check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'KADDARA ko BIYAYYA?? page 20

AUREN K'ADDARA
               ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim 

20 «******» KANO, kano dai basusan ahagalin da ake cikiba, sunsan dai ana biki agidan su mom, dan abban Sadiq baffa Muh'd saida yagayya cesu, amma suka kawo uzirin suna da ayyuka ranar,
Sai bayan an d'aura aure wani magul maci yakira abban ikilima, wai ya baigansu wajan d'aurin auren d'ansuba Abdul'aziz? abban ikileema yace a'a ai banda Abdul'aziz yaran alhaji muh'd ne zasuyi aure,
Mai gulma yace a'a kadai bincika amma tabbas harda Abdul'aziz naji an d'aura ma aure yau.
 Ahauka ce abban ikileema ya kashe waya yanufi cikin gida dama aharabar gidan yake tsaye, ya danna kai cikin falon matarsa batare da yayi sallama ba,
Zumbur maman ikileema ta tashi tana fad'in alhaji lafiya kuwa?
Inafa lafiya yafad'a cikin k'araji, wai mu Mansur zai munafinta yaje yola ad'aurama d'ansa aure batare dasanin muba.
Cikin d'imauta tace alhaji wana d'annasa?
Saida ya harareta sannan yace yanada wani d'a bayan Abdul'aziz yak'arashe maganar cikin huci kamar mai shirin dambe.
Tahau tafa hannuwa tana sallallami yanzunan abinda Mansur zaimana kenan kuda kuke 'yan uwansa jini d'aya uba d'aya amma yakasa shawartarku saboda yana ganin yatara dukiyar datafi taku,
Dukiyar banza tasa abban ikileema yafad'a, wallahi nayi alk'awarin saina raba wannan auren indai ina nunfashi, shikuma alhaji Muh'd saina koya masa hankali munafiki kawai harda gayyatar mu d'aurin aure, ai wlh dana san annamiman cin daya shirya kenan da munje d'aurin auren amma ko yanzu ina dai dai dashi, yafad'a yana fita.


Gidan umma mamarsu yatafi, tun ahanya yakira abban husna yace su had'u agidan umma,
Ya  afka falon umma bako sllama yatarar itama tana waya ana gaya mata maganar d'aurin auren, bayan ta k'are wayar takalli abban ikileema hala kaima kajiyo abinda naji, yanzu ake gaya min Mansur yaje yola an d'aura  wa d'ansa aure da adangin uwarsa,

Kafin yayi magana abban husna yashigo da sallama, bawan da ya amsa masa acikinsu sai kallonsa dasukeyi kamar wani bak'onsu,
A'a yaya, umma lafiya dai naganku haka atsaye cirko cirko......

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *