check your best novels here

Monday 20 February 2017

NI DA AMINIYATA!!! 32to36

[29/10/2016 20:04] bilyn Abdul: 30~October~2016


30~October~2016




NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM 




32

.........A garin GURUM su Sopy sun sami tarba mai k'yau, daga dangin uncle G!, Suma sunada kirki, ananma biki aka d'ora, da daddare matasa suka warware kid'in daya bama dangin sopy sha'awa, atak'aice an dai sha shagali.
   Washe gari bayan sallar azuhur dangin sopy sukayi haramar komawa kano, bayan an k'ara yima amarya nasiha da jan kunne akan sirikanta da dangin mijinta, suka tattaro suka taho, aka baro amarya tana kwasar kuka.
   Da k'yar gwaggo ta lallasheta dan ad'akinta suka barota, daga k'arshe gwaggo ta lallab'ata tayi barici, kunga sirikan kwarai masu tattalin matan 'ya'yansu.
   Libabatu ta gyara b'angaren da su sopy zasu zauna kafin sutafi, wato b'angaren uncle G! Kenan, acan gefe yake akatange babu ruwanta da sirikanta saidai idan sun shiga, gyara sosai tayi ma b'angaren, ta amshi turaren wuta wajen gwaggo taje takunna, tak'ara da da wasu turarurrukan data gani ad'akin, azuciyarta ta ce, "oh ni liba, kaga d'akin yaya kamar na mace, nan dai tagama tafito.
   Uncle G! Kuwa bayan yagama hidimar sallamar bak'i masu tfy, saikuma yashiga sabgogin sallamar 'yan uwa da abokan arzik'i dake nan, dakuma mammaida kayayyakin da'aka aro na mutane.
    Sai gab da magriba aka maida Sopy b'angarenta, aunty hafsa da kanta ta had'a mata ruwan wanka, Sopy ta ce, "nagode aunty!, aunty hafsat tayi murmushi bakomai k'anwata jekiyi wankan, dan muma tafiya zamuyi, lubabatu nacan tana jirana, sai da safe.
  " Sopy ta ce, "to ALLAH yakaimu.
 Bayan fitar aunty hafsa Sopy tashiga wanka zuciyarta cike da tunani iri-iri, tagama wanka tafito sukayi kicib'is da lubabatu, lubabatu ta ce, "to amarya muzamu gudu gida, sai gobe nazo cin kazar amarci, kifa ragemin.
   Sopy tayi d'an murmushi ta ce, "to.
    Libabatu tana tafiya sopy tashiga d'akin, tabi d'akin da kallo babu wani tarkace, katifa ce k'atuwa an lailayeta da zanin gado, sai wardrobe ta zuba kaya itama k'arama, sai kujera doguwa a gefenta akwai firij, saikuma wani tebir da kujera agefensa cike yake da littatafai, da alama library d'in uncle G! Ne, ba laifi d'akin yayi k'yau a talauce ba a sarauceba.
   Ta zauna tashafa mai tayi kwalliya mai d'an sauk'i,  wata atamfa tasaka siket da riga, sun kama jikinta sosai, ta ja k'aramin tsaki nikam bana son kaya su matseni, amma na lura duk haka aunty hauwa'u ta d'inka min kayana.
   Haka ta zauna tana gyaran kai tana mitar d'inkunan, nace ashe Sopy tanada gashi ba laifi, dan dai tana b'oyeshine, tagama ta gyara gurin, sannan tahau sallah, bayan ta idar ta zauna agurin har aka kira sallar isha'i, ta tashi tayi.
   Ta cire hijjabin kenan tanufi waje akwatin ta dan d'aukar k'aramin hijjabi wanda baikai girman wanda tayi sallarba.
   Uncle G! Ya shigo d'akin da sallamarsa, Sopy tarikice tarasa inda zata dosa, wajen akwatin ko kuwa wajen hijjabin data gama sallah yanzu?.
    Shima uncle G! Tsaye yake kam cikin farar shadda k'al yaukam harda hula, sai bulbula k'amshi yakeyi, fuskar nan tasa fayau da annurin angwanci, ya kasa koda motsi dan d'imautuwa da surar Sopy, ya tambayi kansa? wai dama haka sopy take da diri da cikakkiyar sura ta d'aukar han kali, lallai dolene ya godema ALLAHn daya halicci wannan k'ak'yk'yawar sura.
    Ahankali ya k'arasa gareta, tasaka hanu tana kare k'irjinta, ta rintse idanu danjin uncle G ya mannata da jikinsa, cak ya d'auketa ya dire saman kujera, shima ya zauna, kallonta yakeyi sama da k'asa kamar yau yafara ganinta.
   Itako kanta yana k'asa tana wasa da zoben hannunta, ta daure ta ce, "ina yini?, yaja wata sassanyar ajiyar zuciya tareda kama hannunta ya r'intse anasa.
  Jitayi tsigar jikinta ta tashi yarrrrrrr, yaune rana ta farko da namiji ya tab'a kama hannunta, ta runtse manyan idanunta.
   Uncle G! Yay murmushi, cikin muryarsa mai dad'i da amo ya ce, "kin wuni lafiya ??.
   Cikin jin kunya ta ce, "lfy law.
  Ya ce, "ya gajiyar biki??.
"Nanma saida tayi k'asa da kai sannan ta amsa.
   Ya ce, "my Sopy aii kuma kunya ta k'are yau, domin kin zama tawa nazama naki har abada.
    Ita dai tayi masa shiru, idonta arufe saboda tsananin kunyarsa datake ji, gashi kuma yak'i sakar mata hannu, ya matso da fuskarsa kusada tata, harsuna jin fitar numfashin juna, batayi aune ba taji ya manna mata wata k'yak'yk'awar sumbaa kumatu. (Kiss)
   Tayi wata 'yar girgiza dan sumbar ta shigeta har cikin kwakwalwa......................




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's

NI DA AMINIYATA!!!




NA BILKISA IBRAHIM 




33

...........ya d'an murmusa dan ganin yanda taketa kare k'irjinta, yasak'ala hannunsa ta bayanta ya rungumota zuwa jikinsa, aii sai jikin mutuniyar taku ya hau rawa, cikin kunnanta ya ce, "tsawon kwana goma kina b'oyema ganina, yau kuma gani daga ni saike!!.
  Ita dai jikinta sai rawa yakeyi, takuma kasa magana, ya hura mata iska a kunnenta, ta bud'e ido da sauri, yay murmushi, Sopy sarkin kunya yafad'a yana shafa jikinta, ya kuma matseta sosai ajikinsa, har saida tayi 'yar k'ara sannan ya sassauta mata, ya ce, "haba sopy yau baza a yima uncle G!; magana bane? Ko har yanzu fushin tafiyar su uncle kabeer d'in akeyi?, dan ya ce, "min har kukayi sallama kuka kikeyi, kokuma garinmune babu dad'i??.
   Sopy ta girgiza kai alamar A'a.
 Ya ce, "to minene yasa aka k'iyimin magana??.
   Ta daure ta ce, "ba komai kainane yake d'an ciwo.
   Uncle G! Yay 'yar dariya, to ALLAH yabaki lafiya Sopy na!, amma ko dai ana tsoron uncle G! ne??.
     " nanma ta girgiza kai batare da tayi magana ba"
  Ya mik'e yana fad'in shikenan idan anzo wajen kwanciya zamu gani.
   Gaban Sopy yafad'i rasss, bata san sanda hawaye ya zubo mata ba a kumatu, tayi saurin sharewa, itakam gsky tanada tsoro, ALLAH dai yasa karyay mata komai.
   Ledar daya shigo da ita ya d'akko, wadda santin ganin surar sopy yasakashi yarda ta ak'ofar d'aki, ya zauna yana lallashinta akan taci kazar dake ciki, da k'yar yasamu taci akunya ce, yana mamakin kunya irinta sopy, gsky da haka kowace mace take, da ansamu sauk'in lalacewar 'yammata kai harma zawarawa da matan aure, ALLAH dai ya shirya.
    Bayan sun gama cin kazar wadda rabinta duk shi yaci kayansa, dan yana jin yunwa sosai, tunda aka fara bikinnan bai nutsu yaci abincin kirkiba, yaje yay brosh ya dawo, itama taje tayo.
   Ya ce, "yana zuwa yanzu zai dawo.
  Yana fita ta tashi tacanja kayan barci a gurguje, wani zani tasaka da riga tishet mara nauyi, tasaka k'aramin hijjabi, tayi kwanciyarta bisa kujera.
   Ya kai tsawon minti talatin sannan yadawo, yarufe ko ina, yabi sopy da kallo yana d'an murmushi, ahankali ya furta safiyya sarkin tsoro, shima kayan barci yasaka, yad'an fesa turare.
   Wajen kujerar datake kwance ya k'araso, ya shafa kuma tunta yana fad'in my sopy aii duk wayon amarya sai ansha manta.
   Cak ya d'auketa yana fad'in kinga gurin barcinki nan ya nuna k'irjinsa da baki, saman katifar ya direta, tana jinsa amma tayi shiru, tak'iyin ko motsi dan tsoro da kunya.
   Yashiga k'ok'arin cire mata hijjabin jikinta, sai asannan ta motsa ta rik'e hannunsa.
  Yay murmushi mai sauti ya ce, "aii dama nasan idonki biyu.
   "Tai masa shiru"
 Ya ce, "okey aii nasan maganinki, bari kiga nasan yanda zanyi kiyi magana, batayi aune ba taji bakinsa cikin nata, duk iya k'ok'arinta na ta kwace kanta amma ta kasa, ta shiga tsungu ninsa, amma ina shikam baisan tanayiba, tsotsar bakinta yake cikin zafin nama, tamkar mafa raucin zaki, ayayin dayaga abinci, Sopy tun tana tsungu ninsa harta hak'ura tabarma ALLAH.
    sai da ya tsotse bakin tamkar zai rabata dashi sannan ya janye jikinsa yana maida numfashi.
  Sai a sannan Sopy tasamu bakin yin kuka.
  Ya rungumota tsam akan faffad'an k'irjinsa daketa tashin k'amshin turare, ahankali yashiga buga bayanta tamkar wata jaririya, cikin sark'ewar murya ya ce, "to kukan ya isa haka, kinga yi hak'uri ni babu abinda zan miki, yi barcinki kinji my sweet Sopy, cikin sigar lallaahi yake maganar, iska ya shiga hura mata a cikin kunne mai dad'i, ita kanta bata san sanda barci yay awon gaba da itaba, dama ga gajiyar biki.
   Shikam ya dad'e baiyi barcin ba, dan kuwa hanka linsa yakai k'ololuwar tashi, anya zai iya cika alk'awarin daya d'auka na barin Sopy har sai sun koma gidansu, yaja wani gwauron numfashi tareda sake manneta a jikinsa, sanda bashida matarma baidamu ba haka, amma yau kodan yaganta a kusa dashine oho, ya tsurama fuskarta idonu, tanata barcinta, dukda yasan barcin cikin tsoro da fargaba ta yishi, ya shafa kanta tareda sumbatar ida nunta yana murmushi Sopy sarkin tsoro yafad'a yana gyar kwanciya.
   Haka yayta sak'a wasik'ar jaki har barci yay awon gaba dashi.

Muma muka fito, dan komawa masaukinmu nida marak'isiyya, da madina, da aunty pii pii, da saratu, dan sunce ba inda zasu labari ya wucesu.
   Na ce, "magulmata saiku tsaya, nasan kuna bak'in cikin d'an abinda uncle G! Zai banine,  idan nagama yad'a labinsune, to kusani kad'an zan baku eheee .....................




Bily
Mrs Abdus'sala
I LOVE YOU MY FAN's
[02/11/2016 10:06] bilyn Abdul: 2~November~2016




NI DA AMINIYATA!!!




NA BILKISA IBRAHIM




34

........Da asuba yatashi yay alwala sannan yatada ita ya ce, "nawuce masallaci, kanta ak'asa ta ce, "to adawo lfy. 
   Bayan fitarsa itama alwalar tayo tayi sallah, ta d'auki alkur'anin data gani a d'akin tayi karatu, zuwa sannan gari yafara haske, harzuwa sannan uncle G bai dawoba, ta tashi ta gyara d'akin fes, tashare d'an lungun nasu ta wanke bayin sannan tashiga wanka.
   Uncle G yadawo motsin dayaji abayi ya tabbatar masada tana wanka, d'akin yashiga yashaki wani k'amshi mai dad'i ya lumshe idanu, yay murmushi mai k'ayatarwa ya ce, "lallai ina son mutum mai tsafta da rashin son jiki, gashi kuma ALLAH ya azurtani da samun mace, ALLAH nagodema da irin wannan tarin ni'imomi daka min.
   Batayi zaton yana cikiba, dan haka tashigo d'akin kanta tsaye, gabanta yafad'a yayinda taga uncle G zaune, takalli jikinta daga ita sai zanifa, ta faki idonsa ta rarumi hijjabin sallah ta rufe jikinta.
    Lamarin yayi matuk'ar bawa uncle G! dariya amma saiya gimtse ya ce, "yayadai ko kina jin sanyi ne?.
  Ta ce, "A'a".
 Ya girgiza kai yana murmushi, taso wa yayi yanufo inda take, aii tunkafin yazo ta durk'ushe k'asa, ya tallafota zuwa jikinsa, saman kujera ya zauna ya d'orata saman cinyarsa ya ce, "haba autar inna aii komai na Sopy mallakin uncle G! ne, kokin manta baba da uncle kabeer sun bani har abada?.
   Ta cusa kanta cikin hijjabi, tana mamakin uncle G wai dama haka yake?, wlhy da idan aka fad'a mata haka yake zata k'aryata, amma dan ALLAH jibi abinda yayi mata jiya da daddare, tamkar ba malamin taba.
   Jin tayi shiru saiya d'an girgizata, yasa hannu yacire hijjabin daga fuskarta ya ce, "Safiyya! wannan kunyar takifa tayi yawa, nikam zata hanani shan sharafin amarci, amma bari nafara rageta, yafara k'ok'arin kwance zaninta.
    Da sauri ta rik'e hannunsa tana fad'in plz uncle!  kayi hak'uri na tuba.
  Ya tsaya yana kallonta ya ce, "to kin yarda na shafa miki mai da kaina!.
  Ta waro ido waje tana kallonsa ta ce, "saikace wata jaririya?", ya lumshe manyan ida nunsa yana murmushi, aii kema jaririya tace, kafin ki haifa mana wasu jariran.
  Ta sinne kanta ak'irjinsa dan kunya.
   Sallamar dasukajine yasa ta tashi daga jikinsa, ta d'auki hijjabin tasaka, uncle G ya ce, "kowa nene yashigo, Aysha! tashigo da tire a hannu ta, ta dire sannan ta gaishesu, harta mik'e uncle G ya ce, "Aysha akwai ruwan zafi kuwa agidannan?,  zanyi wanka, ta ce, "e, yaya akwai wanda aka dafama baki na wanka, ya ce, "okey to d'auki botiki ki d'ebo min, ta ce, "to.
   Babu dad'ewa Aysha takawo masa ruwan wankan, yaje yay wanka, kafin ya fito tayi sauri ta shirya, yashigo yana fad'in sopy kedai bak'ya gajiya da hijjab ko? Murmushi kawai tayi batareda tace komaiba, ya shirya cikin k'ananun kaya, sannan sukayi karin kumallo.
   Dole ya fita don muta nen daketa zuwa ganin amarya.
   Haka rayuwa tacigaba da tafiya a Gurum sopy tana ganin soyayya wajen dangin mijinta da iyayensa, kowa sonta ya ke da son faranta mata, sai abinda takeso zata ci, uncle G kam aii yafi kowa nuna mata kulawa, kuma yanzu baya shige mata, dan yaga tana matuk"ar jin kunyarsa, shima yakula idan yaci gaba da shigemata tofa zai cutu, dan haka ya shareta ko wajen kwanciyama kaida k'afa sukeyi.
  Hakan yayima sopy dad'i kuwa, takan fita tsakar gida ta taya gwaggo aiki, da gwaggo tafara aiki ita kuma zataje ta karb'e, hakan yana k'arama gwaggo son sopy a zuciya, dan suna yabawa da halayen yarinyar itada baba.
  Da haka sati guda yacika suka fara shirin dawowa kano, saidai nakula sopy bata son dawowa dan garin yayi mata dad'i.................



Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[02/11/2016 11:34] bilyn Abdul: 2~November~ 2016



NI DA AMINIYATA!!!




NA BILKISA IBRAHIM 




35

.........WASHE GARI suka tashi da shirin tfy, uncle G! Yana kula da sopy bata son a tafi.
   Nasiha sosai baba da gwaggo sukai musu, dan sunce sopyma tazama d'aya daga cikin 'ya'yansu.

 " Haka yakamata surukai su rink'a d'aukar matan 'ya'yansu, bawai ki zauna kina kishi da matar d'ankiba, wannan ba dai dai bane, idan kika d'auketa d'iyarkima wlhy saitafi girmamaki da baki daraja, amma daga lokacin dakika fara kishi da ita, tofa rainine zai shiga tsakaninku, shima d'an naki yazo yana jin haushinki a baza awofi, ALLAH yasa mugane".

Sai bayan sallar azahar suka tafi sopy harda kuka, shi dariya ma take bashi, har sukazo tsanyawa tana kuka, daya kula idan ya k'yaleta ba bari zatayiba, sai ya fara janta da hira, tun tana amsawa ciki ciki harta ware tana kallon hanya da garuruwa, ya tsaya a bichi suka sha mai, sannan suka cigaba da tfy, ta ce, "to nan wane garine?, ya ce, "bichi kenan indai kinji ana fad'in bichi to itace wannan, A'a ni yauma natab'a jin sunan garin, yay murmushi kawai batareda ya ce komaiba.
   Gab da la'asar suka shiga cikin kano, ya ce, "yanzu ina kikeso mu fara zuwa? Kona kaiki ki gaida su inna?.
   Da sauri ta ce, "e, muje gidan su inna.
 Yad'an murmusa batare da ya ce komaiba.
   Ganin sun wuce titin layinsu ta ce, "munfa wuce uncle koka manta ne?, yad'an kalleta sannan ya maida kallonsa bida titi, na canja shawara ne aii.
  Saboda mi? Sopy ta tanbaya.
Ya dafe sitiyari da hannu biyu saboda naga kamar bai daceba ne, sun kaiki gidan miji kuma kin zo musu yanda suka kaiki, yakamata a samu canji.
   ALLAH sarki Sopy ita kam bata fahimci inda ya dosaba, amma ta lura kamar da wata fassara yay maganar, daga nan tayi shiru bata sake maganaba, shima dai bai kuma cewa komaiba, har suka isa anguwarsu.
   Gidan ma daidaicine, ginin talaka mai wadatar zuci, da kansa yafita ya bud'e get d'in sannan suka shiga, inda motar ta tsaya nanne kawai fili, daga ita kuwa babu abinda zai k'ara shiga koda mashin ne, suka fito ya ce, "Safiyya ga gidanki to.
  Sopy tayi 'yar dariya ta ce, "naganshi kuma yayi k'yau.
    Shima ma dariyar yayi yana bud'e but d'in motar ya sauke kayan duka, ya d'auki wasu yana fad'in namanta kefa makauniyace sai nayi miki jagora a gidan naki, itama d'auka tayi tabishi, yasa mukulli ya bud'e k'ofar falon, wani k'amshi ya daki hancinsu, suka ajiye kayan, ya ce, "zauna na k'arasa d'akkowa.
    Sopy tabi falon da kallo tana jinjina kai, lallai iyayenta sunyi k'ok'ari, falon yayi k'yau, komai acikinsa jaa da farine, kujerune set guda sai santa rok (center rug) atsakkiya kujerun shima jaa anmasa kwalliya da fararen fula woyi, sai tebir a tsakkiyarsa shima dai tare suke da kujerun, falon zagaye yake da labulaye suma jaa da fari, sai tv sitan  shima irin kujerun an d'ora filasma k'arama akai ta dai dai talaka.
   Takai dubanta a dani (dinning) shima ank'awatashi da kujeru da firij, idan bata mantaba ta dad'e da ganin kujerun dani d'innan a gidan aunty Nafisa an lillib'esu da wani k'yalle ashe natane, hawaye suka gangaro a kumatunta na dad'i, bata san da bakin da zata godema iyayentaba da yayyenta musamman ma uncle kabeer dan yafi kowa taka rawar gani acikin rayuwarta, dama yayyenta sunsha gaya mata saboda aurenta suke sana'a tabbas yau ta shaida haka.
    Uncle G! ya kamata ya zaunar saman kujera, dan tun d'azu yana kallonta, yasa hannu yana share mata hawayen fuskarta, ya ce, "Safiyya ba kuka zakiyi ba addu'a yakamata kiyima 'yan uwanki domin sun taka rawar gani a kanki, ko mak'iyi  yaga kayannan saiya jin jina musa, hannunta yakama yanufi kichin da'ita aii sai sukaga abin kallo yana kichin, lallai kicin d'innan ya tsaru nanama komai jaa aka tsara, ya ce, "ga sito d'inki ya nuna mata wata 'yar k'ofa, koda yake zomuje ki gani, suna bud'ewa kayan abinci suka bayyana uncle G! yasaki baki yana kallon ikon ALLAH harda su drinks yasan wannan tabas aikin uncle kabeer ne, uncle G ya rungume sopy cikin farinciki, ya ce sopy narasa bakin maga wlhy saidai muyita yima su baba addu'ar gamawa lfy, zomuje ki ida ganin ko ina.
   Bedroom d'inta ya kai ta, sannan sukaje nasa nanma ya had'u saidai nasa komai ruwan ganyene (green) kenan, ya zaunar da ita a bakin gadoyana fad'in Safiyya kinga gidanki sai dai k'aramine dan na talakane, a hakama nakai tsawon shekara hud'u ina ginashi, dan cikin albashi ake cire wani abu ad'anyi aikin, amma mun godema ALLAH da baiwar da yayamana ta rai da lfy, ahakama munfi wasu, ina fata zakizo mu had'a kai mu zauna kfy, mukuma yarda da k'addara aduk lokacin data riskemu, muyi hak'uri a lokacin da babu ta waywayemu, muzama masu wadatar zuci akan abinda ALLAH ya azurtamu dashi, mukuma gode masa.
   Arzik'i bashine rayuwa ba dan da wani arzik'in gara dawwama a talauci, nayi alk'awarin zan rik'eki amana, sannan ina rok'onki damuyi hak'uri da juna a yayin da muka samu sab'ani, mukuma fahimci juna alokacin da wani abu yashige mana duhu, na tabbata wannan zai taimaka mana wajen zaman aure.
   Sopy ta ce, "insha ALLAHU zaka sameni mai biyayya a gareka.
    Ya ce, "ALHAMDULILLAH.
yanzu tashi muje na rakaki d'akinki kid'an watsa ruwa ko?.
  Ta ce, "to......................




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[02/11/2016 14:20] bilyn Abdul: 3~November~2016



NI DA AMINIYATA!!!



NA BILKISA IBRAHIM



36

.........Har d'akinta yarakata, bayan fitarsa takuma k'arewa d'akin kallo, sannan tashiga wanka, tai murmushi dan ganin jininta yazo, lallai tayi farinci da faruwar hakan, tayi wanka tafito sai dai matsalarta d'aya batada always to yaya kenan zatayi?, tasan daga nan zuwa dare dole ta nemi mafita, inko ba hakaba zai rink'a b'ata mata jikine, tana nan zaune tana sak'a wasik'ar jakai saitaji sallama, ta fito da sauri tana amsawa, saitaga wata 'yar matsakaiciyar budurwace hannunta rik'e da kwando.
   "Yarinyar ta gaidata."
"Ta amsa cikin sakin fuska".
    Yarinyar ta mik'o mata kwandon dake d'auke da kuloli ta ce, "gashi inji aunty Asiya.
   Sopy ta ce, "aunty Asiya kuma?, wace aunty Asiya nasani anan anguwar?.
   Uncle G yafito sanye da jallabiya fara, yarinyar ta gaidashi, saida ya amsa sannan ya ce, "Asiya matar kabeer fa, aii bamuda nisa gidansu na nan k'asanmu.
   "Lah aii ban saniba".
 Ya ce, "na mantane nagaya miki, ni bari naje masallaci lokaci yana k'ara k'urewa, ta ce, "adawo lfy, yafita yana fad'in ALLAH yasa.
   Yana fita Sopy ta Cema yarinyar ya sunanki?.
   Ta ce, "sunana fatima amma anace mini ummy, nice name sopy tafad'a.
    To ummy dan ALLAH ina zaki sayo mini always ?, ummy ta ce, "aii akwai shago nan bayanku kawo na siyo miki.
   Yauwa ngd ummy 'yar albarka, taje ta d'akko mata d'ari biyar tabata ta fad'a mata irin wanda takeso.
    Babu dad'ewa uncle G yadawo, sannan sopy tana kicin tana d'auraye inda zasuci abinci.
   A falo yazauna ya kunna tv dan anhad'a komai, wannan duk aikin uncle kabeer ne, ummy tayi sallama ta shigo, ya ce, "O, baki tafiba?, ta ce, "e, aunty ce ta aikeni.
   Okey to kawo, ta mik'a masa ledar da canji ta ce, "bari natafi zanje islamiyyane, ya ce, "to ki gaishesu kice mun gode sosai ya mik'a mata naira d'ari, ta ce, "A'a, ngd, ya ce, "karb'i aii ni nabaki, ta amsa tana godiya ta tafi.
   Ya bud'e ledar dan son ganin minene aciki, ya ce, "tofa, abinda kuma yafaru kenan, ya ajiye yana fad'in an rusa mini show d'ina kenan.
   Sopy tafito da kayan filet, ta dire a saman tebirin dake tsakkiyar falon ta ce, "ga abinci ko akai dinning?, ya sakko k'asa yana fad'in aii ak'asama zanci, dan nagaji dayawa, saida tafara zuba masa abinci ya ce, "af, nama manta yarinyar ta ce, "tawuce gama sak'onki".
    Sopy ta ce, "to, ngd".
Tagama zuba masa farar shinkafar da miya da lemon kwakwa, sai salat.
  ya ce, "kefa?, ta ce, "sai anjima, harararta yayi, ya ce, "sa hannu muci kikuma cire wannan hijjab d'in kisha iska.
   Ganin ya d'an d'aure fuska, yasata bin umarninsa, ta cire hijjabin tazauna sunacin abincin, dukda tsakura takeyi kuma a kunyace takeci, bai kuma ce mata komaiba yacigaba da kallonsa yana cin abinci.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Da daddare ya tarar da ita a d'akinta tagama shirin barci harma ta kwanta, ya ce, "taso muyi sallah, saida tayi k'asa da kai sannan ta ce, "ina fashin sallah.
   Ya ce, "okey, dama ya tanbayane dan ya tabbatar.
   A zatonta d'akinsa zai kwana amma saitaga ya hawo gadon ya kwanta kusada ita, ya jawota jikinsa ya rungume, to ba yadda zatayi tunda babu damar korarsa, saita maida kanta ta kwantar akan k'irjinsa ta hau barci.

♡♡♡♡♡♡♡♡
Rayuwa mai dad'i akeyi agidan uncle G dukda har yanzu babu abinda yashiga tsakaninsu, amma suna mutunta juna kuma uncle G yana nuna mata soyayya, danma kunyarsa datakeji tana sashi k'in yimata wasu abubuwan.
   Kullum aunty Asiya saita turo mata kalar girkin daya dace tayi masa ta whatsapp, dan haka take girki mai dad'i da gamsarwa, ta kuma gyare gidan tsaf, uncle G yana jin dad'i dan yanason mutum mai tsafta, kullum sai tayi bak'i 'yan anguwar suna shigowa ganin d'aki da kuma amaryar kanta, kunsan amarya da farinjini, har yara da 'yammata ba a barsu abayaba, kuma duk wanda yazo saita kulla masa cin cin da dubulan, dan sopy bata da rowa, abokansama suna zuwa wasu harda matansu, su aunty Nafisane dai har  yanzu babu wanda yazo acikinsu, har aunty Asiya datake kusa, garama uncle kabeer yazo sau d'aya shima da daddarene, kuma bai dad'eba yatafi...............



Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
[02/11/2016 21:19] bilyn Abdul: 3~November~2016
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *