check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 25

AUREN K'ADDARA
              ko  BIYAYYA


Na billkisa ibrahim

25 «*****»  ganin yanda yake magana cikin jin haushi tasan gatse yay mata, dan haka tace to bari nagyara,ta fara kakka b'e gadon, dady dake kan kujerar madubi zaune, yace ai wannan zanin gadon saidai ki cire shi, dan bazan iya barci akansaba,sai jikina yazo yana kaikayi,
Azuciyarta tace magulmaci ai k'ilama nan gaba uwarkama saikace mata k'azama, dole ta canja zanin gadon suka kwanta,shikam harga ALLAH ya gaji barci yakeji, amma yasan fitinar husna,jiyyayi ana shafashi doleya daure yabata hakkinta sannan sukayi barci.

Da safe bayan sunyi sallah suka koma barci , cikin barci sukaji ana buga k'ofa kamar zata cire, dady ya daure ya tashi husna ma ta mik'e, sanda suka fito ikileema ma ta fito har tana k'ok'arin bud'e k'ofar, 
Jabir ne da umma kakarsu da alama ma jabir abuge yake, ikileema tad'anja baya danganin jabir  yana k'ok'arin fad'owa kanta.
Cikin muryar maye yace ina Abdul'aziz d'in dan uwarsa bilkisu, yau saika gaya mana ubanda ya d'aura maka aure batare da saninmuba,
Dady yana tsaye jingine da bango hannuwan sa hard'e ak'irjinsa, yace jabir ganinan ince ko kazo ka dake nine??
Umma tace to mara kunya koka manta jabiru yayankane, dady yace ban mantaba umma, amma kinaji ya kira sunan mom d'ina yazaga,saboda tarbiyya tamasa k'aranci, dady ya nuna jabir kasn ALLAH ka k'ara zagin iyayena saina yimaka rashin mutunci.

Umma tace kai Abdul'aziz rashin mutincinka har yakai haka, tsaki dady yaja yay shigewarsa d'aki harda saka key.
Ikileema da husna sunyi mutuwar tsaye danjin furicin yayansu jabir, cikin k'arfin hali ikileema tace umma bafa mugane abinda kuke nufiba, waye yayi aure??
  Jabir yay taga taga zai fad'i ALLAH yabashi sa'a yadafe kujera, yace wannan d'an iskan mijin naku mana, shine yaje yole shida wad'ancan muna fikan iyayen nasa suka d'aura masa aure, yanzu haka amaryar tana gidansu,
    K'ara suka kwallah atare suna fad'in dady ka cucemu, ikileema tanufi kofarsa tana bugawa da k'arfi tana masifa.

Shikam yana jinsu yay musu banza k'arshe ma dayaji sun damesa da hayaniya sai ya kunna karatu awaya yasaka iya fis ya k'ure k'arar

Bayan kamar minti talatin yaji gidan shiru saiya cire ya kashe yay murmushi sannan ya mik'e ya bud'e kofarsa ya lek'a falon, dariya yayi mai sauti yara darabon tafiyarku ta kasance kun tafi kenan, dan dama hanyar rabuwa daku nake nema wallahi, ya koma cikin d'akinsa yana k'yalk'yala uwar dariya, kamar wanda akaima bishara da gidan aljannah........


billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *