check your best novels here

Sunday 19 February 2017

AUREN 'K'ADDARA ko BIYAYYA? page 33

AUREN  K'ADDARA
               ko  BIYAYYA

Na billkisa ibrahim 

33 «*****» miye labari su husnane ??
   Su husna suna gida abinsu umma anata lek'e lek'en gidajan malamai da bokaye, acewar ta sai dady yazo dakansa yana kuka abashi su ikileema.
To suma sunanan sunata fankama akan sai yazo, iyayensu mata ma suna nemomusu agefe kowa tana shirya d'iyarta acewar su, amma gashi yau har tsawon sati uku ba labarin dady bare zuwansa.

Su har ma abin basu tsoro yakeyi dan sunsan halin dady sarai da,miskilancinsa,
Ikileema tana kwance bisa doguwar kujerar dake falonsu, sauran k'annenta sunata hirarsu.

Maman ta ta fito tazauna kusa da ita ikileema lafiya dai ko naganki akwance?
ga kuma sauran 'yan uwanki sunata hirarsu.
    "Ta turo baki gaba gaskiya nifa mama nagaji da zamannan hakanan, nifa gidan mijina zan koma, yakama ta ku daina biyema waccan tsohu war hakanan, dan wallahi nasan dady bazaizo bikonmuba, garama tun wuri kubarmu mu koma, dan gaskiya nidai inason mijina, tafad'a tana juyama uwar tata baya.

Mamarta tace ikileema kefa shashaahace duk wannan k'ok'arin da akeyi dansu ubanwa akeyi badan kuba, shine har kike fad'a mini kefa kina son mijinki.

ALLAH mama ba haka bane ba gara ku bari mukoma ba, dukma abinda za'ayi ayishi muna can, agidan amma azo ahanamu komawa gidan mijinmu, ita kuma waccan she giyar tana can tan shan shagalinta awannan had'ad'd'en gidan.

Maman tai ahiru tana kallonta, kai ikileema dafa gaskiyarki wlh, kumafa hakane mumu nanan muna bad'oso goyon jirge, ita tana can tana shan lagwadar dad'i dak'ara mamaye gida, da mai gidan, nasan hajiya salaha sarai da iya kissa, kuma tana koyar da 'ya'yanta.

FAD'AKARWA :- ni aganina dan mace ta koyar da yaranta kissa inhar bata cutar da wani bace, tofa tayi dai dai, dan kissa nad'aya daga cikin halayyar dake jan ra'ayin miji ga matarsa, ba sai ta hanyar boka da malam ake jan ra ayin mijiba, a'a kema malamar kankice, bari nabarku haka ku biyoni kuji yanda Munneerah take damk'e dady ahannunta cikin ruwan sanyi da kissa irin wadda ta halatta.......

billy
{Mrs Abdus'salam}
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Blog Archive

Contact Form

Name

Email *

Message *