check your best novels here

Tuesday 14 March 2017

SABON A L'AMAREE 46/49

[11/03 12:19] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》







NA BILKEESA IBRAHEEM 
    {♡Bilyn Abdul♡}





47

.........Tafara hawaye nidai yaya wlhy gidan daddy zanje, yana jinta kala bai ceba, aunty bily ta ce, "yaya tunda can takeso ka maidata mana, harara ya sakarma aunty bily ta madubi.
   Tuni tayi gum da bakinta.
  Ya mahmud da aunty bily suka fito amma Nurr tayi zamanta amota, ya buďe inda take ya sunkutota gaba ďaya, da 'kafa yarufe motar, sai wuntsile2 takeyi amma shi ko ajikinsa, saman gadonta ya direta, ya zazzare mata idanu ki nutsu mana!!, kalli agogo 'karfe goma harta gota, yanzu su dady sun rufe gida, gobe idan ALLAH yakaimu da safe basai ki komaba.
   Tsagaitawa tayi da kukan datakeyi ta ce, "da gsk kakeyi?.
   Ya lumshe idanunsa yana gyaďa mata kai.
   Tayi murmushi to shikenan, murmushin mugunta yasaki yabar ďakin, Nurr ta murguďa baki aii wlhy yau dakaga bore dan kuka zanta zumbuďa maka, gobe idan ALLAH yakaimu tunda farar safiya zan koma gidan dady, (nace lallaikam ashe kinada aiki).
     Wanka ta tashi tashiga, tayi mamakin gani ďakin face kai badai aunty bilyce ke gyara ďakinnan kullumba??, wayyo auntyna shiyyasa nake bala'in sonki ALLAH yabarmu tare (nace ameen).
   Wanka tayi tashirya cikin wando iya guywa da 'karamar riga tashan iska, ta shafa cikinta kai nafara jin yunwa bari nagano kosunada abincin dazan iya ci, falo tafito, ya mahmud da aunty bily suna zaune suna cin abinci.
   Ta zauna saman kujera cikin shagwa6a ta ce, "aunty yunwa nakeji wlhy, da sauri aunty bily ta ce, "yunwa kuma Nurr?, mikike sonci??.
    Tayi shiru alamar tunani, koma gari zansha da suga da gyaďa.
   Ya mahmud ya tuntsure da dariya, gari kuma?, yau aikin inyamurai (ibo) za aimana agidan?, to mukam yanzu a darennan ina zamu samo garin kwaki harma da gyaďa??.
   Aunty bily ta ce, "miyasa baki faďaba kafin mu shigo gida, anguwar damukaje za'a iya samu, gashi dare yayi yanzu bare a aiki wani, faďi wani abun kuma dakike sha'awa.
    Taďan turo baki dantaji haushin dariyar da ya mahmud yay mata, aunty kinga yaya yana mun dariya ko??, murmushi aunty bily tayi kinga 'kyaleshi aishima munan zaiyi zazza6i idan yana irin wanan kwaďayin saimu rama ko??.
   Ta ďaga kai".
  Ya mahmud ya murmusa, ashe zaku daďe bakuyiba.
    da wanan tunanin da kwakwule2n dama zuwa kikayi kika zauna mukaci abinci, ta ta6e baki tareda yamutse fuska idonta akan abinci, Tab wlhy bazanciba, ko kallon shinkafarma bana sonyi, yanzuma haka shirin amai sakani amai take.
   Cikin tausayawa ya Mahmud yake kallonta to mikike son ci yanzu?.
" ta ce, "tuwo.
     Ito dama2 wanan kila asamu a gidan fahad tunda baya rabo da cin tuwa, bari muga nakirashi, ya ďauki waya yana kiransa, bayan sun gaisa da tambayar lafiyar yara,  ya mahmud ya ce, "Fahad kozamu samu tuwo agidannan naku?.
    Eh akwai yaya amma wazaici tuwo yanzu??.
   Wlhy Nurr ce wai tuwo takeso, kai babymu yana bama auta wahala fa.
   To yaza'ayi, anyi maganin mai bakin tsiwane yafaďa yana kallon Nurr.
  Dariya ya Fahad yayi, hakadai kace yaya, yanzu gidan dady za'a kawo mata??, A'a tana nan gidan tadawo ďazu, okey bari hinde mai aiki takawo mata, to shikenan ka gaidamin yarana.
   Zasuji duk sunmayi barci tun ďazu, okey saida safe.
  Aunty baly ta ce, "ansamu ne yaya?, eh ansamu gashinan za'a kawo mata.
   Babu daďewa saiga hinde mai aiki da kular tuwon alkama miyar ďanyar ku6ewa, ta risina ta gaidasu tareda faďin gashi inji aunty.
    To sannunki kema hinde ya mahmud sarkin'kyauta saida yayimata, tako tafi tana zuba godiya.
   Nurr tasakko tazuba tuwo, kai ammafa tuwonan yayi daďi, ya Mahmud ya ce, "k dai ci 'yammata.
   Takoci tiwon sosai ta ďora da ruwa, ta baje a falo tana maida Numfashi, sha ďaya nayi ya Mahmud yami'ke kunga bari nayi nan gobe idan ALLAH yakaimu inada office, suma suka mi'ke kowa yatafi ďakinsa.

Nurr na zaune bakin gado bayan tagama shirin barci saiga ya mahmud, taďago matsakaitan idanunta tana kallonsa, sanye yake cikin milk ďin kayan barci sun masa 'kyau sosai kuwa, ya hure mata idanu dan ganin takasa janyewa daga kallonsa, ajiyar zuciya tasaki tareda yin 'kasa da kanta dan taji kunya.
   Shima ya lura da hakan ya zauna kusada ita yana murmushi, bakiyi barciba??, yafaďa yana tallafo 'kugunta da hannunsa na dama.
   Taďan matse jikinta kamar bataso ya ta6ata ta ce, "yanzudai nake shirin yinsa, damma nayi barci ďazu agidan deena ne, okey to ya jikinki??.
   Taďan matso gaba dan son raba jikinta da hannunsa amma saiya 'kara ri'keta guduna ake kuma Nurri?.
   Kai ta girgiza batareda tayi maganaba, ďan ta6e baki yayi yana mi'kewa to tashi mutafi.
   Ta kalleshi cikin mamaki ina kuma zamuje??, ďakina mana, ďakinka kuma?, mizanyo acan??, samun lada mana.
    Hummm lada kuma?, nikam dai ka barni anan, duk inda mutum yake indai zai aikata aikin al'kairi aii zai samu lada..      hakane kam Nurri amma aii zan nuna miki wani muhimmun abune.
    Ta ce, "to amma daka nuna min zan dawo ko?, yaďaga kafaďa tareda ďan ta6e baki babu damuwa yafaďa yana sauke numfashi da đan karfi.
   Mi'kewa tayi tana ďan zum6ura baki dan itafa an takura mata sotake ta kwanta.
   Cak ya ďauketa kuwa,, yaya plz ka ajiyeni zan tafi da 'kafata, a'a gimbiya na hutashsheki, ta maimaita sunan wai GIMBIYA!! yau kuma wani SABON AL'AMAREEN akazo dashi??.
    A ďakinsa ya direta saman gado, taďan zaro idanu dan ita tsoron gadon nan take, yazama tauraruwa mai wutsiya hawanshi ba alkairibane, tun randa akayimata shigo2 akansa take tsoronsa, ta zuro 'kafafunta da niyyar sauka amma sai ya Mahmud ya ri'keta ina zuwa kuma??.
    Sauka zanyi yaya kaida kace zaka nuna mini abu miye kuma na ďoranai a kan gado??, yaďan murmusa aii abunda zan nuna mikin a kan gadon yake, kangado kuma?, tafaďa tana yun'kurawa da Nufin tashi, da sauri ya ri'keta shima ya zauna tareda rungumeta Nurrina miyasa kike gudun mijinki kuma yayanki??, ta shagwa6e fuska yaya dan ALLAH kabarni naje nayi barci.
    Bakinta ya sumbata, nima aii barcin zanyi bayan nagama sunna kinga aii saimuyi tare ko?, inaso mugaisa da babynane, tabuďe baki zatayi magana ya haďe bakinsa danata, tuni tafara zille2 amma ina tazo hannu, nima lalla6owa nayi nafito dan karna wuce gona da iri.

Bayan lafawar komai tafara rera masa kuka, shikuma yashiga lallashi, dakansa yay mata wanka sanan ya rungume matarsa yana lallashi dan har yanzu kuka take, babu daďewa barci yay gaba da ita.
   Ya tsura mata idanu yana kallon 'kya'ky'kyawar fuskarta, Nurr rigima kenan, yasan duk mace mai yaron ciki abinson kowanne ďa namiji ce, amma yaufa Nurr ďin tasa ta 'kara rikitashi da sake tsundumashi a'kaunarta, niko ina zani da wanan shagwa6a taki, gakuma mai kwace miki fada yana zuwa, yafaďa yana murmushi tareda kai hannunsa kan cikinta, cikin a ďame kamar babu alamar ďa, ko sai yaushe zaiyi girma??, yanaso yaga tafara tafiyar nan tamasu ciki, lalai zuwa sanan sunga takansu,, dan Nurr dai 'kara shagwa6e musu zatayi, haka yayta tunane2n sa har barci ya kwasheshi.

Da asuba suna cikin yin sahur shida aunty bily saiga Nurr ta sakko daga saman ya mahmud, suka bita da kallo yayinda take 'karasowa wajensu, ya mahmud ya ce, "yadai Nurr??.
    Ta zauna kusada aunty bily, nazo nayi sahurne nima azumin zanyi, aunty bily ta ce, "azumi kuma Nirr kiyi ha'kuri ki 'kara samun sau'ki mana saikiyi.
    Na samu sau'ki aunty bily, ALLAH zan iya.
   Ya mahmud ya ce, "shikenan to mizakiyi sahur ďin dashi??, zansha shayima ya isa, da kansa ya haďa mata shayi maiďan kauri amma ba sosaiba, takar6a tanasha, Alhmdllh bai kuma sakata amaiba harsuka gama, suka koma ďaki ya mahmud yatafi masallaci.
   Nurr tana idar da sallah ta 6ingire akan sallayar barci yay gaba da ita.
    Ya mahmud bai dawoba saida gari yayi haske, ďakinsa yawuce ya 'karasa lazumi sanan yay shirin office, ďakin aunty bily yafara shiga yay mata sallama sanan yafito zuwa gun Nurr.
   Murmushi yayi dan ganinta kwance a 'kasa, ya ďauketa ya maida saman gado, ya gyara mata kwanciya sanan ya sumbaci kumatunta yafice.
      Sai wajen sha biyu ta tashi, agurguje tayi wanka ta shirya, itada tace zata gidan dady da sassafe amma itace har sha biyu tana barci, hijjab ta ďauka tasaka, gashi tana ďan ganin juwa anya kuwa wannan azumin zata iya kaishi??, cikin hanzari tafito daga ďaki, ALLAH kuwa ya taimaketa babu kowa afalo aunty bily tana ďaki tana barci, tafice da sauri.
    Saidai kash tana fita suna cin karo da ya Mahmud yana kulle mota, tayi tsaye tana kallonsa, 'karasowa yayi inda take jikinsa sanye da sut ba'ka'ke, ya sagala jakkar aikinsa a kafaďa, hannunsa ri'ke da leda ďayan kuma ri'ke da key ďin mota.
    Ina kuma zuwa da ranarnan??.
   Gidan dady mana.
   Tofa gidan dady kuma?, aida kin bari sai yamma yanzu ranar akwai zafi, ta turo baki nidai yanzu nakeson zuwa, key ďin yasaka aljihu kinga share kawai zomu koma anjima zan maidaki da kaina kamar yanda na ďakkoki.......yaja hanunta batareda yajira amsar bakintaba.............









Luv u oll my fan's
©2017
[11/03 13:46] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》









NA BILKEESA IBRAHEEM 
     {♡Bilyn Abdul♡}






46

..........yau kwanan deena biyu da haihuwa Nurr kuma batajeba dan an hanata, yaudai data dage da mita mama ta ce, "ta tambayi ya mahmud idan yazo, ta ce, to.
     Tunda wuri tayi wanka ta shirya cikin siket da riga na les, idan baka saniba saikace batada wani ciki, tana zaune abakin gado tana gyara 'kumbarta da jiran zuwan ya Mahmud.
    Babu daďewa kuwa saigashi, ta gaidashi, ya amsa yana zama hannunsa ri'ke da leda, ya ce, "ya jikinnaki?, nasamu sau'ki yaya tafaďa da 'karfin gwuywa dan abarta zuwa gidan deena..        ya ce, "masha ALLAH ai haka akeso, ya mi'ko mata ledar hannunsa ga ďata ďin dakikace kinaso, hannu tami'ka takar6a tana faďin yauwa yaya ngd kuwa, harta kai ďaya baki zata gutsira ya ce, "kinga tsaya madam tashi ki kaiwa su marka su wanke miki tukunna.
    Ta janye ďatar daga kusada bakinta, ni wlhy daka barni naci haka babu abinda zai sameni, eh nasani tashida kikai su wanke miki, mi'kewa tayi batareda ta tanka masaba tafice, mintuna kaďan saigata tadawo da ďatar afilet anwanketa fes.
    Ta zauna bakin gadon tana ci, yaya dan ALLAH zanje gidan deena naga babyna, a'a keda bakida lafiya kibari ki 'kara samun sau'ki sannan.
    Ta haďiye ďatar nidai nace maka na samu sau'ki yaufa kwananta biyu da haihuwa kowa yana zuwa ganin baby amma bandani, sai kowa yagama gani niban ganiba tafaďa cikin shagwa6a.
    Yanda tayi maganar ta burgeshi dan haka yataso yadawo kusada ita, rungumota yayi zuwa jikinsa, indai kinason zuwa gidan deena yau tofa da sharaďi..  
     Da sauri ta ce, "nayarda da sharaďinka,, huummyim komin wuyarsa Nurri??.
   "Eh wlhy yaya".
  Yaďan murmusa, to kije gidan deena amma zuwa anjima idan ALLAH yakaimu zakiga saka makon sharaďin nawa, aituni ta rungumeshi tana tsallen murna, ya ri'keta dankarta yimasa aika aika ana ďan lalla6a cikin ta 6arar masa, gashi kuma gefe tana shirin karya masa azumi.
   To kinga zauna hakanan yafaďa yana cirota daga jikinsa, irin wanan murna haka maryam aisaiki karyamin azumi.
   Ta yayibi hijjab tasaka babu wani karya axumi yaya, tafaďa tana shirin kama hanyar fita.
   Ya ce, "kinga zonan mana.
   Dawowa tayi kusadashi amma bata zaunaba, yakama hannunta ya zaunar da ita kusadashi, ai'kya bari natafi ko 'yammata, daga cewa ki tafi saiki kama hanya.
   To yaya mizan maka?, kabarni kawai natafi dan ALLAH, khairat ma tana can 'kila yanzu.
   Okey kice mitin kuka haďa nazuwa yau???.
    A'a wlhy jiya datazo tace mini yau zata can ta wuni, mi'kewa yayi yana faďin to shikenan adawo lafiya, muje tunda amota nake saina ajiyeki, to tafaďa tana ficewa, afalo sukayima su mami sallama, mama ta ce, "banda wautadai Nurr kinga ba cikakkiyar lafiya garekiba.
   Kai taďaga cikin zumuďi.
Suka fice tana musu bey bey kamar wadda zata wata anguwa daban.
    Mami tayi dariya kai kuruci dangin hauka, lallai za'aga masu 'ya'ya awajan nan, daga Nurr ďin har deena hankali bai wadacesuba.
   Mama ma tayi dariya aibakisan hankali bai wadacesuba sairanda Deena ta haihu, kai yaranan ALLAH dai ya gyara, amin mami tafaďa.
     
Acan kuwa ya mahmud yatafi da Nurr a mota tunda suka tafi babu wanda yayma wani magana, saida suka isa 'kofar gidan takama murfin motar zata fice, ya ce, "Nurri ko sallama babu??, lah yaya sonake na fita zance maka sai anjima aii, ya ďan murmusa dan ganin rawar kan datakeyi, tazagayo ta gefensa ta ce, "yaya sai anjima, yaďan lumshe idanu tareda kamo hannunta ya sumbata, to maman babyna sai anjima.
   Ta jinjina kai tana ďaga masa hannu dan batasan inda maganar tasa tadosaba, catake maman baby da deena ta haifa yake nufi, yabita da kallo harta shige cikin gidan, kamar bamai cikiba yafaďa azuciyarsa, yaďan lashe la66ansa gsky yana bu'katar kasancewa da Nurrinsa, dan yana kwaďayin sake ďan ďanar Ni'imominta, yaja ajiyar zuciya tareda tada motar yabar anguwar, dama da inda zaije.

Acan kuwa da gudu ta 'karasa cikin gidan, suka rungume juna da deena suna murna, saiga Khairat gaba ďaya suka kaure da ihu, (nace kai ALLAH ya shirya dai), suka ďauki baby sunata yaba 'kyawunsa, khairat ta ce, "oohni wai deenace da ďa lalai su deena anzama manyan mata.
   Deena ta harareta 'yar iska saura ke ya mustapha zamu bawa nanda wata shekarar mudawo suna koya kikace Nurr??.
    Wlhy kuwa gskyar ki 'yar uwa kai wlhy summafa dace.
   Khairat tayi far da ido, idanma bamu daceba nidama inason kayana kunyace kawai ta hanani furtawa.
   Ihu sukasa tareda tafawa, Nurr ta ce, "khairat da gsk dan ALLAH??, Wlhy da gsk nake 'yan uwana nadaďe inason ya Mustapha kawai dai ina tsoron furtawane dan karya'ki kar6ata amatsayin matarsa.
   Wlhy zai yarda khairat, babu abinda baki haďaba da namiji yadace yasoki, nasan kuma wlhy ya mustapha zai soki kuma kun dace ALLAH ya tabbatar mana da alkairi, kibar komai a hannunmu insha ALLAH saikin zama matar ya mustapha.
   ALLAH ya yarda khairat tafaďa cikin raunin murya.
   Daga nana suka cigaba da shan shargallensu agidan, deena ta ce, "Nurrin ya Mahmud ya babynmu??.
   Nurr ta harareta wane baby kuma?, wakuma yagaya miki wannan sunan??, deena da khairat suka tuntsire da dariya, randa aka kwantar dake a asibiti ya Mahmud mukaji yana faďa, Nurrii nice name!!! fa.
   Kudai sa'idonku yayi muku yawa, ni wlhy haushi yake bani idan ya ce, "wani Nurri ďinnan, jinake kamar na haďiye zuciya dan haushi.
   Khairat tayi mata kallon sama da 'kasa, 'yar rainin wayo bakiji haushin shigewa jikinsa kusha soyayyaba harda samo tsaraba, sai haushin dan yace miki Nurri??.
    Nurr ta ta6e baki, wlhy dan babu yanda zanyine kuma yafi 'karfina, sanan kuma tsarabar ubanmi muka samo??, dariya sosai suke tuntsura mata 
Harda hawaye, tuni tacika da haushi ta ce, "miye kuma na dariya........shigowar ya suraj yahanasu bata amsa, ya ce, "A'a 'yan uku kune agidan namu??, suka haďa baki wajen faďin eh, suka gaisheshi, ya amsa da fađin Nurr yajikin ki??.
   Da sau'ki yaya, ashe munsamu baby??, yayi murmushi aiko kunsamu baby, kuma kunzama iyaye.
   Suduka dariya sukayi, deena taje takama hannun ya Suraj suka nufi ďaki, tuni Nurr da khairat sun she'ke da dariya, ta6ara!! suka faďa atare suna ta6awa.
    Haka sukaita shan shagalinsu, har gidan yafara cika da dangi, zuwa 'karfe ďaya Nurr tashige ďakin deena ta kwanta bayan tayi sallar azhur, babu daďewa barci yay gaba da ita.
     Har yamma sunan, saida suka gyarama deena ko'ina afes sukayi musu abinci, koda yake duk khairat ce tayi aikin Nurr tana kwance, dan bakowane 'kamshin abinci takesoba, saida mama takirata ta ce, "ta taho gida hakanan.
   Humm batasan ya mahmud ne ya 'kulla mataba, tana zuwa kuwa ta iskeshi zaune abakin gadon mama yana shan kunun gyaďa, ta 'karaso ďakin jiki a sanyaye, mama dake zaune saman kujera ta ce, "yan yini sai yanzu??.
    Nurr ta zauna kusada ita eh wlhy mama, naje naga baby mai 'kyau kamar tabani, dariya mama tayi tareda shafa kan Nurr to ai shima wanan nakine, hakane mama aii anayin suna kullum sainaje na ďakkosa, mama ta ce, "to ALLAH yakaimu.
   Ya Mahmud yana zaune yana jinsu, azuciyarsa ya ce, "kema aii kinkusa ri'ke naki Nurrina.
   Mama ta mi'ke tana faďin ina zuwa bari naje na sha Ruwa, to mama Nurr tafaďa tana ďagata, mama na fita ya Mahmud ya hararai Nurr, maryam wai yaushe zaki iya gaisuwane??.
    Ta turo baki gaba kayi ha'kuri na shafa'a ne, kai ya girgiza yacigaba da shan kununsa, ya ce, "tun ďazu kina can sai yanzu kika dawo??, ta ďaga kai batareda tayi maganaba.
   Shima saiya shareta dan soyake ya lala6ata su tafi, yanzu yana takura mata zata rikice ta 6ata masa shiri, bayan dakyar ya shawo kan dady da mama, saidama mami ta taimaka masa sananan suka yarda yatafi da Nurr ďin.
    Bayan ya kammala ya ce, "tashi muje kirakani wani waje, taďan kalleshi yaya ina kuma zamuje da darennan?, kuma naga ko ruwa baka shaba.
   A'a nikam nasha ruwa bayanzu nagama shan kunu agabankiba, kinga tashi muje bily tana jiranmu.
   To bari na sanar da mama".
  Kinga bama sai kin sanar mataba nariga na sanar mata muje kawai.
  Kai kawai ta ďaga masa ta kama hanyar fita dama bata cire hijjab ďin iikintaba, afalo suka iske su ya mubarak suna shan ruwa, tayi musu barka da shanruwa kamar yanda ta saba.
   Ya mahmud yay musu sallama suka fice.
   Dakansa ya buďe mata mota tashiga ta zauna, shima yazagaya yashiga, gidansa yanufa itadai kallonsa take kawai ammafa tana shirin yin magana, gani tayi ya tsaya a kofar gate ďin da'alama bashiga zaiyiba saitaji daďi aranta.
   Ya ďauki waya yakira aunty bily, babu daďewa saigata tafito, ta buďe baya tashiga tana faďin sorry na 6ata muku lokaci.
   Ya mahmud ya ce, "no yanzu muma muka zo, Nurr ta ce, "auntyna ykk ya azumi?, lafiya lau Nurr ďin mama ya jiki?, na warke aunty.
   Ya mahmud yay dariya 'kyadai warke yarinya, aunty bily ta ce, "yaya abin 'yar tsokanace kuma??, ya murza sitiyarin motar ya hau babban titi, babu wani tsokana gsky ce aii.
   Itadai Nurr tana jinsa bata tanka musuba.
   Wani haďaďďen shagon ďinki sukaje, gsky shagon ya haďu, da sauri mai shagon yataresu bakinsa cike da murmushi, yabama ya mahmud hannu suka gaisa, sanan yanuna musu gurin zama tareda gaida su aunty bily suma.
   Nandai yay masa bayani akan ďinki yakeso, aka basu ďunkuna suka za6a sannan yabiya haďe dabashi kayan suka fito.

Tunda suka fito suke santin shagon ďinkin, amma tuni fuskar Nurr ta canja dan ganin ya mahmud ya wuce gidan dady yanufi gidansa kai tsaye.
   Yaya inakuma zaka kaini??, naga ka wuce gidan daddy.
   Baice komaiba illa hon dayayi mai gadi ya buďe masa gate.............








Luv u oll my fun's 
©2017
[11/03 19:50] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》







NA BILKEESA IBRAHEEM
   



48

........Koda suka shiga falon saiya kulle ya zare key ďin, ya ce, "bilkeesu fa tana ina??.
    Nurr ta turo baki idanunta cike da kwallah, ta ce, "tana ďaki tana barci.
  Uhhmeeyim shine zaki gudu bata saniba?, yafaďa yana jan hannunta har samansa, tanayi tana tirjewa ahaka sukaje ďakin, taja tunga afalo, yaďan kalleta yaya dai??, ta matso hawayen datake makalewa ni kabarni anan kaiwai.
   A'a kizo muje ki haďaminma ruwa nayi wanka ai'kya samu lada, nidai wlhy ban yardaba salon ka 'karamin abunjiya, dariya taso kufce masa amma saiya gimtse ya tsura mata idanu "k idan banda shirmenki kin ta6a ganin mai azumi yayi abinda kike tsoro, yasake jan hannunta ni babu abinda zan miki ruwan wanka kawai nake bu'kata, babu yanda zatayi dole tabishi, acanma ďakin yasakama key bayan tashiga bayi ta haďa masa ruwan wankan.
    Tafito tana goge hannu da tawul, ya tashi daga kwanciyar dayayi abakin gado, kallo ďaya tayi masa ta kauda kai gefe saboda guntun tawul ďin dake jikinsa, shimadai ratseta yayi yashige bayi batareda ya tanka mataba, yana shiga tanufi 'kofa da nufin guduwa amma saitaji gam, ta huro hanci tareda sauke numfashi da 'karfi wato kulleta yayi kenan yayi masa 'kyau aii.
   Ajikin 'kofar ta jingina tana sa'ka wasi'kar jakuna harya fito, yaďan kalleta lfy kika tsaya anan??, kanta a 'kasa ta ce, "key nake jira kabani natafi ďaki, yaďan ta6e baki yana cigaba da goge jikinsa da 'karamin tawul, nanma aii ďakine ba dajiba yafaďa yana zama akan kujerar dake gaban madubi, hidimar shafa mansa yacigaba dayi batareda yasake bi takantaba, itako sai hararsa take.
    Tazame ta zauna saboda azumin yafara kolata, duk abinda take yana kallonta ta madubi, yagama shafa mai yasaka 'kananun kaya, saman gado yakoma yazauna zoki kwanta kihutama rayuwarki.
   A'ina zan kwanta ďin??.
  Anan mana yanuna gado.
Kai ta girgiza tab ďi nice za'a 'kara zirawa na kwanta a wannan gadon?, ALLAH yakiyaye wlhy.
       Yayi murmushi tofa yau naga matar datake gudun ďakin mijinta, tasowa yayi yakamo hannunta, ta ma'kale hannun kamar zatayi kuka yaya plzz dan ALLAH kabarni natafi ďakina ALLAH banaso.
    Kinga kwantar da hankalinki tashi na rakaki ďaki, ta mi'ke da sauri aibama saika rakaniba kayi kwanciyarka sai anjima, murmushi yasaki yana buďe ďakin, kafin ya ankara tafice, shima take mata baya yayi, tana shiga yana shigowa ta kalleshi da sauri yaya miya faru kuma??.
    Sai wani abu yafaru miji ke shiga ďakin matarsa??.
   Shiru tayi tana cire hijjab, ya wuce saman gado ya kwanta, wani haushi ya turni'keta, wai wannan wane irin binbinine yake mata haka??, itafa wlhy bazata iyaba, taja 'karamin tsaki amma bai jiba, saman kujera ta kwanta itama.
    Saida aka kira sallah sanan yatashi yay alwala yafice, tabaya ya kulle 'kofar falon yafita.
     Nurr tana idar da sallah tayo waje danufin fita, tana shirin buďe 'kofa saiga aunty bily, A'a Nurr sai ina kuma??, aunty gidan dady zankoma mana, gidan daddy kuma Nurr? Ta ďaga kai, aunty bily ta girgiza kai....kafin tace wani abu ya Mahmud ya buďe 'kofar yashigo.
   Lfy naganku a tsaitsaye??.
    Wai Nurr ce zata tafi gidan dady, ya mahmud ya haďe rai kamar bashiba, ya watsama Nurr harara waike mike damunki??, kodan kinga ina lalla6akine??, to bazaki koma gidan dadyba, ga gidan mijinki nan dan haka idan zaki zauna ki zauna, banason nasakejin wanna maganar kuma, karkuma ki 'kara yun'kurin sake fita agidanan wlhy, ya buďe 'kofarma sanan yakoma saman doguwar kujera ya kwanta.
    Durkushewa Nurr tayi zata fara rera kuka, ya ce, "wlhy karnaji wani sautin kuka anan, kima tashi awajen.
   Yanda yake magana cikin faďa sai duk tsoro ya kamata, dan yakoma ya Mahmud ďinsa nada.
   Da sauri tami'ke ya nuna mata kujera oya zoki zauna anan, jiki na rawa tazo ta zauna(na ce, "Nurr kenan kedai lamarinki saida jan ido).

Haka rayuwar tacigaba da tafiya yauda gobe azumi yana tafiya yanda yakamata, Nurr ma tana 'ko'karin yi, amma idan tayi yau saita huta gobe, dahaka lokaci yacigaba da tafiya.
   An ďaga sunan deena sai bayan sallah.
   Cikin Nurr yanata girma, amma har yanzu batasan sirrinba, babu kuma wanda ya gaya mata, ya mahmud yana kula da ita shida aunty bily duk abinda takeso shine ake mata.
    haka kuma duk ranar girkinta tana iya bakin 'ko'karinta wajen yima ya Mahmud abinda yakamata, dukda aunty bily ta sauke mata shiga kichin dan bakomai takeson 'kamshinsaba,      a 6angaren ya mahmud ma duk dabarar dazaiyi ya kusanci Nurr ranar girkinta ya sani, cikin hikima yake lalla6ata yabiya bu'katarsa, saidaga baya taitayi masa kuka tana jin haushin kanta.
    Takan rasa miyasa take sakankancewa tabashi kantane?, saidai tana danganta hakan da shegen wayo irinna ya Mahmud, yanada wayo da iya salon soyayya iri iri, dolene duk mace data kasance a 'karkashin ya mahmud duk kiyayyarta dashi ta sakankance da shi ayayin dayake nuna mata soyayya.
    Mutumne dayasan hakkin soyayya dakuma yanda ake nunama mace, yakan mantar da ita kanta balle kuma kiyayya datake ikirarin tana masa, lokuta da dama sai komai ya lafa take farga da tuna kiyayyar datake masa, bansan yanda zan fassara muku malamin nawaba a 6angaren soyayya, saidai kawai nace muku ya kware matuka harma ina ganin babu wani namiji dake nunama matarsa irin wanan salon son, amma har yanzu ina kan bakana nason yasakeni nakoma makaranta harma nasamu wanda nakeso mu kasance a karkashin inuwa ďaya....
     Ya mahmud yajanye hannunta daga tagumin data rabga, taja ajiyar zuciya tareda ďago idanunta dasukayi ďanja tana kallonsa, durkusawa yayi agabanta ya kamo hannunta ya rumtse anasa, suka tsurama juna ido nawani lokaci, akasalance Nurr ta janye nata idanun dan ganin wani abu take yana fitowa daga idon ya mahmud yana shiga nata idon.
   Tayi 'kasa da kai tana hawaye, yayi ajiyar zuciya, yatsunsa biyu yasa ya ďago ha6arta, tayi 'kasa da idanunta, yaďan lumshe idanunsa cikin muryarsa mai daďi ya ce, "Nurrina miye damuwarki??, miyasa aduk lokacin dana kusanceki saikinyi kuka??, Nurr kodai baki sona har yanzu.
    Kai taďaga tana cigaba da hawaye?, ya ce, "baki sona ko?, cikin karsashi yayi maganar, ta 'kara ďaga kai, yacije la66ansa, muryarsa takoma kamar zaiyi kuka, miyasa baki sona Nurri??, miye laifina??.
    yanda yayi maganar kamar yana kuka yasa Nurr taďago tana kallonsa, kamar idanunsa da kwalla aciki saboda tana hangen 'kyallinsu, ta maida idonta 'kasa, ya murza hannunta dake ri'ke aďayan hannunsa, kiyi magana Maryam.
    Ta zubo da hawaye, ni basonka bane banayi, ina sonka amatsayin ďan uwana kuma yayana, amma bana maka so irin na aure, wani numfashi ya sauke da 'karfi tareda matse hannunta sosai har saida taji zafi taďan matse fuskarta, yami'ke daga tsugunnon dayayi agabanta, yakoma bakin gadon shima yazauna.
   Wani uban tagumi yayi, Nurr ta kalleshi saikuma taji yabata tausayi, inama bata faďa masa hakaba?, to amma gara data gaya masa gskyar ta aii, dan masu iya magana nacewa( idan zaka faďi faďi gaskiya komai takaja maka kabiya).
    Taďan ta6a hannunsa dayayi tagumi dashi, da sauri yajuyo yana kallonta saita kauda kai, cikin zafin nama yajawota jikinsa, ita tsoroma yabata, kwantar da ita yayi saman gadon yay mata bargo da 'kirjinsa, tuni ya haďe bakinta danasa, da zafi2 yake nuna mata zallar soyayyarsa yanda zata fahimci shi da gske yana 'kaunarta, tuni jikin Nurr yafara rawa, yanzufa yagama yi, amma yanzu zai 'kara itako tashiga uku yau, dama bata faďa masa kalmarnanba, kuka tafara yimasa amma ko ajikinsa, abinda yayi niyya shiyyake aikatawa, gaba ďaya idonsa arufe yake (nace humm sai da safenku).
     
AKWAI MATSALA.
    Sakamakon abinda ya mahmud yayma Nurr jiya ta tashi da zubar jini wanda yarikita ya Mahmud da aunty bily, Asibiti suka tafi cikin gaggawa.
   Tuni likitoci suka kar6eta, ya mahmud sai safa da marwa yake akofar ďakin da'aka shiga da Nurr, yana dana sanin abinda ya aikata mata.
  Shi miyysa ma ya aikata hakane??, miyasa bai 'kyaletaba?, tabbas ransane ya 6aci ayayin da Nurr tafurta kalmar bata sonsa, gashinan yanzu yajama kansa ďan cikin dasuke ďoki ya zube..........Dr Ashir ya ce, "sardauna ina son ganinka a office.
     Yanda Dr Ashir yayi maganar ta rikita ya Mahmud yasanma tafaru ta'kare kawai, wannan karonma yayi asarar babynsa.
   Jiki asanyaye ya zauna kujerar da Dr ya nuna masa.
   Dr Ashir yaďago yana kallonsa Sardauna akwai matsalafa......................

Kai masa karatu nimafa atsorace nake





Luv u oll my fan's
©2017
[12/03 14:37] bilyn Abdul: 《《SABON AL'AMAREE》》






NA BILKEESA IBRAHEEM 
    {♡Bilyn Abdul♡}









49

........cikin yanayin tausayi ya ce, "Dr wannan karonma narasa babyna ko??.
   Dr Ashir ya tsurama ya Mahmud idanu, ya cire biron dake bakinsa sannan ya nisa, hakane sardauna kaďan yahana wanan karonma murasa babyn, amma Alhmdllh munyi nasara bai zubeba sakamakon 'ko'karin saurin kawota dakukayi asibiti, kunyi farar dabara.
    Wata wawuyar ajiyar zuciya ya Mahmud yasaki, tareda faďin Alhmdllh.
   Dr yacigaba da faďin, saidai gsky Sardauna wannan karon kaine kajawo matsalar dan bincikena ya nuna kana yawan kusantar matarka.
   Dolefa saida kula, mace mai 'karamin ciki batason yawon tajura saboda samun matsala irin wanan, Alhaji wannan shine hikimar ajiye mata sama da ďaya, idan wannan tana da uzurin ta kaima saika sauke uzurinka acan, yakamata aďan barta ta huta plzz sardauna.
    Murmushi ya Mahmud yayi, karka damu Dr insha ALLAH za'a kula, yanzu ya jikinnata??.
  A Alhmdllh, munsami nasarar tsaida jinin yanzu hakama barci takeyi, ba'ason ayi mata hayaniya amma zuwa anjima ma insha ALLAH zamu sallameku.
   To Alhmdllh doctor ngd sosai da 'kokarinka akanmu, ALLAH yabar zuminci.
   Ameen sardauna karka damu ai munzama ďaya, sukayi musabaha ya mahmud yafita,    da sauri aunty bily ta tarbeshi yaya miya faru??, ya ri'ke hannunta Alhmdllh bily komai Normal ALLAH yasomu cikin bai zubeba.
   Alhmdllh aunty bily tafaďa tana ďaga hannu sama domin nuna godiyarta ga ALLAH sarkin sarakuna mai komai mai kowa.
   Ta ce, "yanzu sun kwantar damune??, A'a zuwa anjima ma zasu sallamemu insha ALLAH, yanzu sunce abarta ta huta basa son ayi mata hayaniyane.
  Okey babu damuwa ALLAH ya kiyaye gaba.
   Amin bilyna.

5:13pm 
    Sai 'karfe biyar da minti sha uku Nurr ta farka, normal tafarka dan jikinta Alhmdllh, idan baka sanibama babu wanda zaice wani abu yafaru da ita ďazu, shiyyasa babu wanda suka sanar mawa kosu mama basu saniba.
   Dr ya ce, "ya mahmud zai iya shiga, to ya amsa tareda tura 'kofar ďakin yashiga da sallama, ita aunty bily tatafi gida tun ďazu domin nema musu abin buďa baki.
   Nurr nazaune akan gado ta jingina da filo, amma ko motsi batayinba barema ta amsa masa sallamar, ya 'karasa gareta cike da farin ciki ya kamo hannunta ya rumtse anasa kai Alhmdllh Nurrina, naji daďin ganinki haka, yanzu yajikin naki??.
    Shiru tai masa dan jitake ta 'kara tsanarsa, ya ďago ha6arta da yatsunsa biyu, cikin sanyin murya ya ce, "haba Nurrina yanzu nan koma amsani baza'ayiba??, ta ďago ido suka kalli juna idonta cike da hawaye, ta matsosu suka zubo masu zafi ma kuwa, ďayan hannunsa yasa yana share mata, ya rungumeta sosai ajikinsa yana lallashi, ya isa haka kinsan banason kuka Nurri dan ALLAH kibar yin kukan kinji.
  Cikin muryar kuka ta ce, "nidai ka kaini wajen mama, ďagota yayi yana kallon fuskarta amma shi tasa fuskar taďan canja, yaďan kausasa muryarsa, haba Nurri yakamata kisan kin girma, kinga abinda yake haďani faďa dake, plzzz ki kwantar da hankalinki kamar kowacce mace dake gidan mijinta, kefa yanzu ba yarinya bace tunda har kina shirin zama uwa, bai kamata komi yafaruba kiringa saka rigimar tafiya gidan daddy, bakiga yanda madeena tayi zamanta lafiya agidan mijintaba hargashi sun haifi babynsu, tunda akayi bikinmu madeena bata ta6a zuwa gida daniyyar zamaba saidai tayi musu yini takoma gidanta, dan ALLAH kema inaso ki koma haka, ki kwantar da hankalinki ki zauna gidan mijinki kamar kowa, namiki al'kawarin zan zauna dake koda baki sona nikuma zan cigaba da sonki har karshen numfashin.
   Nurri 'kaunata dake musammance, tun kina ciki nake 'kaunarki, alokacin bansan k wace jinsi bace, macece ko Namiji??, nidai kawai inason abinda ke cikin momyne, ya share hawayenda suka zubo masa wanda Nurr batasan dalilinsuba, (nima danake gefe bansan dalilinsu ba), Nurri ALLAH yaji'kan momy kawai amma tabbas ta tafi tabar zuciyata da tabo na begenta amatsayin uwa nagartacciya agareni, plz ki kwantar da hankalinki kinji Nurrina, kwanciyar hankalinki zai ragemin raďaďin rashin momy arayuwata........yay shiru saboda hawayen dake cigaba da zirara adanunsa.
    Tuni itama Nurr kuka take, tasan momy yana nufin mamarta mahaifiya, gsky tanason 'karin bayani akan nahaifiyarta, tanaso adaina mata 6oye2 akan iyayenta, tanason afayyace mata komai game dasu dantasan matsayinta.......ta share hawayenta yaya dan ALLAH kasanar dani wani abu gameda iyayena mana.
    Hannu yasa ya karasa sharemata hawayen fuskarta, lokaci baiyiba maryam, kiyi hakuri lokaci zai nuna kansa dazakisan komai, nidai ki kwantar min da hankalinki yanzu, nayi miki al'kawarin sanar miki komai anan gaba insha ALLAH.
   Nurr ta jinjina kai kawai dan batada yanda zatayi....... shigowar doctor yasa Nurr zame jikinta daga na ya Mahmud, Dr Ashir yabashi hannu sukayi musabaha, Sardauna yanzu kuna free zaka iya ďaukar amarya ku koma gida ta huta, saidai dan ALLAH a kiyaye gaba.
   Babu damuwa Dr insha ALLAH haka bazata sake faruwaba mun gode sosai.
  Karka damu ALLAH ya 'kara lafiya.
   Ameen Dr ya mahmud yafaďa yana sauka.
    Har mota Dr Ashir yarakasu, saida yaga tafiyarsu sanan yadawo office, tunda sukatafi babu wanda yay magana, kowa ya lula duniyar tunani, kowa da abinda zuciya take sa'ka masa, dahaka suka isa gida, yay hon mutta'ka mai gadi yazo da gudu ya buďe.
   Saida yatsaya suka gaisa da maigadi, yayma Nurr sorry sanan yaja motar zuwa ciki, inda yadace yatsaya yakashe motar sanan suka fito, yakaraso inda Nurr take yana faďin zaki iya kokuwa na ďaukeki???.
   Kai ta girgiza masa, ahankali tace na hutashsheka zan iya da kaina.
   Okey yafaďa yana kama hannunta.
    Aunty bily tayi farinciki da dawowar Nurr, dandanan ta haďa mata abinci taci, sai kaffa kaffa ake da ita, wankama ya Mahmud ne yay mata da kansa dukda tanata wani no'ke2 saboda kunya, amma ya salle matarsa, ya shiryata cikin kaya marasa nauyi, tasha magani ta kwanta, shikuma yafito domin yin buďa baki.

Haka azumi yayta turawa har gashi yau saura kwana uku sallah, duk wani musulmi yana tanajin shirin bikin sallah acikin kwana uku ďinnan, yara kam sunfi kowa farincikin hakan.
    Yaune ya mahmud ya kar6o musu ďunkunansu, masha ALLAH komai yayi, ďunkunan sunyi 'kyau sosai abin sai wanda yagani, su Nurr sai daďi akeji dukda ita ba ma'abociyar son kaya dasuka danganci haka bane, amma a wanan karon tayi sha'awar saka wa kodan yanda ďinkin yazauna da 'kyau.
   Ya Mahmud ma yaji daďin yanda ta nuna farincikinta da ďinkin, burinsa kullum yaga Nurrinsa cikin farinciki da walwala, bayason damuwar yarinyar ko kaďan, washe gari yakwashesu sukaje sukayo shopping na sauran kayan kwalliya da takalma jakunkuna dadai sauransu.
    Balaifi Nurr taďan saki jikinta saidai abinda ke bata mamaki yanda cikinta kullum yake 'kara girma tarasa wanan dalili haka, yaudai ta ďauri aniyar gayama ya mahmud dan tana ganin kodai wani ciwone yashigeta basu saniba.

Yau takama daren sallah, bayan sungama shanruwa da rage wasu aiyukan na abincin gobe idan ALLAH yakaimu safiyar sallah, agajiye Nurr tashigo ďakinta, ya mahmud yana zaune bakin gadonta da tebir agabansa da takardu kekai saikuma laptop da alama yana yin wani aikine daya shafi office, ya amsa mata sallamar batareda ya kalletaba.
   Ta ce, "sannu da aiki.
   Yauwa kuma sannunku da naku aikin..  
   Lemo ta ajiye masa da kofi saikuma filet daya kunshi cincin da semosa da kek, ta 6alle murfin lemon ta tsiyaya a kofi, har yanzu hankalinsa yana kan danna laptop, ta mi'ka masa lemon yaya ga wannan kaďan sha mana, sai yanzu ya kalleta yauwa Nurrina ngd miki sosai ALLAH yay miki albarka.
   Amin tafaďa akan la66anta.
  Ya kur6i lemon tareda maida kansa ga laptop ďin.
   Nurr ta shiga bayi domin yin wanka, bayan wasu 'yan mintuna tafito, har yanzu ya mahmud yana aikinsane, tagama shirinta cikin kayan barci sanan tazo bakin gadon itama ta zauna amma ďan nesa dashi.
   Yaya ta ambata cikin sanyin murya.
   Na'am Nurrina ya amsa idonsa nakan aikinsa, ya akayine??, ta marairaice murya, yaya inaso ka kaini asibiti adubani, da sauri ya ďago yana kallonta bakida lafiyane??.
   Ta ce, "eh nidai kawai naga cikina yana 'kara girma shine abin yafara bani tsoro, kowani ciwone yakeson kamani bansaniba??( a ce, "hmm Nurr kenan sarkin shirita)............






Luv u oll my fan's
©2017
Share:

0 comments:

Post a Comment

Recent

Contact Form

Name

Email *

Message *