check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 22

AUREN K'ADDARA
              Ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim

22 «******» dady yana isowa gidansa yanufa kai tsaye, sai dai yana farga bar abinda zai tarar duk da ba son matan nasa yake yiba, amma yasan ba abinda mata suka tsana irin kishiya,tunda gasunan su biyu ma ya aka k'akare bare an k'aro ta uku,

Haka dai ya sauka daga motar da ya d'akko haya daga air port, yabiya kud'in sannan yanufi gidan, sun gaisa da mai gadi, sannan ya wuce cikin gida.

Cikin sanyin jiki ya tura kofar palon ya shiga da sallama, ikileema ce kad'ai apalon  take karatun littafi,amamakin sa sai yaga tazo ta tarbe shi, harda dariya tana masa sannu dazuwa ya amsa fuskarsa ba yabo ba fallasa, yasan dai labarin auren sa yazo musu, ya kalli palon kaca kaca, da alama tunda yabar garin ba agyara palon ba.

Ya d'akko key ya bud'e d'akinsa, suka shiga,  kamar daga sama husna tafad'o ko sallama babu, ta fisge jakkarsa dake hannun ikileema, malama ince dai yau kinsan nice dashi, amma dan tsabar muna finci kikaje kika tarosa.
Ikileema tace waike husna wacce irin dabbace ne, aiba gado d'aya kika gammuba, bare kice anacin amanar ki,
Husna ta harzik'o kin san ALLAH kika k'ara cemini dabba sai naci uwarki anan gidan banza jaka.

Dady ya daka musu tsawa kun ga, dan ALLAH ku barni nahuta daga fa anguwa nake amma ba wadda tabani ruwa bare abinci, amma kun tarbeni da masifarku dakuka iya, kwana biyunnan dabana gidannan har na fara k'iba, amma daga dawowa ta nafara karo da jarabar ku,
 Husna tai fari da idanu kayi hakuri honey ai gara nako yama wannan shegiyar hankali.

Ikileema tayi dariya yo husna ko uwarki ta isa ta koya mini hankali bare ke,
Dady yace ALLAH in baku yimini shiruba zan b'ata muku rai, ya shige bayi abinsa, ikileema kuma tafice tabar husna......

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *