince, gasunan dai dayawa.
   Hannu tasa ta rufe fuska tamkar yana gabanta.
   Jin tayi shiru yasashi fad'in ya dai?
  Nanma shiru tayi.
Ya ce, "okey, sarkin kunya, amma yakamata arage kunyarnan ko? Dan zata d'an cutar dani, in tambayeki mana??
   Ta ce, "to, tambayeni?
  Okey ince dai kinyi mana addu'a?? yayinda zaki sha ruwa, dan kinsan ana karb'ar addu'a a irin wannan lokacin.
   Sopy ta gyara zama, ta ce, "e, nayi.
  To, mikika rok'ar mana?.
"Komaima, na rok'a" sopy tafad'a, asanyaye. 
    Ya ce, "nice, "to d'an fad'amin mana naji.
  Cikin shagwab'a ta ce, "ni dai basaina fad'aba.
  Uncle G! Yay dariya, ya ce, "nice, my sopy karki damu wataran zaki fad'a, bari nabarki kiyi barci, goodnight.
  Kafin ta ce, "wani abu ya sumbaci wayar, ya kashe, sopy ta rintse idanu tabud'e, ya salam ta fad'a tana kwanciya, dama maza basuda kunya, duk jan ajinsu dawani jijida kai, idan akazo fagen soyayya saisu canaja, duba dai kiga uncle G!, ni wlhy mamakima yake bani, ta lumshe ido tana murmushi, wanda itama batasan dalilin saba.
   Ta dafe k'irjinta tana fad'in oh ni safiyya, waiy mike shirin faruwa dannine?? Miyasa nike shiga farinciki aduk lokacin da uncle G! Ya kasance danine?? Idan ban ganshiba nakanyi kewarsa? Shin miye dalilin hakan??.
   Zuciyarta ta ce, "kin kamu da sonsa ne.
   Ta girgiza kai tana fad'in ban yardaba, alokacin dana keson Abdul bahaka nakejiba aii, akwai dai dalili, to amma miye dalilin??
   Uncle G! Yana burgenine kawai, amma bawai ina sonsa bane, zan iya cewama har yanzu ban amince da batunsa na d'azuba, domin kuwa Abdul yasa nayima dukkan maza kud'in goro a fannin yaudara, bana tunani zan sake shiga tarkon son wani namiji ahalin yanzu, nariga na shafe babin soyayyar wani namiji arayuwata, nasan ban isa nace, "bazanyi aureba, tunda nima saida akayi aure aka haifeni, amma koda nayi aure mijin dana aura bazai samu wata soyayya agareniba, sai dai kuma bazan iya nuna hakan ga uncle G! ba, saboda yanada girma a idona, malaminane abokin uncle d'inane, sannan koba komai ya girmeni, ta jawo book d'in domin karantawa.
   Kubiyoni masu karatu, dominjin tarihin, youseef hussain Ahmad, wato uncle G!!!....................




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 24~October~2016



NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM 



24

.............TARIHIN UNCLE G!!!.
uncle G!, kona ce youseef hussain Ahmad, d'an asalin garin gurum ne, a k'aramar hukumar tsanyawa.
   Malam hussain shine mahaifinsa, suna kiransa da baba, sahura itace  mahaifiyarsa suna kiranta da gwaggo, su hud'u iyayensu suka haifa, hafsat itace babba tana aure anan cikin gurum harda yaranta, yusif shine nabiyu uncle G! Kenan, sai Libabatu itama tayi aure tanada yara,  sai auta Aysha tana karatu yanzu tana (jss, a secondary ).
    Gidan su uncle G! Talakawane sosai, saidai mahaifinsu yana son karatun boko sosai, wannan yasa ya tsayama 'ya'yansa sukai karatu, duk da matan daga secondary ake musu aure, amma sun tsayama uncle G! Yayi karatu mai zurfi, dukda kwakwalwarsa ta taimaka masa wajen kaiwa ga matakin dayake a yanzu, bak'aramar gwagwar maya akashaba wajen karatun uncle G!, amma idan ALLAH ya ce, "kaine tofa kaine".
   Bayan ya kammala deploma d'insa ya samu aiki a primary school d'in Gurum, wannan ma ya taimaka masa wajen cigaban karatunsa, dan yana koyarwa ya rubuta takardar izinin komawa k'aro ilimi, da taimakon wani bawan ALLAH yasamu shiga (Ado bayaro university kano) anan ne ALLAH Yahad'ashi da uncle kabeer, duk talaucin gidansu sopy! Sunfi su uncle G! Arzik'i, dan haka uncle kabeer yataka rawa mai yawa arayuwar uncle G!, tab'angaren kud'i da wasu abubuwan, sun shaku da juna sosai shida uncle kabeer.
    Uncle G! Bashida aure, dukda iyayensa suna damuwa da zamansa haka, akullum yana fad'a musu aure lokacine idan lokacin yayi zaiyi aure, yaso auren wata yarinya anan cikin garin gurum, amma sai ALLAH ya d'auke kayansa tarasu tunda ga nan bai sake yink'urin aureba sai yanzu dayaga sopy.
   Uncle G! Yazama wani tauraro mai haskawa agarinsu, dan mutumne mai girmama manya, dakuma son cigaban matasa, har k'ungiyar taimakon matasa gareshi a k'auyensu, dukda bawani kud'ine dashiba saidai rufin asirin ALLAH,
  Wannan shine tarihin uncle G!, atak'aice, nan gaba zaku rink'a jin sauran bayani akansa.

Sopy taja ajiyar zuciya, fuskarta d'auke da murmushi, lallai uncle G!, Ansha gwagwar mayar rayuwa, gsky yabata tausayi, dama ance babu maraya sai rago.
    Tarungume littafin tashiga barci.

Dak'ar ta iya tashi da asuba tayi sallah, shed'an yaribace ta ta hau barci, wannan yasata makara gashi tanada lecture d'in safe, agurguje ta shirya tanufi aji.
    Duk da haka saida ta makaro domin kuwa uncle G! Yarigata shiga, taja tunga ak'ofar class d'in, inda sauran d'alibai makararru suke irinta.
    Tsaye yake yana gabatar da lecture, jikinsa sanye da blue d'in shadda d'inkin boda, bawata mai tsada bace, amma yayi k'yau, domin dama mai k'yawunne, babu abinda kakeji sai k'amshin turarensa, jiyay hancinsa yana shak'o masa kamshinta, yad'an juyo inda yake zatonta, kallon ido cikin ido sukayima juna, dukda idanunsa suna cikin gilas wannan bai hanata jin wani yarrrrrr! Ba, tai saurin kauda kai daga kallonsa, ya gyara tsayuwarsa yana wani d'an murmushin mugunta, yacigaba da gabatar da darasi.
     Su sopy suna tsaye tareda suran maka rarrun d'alibai, har yagama lecture yafito, kallo d'aya sopy tai masa ta kauda kai, shikuma yawuce yana murmushin mugunta, wanda yabama sauran d'aliban mamaki, wasu kuma yabasu haushi dan aganinsu ya raina musu hankali, tunda akwai sa'aninsa agurin.

Ya k'arasa office d'insa amma saiyayi turus ak'ofa domin ganin kairat zaune, ya had'e rai ya ce, "lafiya dai??
    Kairat tad'ago tana kallonsa, lafiyarce takawo hakan.
   Yakuma tamke fuska ya ce, "miya kawoki office d'ina nace??.
    Yanda yayi maganar cikin tsawa saita tsorata, dan tasan baya son wargi, cikin rawar murya ta ce, "dama nazo nasanar dakai dadyna zai maidani karatu AMERICA.
    Uncle G! Ya tab'e baki, lallai yayi dabara, to ALLAH ya taimaka, zaki iya tafiya.
   Kairat ta kalleshi cikin matuk'ar bak'in ciki, dan ganin yanda yake korarta, ta daure ta ce, "to ya maganarmu dan inaso nasan matsayina agurinka!!.
    Saida yay mata kallon sama da k'asa sannan ya ce, "bakida wani matsayi agurina kamar yanda nasanar dake, sai dai ina miki fatan alkairi a rayuwarki",     ya nuna mata k'ofa akaro na biyu, zaki iya tafiya dan inada abinyi.
     Wani bak'in cikine ya tokare mak'oshin kairat, tai waje cikin bak'in ciki, dan idan tayi magana kuka zai iya zuwa mata.
    Uncle G! Yaja tsaki, yana fad'in 'yar wahala, indai so nane kin d'akko abinda yafi k'arfinki, domin tuni wata ta karb'e zuciya ta,  useless! Kawai.

Kairat d'iyar wani mai kud'ice, tunda aka kawota makarantar nana ta k'yalla ido akan uncle G! Taji takamu da sonsa mai tsanani, sai dai shid'in batai masaba, yafison ya auri d'iyar talakawa irinsa.....................






bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 25~October~2016



NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM 



25

............Safiyya! kam tunda uncle G! Yafita tashiga aji tazauna zuciyarta cike da tunani iri iri, koda zaliha! ta zauna kusada ita tana mata surutun data saba bata kulataba, saima ta d'akko wayarta tana catin da uncle kabeer.
    Wani sak'o yashigo amma saitayi burus dashi, dan azatonta wanine ya d'auki nomber d'inta a group dan haka wasu keyi, musamman ma samari.
     Shigowar wani malami yasa ta daina catin d'in, tanatsu domin d'aukar lecture.
   Bayan fitarsa batada wata lecture sai k'arfe uku, dan haka tanufi library domin wani bincike.
    Ta shak'i wani k'amshi wanda tabbas tasan mai shi, amma saita share tacigaba da karatunta, jin k'amshin ya yawaita agurin yasata juyowa domin tabbatar da zarginta.
    Uncle G! Ne tsaye yana binciken wasu books saidai da alama bai gantaba, dan haka tak'ara k'asa da kai, bata buk'atar yaganta.
   sai dai ta makaro, domin kuwa tunda ya shigo da ita yafara tozali, ya basar ne kawai yanuna bai gantaba.
    Cikin takunsa na masu aji da gayu yanufo inda take zaune, hannu biyu yasa yadafe tebir d'in gabanta, tareda fad'in Assalamu alaiki?.
   Da sauri tad'ago dan batai tsammanin zuwansa ba.
  Ya ce, "bakijin sallama ??.
Cikin rawar murya ta amsa, ta d'ora da gaisheshi.
   Yaja kujera ya zauna yana fad'in ya ykk?
  Sopy taja numfashi tana fad'in lfy law.
  Ya ce, "good".
Kafin yayi magana wayarsa ta hau k'ara alamun kira, ya cirota daga aljihun gaban rigarsa ya amsa.
  Saida yagama wayarsa sannan yadawo da dubansa gareta, yayinda wasu d'alibai dake library d'in suke kallonsu.
   Ya mik'e yana fad'in kisameni a office inaso muyi wata magana dake, domin inaso naje gida wannan week d'in akan maganar aurenmu!!.
   Da sauri ta kalleshi, shima kallonta yakeyi, dan haka ta maida kanta k'asa, ya kwashi wasu takardunta data ajiye, ta daure ta ce, "uncle zanshiga lecture dasune fa.
   Yatafi yana fad'in nasani idan kinzo saiki karb'a ina jiranki karki b'ata min lokaci.
   Sopy ta dafe kai tana fad'in nashiga uku ni safiyya mutumin nan fa yafara shiga min hanci, yakamata na face shi, kanta ta maida ga karatu amma saita kasa karatun dole ta mik'e tafice, tadad'e tana tunanin zuwa office d'insa, dan gsky bataso azargeta akan yawan shiga office d'insa.
   Wayarta ta hau wringing, tad'aga tana mita.  
  Muryar uncle G! Taji yana fad'in ina jiranki fa!!.
  Kafin ta ce, "wani abu ya yanke wayar, ta dafe kai tana fad'in ya salam, dole ta daure ta nufi office d'in.
   Ta kwankwasa, ya ce, "shigo mana, dan yasan ita ce!!.
  Da sallama tashiga kanta ak'asa, yad'ago yana kallonta batareda ya ce komaiba.
  Jin yayi shiru, ta ce, "gani!!."
Ya ce, "aii naganki, ya maida kansa kan abinda yakeyi.
  Sopy tabishi da kallo cikin takaici, takardunta yake dubawa, taja k'aramin tsaki amma baiji ba, a zuciyarta ta ce, "kaidai kana son sakani cikin matsala, banason wani yazargeni wlhy.
   Ya d'ago yana fad'in wai bazaki zaunaba ne??.
   Ta ce, "nanma ya isa.
Ya ce, "okey nima bari nataso tunda yau tsayuwar kike sha'awa.
   Kafin ta ce wani abu yataso, ya k'araso inda take tsaye, jingina yayi ajikin bango ya hard'e hannayen sa a k'irji, ya dasa mata fararen idanunsa manya masu yalwar gashi.
   Ta k'ara k'asa da kanta dan ganin irin kallon k'urullar dayake mata, ya murmusa dan ganin yanda taketa sinne kai kamar wadda tayi k'arya, ya gyara tsayuwarsa, sopy!! Wai sai yaushe zaki kalli cikin idanuna ne, kunyarki tayi yawa fa.
   Hannu tasa ta rufe fuskarta.
 Yay dariya tareda fad'in okey to shikenan, dama inason nasar dake jiya da daddare naje gidanku!!.
    Ta zaro idanu, gidanmu kuma??
  Ya jin jina kai, e, gidanku, aii dama na ce, "miki bada wasa nazoba, yacigaba da fad'in, munyi magana da baba, nasar dashi komai nida kabeer, yakuma karb'eni fiye da zatona, yanzu haka yabani izinin turo iyayena! Sai dai ya ce, "bikinmu zaikai nanda watanni dan yanzu suna shirin bikin kabeer, amma bayan bikin kabeer da wata uku zuwa hud'u sai ayi namu.
    Sopy ta zame ta zauna a k'asa, bayanta jingine da k'ofa.
  Ya bita da kallon mamaki, ya daure ya ce, "yaya dai? Ko hakan bai mikibane??.
  Ta d'an kalleshi, ta girgiza kai.
Ya ce, "to miye matsalarki??.
Ta ce, "babu, ta cigaba da fad'in nasan iyayena bazasu cutar daniba, dan haka na amince da duk abinda suka yanke, kuma zan yimusu biyayya.
   Uncle G! Yaja ajiyar zuciya yana fad'in ALHAMDULILLAH!!, ya tsugnna a gabanta, ya ce, "karki damu safiyya!, kabeer ya sanar dani abinda yafaru dake a baya, tsakaninki da AMINIYARKI da kuma SAURAYINKI, to inaso ki manta da abunda yafaru a baya, ki gogeshi a arayuwarki, kid'auka yanzu zaki sake sabuwar rayuwane, ki yarda ni ne!! Zab'in alkairin da ALLAH yay miki, zan baki mamaki insha ALLAHU, Zan rik'e amanar da baba yabani taki kinji.
   Yaja numfashi, gobe idan ALLAH yakaimu kabeer zaizo, zai sanar dake sauran bayani, ni kuma jibi idan ALLAH ya kaimu zanje nasanar da iyayena, ya mik'a mata farin hankici daketa tashin k'amshi, karb'i ki goge hawayenki dan banason su zuba k'asa.
   Sopy ta karb'a dan ita bama tasan tana kukaba, saidai batasan kukan na miyeba?? Farinciki ko bak'incikin rabuwa da Abdul, tasan tabbas uncle G! Yafi Abdul komai kyau, ilimi, aji, da sauran abubuwa masu yawan gske, kud'i kawai mahaifin Abdul zai nunawa uncle G!, itakam bata d'auki kud'i wani abu mai muhimmanciba arayuwarta, dan itama talakace tib'is, tanada tabbacin samun nutsuwa a gidan talaka d'an uwanta.
   Jitai uncle G! Yana fad'in to kukan ya isa haka, inko bahakaba zan lashe hawayen dasuka sake zubowa.
  Hannu tasa tasa tarufe fuska tana dariya.
  Shima dariyar yayi, "wai yau miyasaki makara ne??
  Cikin sanyin murya ta ce, "karatun tarihinka mana.
Ya ce, "nice, hakan yayi nasan yanzu kinsan ni kowaye, ni talakane tib'is, sai dai rufin asirin ALLAH kawai, ina fata wannan bazai shafi auren muba ko??, Dan kinji wayeni dakuma inda nafito,  kinji su waye family nawa, zaki iya neman k'arin bayani a wajen kabeer, dan yasan komai a kaina. 
   Tai murmushi to aii nima talakace, nasan kuma kasani, tunda kana tareda uncle kabeer.
  Yad'an murmusa yana fad'in to shikenan ALLAH ya tabbatar mana da alkairi, amma daga yau idan kika k'ara makara a lecture d'ina tofa bayan horon hana shiga aji, akwai horo tsakanina dake, dan haka ki kiyaye, yafad'a yana mik'ewa.
   Itama ta tashi tsaye, to bari na tafi.
  Kai habadai tun yanzu, nifa ban gaji da ganinkiba!!.
   Hannu tasa ta rufe fuska ta ce, "aii munkusa shiga lecture ne.
Yay dariya to sarkin kunya, ga kayanki can jeki d'auka.
   Ahankali ta nufi tebir d'in sa, ta tattara takardunta ta kwaso zata juyo wayarsa ta hau wringing, ya ce, "taho min da phone d'ina!.
   Saida ta d'an rissina sannan tabashi tay waje da sauri,  dan batason yasake tsayar da ita.
   Yay murmushi, yana binta da kallo..................




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *