check your best novels here

Monday 20 February 2017

NI DA AMINIYATA 11 to 15

[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 11~October ~2016



NI   DA   AMINIYATA 



NA BILKISA IBRAHIM 




11


...............fareeda tai saurin cewa  kinga sopy zoki b'uya naje wajansa Dan naji ina zaije ne???
   " sopy tace" gsky ne K'AWATA shawararnan tayi jekiji mizai ce.
Fareeda ta nufi Abdul itakuma sopy ta b'uya.  
Tunda ya hangota yake murmushi,, tak'arasa wajensa da sassarfa tamkar zata kifa,, yay saurin cewa my love! Daga ina??? Tace" A'a kaizan tanbaya daga ina Abdul?? Yace" ni wajenki nazomana.
Tad'an zaro ido waje Abdul miyasa bazaka kirani muhad'u a wani wajenba,, ko ka manta muna tareda sopy anan,, yanzu haka tare muke kuma itace tafara ganinka ma,, sai wayo naimata nace" bari na tanbayeka inazaka??
  " yad'anja tsaki nikam gsky fareeda lamarin nan yafara isata yaza muyita b'oye b'oye akan abinda bashida muhimmanci bayan kuma miji da mata zamu zama,, way ko kina tsoron safiyyane??
  Fareeda ta girgiza kai bawani tsoro Abdul inadai son kozata sani tofa sai bayan an d'aura aurenmu jibi,, yanzu kazo muje kace" mata wajenta kazo dan ALLAH karkayi abinda zaisa sopy ta fahimci wani abu plz kataima keni mijina abin sona!!!!;!! Tafad'a tana matse kwalla,, yay saurin cewa karkiyi kuka amaryata zanyi duk abinda kikeso plz karkiyi kuka.
     "Fareeda tayi murmushi toshike nan muje.

Abdul yazagayo tabayan sopy yace" mai b'uya aii gani naganki.
Sopy tayi saurin juyowa danjin maganar habibinta,, tai murmushi to waya gayamaka ina nan?? Yay d'an murmushi aii basai anfad'a minba zuciyata ma zata iya ganoki,, barema ina kallonku keda fareeda kuna kullawa.
            " sopy tai dariya sosai tace" to naji ina ka kaimin k'awata ne?? Yace" taje sayo muku gyad'a ne, yanzu zata dawo,, tace" okey tokai mike tafe dakaine?? Ya murmusa nazone kawai naganki gimbiyata,, ya d'akko kud'i har dubu goma ya mik'a mata ga wannan kiyi hidimar biki dasuko, saidai kiyi hak'uri babu yawa gashi kuma sunzo miki ak'ure.
Sopy tace" to ngd saidai karage domin kud'in sun yimin yawa, dan mun gama komai,,, Abdul ya girgiza kai kinsan bana son musu kuma babu k'yau maida hannun k'yauta baya.
  Bayanda zatayi dole ta karb'a tai masa godiya.
Ya harareta batare data ganiba azuciyarsa yace" ' yar son banza.
""kud'inda Abdul yabama sopy fareedace tabashi yabata tunda tasan kud'in zasu dawo hannunta ne.

Fareeda tak'araso sukad'an sake tattaunawa sannan Abdul yatafi,, bayan tfyr Abdul suma suka nufi gidan aunty zainab sopy tamik'awa fareeda kud'in my sis ga wannan habibine yabani ki ajiyesu awajenki ko wani abu zai taso mana.
Fareeda tace" ALLAH yasaka masa da alkairi.

RANA BATA K'ARYA SAIDAI UWAR D'IYA TAJI KUNYA:- yaune aka d'aura auren fareeda d'ahiru da Abdullahi Abubakar mai fata,, d'aurin auren dayabawa mutane mamaki, domin mutane dayawa sun san Abdul da k'awar fareeda yake soyayya,, amma gashi yanzu ya auri fareeda, dan danan surutu yafara yawa acikin anguwa.

Su sopy suna makwafta gidan wata saddik'a anan suke zaune,, sopy tagama shirinta cikin ankon dasukayi itada fareeda kawai,, saidai ta manta sark'arta agidansu dan haka tamik'e tana cema fareeda bari ta d'akko,         sopy ta fito tana gaisawa da mutane,, amma sai mamki yakamata dataga anata nunata ana kus kus, bata kawo komai arantaba tayi wucewarta.

Da daddare aka kai fareeda d'akin mijinta dake cikin gidan su Abdul,, dukda darene lamarin yayi matuk'ar bama sopy mamaki,, saikuma gabanta yashiga yawan fad'uwa da sauti da sauri,, bayan raguwar mutane 'yan kai amrya fareeda tacema sopy dan ALLAH ta samomata ruwa tasha,, sopy tace to amrsu ta ango mai dad'in suna aii dole naje neman ruwansha,, bayan fitar sopy fareeda ta d'auki wayarta takira Abdul,, dan dama shitakeson kita shiyyasa ta aiki sopy.

Sopy tana tsaye a k'ofar gidansu Abdul tanata kalle kalle zuciyarta cike da fargaba,, can saitaji muryar adam yana fad'in Abdul kana ganin hakan dakayi shine dai dai tun d'azu nakeson muyi magana kanata min hanya hanya,, yanzu kai kana ganin idan sopy tagano kaine ka auri fareeda mi kake ganin zai farune???
Abdu yay magana cikin tsawa kaga adam kafita hanyata wlhy to miye idan sopyn tagane nine na auri fareeda,, ita uwatace kokuwa zata tsirenine??? 
 Bazata tsirekaba amma tabbas sai ALLAH ya saka mata kuma karubuta ka ajiye ranar nanan zuwa gareku daga kai har fareedar daka aura.

Tun sopy najin abinda suke fad'a harta dainaji,, garin yafara juya mata kafin kace me ta yanke jiki ta fad'e awajan,, dan dana hankalin mutane yadawo gurinta,, Aka fara fad'in "inna lillahi wa inna ilaihirraji un."  Wanine yay k'arfin halin fad'in ad'auketa mana atafi asibiti dan asume take...................




Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
                                            
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 12~October ~2016



NI  DA  AMINIYATA



NA  BILKISA IBRAHIM

  


12


..............Asibiti mafi kusa aka nufa da sopy,, sannan labari yakai gidansu sopy,,, ALLAH ma yasa uncle kabeer yana nan,, shima yazo d'aurin auren fareeda,, babu b'ata lokaci suma suka nufi asibitin da aka kai sopy,, wadda likitoci suka rufu kanta,, amma ko motsi batayi kwance take tamkar gawa.
     "Ganin dare yafarayi likitoci sukace su inna suje gida abarwa gobe,, aga abinda ALLAH zaiyi kuma,, inna tace" babu inda zataje tananan tareda sopy,, dak'ar aka lallasheta suka tafi akabar uncle kabeer awajenta.

Awannan lokacin kuwa amarya da angonta suna can ana ragargazar amarci,, dan ango bai d'agawa amaryar tasa k'afaba,, dukda yalura tana cikin damuwar abinda yafaru da AMINIYARTA,, itama dai tabada gudummawa dan tasan wannan shine zai k'ara kusanci tsakaninta da Abdul,, zai kuma k'ara zama dalilin da dole iyayensu su barta tazauna tareda mijinta,,, ba k'arya tasha wahala amma ta daure sosai dan tana son Abdul,, to fareeda saimuce ALLAH Yasanya alkairi yakuma shirya masu irin halinku nacin amana da yaudara. Amin

A asibiti kuwa har yanzu sopy bata farfad'oba  kuma likitoci sun dage akan tanada rai bata mutuba,, to ALLAH yasa haka, dan gsky masu karatu indai sopy ta mutu to nimafa 'yar rahoton taku bazan sake kawo muku rahotoba,, ALLAH dai yasa da ranta.
 Shagalin biki yakoma zaman jigum jigum,, dan maman fareeda sai kuka takeyi tana fad'in wlhy saita kashe auren fareeda,, tunda har taci amanar safiyya,, in kuma ba hakaba zata tsinema fareeda inhar bata rabuda Abdul ba. 
      ""Tofa turkashi kunji wata sabuwa masu karatu.""

Har zuwa yamma sopy bata farfad'oba,, dayawa mutane sun fara yarda tama mutu,, dan ko mahaifinta ma cayayi likitoci suyi hak'uri subada gawar safiyya aje amata suttura.
   "Wani likita yace" way baba wayace maka ta rasu?? Yarinyar nan tanada ranta dan ALLAH  kubarmu muyi aikinmu.
 Sai wajen k'arfe 4:46pm sopy ta farfad'o saidai sun hana kowa ganinta,, dansun yimata allurar barci,, saboda ta sami hutu,, dukkan 'yan uwa suna asibitin kowa ka kalla baya cikin walwalarsa,,, labari kuwa sai k'ara baza anguwa yakeyi,, kunsan dai mutane da gulma,, dan yanzu gulma maza da mata kowa ya iyata,, ALLAH dai ya shiryar damu jama'a.

Mahaifin fareeda ya aika hargida aka kira masa Abdul da fareeda,, bayan d'an wani lokaci suka iso,, dukkan dangi sun had'u, mamar fareeda da babanta sai yayunta biyu yaya lawan, da yaya saminu, da zainab, sai k'anin babanta. 
    Sai baban sopy da inna, aunty Nafisa da hauwa'u,, sai uncle kabeer,, fareeda duk tabisu da kallo azuciyar ta tace" tofa wannan gangamin namiye?? Zuciyarta tace mata duk anyishine saboda "k",, tai wani d 'an guntun murmushi aiko sama tarwatsashi dan fad'ansu ko wani hargaginsu bazai tsorataniba,, tuni nashiryama fuskantar wannan matsalar.
 Yaya lawan yadaka mata tsawa to mara kunya idan kin gama yimana kallon rainin arzik'in saiki zauna ko,, mara mutunci kawai.
Fareeda tad'an tab'e baki sannan ta zauna kusada mijinta,, babanta yay gyaran murya, yad'ora da fad'in assalamu alaikum!!! Kowa ya amsa,, yabi fuskokin kowa da kallo sanna yagyara zama yace" Abdullahi!!! Abdul ya amsa kansa ak'asa.
 Baban fareeda yace" miyasa ka auri fareeda bayan kuma da safiyya kuke  tare??? Kuma har munyi maganar aurenka da safiyya harda iyaye aciki??? 
                     Abdul yagyara zama, baba ku gafarceni dacan safiyya nakeso amma yanzu fareeda nakeso kuma gashima har kun auramin ita.
Baba ya k'ara d'aure fuska, to miyasa lokacin da maga batanka suka zo basu fad'i hakaba??? Saima sukace mana yayanka ne zai auri fareedan??
Abdul yace" nine nace sufad'i haka dan karka hanani auren fareeda.
  Baba yaja tsaki to aii har yanzu bata sake zaniba domin dolene kasaki fareeda yanzu anan wurin,,, gaba d'aya wajen saida suka d'ago suna kallon baba banda mama da tace" wannan batu kam tilas ne dole kasaki fareeda ka auri safiyya.
  Baban sopy yay saurin tareta amma dai ba haka mukayi dakaiba malam d'ahiru,, gsky karku raba musu aure.........baban fareeda yay saurin katseshi, saidai kayi hak'uri malam ibrahim nariga nagama yanke hukunci.

Abdul yace" gsky baba saidai kuyi hak'uri wlhy bazan iya rabuwa da matataba ina sonta,, ina kuma burin kasancewa da ita har abada.
  Fareeda ta karb'e wlhy nima baba inason mijina dan ALLAH karku rabamu,,,, aii kafin tarife baki yaya lawan yabata duka jikake taffff,, ta kwalla k'ara tana fad'in wlhy sai ALLAH yasaka min tunda ban yimimaka komai ba mugu azzalumi.......yako tashi yashiga dukanta tako ina,, Abdul yamik'e yashak'i wuyan yaya lawan yana fad'in kai bagidaje mahaukaci wlhy idan hannunka yak'ara sauka akan matata saina kasheka.
Uncle kabeer yadaka ma Abdul tsawa yace" sakeshi,, jikin Abdul yana rawa yasaki yaya lawan yakama hannun fareeda yana fad'in muje gida,,, baban fareeda yamik'e murya a sark'e yace" fareeda inhar kika koma gidan Abdullahi to babuni babuke, nacireki daga cikin 'ya'yana kije nabar masa ke.
            " fareeda tace" baba nasan rankane ab'ace amma wataran zaka gane hikimata ta auren Abdul, harma kayi alfahari da hakan,, mama tace lallai fareeda wuyanki ya isa yanka yanzunan mahaifinki kike fad'ama haka saboda d'a namiji,, fareeda ta tab'e baki mama kema nasan bazaki tab'a ganewaba sainan gaba,, kamar yanda kuka buk'ata zanyi nesa da ku da 'ya'yanku har zuwa lokacin da zaku huce,, aunty zainab dake kusada ita ta wanka mata mari taka'ara mata nabiyu, Abdul yarik'e hannun cikin masiba zainab tace" kaid'an akuya sake min hannu ke kuma wlhy nan bada dad'ewaba zakiyi nadamar abinda kika aikata,, kuma saikinyi mamakin mijin da safiyya zata aura maci amana kawai.
 Fareeda ta tab'e baki wannan kuma bai dameniba,, idan safiyya zata auri mazan duniya bai dameniba tunda nidai nasamu muradina,, taja hannun Abdul suka tafi,, mahaifin fareeda ya yanke jiki yafad'i agurin......................





Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
                                            
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 13~October ~2016


NI   DA  AMINIYATA


NA BILKISA IBRAHIM 




13


.............gaba d'aya suka nufo kan baba,, uncle kabeer ne yay k'ok'arin yayyafa masa ruwa ya kawo numfashi,, yad'ago yana kallonsu dagaske fareeda tatafi ta zab'i yaron nan sama dani??
 Aunty zainab tace" baba ta tafi kabarta kawai aii "DUNIYA MAKARANTA CE"" yace" shikenan ku shaida nacire fareeda acikin 'ya'yana kuma duk wanda yay mu'amulla da ita acikin ku ban yafe masaba,, kamar yanda ta buk'ata nabarta da Abdullahi.
         Baban safiyya yace" dan ALLAH malam d'ahiru kabar wannan furicin da fareeda da safiyya duk d'ayane agurinmu,, in akayi hak'uri itama safiyyan ALLAH zaibata wani, dama can ALLAH ya rubuta ABDULLAHI mijin fareedane ba safiyyaba......baban fareeda ya k'atseshi malam ibrahim kabarni kawai wlhy nariga na yanke hukunci dan haka kabarni ina ganin mutuncinka.
  Dole kowa yay shiru,, dan sunsan ransa ab'ace yake,, daga nanma kowa yakama gabansa.

Agidan su sopy uncle kabeer yace" wlhy ni abunma ganinsa nake tamkar a mafarki,, dama  akwai iyaye irinna Abdul??
 Baban fareeda yay murmushi abba akwaima wad'anda suka fisu,, ni tun ranar da aka kawo kud'in auren fareeda na fahimci ko mai,, dan haka daga baya na yi bincike,, nagano Abdullahi fareeda zata aura.
 aunty Nafisa tace" amma baba kayi shiru baka fad'awa kowaba??
 Baba yace" hakane Nafisa fad'ar fashida wani amfani, tunda fareedar yakeson aure, dan haka ina mai gargad'inku kada kowa yad'auki wannan abin da zafi,, mutaya safiyya addu'ar samun lfy kawai, dakuma fatan ALLAH yabata miji nagari wanda yafi Abdullahi bawai dukiya nake nufiba,, A'a wanda yafishi k'yawawan halaye.

Kowa ya amsa da to,, yace" kukuma yakamata kushirya kutafi gida jenku,, tunda sunce yau zasu sallamo safiyyar daga asibiti.
  "Suka amsa da to baba"

Da daddare aka sallamo safiyya, koda sukazo gida wanka kawai tayi tasha shayi da magani ta kwanta, dan akwai maganin barci aciki,, baba yace mai sunan baba!! miye likita yace gameda ciwon nata?? Uncle kabeer yaja numfashi,, yaya!! likita yace sopy tasamu matsala a zuciyarta,, dan tadad'e acikin damuwa da yawan fad'uwar gaba,, saikuma fad'uwar datayi shekaran jiya tayitane sakamakon jin abinda bata zataba,, amma yace" idan aka cigaba da lallashinta da yimata abinda zai sakata farinciki to zata dawo kamar yanda take,, inkuma bahakaba zuciyarta zata kamu sosai.
              " inna tafashe da kuka,, ALLAH sarki safiyya kekuma taki jarabawar kenan?? Baba yace" hajara ba kuka zamuyiba addu'a safiyya kawai take buk'ata daga garemu.
 Uncle kabeer yace"gsky ne wannan, nan dai suka cigaba da tattauna matsalar.

Yau da gobe ahankali jikin safiyya yafara sauk'i dan tana samun kulawa wajen baba da inna dakuma uncle kabeer,, yayyen tama suna bata kulawa,, haka mamar fareeda kullum saita shigo dubata itada baban dasu yaya lawan,, jikinta yana yin k'yau saidai yanzu bata son yawan magana,, ko hayaniya, ko fira ake akusada ita saidai kallo,, koda yaushe tana kwance, sallah ce kawai ketashinta abincima bata son ci,, sai uncle kabeer ya lallab'ata.
      " lokuta da dama idan ta tuna cin amanar da AMINIYARTA tayi mata da SAURAYINTA wanda take matuk'ar SO sai kaga hawaye nazuba akumatunta,, takanyi bak'in cikin kub'ucewar mutane biyu masu muhimmanci agareta alokaci d'aya,, sun barta alokacin datake buk'atarsu fiye da kowa,, sun tafi lokacin datake buk'atar abokin shawara,, sun barta lokacin datake buk'atar mai d'ebe mata kewa,, sunyi nisa da ita alokacin datake buk'atar mai share mata hawaye,, tafashe da wani irin kuka mai ban tausayi, nima bansan lokacin danawa hawayen suka fara zaryaba, dan nasan zafin rabuwa da masoyi,, saidai nawa mutuwace tarabamu, bakamar na safiyyaba da yana raye yayi nisane da'ita saka makon makircin AMINIYARTA.
          inna tashigo d'akin da sauri danjin kukan safiyya,, ta rungumeta ajikinta tana lallashinta,, haba safiyya kiyarda da k'addara mana alokacin data riskeki,, ki godema ALLAH mana alokacin daya jarabceki,, karki jahilci kanki kiyi hak'uri irin hak'urin manyan ANNABAWA mana ayayinda jarabawa ta riskesu,, inkikai hak'uri sai ALLAH yayi alfahari dake domin yana tare damasu hakuri,, indan kikayi hak'uri sai ALLAH ya musanya miki da mafi alkairi.
 Sopy ta kuma rungume inna tana fad'in to inna zan daina,, kawai abinne yana bani mamaki,, wai fareeda da'ita aka had'a baki wajen cin amanata,, dama tuni tasan dukkan matsalata amma tarufeni,, duk halin k'unci da yawan damuwa dana shiga fareeda tanada masaniya akai,, shiyyasa kullum saitace zataje ta tanbayo miyasa Abdul yadaina zuwa wajena,, kullum da irin tsarin da zata yi min,,, ashe itace kecin dunduniyata ban saniba,, ashe fareedace tushen damuwata tafad'a tana rushewa da kuka,, haba AMINIYATA miyasa kika aikata?? Miyasa kika yimin haka?? Miyasa kika zama mai irin halin muna fukai??? Miyasa saida nayarda dake kikaci amanata??? Miyasa kika zab'i mu rabu akan saurayi???? 
Inna tace" kinga ya isa haka kiyi hak'uri. Sopy ta d'ago tana kallon inna, wlhy inna ba rabuwa da Abdul bane matsalata nafi jin ciwon rabuwa da fareeda,, domin zuciyata da ruhina suna matuk'ar k'aunar fareeda,, itace K'AWA tafarko da zuciyata ta yarda ta ita harta zama AMINIYA mafi soyuwa a zuciyata,, ashe zata rabuda ni akan saurayi,, zata raba tsantsar SO da k'auna da zumincin dake tsakaninmu,, ashe zata saka shakku da fargaba azukata guda biyu da tsantsar yarda ta cikasu??  Ashe duk so da k'aunar dana nunama Abdul da fareeda su babu abinda suka ajiye mini sai tari yaudara da cin amana??? Nikam nayi asarar AMINIYA da miji mafi soyuwa azuciyata,, inna banyi tunanin sake maye gurbin wad'annan mutanen biyuba arayuwata,, domin nayi asarsu alokacin danafi buk'atarsu.
    Inna tace" kiyi hak'uri safiyya ki barma ALLAH shine mai kowa da komai,, inkinyi hak'uri zai musanya miki da wad'anda suka fisu,, kedai ki kasance mai gsky aduk inda kika tsinci kanki,, da ace kekika cutar gara ace ke aka cutar kinjiko???
  Sopy tad'aga kai tana hawaye, insha ALLAHU inna karkiyi shakku akaina,, zan kasance kamar yanda kika buk'ata.
To shikenan yanzu dai ki kwantar da hankalinki kibar yawan damuwa kinga likita yahanki tunani saboda ciwonki,, muma bamu son mu rasaki.
            " to inna zanyi k'ok'ari insha ALLAHU kodan hankalinku ya kwanta.
Inna tayi murmushi to shikenan auta ta.
Sopy tace" inna ina uncle yake??
Yaje siyo miki maganinki yanzu zai dawo,, wlhy inna bana son uncle yatafi yanzu dan ina jin dad'in zama dashi.
To aiko saidai hak'uri auta kinga dole ya koma wajen aikinsa,, dan kinga bikinsa shima yanata gaba towa.
       Sopy tace" hakane kuma inna, ALLAH dai yakaimu lokacin.
Inna tamik'e tana fad'in amin autata.................



Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
                                           
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 14~October ~2016



NI   DA  AMINIYATA




NA BILKISA IBRAHIM 



14


..................Safiyya tasamu sauk'i Dan jikinta yayi k'yau saidai tayi matuk'ar rama,, fuskarta tayi wani fayau,, bata zuwa Ko ina koyaushe tana gida tareda innarta,, uncle kabeer yasaya mata waya mak'yau,, yabud'e mata watsapp da facebook duk dan surink'a d'ebe mata kewa,,, indan baya aiki saisuyita hirarsu a watsapp,, yabama budurwarsa nomber ta,, ta sakata a group's 2  dayawa NA Novels dana hirar duniya dana addini irinsu HANYAR TSIRA  dan wannan gidan bayin ALLAH suna k'aruwa dashi sosai ALLAH yabiya masu tunatar damu aduk inda suke. 
       "" irin wad'annan abubuwane sukan d'auke mata hankali bata samun lokacin tunani,, data ta  wata 1 uncle kabeer ke siya mata,, shiyyasa batada matsalar MB,  saidai takanyi kewar fareeda, Dan tunda suke basu tab'a yin kwana biyu basa tareba,, Dan haka duk kewarta ta addabeta, takan kwaso pictures d'insu taita kallo tana tuna baya,, duk abinda yashafi fareeda sopy ta maidashi wani madubinta,,sai dai idan inna taganta ta gurgiza kai kawai amma tana matuk'ar tausayin 'yar tata.

Su fareeda anata shan amarci,, komai yanata tafiya yanda takeso,, Abdul yana tattalinta komai takeso shi yake mata,, inagama ansamu rabo dan naga tayi wani fari,, kokuwa duk amarcinne oho dai,, mudai 'yan kallone. 

Yau sopy anacikin farin cikin zuwan uncle kabeer,, sai hidimar girka masa abinci takeyi, inna taji dad'in yanda taga tasaki jikinta yau tana walwala, dan tunda abinnan yafaru basa ganin dariyar sopy,
 Amma yau daka kalleta zaka gano farinciki a tareda ita.
     "Sai wajen k'arfe biyu uncle kabeer ya iso, shima yayi farincikin ganin yanda jikin sopy yayi k'yau saidai kawai ramar datayine, tana zaune kusada uncle kabeer dake cin abincin data dafa masa,, takalle sa uncle kana ganin baba zaiyyarda da k'udirinmu kuwa? ?? Uncle kabeer ya ce, "aii dama tunda naga farincikinki ya yauta nasan akan maganar damukayine", karki damu zanyi iya k'ok'arina tayanda zai fahimceni, insha ALLAHU  zai amince.
   Sopy ta ce, "danayi farinciki mai tarin yawa uncle, nasan hakan zaik'ara nisanta zuciyata daga damuwar data tsinci kanta. 
  Uncle kabeer yay murmushi hakane my daughter! Insha ALLAHU nan gaba kad'an komai zai zama labari, kedai kiyi k'ok'arin cika min burina,, dan yanzu zaki shirya muje makarantarku mu amso exam d'inki.  
  Cikin zumud'i ta ce, "angama my dear uncle! Inna dai tanajinsu bata tankaba, dan bata fahimci inda zancen nasu yadosaba.

Sun karb'o sakamakon  jarabawar saidai sopy batayi k'ok'ari a WAEC nataba.
  Uncle kabeer ya ce, "sopy ya akayi haka tafarune??  Sopy tad'an sosa gefen wuyanta, wlhy uncle! Sannan ina cikin wani yanayine!!
  Uncle yay murmushi sannan kina cikin shauk'in son Abdul ko?? "Tasa hanu ta rufe fuskarta tana fad'in "kai uncle".
  Ya ce, "i, mana hakane", amma babu damuwa saimuyi amfani da NECO kawai, dama mun gama magana da abokina,, shima malamine a "B,U,K", nasan zai taimaka mana sosai.
  To uncle nagode sosai ALLAH yabiya ka kaidai!! Yay murmushi  to amin sopy na.

Sai dare uncle kabeer yasamu zama da baba, bayan sun gaisa ya ce, "yaya dama maganar yarinyar nan ne yakawoni.
   Baba ya ce, "wace yarinya kenan?? 
 Uncle yagyara zama, yaya yarinyar dazan aura!
 Baba ya ce, "to miya faru da ita??
Babu komai yaya babanta ne , dama ya rok'eni akan dan ALLAH nabarta ta k'are karatunta, tunda saura shekara d'aya kacal, to nima sainaga hakan zai taimaka minma na k'arasa gidana, amma yaka gani??
   Baba yaja numfashi, to idan haka yafi alkairi ALLAH ya tabbar abba, mudai kullum addu'ar fatan alkairi muke maka, da fatan gamawa lafiya, dan kai yaron kirkine, nak'agu naga ka ajiye iyali kaima.
  Uncle kabeer yay murmushi karka damu yaya insha ALLAH zanyi adai k'ara tayamu da addu'a,, sai dai yaya bayannan inada wata buk'ata awajenka!! Inhar ban takuraka ba?? 
  Baba ya murmusa karka damu mai sunan baba fad'amin buk'atarka indai batafi k'arfinaba zan yi maka ita.
  Uncle ya ce, "batafi k'arfin kaba yaya! " dama dan ALLAH ina son kayarje min namaida safiyya makaranta, dan wannan zaman nata bashida wani amfani, karatu zai matuk'ar taimaka mata wajen mance abubuwan dasuka faru abaya..................



Bily
(Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
                                             
[19/11/2016 15:44] bilyn Abdul: 15~October ~2016



NI   DA  AMINIYATA 



NA BILKISA IBRAHIM 


15


...............Baba yaja numfashi, abba ban katse maka hanzariba, amma da dai anhak'ura da karatunnan hakanan, tunda ansamu na zaman duniya, sai kuma ayi aure.
   Uncle ya ce, "hakane yaya, amma yanzu naga bawani tsayye bane ahannu, amma dazaman banzar gara ace karatu takeyi,, kotana karatun tasamu miji saitayi aurenta.
   Baba ya kalli inna, to hajara kinji abinda abba ya ce, "amma ya kika gani??
  Inna tai dariya, malam nikam banida shakku akan babnmu, dan haka kabashi dama, nima inaga hakan zai taimakawa safiyya wajen mance wasu abubuwan.
   Baba ya ce, "to akira safiyya muji ta bakinta"
Uncle yay murmushi karka damu yaya indai safiyyace mungama magana da'ita.
  To, to, kace dama saida kuka gama shawararku sannan aka tuna damu!  Dariya sosai uncle yakeyi "cikin dariya ya ce, "A'a yaya mu mun isa; nan dai sukayita hirarsu da wasa da dariya.

TUNATARWA:- inaso naja hankalin iyaye akan ilimin 'ya'yansu, mafi yawan iyaye sukan d'auki ilimin 'ya'ya mata ba'abu mai muhimman ciba,, ni anawa ganin ilimin d'iya mace yafi na kowanne muhimmanci, karku manta uwa itake bada tarbiyya, kuma yara suna tashi ne da harshen mahaifiya, kunga kuwa ilimin d'iya mace yanada muhimmanci matuk'a,, dan zata zama foundetion na ilimin 'ya'yanta,, wannanma kad'ai ya isa yazama abu mai muhimmanci ga bawa mace ilimi,, sannan ko a gidan aure zakaga mace mai ilimi tafi kowa iya rik'e miji da tattalinsa,, dan haka mubama 'ya'yanmu mata ilim addini dana zamani,, ALLAH YASA MU GANE.

UNCLE kabeer yanata k'ok'ari wajen nemawa sopy Admission a (BUK ) da taimakon wani abokinsa aka dace,, dakansa yaymata komai.
   To ALHAMDULILLAH komai dai ya kammala,, ranar monday sopy zata fara zuwa makaranta,, dan haka tafi kowa fareenciki,, harta k'agara ranar tazo.

Su dai su inna sunata yima sopy nasiha, akan tazama mace tagari mai rik'e mutuncinta da darajarta,, idan ance 'ya mace taje tayi ilimi, bawai ananufin taje tayi iskanciba,, dan dayawa 'yan uwa mata idan suka samu saken zuwa nema ilimi,, sukan d'auka sun samu wayewa daganan sai afara iskanci,, kaiconmu wlhy 'yan uwana mata, har yanzu wasunmu basu fahimci miye wayewaba dayawanmu muna jahiltar wayewa,, ballagar mace wadda ta maida kanta akuya ba ita bace wayayyiyaba,, wanna itace bagidajiya jahila,, mace mai kamunkai da girman kai awajen maza marasa tarbiyya,, mai adiini itace wayayyiyar mace, kuma suma mazan sunfi sonta,, zakaga duk iskancin namiji da mugun halinsa yana burin auren mace tagari, kodashi bai kasance miji nagariba, to 'yan uwana ya kama ta mu gyara, kodan cin ribar rayuwarmu,  ALLAH dai yasa mugane.
    Su inna dai sunyima sopy nasihohi masu ratsa jiki da zuciya,, sunkuma yimata fatan alkairi da samun nasara arayuwa.
  Saboda yanayin rayuwa,, sai uncle kabeer ya nema mata gurin zama a hostel, dan kar wataran kud'in mota ya gagareta,, itama hakan yayi mata dad'i, dan zaman anguwar yana d'an sata tayita tuna wasu abubuwan,, kuma idan tafita sai mutane suyita kallonta, wasuma har nunata sukeyi, to, tasan idan tayi nisa da anguwar zata sake, ta kuma manta da abubuwan dasuka faru abaya. 

Ku kasance dani akoda yaushe, ina muku fatan alkairi ...................



Bily
Mrs Abdus'salam
I LOVE YOU MY FAN's
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *