check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 40

AUREN  K'ADDARA.    
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 


40 «******» tafara k'ok'arin kiransa, saigashi kiransa ya shigo, jiki a mace ta d'aga cikin sanyin murya tai sallama??
Yakai tsawon second, goma bai amsaba, tasake yin sallama akaro na biyu, saida yaja ajiyar zuciya sannan yace wa'alaiki, cikin muryarsa mai dad'i,
Tace dan ALLAH yaya kayi hak'uri, kakirani ban d'aukaba ina kichinne, wayan kuma tana bedroom, 
nanma yaja lokaci bai amsaba, 
Saican yace ya jikin naki??
   "Dasauk'i ta fad'a"
   "Maran naki ya daina ciyon??
 "Cikin jin kunya kamar tana gabansa, tace ya daina"
To shikenan ALLAH yak'ara sauk'i"
    "Amin ta fad'a asanyaye"
   "Yaya ka aiko akarb'i abinci nagama tun d'azu"
       "Amma banace karkiyi komaiba ki kwanta kihuta keda bakya jin dad'in jikinki??
Kayi hak'uri yaya aina samu sauk'i".
     "Yaja nummfashi !!!, to shikenan zan aiko salisu ya karb'a idan mun fito sallah"
To sai yazo, saida tabari ya kashe sannan itama ta kashe.

Dady ya jin gina da kujera ya lumshe idanu, ya bud'e ahankali waishi mike damunsane, akan yarinyar nan??
Yakuma lumshe idanu
 Zuciyarsa tace kakamu da sonta ne, yazaro ido kai so kuma, canza dai zuciya ya za'ayi naso wannan 'yar shilar yarinyar, duka yaushe tazo duniyarma, kawaidai ina girmama tane dan hidimar datake yi dani.
  Amma batakai nasota ba.
Ya bud'e idanunsa ahankali danjin anamasa magana, Dr Anuwar yace a'a my friend lafiya dai, nazatama kayi alwalah, ashe kanana kana tunani, miye damuwarka??
 Dady yaja ajiyar zuciya yana mik'ewa, bakomai, inadai hutawane, ya shige bayin dake office d'in batare daya jira amsar Dr Anuwar ba.
Dr Anuwar ya girgiza kai yana binsa da kallo, bayan ya fito suka wuce masallaci.

Salisu masinjansa yaje ya karb'o masa abinci kamar yanda ya saba.......

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *