check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 21

AUREN K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

21 «******» umma tace oh kai bakaji a cikin tashin hankalin damuke cikiba??
Umma tashin hankali kuma waye ya mutu??
Cikin k'osawa da tanba yoyin abban husna, abban ikileema ya katseshi tobagarama mutuwaba da wannan mummunan labarin ba, Mansur ne yaje yola  aka d'aurama d'ansa aure da d'iyar alhaji muh'd.

Abban husna ya zaro idanu waje aure kuma yaya ?? Batare damun saniba? 
Kakyale matsiyaci zamuyi maganinsa ne, aizaizo ya samemu,

Umma tace nibama auren yafi b'ani haushiba, yanda saida burin mu yakusa cika sannan akai auren, suma wad'annan sakar karun yaran naku, har yanzun sun kasa d'aukar ciki saikace ba mataba,
 Baban husna yace yaya!!!  umma!!!  mizai hana mu shirya yanzun mu tafi yola ne wai tumma kafin akawo amaryar musa yasake ta acan? 
  Umma tace yaro dai yarone, ai wannan shawarar taka bata dace ba, mubarsu su iso aidai nasan bazasu wuce gobe ba kuma ku gargad'i matanku kar wadda tasanar dasu husna maganarnan, dan banaso su tashi hankulansu.
Sukace to shikenan, kowa yatafi gida zuciyarsa nazafi sai dai sund'an samu kwarin gyuywa dan sunsan halin mahaifiyarsu awajan iya makirci, sunsan zata samo musu mafita kafin gobe

***************%
YOLA :- washe gari bayan anyi walima da safe, aka rankayo kano kawo Munneerah, tanata kuka da far gabar abinda zata tarar gurin angon nata,
      ""Shi kam  angon nata camma suka baroshi sai karfe 5:pm ya biyo jirgi zuwa kano ,

Agidan su mom suka sauka dan sai anneawa amarya gurin zama, abinda yabama mom mamaki shine ganinsu maman ikileema wai sunzo tarbar amarya, saigasu abban husnama sun iso harda umma, shima dai dad abin yabashi mamaki amma saiya b'oye mamakinsa ya taresu da gir mamawa,da ban hakuri, yace suyi hakuri gobe zaizo gidan umma su zauna suyi magana,

Carab umma ta anshe ba komai yarona ALLAH yakaimu, ai mudasu alhaji muh'd duk d'ayane, ALLAH yasa alkairi yasa rai akaiwa.
     "Sukace amin"
Yanayin yanda tayi maganar ma kawai yasa mom ta harbo jirginta amma batace komaiba sai dai azuciyarta tanemi tsarin ALLAH daga dukkanin sharrinsu.
To shima dai dad haka take agurinsa bawai ya yarda dasu bane, to ALLAH ya tsare mu 'yan uwa da wannan irin hali na yaudara........

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *