check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 23

AUREN K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

23 «******» ikileema har ta fita tadawo ta zauna,
Dady ya fito wanka ya kalli matan nasa dasuke  ta harare harare,
Shikam wataran dariya suke bashi, tamkar ba 'yan uwaba,kuma k'awaye masu matuk'ar so da k'aunar junansu, yay murmushi, sannan ya fara shafa mai, ya gara sumarsa, jalla biya yasaka yace musu zaije masallaci, yafice abinsa batare daya jira amsarsu ba.
Yana fita suka hau danbe kamar dama jira sukeyi ya fita.

Daga masallaci gidan su ya wuce, gidan cike yake da dangi anata hidima, ya shiga sunata gai suwa da mutane, kai tsaye d'akin mom ya nufa dan bai ganta apalon ba,ba kowa ad'akin sai Munneerah dake bakin gado zaune,daga ita sai zani d'aurin k'irji, da alama wanka tafito, tana k'ok'arin bud'e akwati dan canja kaya amma sai fama take da key d'in yak'i ya bud'e,
Shikam ya tsaya yana kallonta, jitai ajikinta ana kallon ta, dan haka ta d'ago da sauri, ta kalli inda take zaton mai kallonta yake, da sauri ta rarimo gyale ta lullub'a dashi dan ganin dady yana mata kallon kurillah.

Baice komai ba itama ta maida kanta taci gaba da k'ok'arin bud'e akwatinta, a han kalli ya k'arasa wajanta, ya d'ora hannunsa akan nata batare da yayi maganaba, yazare key d'in daga hannunta ya dur kusa gaban akwatin yana bud'ewa, tad'an saci kallonsa kad'an ta kauda kai, mutum kullum fuska ad'aure kamar wani soja.

Mom ta shigo d'akin tana fad'in a'a babana kaine?
" yajuyo da sauri yana kallonta ya d'an sosa kai nine mom"
"Ina kika shigane"
 "Tace ina kichin ana k'ok'arin had'ama bak'i abinci"
 Ya mik'e daga gaban akwatin daya gama bud'ewa yana fad'in to sannunku da k'ok'ari.
"Mom ta zauna tana fad'in yawwa babana.
Shima ya zauna kusada Munneerah abakin gado,
     "Mom ta kalli Munneerah, Munneerah har kinyi wankan??
"Tace eh mom nayi"
       "Yawwa kinga yanzun zakiji k'arfin jikinki"
Mom.tace ai garama dakazo dama bata da lafiya kaga saika dubata, ya d'an kalli Munneerah miya ke damun ta?
 "mom tace zazzab'ine''
  "Tasamu  paracetamol tasha, kawai zai sauka gajiyar tafiyace,
To shike nan bari taci abinci.

Babana karfe nawa kabaro yola?
Wlh mom sai k'arfe biyar nataho ina zuwa nasamu jirgi, gashi harna je gida nayi wanka,

Ya kalli Munneerah dake sallah to mom yanzu yaza ayi??
Itama mom ta kalleta to sai dai mujira muji abinda dad d'inku zaice ko,,
To shikenan zuwa gobe zan samu dad muyi magana dan nasan yau yagaji danni ko ganinama bazaiyiba, nima d'in zuwa zanyi na kwanta duk nagaji, yinwace ma ta kawoni gidan,
Mom tace to bari na kawoma abincin.
Bayan fitar mom dady ya kalli Munneerah data idar da sallah tun d'azu, amma takasa tashi,
Waike bazaki cire wannan hijja binba, ko zafi bakyaji, tace ai bangamaba, ya tab'e baki, mom tace ya akayine, yace mom naga tun d'azu ta idar da sallane, amma tak'i tashi ta cire hijjab d'in,
Mom tai dariya to ai kasan Munneerah da kunya.
Yace to mom kunyar wa zataji anan ai mu ba bak'inta bane, ya d'auki abincinsa ya hau ci,.........


billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *