check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 54 to 58

AUREN  K'ADDARA
              ko  BIYAYYA

Na billkisa ibrahim 

54 «*****» dakansa yagasata tana kukan shagwa6a, shikuma yana aikin lallashi, ya taimaka mata tayi wankan tsarki, atawul yanad'ota kamar wata jaririya, yadire ta akan gado, riga yaska mata tai sallah shikuma yanufi kichin.

Break ya had'o mata mai sauk'i, ta idar tuni harta kwanta akan sallayar, tafara barci, yatada ita yabata, kad'an taci tace ta k'oshi, bai takurataba tunda lalla6ata yakeyi, yabata magani tasha suka koma kan gado, yarungume matarsa suka lula duniyar barci.


Sai k'arfe 11:am suka tashi Munneerah ta shiga wanka, shima yatafi d'akinsa domin yin wankan, dukda batajin dad'in jikinta haka ta daure tagyara d'akin fes,ta kwalliya mai sauk'i, tana fesa turare ya shigo jikinsa sanye da wando iya guywa, da k'aramar riga tashan iska ya rungumeta ta baya my beauty kinyi kyau, ALLAH yabani baby mai kama dake, tasa hannu tarufe fuska, yay dariya cikin kunnan ta, ai yanxu my beauty babu xancen kunya ko, ita dai hannunta yana kan fuskarta tanad'an murmushi, yakama hannunta zomuje kiyi break ko??
    "Yaya break kuma waye ya dafa?
"Ya d'anja hancinta daga gidansu mom aka kawoman, ta zaro  ido waje , ginsu mom kuma yaya?
shima yazaro ido yanda tayi eh gidan su mom my beauty, haba yaya maimakon katasheni na girka"
    "Yaja hannunta suka nufi falo yana fad'in waneni dasaka my beauty aiki a wannan rana mai tsada, ai yau ranarkice, my Angel.

Dakansa ya bata break d'in, kai jama'a yau naga tattali da tarairaya, iri iri da salon so.

~~~~~~~~~~~®
Hakarayuwa tacigaba da tafiya agidan dady, suna zuba soyayya kamar zasu cinye junanasu, sun iya tattalin junansu, wannan yasa kishiyoyinta auka k'ara tsananta kishi akanta dukda atsakaninsu ma babu zaman lafiya kullum fad'a kamar kaji, gashi kullum iyayensu suna k'itsa musu mugayen halaye, iyayensu mazakuma kullum burinsu tayaya zasu mallaki dukiyar dad, shikuma su kaudashi a doron k'asa........


billy
{Mrs Abdus'salam}
AUREN K'ADDARA
                ko  BIYAYYA

Na billkisa ibrahim

57 «****» Munneerah dai ciwo yak'ara karfi harsaida ta kwanta asibiti 2days, ciki ya bayyana d'an wata biyu.
 Karkuga murna wajan dady, za'asamu d'a, mom kullum tana hanyar gidan dan duba Munneerah, dad ma yazo dubata sau uku, shima yayi farin ciki zai samu jika, daga tilon d'ansa namiji, mai kuma biyayya agareshi.
Mutanan yola dai basu saniba, su ikileema kam jin maganar cikin nan yatada hankalin su, suda iyayensu, da kakarsu, sunanan sun bazama bin malamai da bokaye, dan a6ararda cikin, 

Mom tace yadawo da'ita gidansu, sai cikin yayi kwari, tadawo, dady  yad'an sosa kai, mom, idan tataho wazai rink'a yimini abinci??
   "Mom tayi dariya, babana indai dan abincine kullum zamu rink'a dafawa da kai anan, kuma baga ma matanka nanba, ai suma zasu rink'a dafa maka""
Dady yakuma sosa kai to mom aikuma........ sai kuma yaya shiru.
  """Sai kuma mi?? babana k'arasa mana"
       "Yatashi yafita yana dariya.
Mom ma dariyar takeyi, ALLAH ya shiryaka babana.

Yola.... matan su sadiq ne suka haihu suduka, dady yace Munneerah ta shirya suje.
Aiko tadaka tsallen murna ta ruk'unk'ume shi, yarik'eta sosai, ke bi ahankali  baby na baiyi k'wariba, karki zubarmin.

Kai yaya ina murnanefa, ya sumbaci bakinta ai bakinkine murnar, saima afasa.
Tashagwa6e fuska yi hak'uri yayana na bari.

Ranar juma'a suka tafi yola, harsu mom, da 'yan biyu , suna a air port, Munneerah taga mai agwaluma,

Tace" yaya dan ALLAH kasiya min,
Yace" mizan siya miki??
Tace" agwalu6a, yay dariya agwaluma sunanata ba agwalu6a ba.

Mom tace,  kairat taje tasiyo mata.
Dady yaja hancin ta, babyn nanfa yacika kwad'ayi.
Mom tayi dariya, to ai babana cikinka ya biyo, lokacin da'ina da cikinka, haka narink'a kwad'ayinnan, ai har namafi Munneerah.
 Gabad'aya suka sa dariya har kairat data sayo agwaluma,

Badad'ewa yad'aga zuwa yola.

Sun sauka yola gidan su Munneerah, dagudu Munneerah tashiga cikin gida tana ihun kiran ummanta, ummanta tafito daga bedroom d'inta tana fad'in muryar wa nakeji kamar autana,??
Taje tashige jikin umma, umma tarungumeta sosai tana murnana ganinta.

Su mom suka shigo sunama Munneerah dariya, umma tasaketa tana fad'in, a'a kice hardasu haj. Bilkisu, nan suka zauna ana gaisawa, dandanan aka cika musu gaba da kayan ciye ciye.

 Mama kishiyar umma ma tashigo suka gaisa, dady kam tuni ya wuce wajan abokansa, suna can gidan jafar anata kwasar hira,Bayan sun gama suma suka nufi gidan masu jegon.

Gidan su jafarne k'arshe, su Munneerah suka shiga palon yayan nasu dan sugaishe da su, suka gaisar dasu suka fito.

Safwan ya kalli dady, brother naga 'yar yarinyaka kamar mai cikifa??   
       "Dady ya hararesa to d'an sa ido wayakai idonka gurin"
Gaba d'aya sukasa dariya.
 Jafar yace d'an uwa yaushe ka afka,?hardasu tsaraba, kace kwallonka tashiga raga.
Dady yace daga kai sai mai tsaron gida na buga ai, suka kuma saka dariya suna tafawa.....

~~~~~~~~~~~~~~~

 Dan ALLAH kuyi hakuri wlh banida isashshiyar lfy, shiyasa 2days banyi tpy ba, yauma kad'anne, amma zuwa anjima idan naji karfin jikina zankuma turowa, FORGIVE ME MY SISTER's 

billy
{Mrs Abdus'salam}
AUREN  K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 


58 «******» washe gari akayi sunan yaran, yaron ya sadiq, yaci sunana muh'd, sunan baffa kenan, yarinyar ya jafar kuma, khadija, yaron ya safwan, muddansir.

Da yamma akai shagalin suna gabad'aya a gidan baffa masu jegon suka dawo, dankar arabama mutane hankali, dangi duk anhad'u ana barkwanci, anty lubna ta kalli Munneerah, tace auta 'yar yarinyar Abdul, kokema RAINON NAKI YAKEYI??

Anty zainab, tace wana raino kina ganin ciki anty lubna, Munneerah tasa hannu tarufe fuska saboda kunya, kai anty nibani dakomai fa.

Anty jidda tai dariya ko auta ?
 Munneerah tad'aga kai tana rufe da'idanunta.
Ana cikin haka saiga ya safwan da dady sunshigo.
    " anty lubna tace yauwa k'anina dama kai nake nema.
   "Dady yace to anty aigani"
Ta nuna masa Munneerah dama canayi ashe mun samu k'aruwa??
  Yay dariya yana sosa k'eya, kai anty kina neman magana dai kawai", suka kwashe da dariya duka d'akin.
Dady yakamo hannun Munneerah, kinga taso my beauty, dama kenaxo nema.

Dariya sosai 'yan d'akin suke musu, shiko yaja matarsa suka fice, d'akin ya safiq nada suka tafi, suna shiga ya rungume abarsa, yana wani maida numfashi, da sauri da sauri, my beauty  I MISS U""
     "I MISS U 2, my yaya"
Yacurota daga k'irjinsa, ya sumbaci goshinta, nifa yakama acanxa mini wannan yayan gsky.
  Ya xauna bakin gado ya zaunar da'ita akan cinyarsa,yana shafa cikinta, my lovely children ykk,  2days bamu ganaba ko??
 Kai yaya saikace suna jinka, kuma ancemaka yara 2 ne??
  ""Ya sumbaci bakinta, ai insha ALLAHU yara 2 ne, a wannan cikin""
   Tai dariya to ALLAH yasa"
Yace amin.

 Ta yunk'ura zata tashi yaya bari natafi kar suga na dad'e.
Ya rik'eta sosai kar suga kin dad'e ?? Bawajan mijinki kika xoba, ni nanma dakike gani da uxuri naxo.
 Taxaro ido yaya!!!
   "Yaja hancinta, na'am k'anwata!!! Ya akayi ??
  Kai yaya wlh nidai kunya nakeji, agidan mutane.
Yay dariya, my beauty yaukuma kunyar mutane xasu hana asamu lada, tasa hannu ta rufe ido  a'a wlh yaya bahaka bane.
     "To yayane my beauty"
Nidai ina ganin kamar baidace bane kawai.
  Yay murmushi to shikenan yanxu kinyarda idan anjima naxo nad'aukeki muje gidan sadiq.

Kai yaya kayi hak'uri mana harmu koma gida.
  Yazaro ido a'a my beauty kema kinsan ALLAH bazan iyaba.
 Tai murmushi to shikenan ALLAH yakaimu, tafad'a tana yink'urin mik'ewa.
Yakuma rik'eta sosai saikuma ina ??
Tai d'anyi far da idanu, zan koma wajan dangi mana.
 Ya rungumeta sosai ajikinsa, haba my beauty, aikya bari nad'an ragexafi ko??
  Bayanda ta iya dole tabarsa yagama luguyguy tata sanransa, sannan ya rakata har k'ofar falon ya wuce..........



billy
{Mrs Abdus'salam}
AUREN  K'ADDARA
               ko BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

56 «****» hannu tasa tarufe fuskan ta , kai yaya ni bani dakomai,
Yakama hannunta yana dubawa, kai my beauty gsky ban yardaba, akwai ajiyana acikinnan naki, yafad'a yana shafa cikinnata.
     ""Ta k'ara tura kanta cikin k'irjinsa tana wata 'yar darya, wadda yakejinta har cikin tafin k'afarsa, yaja ajiyar zuciya, yana k'ara manneta dajikinsa, har saida tad'anyi k'ara.

Kinga tashi muje d'akaina na dubaki, dan nasan irin maganin dazan baki.
Ta mik'e cikin sanyin jiki, dan itama tayi laushi,suna fitowa saiga husna tafito daga b'angaren ikilima, 
Munneerah tafara k'ok'arin kwace hannunta dagana dady, shiko yak'i sakin hannun,
      "Husna ta kallesu taja tsaki, da sauri dady yace wakikema tsaki??
       "Husna tace wanda ya tsargu mana""
Yafara k'ok'arin kwace hannunsa dagana Munneerah, zaikaima husna duka, Munneerah tarik'eshi sosai yihak'uri yayana, dukan mace babu kyau, kaifa mai hak'urine, minene tsaki dahar zai b'ata ranka, tasumbaci hannunsa, kaga muje kadubani,taja hannunsa suka nufi b'anharan sa.

Dagudu husna tanufi 6angarenta tana kuka, wai ita yazatayi da wad'annan tsinannun matanne, tasan tana son dady, tana kuma kishinsa, bakama shegiyar Munneerah d'innana wlh ta tsani yarinyarnan, tayi alk'awarin sai Munneerah tabar gidanana, itada ikileema, dan Abdul'aziz natane ita kad'ai, 

Koda suka shiga d'akin Munneerah rarrashin dady tak'arayi, tare dafad'a masa magana mai dad'i, daga nan akazarce soyayya, saida suka soyu a soyayyar, sannan ita Munneerah ma abin kunya yabata, shikuma yashige bayi yana mata dariya.

"Ya fito,"
Yace" tashi kishiga wankan.
Tatashi tana kare fuska, tashige bayi,
Ya girgiza kai yana murmushi, my beauty sarkin kunya, ALLAH yasa ki haifa mini yara masu irin halayenki k'anwata, nagodema dad, da mom, da baffa dasuka za6a minke amatsayin mata, ALLAH yasada su da aljannarsa.


Tafito d'aure da guntun tawul, yabita da kallo, saiyaji wata sha'awar ta kuma bijiro masa.
Itama tad'an kalleshi, ganin ya tsuruma idani yasa tad'au hijjabin sallarta dake d'akinsa tarufe jikinta da sauri, dantasan k'arshen zancen.

Ya lumshe ido, yana d'an murmushi........

billy
{Mrs Abdus'salam}
AUREN  K'ADDARA
               ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

53 «******» to ALLAH yasoku ban makaraba lokacin dana isa gidan, ko masu gidan basu tashiba, dama ba'a saka su husna alayi, dansu tashi yin sallar asuba baya cikin tsarinsu, ko k'arfe tara suka tashi zasuyi sallarsu ne.

Sashin Munneerah nanufa, dan nasa acan zan samo rahoto, mai gamsarwa.
Dady ne zaune kan sallaya da'a lama yau agida yay sallah, yana zaune yana karatun,"ALKUR'ANI MAI GIRMA"  bayan yagama  yay addu'a ya tashi, gadon yanufa yana murmushi, Munneerah tana k'udindine cikin lallausa bargo, tanata barcinta, yasa hannu yagyara mata gashinta daya rufe mata fuska, ya sumbaci idaninta dake lumshe, gashin idonta gaxar gaxar gashi bak'i, tad'an motsa kad'an.
  "cikin muryar nan tasa mai d'ad'i yace my beauty  'yar rigima..

Cikin kunnanta yace my beauty!!! tashi kiyi sallah, kinga kina k'ara makara, tasa hannunta dasauri ta toshe kunnanta,yacire hannun yana fad'in places, ta bud'e ido ta lumshe, yamik'e yana fad'in inazuwa, bayin yashiga yahad'a ruwa mai zafi yasaka detol aciki,sannana yadawo wajanata.
  
Yad'agota tashi muje kinji autar baffa, tafara kukan shagwab'a yaya please kabarni barci nakeji.
      "To tashi idan kinyi sallar basai ki koma ki kwanta ba, takuma  kwanciya.
   "yace okey bari nahawo gadon sai ak'ara irin najiya, dan nakula baki gaji ban....
  Aikafin ya rufe baki ta mik'e zaune, ya d'auketa gaba d'aya yana dariya, kedai matsora ciyace my beauty, itakam tasa hannu tarufe fuska........


billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *