check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 26

AUREN  K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim

26 «*****» dady ya shirya ya nufi gidansu dan yau za'a kawo amarya, bayan ya gaida mutane ya haye saman dad  mom ma tana can, ya dur kusa ya gaishesu, cikin fara'a suka amsa, cikin dariya dad yace zonan babana, dady yaje kusa dashi ya zauna, dad yashafa kansa babana kana fushi damu ko ??
   "Dady yad'ago cikin murmushi yana kallon dad, ya girgiza kai dad danmi zanyi fushi daku mikuka yimini, ya cigaba wallahi dad bana fushi daku,ko kad'an kawai na d'auka wannan yana cikin K'ADDARA ta ne, dan haka dan ALLAH ku daina damun kanku, ni yanzuma nazone akan maganar inda za'akai Munneerah ne??
   " dad yay dariya to shikenan babana ALLAH yayi maka albarka ya baka 'ya'yan daxasu yimaka BIYAYYA kamar yanda kayi mana""
   "Amin mom ta amsa"
Dad ya d'akko mukullaye da yawa ya mik'awa dady, cikin rashin fahimta dady yake kallon dad, dad yace karb'a babana wannan makullayen gidankane, dake HOTORO, a SAKKOTO ROUND,
angama zuba ko mai sai kaje kasanar da matanka su shirya yau sukoma, zuwa anjima kuma akawo maka sabuwar amarya.

Dady ya mik'e ya rungume dad yana godiya, ya koma ya rungume mom itama su duka dariya sukeyi dan yau sunga farin cikin d'ansu tilo namiji dasuka dad'e basu ganiba.

Dad yace kar kadamu babana zan iya yimaka komai arayuwa matsawar inda shi dan nima kan mini BIYAYYA, dady yace to dad saidai fa su ikileema basanan, d'azu umma tazo itada jabir sun tafi dasu kuma wallahi dad bazanje nadawo dakowaba tunda bani nace su tafiba

Mom da dad suka dubi juna har suna had'a baki wajan fad'in umma kuma??
"Dady yace eh"
Dad yace karka damu anjima zanje gidan umman da kaina, yanzu kaje kagano tsarin gidan idan yayi maka.
  "Dady ya mik'e yana godiya yatafi.
 Dad yace kinga abinda nake gaya miki ko bilkisu nasan akwai wani kulli azuciyar su yaya amma anjima zanje gidan, mom batace komai ba sai ALLAH ya kyauta kawai ta mike ta fito......

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *