check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 31

AUREN  K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

31 «*****» tunda yadoso b'angaren nata yakejin k'amshi yana bugosa, ya tura kofar falon ya shiga, yashak'i dadda d'an k'amshin ya lumshe idanu, tare da fad'in ya SALAM, yabi palon da kallo yay murmushi yana nufar kofar bedroom d'inta.

Tana tsaye ga ban madubi tana saka lip stick abaki, jin anturo kofa yasata saurin juyowa tana kallon kofar, shima tsaye yake k'yam yadasa mata fararen idanunsa yana mata kallon sama da k'asa, sanye take cikin farin material da d'igon d'igon ja tayi kyau sosai.
" ta zame kasa ta durkusa, yaya ina kwana??
       "Cinkin sark'ewar murya yace kin tashi lafiya??
       "Tace k'alau"
Ya k'araso cikin d'akin yana tanbayar jakkar aikinsa ??
Taje ta d'akko masa saida ta russina sannan ta bashi.
   "Yace to ni bari nawuce aiki ya fad'a yana kallon agogon hannunsa"
     Har ya juya zai tafi, tace yaya !!!
   "Ya juyo yana kallonta ba tare dayayi maganaba"
  Dama.......sai kuma tayi shiru batare data k'arasa fad'a ba
   "Yace ina saurarenki"
 Cikin rawan murya tace dama cazanyi bakayi break ba zaka fita, gashi kuma har na had'a tun d'azu.
      "Cikin mamaki da al ajabi yake kallonta sukaima juna kallon tsakkiyar ido, tai saurin janye nata dan bazata juri kallonsaba"
  "Ya b'oye mamakinsa, yace to muje kibani, dan ina saurine, inada tiyata karfe  11: 30am ya kalli agogon hannunsa gashi har 10: 38am  tayi.

Yay gaba tana binsa abaya, taji dad'i da zaici, dan ita atunaninta zaice bazaici abincintaba tayi k'arama, kamar yanda yakebfad'a
Suka k'arasa wajan tebirin cin abincin yaja kujera ya zauna, ita kuma tafara zuba masa abincin, k'amshin ya daki hancinsa ya lumshe idanu,tare da had'iyar yawu.

Ta gama ta tura masa kofin shayin da filet d'in gabansa, ta mike zata bar wajan 
        Yace, "k" zonan !!!    
  "Wani haushi ya turnik'e ta ta tsani ace mata  "k" amma ta kula shi wannan d'an latsin rainin wayon yana neman maida mata suna haka"
     "Wai ko bakijini bane?
  "Ta dawo da tace  gani"
Ya nuna mata kujera, sannan ya d'auki kofi ya had'a shayi, tana zaune tana kallonsa .
Yak'are had'awa ya mik'o mata , tasa hannu ta karb'a, ya d'auki cokali yasaka cikin filet d'in data zuba masa abincin, oya bismillah, dole taci dan tana tsoron wannan d'an hayak'in.

Bayan sun kammala ya mik'e, itama ta mik'e ta d'auki jakkar aikinsa.

Har wajan motarsa tara koshi, ya bud'e ya shiga ita kuma tazagaya d'ayan b'arin tasaka masa jakkar, ya tada motar, tad'an lek'a tace ALLAH ya tsare ya bada sa'a"
 Yay d'an murmushi batare da yayi maganaba yaja motar ya fice bayan sun gaisa da mai gadi...

billy
{Mrs Abdus'salam}

Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *